Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Ezekiel na Biyu
A WATAN Disamba ta shekara ta 609 K.Z. Sarkin Babila ya soma kai wa Urushalima hari na ƙarshe. Har ila, saƙon Ezekiel zuwa ga masu zaman bauta a Babila yana magana ne a kan jigo guda, wato faɗuwa da halakar ƙaunataccen birninsu Urushalima. Amma yanzu jigon annabce-annabcen Ezekiel ya canja zuwa halakar al’ummai arna da suke farin ciki domin masifar da ta faɗa wa mutanen Allah. Sa’ad da Urushalima ta faɗi watanni 18 daga baya, jigon saƙon Ezekiel ya canja zuwa: maido da bauta ta gaskiya mai ɗaukaka.
Ezekiel 25:1–48:35 suna ɗauke da annabce-annabce game da al’ummai da suka kewaye Isra’ila da kuma ceton mutanen Allah.a Ban da Ezekiel 29:17-20, an ba da sauran labaran bisa lokacin da suka faru da kuma kwanan watan. Ba a rubuta waɗannan ayoyi huɗu bisa lokacin da suka faru ba. Tun da yake yana cikin Nassosin da aka hure, saƙon littafin Ezekiel “mai-rai ce, mai-aikatawa” kuma.—Ibraniyawa 4:12.
‘WANNAN ƘASA ZA TA KOMA KAMAR GONAR EDEN’
(Ezekiel 25:1–39:29)
Da ya hangi yadda za su aikata ga halakar Urushalima, Jehobah ya sa Ezekiel ya yi annabci a kan Ammon, Mowab, Edom, Filistiya, Tyre, da Sidon. Za a ci ganimar Masar. An kamanta ‘Fir’auna, sarkin Masar, da taron jama’arsa’ da itacen al’ul, wato cedar da za a sare da “takobin sarkin Babila.”—Ezekiel 31:2, 3, 12; 32:11, 12.
Watanni shida bayan halakar Urushalima a shekara ta 607 K.Z., wani wanda ya tsira ya zo ya gaya wa Ezekiel: “An buga birni.” Annabin bai “ƙara yin shuru ba” ga waɗanda suke zaman bauta. (Ezekiel 33:21, 22) Zai yi shelar annabce-annabcen maidowa. Jehobah zai “sa makiyayi ɗaya a kansu, shi yi kiwonsu, watau bawan[sa] Dauda.” (Ezekiel 34:23) Edom za ta zama kufai, amma ƙasar da ke gabanta wato Yahuda za ta zama “kamar gonar Eden.” (Ezekiel 36:35) Jehobah ya yi alkawarin cewa zai kāre mutanensa da aka maido daga farmakin “Gog.”—Ezekiel 38:2.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
29:8-12—Yaushe ne Masar ta zama kufai har tsawon shekaru 40? Bayan an halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., Yahudawan da suka rage sun gudu zuwa Masar duk da kashedin da Irmiya ya yi. (Irmiya 24:1, 8-10; 42:7-22) Hakan bai tsirar da su ba domin Nebukadnezzar ya kai wa Masar hari kuma ya mallake ta. Mai yiwuwa Masar ta zama kango ne har tsawon shekaru arba’in bayan da aka ci ƙasar. Ko da yake babu rubutaccen tarihin da ya ba da tabbacin wannan kango, mun tabbata cewa hakan ya faru domin Jehobah Mai Cika annabci ne.—Ishaya 55:11.
29:18—Ta yaya ne ‘kowane kan mutum ya yi saiƙo kuma kowace kafaɗa ta goge’? Kwanton ɓaunar da aka yi wa birnin Tyre ta yi tsanani sosai har ta sa kawunan sojojin Nebukadnezzar ya yi saiƙo don yawan sa hular kwano kuma kafaɗarsu ta goge don ɗaukan kayan gina hasumiya da kuma mahara.—Ezekiel 26:7-12.
Darussa Dominmu:
29:19, 20. Tun da yake mutanen Tyre sun gudu zuwa birninsu da ke cikin tsibiri da yawancin dukiyarsu, ganima kaɗan ne Sarki Nebukadnezzar ya kwashe daga Tyre. Ko da yake sarki Nebukadnezzar arne ne mai fahariya da son kai, Jehobah ya saka masa don hidimarsa ta wajen ba shi Masar a matsayin ‘lada [ga] rundunar yaƙinsa.’ Ya kamata mu yi koyi da Allah ta wajen biyan haraji ga gwamnati don ayyukan da suke yi dominmu. Bai kamata halin masu mulki ko kuwa yadda ake yin amfani da harajin ya hana mu biyan harajin ba.—Romawa 13:4-7.
33:7-9. Bai kamata rukuni mai tsaro na zamani, wato, raguwar shafaffu da abokansu su daina wa’azin bishara na Mulkin da kuma yi wa mutane gargaɗi game da zuwan “ƙunci mai-girma” ba.—Matta 24:21.
33:10-20. Za mu sami ceto idan muka guji mugayen hanyoyi kuma muka yi biyayya da abin da Allah yake bukata. Hakika, hanyar Jehobah “daidai” ne.
36:20, 21. Da yake ba su yi abin da aka san su da shi ba, cewa su “mutanen Ubangiji” ne, Isra’ilawa sun ɓata sunan Allah tsakanin al’ummai. Ya kamata mu nuna ta halinmu cewa mu masu bauta wa Jehobah ne.
36:25, 37, 38. Aljanna ta ruhaniya da muke morewa a yau tana cike ne da “garken tsarkakkun mutane” (NW). Saboda haka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu kasance da tsabta.
38:1-23. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah zai ceci mutanensa daga harin Gog na ƙasar Magog! Gog ne sunan da aka ba “mai-mulkin wannan duniya” Shaiɗan Iblis, bayan da aka kore shi daga sama. Ƙasar Magog tana nufin wajajen duniya, inda aka jefa Shaiɗan da aljanunsa.—Yohanna 12:31; Ru’ya ta Yohanna 12:7-12.
“KA MAIDA HANKALINKA KUMA GA DUKAN ABINDA ZAN NUNA MAKA”
(Ezekiel 40:1–48:35)
Bayan shekara 14 da aka halaka Urushalima. (Ezekiel 40:1) Mutanen suna da sauran shekaru hamsin da shida da za su yi a zaman bauta. (Irmiya 29:10) Ezekiel yanzu ya kusan shekara 50. An kawo shi zuwa ƙasar Isra’ila a cikin wahayi. An gaya masa: “Ɗan mutum, duba da idanunka, ji da kunnuwanka, ka maida hankalinka kuma ga dukan abinda zan nuna maka.” (Ezekiel 40:2-4) Ezekiel ya yi farin cikin ganin wahayin sabon haikalin!
Haikali mai girma da Ezekiel ya gani yana da ƙofofi shida, ɗakunan cin abinci 30, wuri Mai Tsarki da Mafi Tsarki, bagadi na katako, da kuma bagadi don hadayun konawa. Ruwan rafi yana “fitowa” daga haikalin. (Ezekiel 47:1) A cikin wahayin, Ezekiel ya sami aikin raba wa kowace ƙabila ƙasarta, kowace ƙasar da zai ba su za ta zama daga bangaren gabas zuwa yamma tsakanin ƙasar Yahuda da Banyamin. “Wuri mai-tsarki na Ubangiji” da ‘birnin’ da ake kira Yahweh Shamma suna cikin wannan ƙasar.—Ezekiel 48:9, 10, 15, 35.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
40:3–47:12—Menene haikalin da ke cikin wahayin yake wakilta? Ba a taɓa gina irin wannan haikali mai girma da Ezekiel ya gani a wahayinsa ba. Yana wakiltar haikali na ruhaniya na Allah, wato, tsarinsa mai kama da haikali don bauta ta gaskiya a zamaninmu. (Ezekiel 40:2; Mikah 4:1; Ibraniyawa 8:2; 9:23, 24) Wahayi na haikali zai samu cikawarsa ta ƙarshe a lokacin Sarautar Kristi ta Shekara Dubu, sa’ad da ’yan adam masu adalci za su sami cikakken amfanin wannan tsarin haikali. Amma, haikali na wahayi ya sa Yahudawa da suke zaman bauta su sami alkawari cewa za a maido da bauta ta gaskiya kuma kowace iyalin Yahudawa za ta samu gado a cikin ƙasar.
40:3–43:17—Menene gwada haikali yake nufi? Gwada haikalin alama ce cewa babu shakka nufin Jehobah game da bauta ta gaskiya zai cika.
43:2-4, 7, 9—Menene “gawayen sarakunansu” da ya kamata a cire daga haikalin? Babu shakka, gawayen na nuni ga gumaka. Sarakunan Urushalima da mutanenta sun ƙazantar da haikalin Allah da gumaka, wato sun mai da gumakan sarakunansu.
43:13-20—Menene bagadi da Ezekiel ya gani yake wakilta? Bagadi na alama yana wakiltar nufin Allah game da hadayar fansa na Yesu Kristi. Domin wannan tanadin, an kira shafaffu masu adalci, kuma “taro mai-girma” suna da tsabta da kuma tsarki a gaban Allah. (Ru’ya ta Yohanna 7:9-14; Romawa 5:1, 2) Wataƙila shi ya sa babu ‘tabkin’ haikalin Sulemanu, wato, babban tasa inda firistoci suke wanke hannuwansu da ƙafafunsu a cikin haikali na wahayi.—1 Sarakuna 7:23-26.
44:10-16—Wanene rukunin firistoci ke wakilta? Rukunin firistoci na wakiltar rukunin Kiristoci shafaffu a zamaninmu. An yi musu gyara a shekara ta 1918 sa’ad da Jehobah ya zama “mai-gyaran azurfa mai-tsarkakewatta” a haikalinsa na ruhaniya. (Malachi 3:1-5) Waɗanda suke da tsabta ko kuma suka tuba za su iya ci gaba a hidimarsu ta musamman. Bayan haka, za su yi aiki tuƙuru don su zama “marar-aibi daga duniya,” da haka su zama misalai ga “taro mai-girma” da ke wakiltar ƙabilu da ba firistoci ba.—Yaƙub 1:27; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.
45:1; 47:13–48:29—Menene “ƙasa” da rabawarta ke wakilta? Ƙasar tana wakiltar wuraren da mutanen Allah suke ayyuka na bauta. Mai bauta wa Jehobah yana cikin ƙasa da aka maido duk inda yake muddin yana ɗaukaka bauta ta gaskiya. Raba ƙasa za ta samu cikawarta na ƙarshe a sabuwar duniya sa’ad da kowane mutum mai aminci zai samu nasa wuri.—Ishaya 65:17, 21.
45:7, 16—Menene abubuwan da mutanen suka kawo don tsarin firistoci da sarakuna ke nunawa? A cikin haikali na ruhaniya, wannan na nuni ga goyon baya na ruhaniya, suna ba da taimako da kuma haɗa kai.
47:1-5—Menene ruwan da ke cikin wahayin kogi da Ezekiel ya gani yake wakilta? Ruwan yana wakiltar tanadin ruhaniya da Jehobah ya yi don rai, har da hadayar fansa na Yesu Kristi da kuma sanin Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Irmiya 2:13; Yohanna 4:7-26; Afisawa 5:25-27) A hankali kogin na yin zurfi don sababbin da suke shigowa cikin bauta ta gaskiya su sami wurin zama. (Ishaya 60:22) Kogin zai riƙa gudana da ruwan rai mafi ƙarfi a lokacin sarautar Shekara Dubu, ruwan zai haɗa da ƙarin fahimi da aka samu daga “littattafai” da za a buɗe.—Ru’ya ta Yohanna 20:12; 22:1, 2.
47:12—Menene ’ya’yan itatuwa suke wakilta? Itatuwa na alama na wakiltar tanadin Allah na ruhaniya don maido da ’yan adam zuwa kamilcewa.
48:15-19, 30-35—Menene birnin da ke wahayin Ezekiel yake wakilta? “Yahweh Shamma” na cikin ƙasa da aka ‘ɓata’ wanda ya nuna cewa yana wakiltar wani abu na duniya. Kamar dai birnin na wakiltar tsari na duniya da ke amfanar waɗanda za su shiga cikin “sabuwar duniya” ta adalci. (2 Bitrus 3:13) Ƙofofin da ke kowane gefe ya nuna cewa yana da sauƙin shiga. Ya kamata dattawa tsakanin mutanen Allah su zama waɗanda za a iya kusanta.
Darussa Dominmu:
40:14, 16, 22, 26. Itatuwan dabbino da aka sassaƙa a jikin bangon hanyoyin shiga haikali sun nuna cewa sai masu ɗabi’a mai kyau ne kawai ake ƙyale su shiga. (Zabura 92:12) Wannan ya koya mana cewa Jehobah zai amince da bautarmu ce kawai idan mu masu adalci ne.
44:23. Muna godiya sosai don hidimar da rukunin firistoci na zamani suke yi mana! “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana yin ja-gora wajen ba da abinci na ruhaniya a kan kari da ke taimakonmu mu fahimci bambancin da ke tsakanin abu marar tsabta da abu mai tsabta a gaban Jehobah.—Matta 24:45.
47:9, 11. Ilimi, wanda shi ne fanni na musamman na ruwan nan na alama yana warkarwa mai ban al’ajabi a zamaninmu. Duk inda aka sha ruwan, yana sa mutane su sami rai a ruhaniyance. (Yohanna 17:3) A wani ɓangare kuma, za a ba da “gishiri” ga waɗanda ba su karɓi ruwa mai ba da rai ba, wato za a halaka su dindindin. Yana da muhimmanci mu yi ‘ƙoƙari mu rarrabe kalmar gaskiya sosai’!—2 Timothawus 2:15.
‘Zan Tsarkake Sunana Mai-Girma’
Bayan an cire sarki na ƙarshe na zuriyar Dauda, Allah na gaskiya ya ƙyale dogon lokaci ya shige kafin zuwan “wanda wajibinsa ne” ya samu sarautar. Amma, Allah bai yasar da alkawarinsa da Dauda ba. (Ezekiel 21:27; 2 Samuila 7:11-16) Annabcin Ezekiel ya yi maganar “bawana Dauda,” wanda zai zama ‘makiyayi’ da kuma “sarki.” (Ezekiel 34:23, 24; 37:22, 24, 25) Wannan Yesu Kristi ne a cikin ikonsa na Mulki. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Jehobah zai ‘tsarkake sunansa mai-girma’ ta wajen Mulkin Almasihu.—Ezekiel 36:23.
Jim kaɗan, za a halaka dukan waɗanda suka ɓata suna mai tsarki na Allah. Amma waɗanda suka tsarkake wannan sunan a rayuwarsu ta wajen bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace za su sami rai madawwami. Bari mu yi amfani da ruwan rai da ke gudana a zamaninmu kuma mu sa bauta ta gaskiya ta zama abu mai muhimmanci a rayuwarmu.
[Hasiya]
a Don samun bayani a kan Ezekiel 1:1–24:27, ka duba “Darussa Daga Littafin Ezekiel na Ɗaya” da ke fitowar Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuli, 2007.