Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Ezekiel Na Ɗaya
A SHEKARA ta 613 K.Z. Annabi Irmiya yana Yahuda, yana yin shelar halakar Urushalima da kuma Yahuda babu tsoro. Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya riga ya kai Yahudawa da yawa bauta. A cikinsu har da matashi Daniyel da abokansa guda uku, waɗanda suke hidima a fadar Kaldiya. Yawancin Yahudawan da aka kai bauta suna bakin kogin Chebar a “ƙasar Chaldiyawa.” (Ezekiel 1:1-3) Jehobah ya yi wa waɗanda suke bauta tanadin manzo. Ya naɗa Ezekiel ɗan shekara 30 ya zama annabi.
Littafin Ezekiel da aka kammala a shekara ta 591 K.Z., ya ɗauki tsawon shekaru 22. Ezekiel ya mai da hankali sosai a rubutunsa. Ya rubuta kwanan watan da ya rubuta annabce-annabcensa, ya ambata ranar, watan da kuma shekarar. A saƙonsa na farko, Ezekiel ya mai da hankali ne ga yadda za a halaka Urushalima. Na biyun kuma yana ɗauke ne da hukunci bisa al’ummai da suke kewaye da su, na ƙarshen kuma yana ɗauke ne da yadda za a maido da bautar Jehobah. Wannan talifin zai tattauna darussa daga Ezekiel 1:1–24:27, da ke ɗauke da wahayi, annabce-annabce, da kuma kwatancin abin da zai sami Urushalima.
“NA MAISHE KA MAI-TSARO”
(Ezekiel 1:1–19:14)
Bayan an nuna masa wahayi mai ban mamaki game da kursiyin Jehobah, an gaya wa Ezekiel aikin da zai yi. Jehobah ya ce masa: ‘Na maishe ka mai-tsaro ga gidan Isra’ila: domin wannan sai ka ji maganar bakina, ka yi musu faɗaka daga gareni.’ (Ezekiel 3:17) Don ya annabta harin da za a kai wa Urushalima da kuma sakamakonsa, an umurci Ezekiel ya kwatanta abin da zai faru sau biyu. Game da ƙasar Yahuda, Jehobah ya ce ta wurin Ezekiel: “Ni ne, ni zan jawo maku takobi, zan hallaka masujadai naku.” (Ezekiel 6:3) Ga mazauna ƙasar, ya ce: ‘Ƙadararku [ta bala’i] ta abko muku.’—Ezekiel 7:7.
A shekara ta 612 K.Z., Ezekiel ya ga kansa a Urushalima a cikin wahayi. Ya ga abubuwan ƙyama suna faruwa a haikalin Allah. Waɗanda suka karɓi ‘shaida a goshinsu’ ne kawai za su tsira sa’ad da Jehobah ya aiki mala’ikunsa waɗanda (“mutum shida” suke wakilta) don ya nuna fushinsa ga ’yan ridda. (Ezekiel 9:2-6) Da farko, dole ne a zuba “garwashin wuta” a kan birnin, wato, saƙon halaka daga Allah. (Ezekiel 10:2) Ko da yake ‘Jehobah zai komo da alhakin al’amuran miyagu a bisa kansu,’ ya yi alkawarin cewa zai tattara ’yan Isra’ila da suka watse.—Ezekiel 11:17-21.
Ruhun Allah ya mai da Ezekiel ƙasar Kaldiya. Wahayin ya kwatanta yadda Sarki Zedekiya da mutanensa suka gudu daga Urushalima. An yi Allah-wadai da annabawan ƙarya maza da mata. An ƙi masu bauta wa gumaka. An kwatanta Yahuda da lalatacciyar inabi. Wasan ka-cici-ka-cici na gaggafa da inabi ya nuna mugun sakamakon taimakon da Urushalima ta nema wurin Masar. Ka-cici-ka-cicin ya kammala da alkawarin cewa ‘Jehobah zai dasa reshe mai taushi bisa wani dutse mai-tsawo.’ (Ezekiel 17:22) A Yahuda kuwa, ba za a sami “kandirin mulki” ba.—Ezekiel 19:14.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:4-28—Mecece karusa na samaniya take wakilta? Karusar tana wakiltar sashen ƙungiyar Jehobah ta sama wadda ta ƙunshi halittun ruhu masu aminci. Ruhu mai tsarki na Jehobah ne tushen ikonta. Mahayin karusar, wanda yake wakiltar Jehobah, yana da ɗaukaka marar iyaka. An kwatanta natsuwarsa da bakan gizo.
1:5-11—Su wanene masu rai huɗu? A wahayinsa na biyu game da karusa, Ezekiel ya nuna cewa kerubobi ne masu rai huɗun. (Ezekiel 10:1-11; 11:22) A wannan kwatancin, ya ce fuskar bijimi shi ne ‘fuskar kerubim.’ (Ezekiel 10:14) Hakan ya dace domin bijimi alama ne na ƙarfi, kuma kerubobi halittun ruhu ne masu ƙarfi.
2:6—Me ya sa aka yi ta kiran Ezekiel “Ɗan mutum”? Jehobah ya kira Ezekiel haka ne saboda ya tuna wa annabin cewa shi ɗan adam ne, da haka, ya nuna bambancin da ke tsakanin mutum mai idar da saƙo da kuma Allah wanda shi ne ainihin Mai saƙon. An kira Yesu Kristi da wannan sunan kusan sau 80 a cikin Linjila, kuma hakan ya nuna cewa Ɗan Allah ya zo ne da fasalin mutum ba a fasalin ruhu ba.
2:9–3:3—Me ya sa littafin baƙin ciki da na makoki suka yi wa Ezekiel zaƙi a baki? Abin da ya sa littafin ya yi wa Ezekiel zaƙi shi ne saboda yadda ya ɗauki aikinsa. Ezekiel ya yi farin cikin bauta wa Jehobah a matsayinsa na annabi.
4:1-17—Da gaske ne Ezekiel ya kwatanta abin da zai faru da Urushalima? Roƙon da Ezekiel ya yi na a canja masa itacen dahuwa da kuma yadda Jehobah ya amsa roƙonsa ya nuna cewa annabin ya kwatanta abin da zai faru. Kwantawa ta gefen hagu na nufin shekaru 390 na zunubin masarauta ta ƙabilu goma, wanda ya soma daga shekara ta 997 K.Z., zuwa lokacin da aka halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z. Zai kwanta ta gefen dama ne domin zunubin Yahuda na shekaru 40, wanda ya soma daga lokacin da aka naɗa Irmiya ya zama annabi a shekara ta 647 K.Z. zuwa 607 K.Z. Ezekiel yana samun abinci kaɗan ne kawai da ruwan sha a waɗannan kwanaki 430, a annabce hakan ya nuna cewa za a yi rashin abinci a lokacin da aka kai wa Urushalima hari.
5:1-3—Menene muhimmancin abin da aka ce Ezekiel ya yi, wato ya ɗauki wasu gashin kai daga cikin waɗanda ya kamata ya watsa a iska ya ƙunsa su a cikin rigarsa? Wannan ya nuna cewa waɗanda suka rage za su koma Yahuda su kafa bauta ta gaskiya bayan shekaru 70 da zama kango.—Ezekiel 11:17-20.
17:1-24—Su wanene babban gaggafa guda biyu, ta yaya ne aka cire kananan itacen al’ul wato cedar, kuma wanene ‘mai-taushi’ da Jehobah zai dasa? Gaggafa guda biyu suna wakiltar sarakunan Babila da Masar. Gaggafa ta farko ta zo saman itacen al’ul, wato ta zo wurin mai yin sarauta a zuriyar Dauda. Wannan gaggafar ta fige saman ’yan ƙananan itacen al’ul sa’ad da ta ɗora Zedekiya a maƙamin Jehoiachin Sarkin Yahuda. Duk da rantsuwar da ya yi cewa zai yi biyayya, Zedekiya ya nemi taimakon wata gaggafa, wato sarkin Masar, amma bai yi nasara ba. Za a kai shi bauta a Babila kuma ya mutu a can. Jehobah ya fige ‘mai-taushi,’ wato Sarki Almasihu. An dasa wannan a bisa “wani dutse mai-tsawo,” a bisa Dutsen Sihiyona ta samaniya, inda zai zama ‘kyakkyawan al’ul,’ wato tushen albarka ga duniya.—Ru’ya ta Yohanna 14:1.
Darussa Dominmu:
2:6-8; 3:8, 9, 18-21. Kada mu ji tsoron miyagu mu ƙi shelar saƙon Allah, da ya ƙunshi yi musu gargaɗi. Idan muna fuskantar hamayya, ya kamata mu kasance da ƙwari kamar lu’u-lu’u. Duk da haka, ya kamata mu mai da hankali kada mu zama marasa tausayi ko marasa jinƙai. Yesu ya ji tausayin mutanen da yake yi wa wa’azi, saboda haka ya kamata mu ji tausayin waɗanda muke yi wa wa’azi.—Matta 9:36.
3:15. Bayan ya karɓi aikin da aka ba shi, Ezekiel ya zauna a Tel-abib har ‘kwanaki bakwai,’ yana yin bimbinin saƙon da zai sanar. Ya kamata mu sami lokacin yin nazari sosai kuma mu yi bimbini don mu fahimci gaskiya ta ruhaniya.
4:1–5:4. Ezekiel yana da tawali’u da gaba gaɗi shi ya sa ya nuna kwatanci biyu na annabci. Dole ne mu kasance masu tawali’u da gaba gaɗi don mu yi aikin da Allah ya ba mu.
7:4, 9; 8:18; 9:5, 10. Bai kamata mu ji tausayin waɗanda Jehobah ya yi wa hukunci mai tsanani ba.
7:19. Sa’ad da Jehobah zai hukunta wannan zamanin, kuɗi ba zai yi amfani ba.
8:5-18. Ridda tana lalata dangantakar mutum da Allah. “Da bakinsa marar-ibada ya kan hallaka maƙwabcinsa.” (Misalai 11:9) Zai dace mu guji yin tunanin saurarar ’yan ridda.
9:3-6. Samun shaida, wato alamar da ke nuna cewa mu bayin Allah ne da mun riga mun keɓe kanmu, da muka yi baftisma kuma muna da halin Kirista, yana da muhimmanci idan muna son mu tsira a lokacin “ƙunci mai-girma.” (Matta 24:21) Shafaffun Kiristocin da suke wakiltar mutumin da yake da ƙaho na ajiyar tawada, suna ja-gorar aikin sa shaida, wato aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. Idan muna son mu riƙe shaidarmu, dole ne mu taimake su a wannan aikin.
12:26-28. Har ma ga waɗanda suke yi masa ba’a, Ezekiel zai ce: ‘Ba za a ƙara jinkirtadda maganar Jehobah ba ko ɗaya.’ Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaki mutane su dogara ga Jehobah kafin ya kawo ƙarshen wannan zamanin.
14:12-23. Hakkinmu ne mu samu ceto. Babu wanda zai iya yi mana.—Romawa 14:12.
18:1-29. Mu ke da hakkin sakamakon da muka samu na abin da muka yi.
“HALAKA, HALAKA, ZAN HALLAKAR”
(Ezekiel 20:1–24:27)
A shekara ta 611 K.Z., wato shekaru bakwai da zuwa bauta, dattawan Isra’ila sun zo wurin Ezekiel domin su ‘nemi shawara daga Ubangiji.’ Sun saurari tarihin tawayen da Isra’ila ta yi da kuma gargaɗin cewa ‘Jehobah zai zare takobinsa’ domin su. (Ezekiel 20:1; 21:3) Sa’ad da yake yi wa Zedekiya shugaban Isra’ilawa magana, Jehobah ya ce: “Ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma. Halaka, halaka, zan halakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”—Ezekiel 21:26, 27; LMT.
An ɗora wa Urushalima laifin yin abubuwa marasa kyau. An fallasa laifin da Oholah, wato, (Isra’ila) da Oholibah, wato, (Yahuda) suka yi. An miƙa Oholah ga “hannun masoyanta, hannun Assuriyawa.” (Ezekiel 23:9) Halakar Oholibah ta kusa. A shekara ta 609 K.Z., an fara kawo wa Urushalima hari na watanni 18. A lokacin da aka halaka birnin, Yahudawan za su cika da mamaki sosai har su kasa nuna baƙin cikinsu. Ezekiel ba zai sanar da saƙon Allah ga waɗanda suke zaman bauta a Babila ba, har sai ya ji labarin cewa an halaka birnin daga wurin “wanda ya tsira.”—Ezekiel 24:26, 27.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
21:3—Menene ‘takobin’ da Jehobah ya zare daga gidansa? ‘Takobin’ da Jehobah ya yi amfani da shi a wurin halaka Urushalima da Yahuda yana nufin Sarkin Babila Nebuchadnezzar da sojojinsa. Ya kuma ƙunshi sashen ƙungiyar Allah ta samaniya wadda ta haɗa da halittu na ruhu masu girma.
24:6-14—Mecece tsatsar da ke cikin tukunya take wakilta? A lokacin da aka kai mata hari, an kwatanta Urushalima da tukunyar dahuwa wadda bakinta ke da faɗi. Tsatsanta tana wakiltar yanayin birnin kamar su ƙazanta, lalata, da kuma zub da jini da ta yi. Ƙazantarta tana da yawa sosai shi ya sa duk da yadda aka ɗora tukunyar kan wuta kuma ta yi zafi sosai hakan bai cire tsatsan ba.
Darussa Domin Mu:
20:1, 49. Abin da dattawan Isra’ila suka ce ya nuna cewa suna shakkar abin da Ezekiel ya faɗa. Kada mu taɓa yin shakkar umurnin Allah.
21:18-22. Ko da yake Nebuchadnezzar yana yin duba, Jehobah ne ya tabbata cewa wannan sarkin da ba ya bauta wa Jehobah zai shiga Urushalima. Hakan ya nuna cewa aljanu ba za su iya hana wanda Jehobah zai yi amfani da shi don ya cika nufinsa ba.
22:6-16. Jehobah ya ƙi jinin tsegumi, lalata, nuna iko, da kuma cin hanci. Muna bukatar mu kasance da gaba gaɗi a ƙudurinmu na guje wa irin waɗannan mugayen halaye.
23:5-49. Yin ƙawance na siyasa ya sa Isra’ila da Yahuda su soma yin bautar ƙarya da ƙawayensu suke yi. Mu guji ƙulla dangantaka ta duniya da za ta rushe bangaskiyarmu.—Yaƙub 4:4.
Saƙon da ke Raye da Kuma Iko
Mun koyi darussa masu kyau a surori 24 na farko a littafin Ezekiel na Littafi Mai Tsarki. Ƙa’idodin da aka nanata sun nuna abubuwan da suke ɓata wa Allah rai, yadda za mu samu jinƙansa da kuma abin da ya sa ya kamata mu yi wa miyagu gargaɗi. Annabcin halakar da Urushalima ya nuna cewa Jehobah Allah ne da yake ‘bayyana wa mutanensa sababbin al’amura tun ba su ɓullo ba’—Ishaya 42:9.
Irin waɗannan annabce-annabcen da aka rubuta a Ezekiel 17:22-24 da kuma 21:26, 27 suna nuni ga ƙafa Mulkin Almasihu a sama. Ba da daɗewa ba, wannan mulkin zai sa nufin Allah ya tabbata a duniya. (Matta 6:9, 10) Da cikakkiyar bangaskiya da tabbaci, za mu iya yin begen albarkatu na Mulkin. Hakika, “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—Ibraniyawa 4:12.