Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 7/1 pp. 3-5
  • Ta Yaya za a Magance Ƙiyayya Tsakanin Ƙabilu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya za a Magance Ƙiyayya Tsakanin Ƙabilu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zalunci da Ƙiyayya
  • Menene Ya Jawo Haka?
  • Sanin Allah Zai Sa Ƙabilu Su Jitu
  • Allah Yana Kula da Dukan Al’ummai
  • Yesu Ya Koya wa Mutane Alheri
  • Sanin Allah Yana Canja Mutane Kuwa?
  • Kana Ɗaukan Mutane Yadda Jehobah Ya Ɗauke su?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Yi Koyi Da Jehovah, Allahnmu Da Ba Ya Tara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 7/1 pp. 3-5

Ta Yaya za a Magance Ƙiyayya Tsakanin Ƙabilu?

A ƘASAR Spain wani alƙalin wasa ya dakatar da wasan ƙwallon da ake yi. Me ya sa? Saboda ’yan kallo da yawa suna zagin wani ɗan wasa ɗan Kamaru, har ya yi barazanar barin filin wasan. A ƙasar Rasha, harin da ake kai wa ’yan Afirka, Asiya, da kuma Amirka ta Kudu ya zama gama-gari, a shekara ta 2004, harin da ake kai wa ƙabilu a wannan ƙasar ya ƙaru daga kashi 55 zuwa 394 a shekara ta 2005. A wata tambayar da aka yi wa mutanen Asiya da kuma baƙaƙen fata da ke zaune a Britaniya, kashi uku sun ce sun rasa aikinsu ne domin wariya. Waɗannan misalan sun nuna abubuwan da ke faruwa a dukan duniya.

Ƙiyayya tsakanin ƙabilu ta bambanta sosai, wasu suna somawa ne da zagi ko baƙar magana da kuma ƙoƙarin kafa doka a ƙasa don a halaka wata ƙabila. Menene ainihin tushen ƙiyayyar da ke tsakanin ƙabilu? Ta yaya za mu guje ta? Ya dace a yi begen cewa wata rana dukan mutane za su zauna lafiya? Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin haske a kan waɗannan batutuwan.

Zalunci da Ƙiyayya

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.” (Farawa 8:21) Hakika, wasu suna jin daɗin zaluntar mutane. Littafi Mai Tsarki ya daɗa cewa: “Duba, ga hawayen waɗannan da a ke zalumtassu, ba su da mai-taimako; a wajen masu-zalumtassu kuma ga iko.”—Mai-Wa’azi 4:1.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ƙiyayya tsakanin ƙabilu ta daɗe tana faruwa. Alal misali, a ƙarni na 18 Kafin Zamaninmu, Fir’auna na ƙasar Masar ya ce Yakubu da duka iyalansa su zo su zauna a Masar. Daga baya, wani Fir’auna ya razana saboda waɗannan baƙin haure suna ta ƙara yawa. Sakamakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kuwa ce da mutanensa, Ga mutanen nan ’ya’yan Isra’ila sun yi mana yawa, sun fi ƙarfinmu kuma: mu zo, mu zauna da su da azanci; kada su riɓanɓanyu . . . Suka sanya shugabanni na gandu a bisansu fa, waɗanda za su wulakanta su da nawayyansu.” (Fitowa 1:9-11) Masarawa suka ba da umurni cewa a kashe dukan jarirai maza na zuriyar Yakubu.—Fitowa 1:15, 16.

Menene Ya Jawo Haka?

Addinai na duniya ba sa hana ƙiyayya tsakanin ƙabilu. Da gaske ne waɗansu mutane sun ƙi jinin zalunci, amma addinai gaba ɗaya suna goyon bayan waɗanda suke zaluntar mutane. Abin da ya faru a Amirka ke nan, sa’ad da aka kafa wata dokar da ta amince a yi amfani da baƙaƙen mutane wajen bauta, a kashe su ba tare da an yi musu shari’a ba, kuma a hana su su auri fararen fata kafin aka daina hakan a shekara ta 1967. Hakan ya sake faruwa a Afirka ta Kudu a lokacin wariyar launin fata, sa’ad da wata ƙabila da ba ta da yawa ta kāre matsayinta mai muhimmanci ta wajen kafa dokokin da suka haɗa da hana auren wata ƙabila. Sau da yawa, waɗansu mutanen da suke cikin ƙabilar da take goyon bayan ƙiyayya, mutane ne masu ibada sosai.

Amma, Littafi Mai Tsarki ya ba da cikakken dalilin da ya sa ƙabilu suke ƙin juna. Ya bayyana dalilin da ya sa waɗansu ƙabilu suke zaluntar wasu. Ya ce: “Wanda ba ya yin ƙauna ba, ba ya san Allah ba; gama Allah ƙauna ne. Idan wani ya ce, Ina ƙaunar Allah, shi kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne shi: domin wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yohanna 4:8, 20) Wannan furcin ya nuna ainihin dalilin da ya sa ƙabilu suke ƙin juna. Mutane suna ƙin juna ne ko da suna da’awar cewa suna yin ibada sosai ko a’a, saboda ba su san Allah ba kuma ba sa ƙaunarsa.

Sanin Allah Zai Sa Ƙabilu Su Jitu

Ta yaya ne sanin Allah da kuma ƙaunarsa za su sa ƙabilu su jitu? Wane sani ne Kalmar Allah ta bayyana da ya hana mutane zaluntar waɗanda suke ganin sun bambanta da su? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne Uban dukan mutane. Ya ce: “Amma a garemu akwai Allah ɗaya, Uba ne, wanda dukan kome daga wurinsa ya ke.” (1 Korinthiyawa 8:6) Ya kuma ce: “Daga tushe ɗaya kuwa ya yi dukan al’umman mutane.” (Ayukan Manzanni 17:26) Hakika, dukan mutane ’yan’uwa ne.

Dukan ƙabilu suna iya yin alfahari domin rai da Allah ya ba su, amma dukansu suna da wani abu da zai sa su yi baƙin ciki game da kakaninsu. Manzo Bulus marubucin Littafi Mai Tsarki, ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya.” Hakika, “dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3:23; 5:12) Jehobah, Allah ne mai son abubuwa dabam dabam, shi ya sa babu abubuwa biyu da aka halitta da suke da kama ta kowace hanya. Saboda haka, babu ƙabilar da take da dalilin nuna cewa ta fi wasu. Nuna cewa ƙabilarmu ta fi ta wasu bai jitu da abin da ke cikin Nassosi ba. Hakika, ilimin da muka samu daga Allah yana ƙarfafa jituwa tsakanin ƙabilu.

Allah Yana Kula da Dukan Al’ummai

Waɗansu suna tunanin ko Allah yana nuna bambanci tsakanin ƙabilu shi ya sa ya kula da Isra’ilawa kuma ya koya musu su ware kansu daga sauran al’ummai. (Fitowa 34:12) Akwai lokacin da Allah ya zaɓi al’ummar Isra’ila ta zama mallakarsa ta musamman saboda fitacciyar bangaskiyar kakansu Ibrahim. Allah da kansa ya shugabanci Isra’ila ta dā, ya zaɓar musu waɗanda za su shugabance su kuma ya ba su tsarin dokoki. A lokacin da Isra’ila ta amince da wannan shirin, sauran mutanen sun ga bambancin da ke tsakanin sarautar Allah da ta mutane. Jehobah kuma ya koya wa Isra’ila cewa tana bukatar fansa domin hakan zai sa mutane su sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah. Saboda haka, dangantakar Jehobah da Isra’ila ta albarkaci dukan al’ummai. Hakan ya yi daidai da abin da ya ce wa Ibrahim: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.”—Farawa 22:18.

Ƙari ga haka, Yahudawa sun sami gatar fara sanin zantattukan Allah kuma cikin al’ummarsu ce aka haifi Almasihu. Amma an yi haka ne don dukan al’ummai su amfana. Nassosin Ibraniyawa da aka ba Yahudawa sun ƙunshi kwatanci mai kyau na lokacin da dukan ƙabilu za su sami albarka mai girma: “Al’ummai dayawa za su hau, su ce, Ku zo mu hau zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub; za ya koya mana tafarkunsa . . . Al’umma ba za ta zare ma al’umma takobi ba, ba kuwa za su ƙara koya yaƙi ba. Amma kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratadda su.”—Mikah 4:2-4.

Ko da yake Yesu Kristi da kansa ya yi wa Yahudawa wa’azi, ya kuma ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.” (Matta 24:14) Babu al’ummar da ba za ta ji bisharar ba. Jehobah ya kafa misali mai kyau ta wajen ƙin nuna bambanci a yadda yake bi da dukan ƙabilu. “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.”—Ayukan Manzanni 10:34, 35.

Dokokin da Allah ya ba al’ummar Isra’ila ta dā sun nuna cewa yana kula da dukan al’ummai. Ka yi la’akari da yadda dokar ta bukaci fiye da amincewa da baƙin da suke zaune a ƙasar Isra’ila, sa’ad da ta ce: ‘Baƙon da ke sabke a wurinku za ya zama maku kamar ɗan da aka haifa a wurinku, za ka ƙaunace shi kamar kanka: gama ku dā baƙi ne cikin ƙasar Masar.’ (Leviticus 19:34) Yawancin dokokin Allah sun koya wa Isra’ilawa su bi da baƙin haure yadda ya kamata. Shi ya sa, da kakan Yesu, Boaz ya ga wata mata baƙuwa tana kala a gonarsa, ya aikata abin da ya koya daga Allah ta wajen tabbatar da cewa masu yi masa girbi sun bar mata hatsi mai yawa don ta samu na kala.—Ruth 2:1, 10, 16.

Yesu Ya Koya wa Mutane Alheri

Yesu ya bayyana sanin Allah fiye da kowa. Ya nuna wa mabiyansa yadda za su yi alheri ga mutane dabam dabam. Akwai lokacin da ya soma tattaunawa da wata mata Basamariya. Samariyawa ƙabila ce da Yahudawa suka ƙi jininsu, shi ya sa matar take mamaki. Sa’ad da yake magana da ita Yesu ya taimaki matar ta fahimci yadda za ta sami rai madawwami.—Yohanna 4:7-14.

Yesu kuma ya koya mana yadda za mu bi da mutanen da ƙabilarmu ba ɗaya ba sa’ad da ya ba da labarin wani Basamariye mai kirki. Wannan mutumin ya haɗu da wani Bayahude kwance a kan hanya wanda ɓarayi suka ji ma rauni sosai. Basamariyen yana iya cewa: ‘Me ya sa zan taimaki Bayahude? Yahudawa sun ƙi jinin ƙabilata.’ Amma Yesu ya nuna cewa Basamariyen yana da ra’ayi dabam game da baƙi. Ko da yake wasu matafiya sun wuce mutumin nan da ke kwance, Basamariyen “ya yi juyayi” kuma ya taimaka masa sosai. Yesu ya kammala labarin yana cewa, duk wanda yake son Allah ya nuna masa tagomashi shi ma yana bukatar ya nuna ma wasu.—Luka 10:30-37.

Manzo Bulus ya koya wa waɗanda suke son su faranta wa Allah rai su canja halinsu kuma su yi koyi da yadda Allah yake bi da mutane. Bulus ya rubuta: ‘Ku tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa, ku yafa kuma sabon mutum, wanda a ke sabonta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa: inda ba shi yiwuwa a ce da Ba-helleni da Ba-yahudi, da kaciya da rashin kaciya, da baubawa, Sikithiyu . . . Gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.’—Kolossiyawa 3:9-14.

Sanin Allah Yana Canja Mutane Kuwa?

Sanin Jehobah Allah yana canja yadda mutane suke bi da wasu da suka fito daga wata ƙabila dabam kuwa? Ka yi la’akari da labarin wata baƙuwar haure ’yar Asiya da take zaune a ƙasar Kanada wadda ta yi baƙin ciki sa’ad da aka nuna mata bambanci. Ta sadu da Shaidun Jehobah kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Daga baya, ta rubuta musu wasiƙar godiya, inda ta ce: ‘Ku fararen mutane ne masu kirki. Sa’ad da na fahimci cewa kun bambanta da sauran fararen mutane, na yi mamakin abin da ya sa. Na yi tunani sosai, sai na kammala cewa ku Shaidun Allah ne. Littafi Mai Tsarki na taimakawa sosai. A taronku na ga fararen mutane da baƙaƙe, waɗanda zuciyarsu ɗaya ce, wato, zuciyarsu fara ce sal, saboda su ’yan’uwa ne maza da mata. Yanzu na san wanda ya sa suka zama haka. Allahnku ne.’

Kalmar Allah ta faɗi lokacin da “duniya za ta cika da sanin Ubangiji.” (Ishaya 11:9) A yanzu, a cikar wannan annabcin na Littafi Mai Tsarki, bauta ta gaskiya tana haɗa kan miliyoyin taro mai girma da suka fito “daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) Suna jiran lokacin da ƙauna za ta sauya ƙiyayya a dukan duniyar da za ta cika nufin Jehobah ga Ibrahim: “Dukan kabilan duniya za su albarkatu.”—Ayukan Manzanni 3:25.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba