Za Mu Amfana Idan Muka Jimre Wahala
“Waɗanda suka jimre muna ce da su masu-albarka.”—YAƘUB 5:11.
1, 2. Menene ya nuna cewa ba nufin Jehobah ba ne mutane su sha wahala?
BABU wani mutum mai hankali da zai so ya sha wahala, Jehobah Allah Mahalicci ma ba ya son mutane su sha wahala. Za mu fahimci hakan idan muka yi la’akari da hurarriyar Kalmarsa kuma muka lura da abin da ya faru bayan ya halicci namiji da tamace. Da farko, Allah ya halicci namijin. “Ubangiji Allah kuwa ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa, ya hura masa lumfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai-rai.” (Farawa 2:7) Adamu kamili ne a jikinsa da kuma hankalinsa, ba zai yi ciwo ba ko kuma ya mutu.
2 Menene yanayin rayuwar Adamu? “Ubangiji Allah kuma ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin; can kuwa ya sanya mutumin da ya sifanta. Kowane itacen da ke mai-sha’awan gani, masu-kyau kuwa domin ci.” (Farawa 2:8, 9) Hakika, Adamu ya sami gida mai kyau. Babu wahala a Adnin.
3. Wane gata ne ma’aurata na farko suka samu?
3 Farawa 2:18 ta ce: “Ubangiji Allah kuma ya ce, Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” Jehobah ya halicci mace kamila wa Adamu, don ya sami iyali mai farin ciki. (Farawa 2:21-23) Littafi Mai Tsarki ya daɗa gaya mana cewa: “Allah ya albarkace su kuma: Allah ya ce masu, Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Farawa 1:28) An ba ma’aurata na farko gatar faɗaɗa Aljanna ta Adnin har dukan duniya ta zama aljanna. Za su haifi ’ya’ya masu farin ciki, waɗanda ba za su sha wahala ba. Wannan farawa ce mai kyau sosai!—Farawa 1:31.
An Soma Wahala
4. Daga abin da tarihi ya nuna, menene yanayin ’yan adam?
4 Hakika, idan muka duba yanayin iyalin ’yan adam a tarihi, za mu ga cewa akwai abin da ya sa yanayin ya lalace. Miyagun abubuwa sun faru, kuma iyalin ’yan adam sun sha wahala sosai. Tun shekaru aru-aru, dukan zuriyar Adamu da Hauwa’u suna ciwo, suna tsufa, kuma suna mutuwa. Babu shakka, wannan duniya dabam take da aljanna da ke cike da mutane masu farin ciki. An kwatanta yanayin da kyau a cikin Romawa 8:22: “Gama mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.”
5. Ta yaya ne iyayenmu na farko suka jawo wahala ga iyalin ’yan adam?
5 Wannan wahalar da ta kasance da daɗewa ba laifin Jehobah ba ne. (2 Samuila 22:31) Dole ne a ɗora wa ’yan adam waɗansu laifin. “Sun ruɓa, sun yi ayuka masu-ban ƙyama.” (Zabura 14:1) Da farko an ba iyayenmu na fari dukan abubuwa masu kyau. Abin da kawai ake bukata shi ne su yi biyayya ga Allah don su ci gaba da samun abubuwa masu kyau, amma Adamu da Hauwa’u sun zaɓi ’yancin kansu daga Jehobah. Tun da iyayenmu na fari sun ƙi Jehobah, ba za su ci gaba da zama kamilai ba. Za su ci gaba da tsufa har sai sun mutu. Ta haka ne muka gaji ajizanci.—Farawa 3:17-19; Romawa 5:12.
6. Wane matsayi ne Shaiɗan ya cika wajen jawo wahala?
6 Wanda ya jawo wahala da farko shi ne halitta na ruhu da ake kira Shaiɗan Iblis. An ba sa ’yancin yin zaɓe. Amma, ya yi amfani da wannan ’yancin don a bauta masa. Duk da haka, Jehobah ne kaɗai ya cancanci a bauta masa, ba halittunsa ba. Shaiɗan ne ya ruɗi Adamu da Hauwa’u su nemi ’yancin kansu daga wurin Jehobah, don su ‘zama kamar Allah suna sanin nagarta da mugunta.’—Farawa 3:5.
Jehobah ne Kaɗai Yake da Ikon Sarauta
7. Menene sakamakon tawaye ga Jehobah ya nuna?
7 Mugun sakamakon tawaye ya nuna cewa Jehobah Mamallakin Duka ne kaɗai yake da ikon sarauta kuma sarautarsa ce kaɗai take da adalci. Shekaru da yawa da suka wuce sun nuna cewa Shaiɗan wanda ya zama “mai- mulkin wannan duniya,” ya kafa muguwar sarauta, marar adalci, kuma marar kyau. (Yohanna 12:31) Muguwar sarautar mutane ta shekaru masu yawa a ƙarƙashin ja-gorancin Shaiɗan ta nuna cewa ba su da ikon yin sarauta mai adalci. (Irmiya 10:23) Da haka, kowace irin sarautar da ’yan adam za su yi idan ba Jehobah ba, ba za ta yi nasara ba. Tarihi ya tabbatar da hakan.
8. Menene nufin Jehobah game da dukan sarautar ’yan adam, kuma yaya zai cika nufinsa?
8 Yanzu da Jehobah ya ƙyale ’yan adam su gwada sarautarsu shekaru da yawa, ya dace ya kawar da dukan sarauta ta duniya kuma ya canja ta da gwamnatinsa. Annabci game da wannan ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [sarautar ’yan adam] kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki [mulkinsa na samaniya a hannun Kristi], wanda ba za a rushe shi ba daɗai . . . Za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Daniel 2:44) Za a kawar da sarautar aljanu da ta ’yan adam, Mulkin Allah na samaniya kaɗai ne zai wanzu kuma ya yi sarauta a duniya. Kristi zai zama Sarki, kuma zai sami abokan sarauta mutane guda 144,000 masu aminci da aka ɗauka daga cikin duniya.—Ru’ya ta Yohanna 14:1.
Shan Wahala na Iya Kawo Amfani
9, 10. Ta yaya ne Yesu ya amfana daga wahalar da ya sha?
9 Yana da kyau a tattauna farillan da waɗanda za su yi sarauta a Mulki na samaniya za su cika. Da farko, Yesu ya nuna cewa ya cancanta ya zama Sarki. Ya yi rayuwa shekaru aru-aru tare da Jehobah yana yin nufin Ubansa, kuma ya zama “gwanin mai-aiki.” (Misalai 8:22-31) Sa’ad da Jehobah ya ce masa ya zo duniya, Yesu da son rai ya yarda. A duniya, ya mai da hankali ne wajen gaya wa mutane ikon mallaka ta Jehobah da Mulkinsa. Yesu ya kafa wa dukanmu misali mai kyau ta wurin yin biyayya ga wannan ikon mallaka.—Matta 4:17; 6:9.
10 Yesu ya sha tsanani, kuma a ƙarshe aka kashe shi. A lokacin da yake hidima, ya lura da yanayin ban tausayin da ’yan adam suke ciki. Akwai amfanin da ya samu daga ganin irin yanayin da ’yan adam suke ciki da kuma wahalar da ya sha? Ƙwarai kuwa. Ibraniyawa 5:8 ta ce: ‘Ko da shi ke Ɗan [Allah] ne, duk da wannan ya koya biyayya ta wurin wahalar da ya sha.’ Abin da Yesu ya fuskanta sa’ad da yake duniya ya sa ya ƙara kasancewa da fahimi da kuma juyayi. Ya fuskanci yanayin ’yan adam. Zai nuna wa waɗanda suka sha wahala juyayi kuma zai fahimci hakkinsa wajen cetonsu. Ka yi la’akari da yadda manzo Bulus ya nanata wannan a littafin Ibraniyawa: “Ya wajabce shi shi kamantu ga ’yan’uwansa a cikin dukan abu, domin shi zama babban priest mai-jinƙai, mai-aminci, cikin matsaloli na wajen Allah, domin shi yi kafarar zunuban jama’a. Gama yayinda shi da kansa ya sha wahala ana jarabtassa, yana da iko ya taimaki waɗanda a ke jarabtassu.” “Ba mu da babban priest wanda ba shi taɓuwa da tarayyar kumamancinmu ba: amma wanda an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai banda zunubi. Bari mu guso fa gaba gaɗi zuwa kursiya na alheri, domin mu karɓi jinƙai, mu sami alheri kuma mai-taimakonmu cikin lotun bukata.”—Ibraniyawa 2:17, 18; 4:14-16; Matta 9:36; 11:28-30.
11. Ta yaya ne abin da waɗanda za su zama sarakuna da firistoci a nan gaba suka fuskanta a duniya ya amfane su a matsayin masu sarauta?
11 Haka yake da mutane 144,000 da ‘aka fansa’ daga cikin duniya su zama abokan sarautar Yesu Kristi a Mulki na samaniya. (Ru’ya ta Yohanna 14:4) An haifi dukansu a duniya ne, sun yi girma a duniya da ke cike da wahala, kuma sun sha wahala. Yawancinsu sun fuskanci tsanani, an kashe wasu saboda sun riƙe amincinsu ga Jehobah kuma sun yarda za su bi Yesu. Amma ba su ‘ji kunyar shaidar Ubangijinsu ba, amma sun daure shan wuya tare da bishara.’ (2 Timothawus 1:8) Abin da suka fuskanta a duniya ya sa sun dace su yi sarauta bisa ’yan adam daga sama. Sun koyi yin juyayi, alheri, kuma suna ɗokin taimaka wa mutane.—Ru’ya ta Yohanna 5:10; 14:2-5; 20:6.
Masu Begen Zama a Duniya Suna Farin Ciki
12, 13. Ta yaya ne waɗanda suke da begen zama a duniya za su amfana daga wahala?
12 Waɗanda suke da begen zama a aljanna ta duniya wadda babu ciwo, wahala, da kuma mutuwa za su amfana daga wahalar da suke sha kuwa? Azaba da baƙin ciki da wahala take kawowa ba abin sha’awa ba ne. Amma idan muka jimre irin wannan wahalar, za mu kyautata halayenmu masu kyau kuma mu yi farin ciki.
13 Ka yi la’akari da abin da hurarriyar Kalmar Allah ta ce game da wannan: “Amma idan kun sha wuya sabili da adalci, masu albarka ne ku.” “Idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku.” (1 Bitrus 3:14; 4:14) “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama.” (Matta 5:11, 12) “Mai-albarka ne mutum wanda ya daure da jaraba: gama sa’anda ya amintu, za shi karɓi rawanin rai.”—Yaƙub 1:12.
14. Ta yaya ne wahala za ta iya sa masu bauta wa Jehobah su yi farin ciki?
14 Hakika ba wahalar da muka jimre ba ce take sa mu farin ciki. Amma za mu sami farin ciki da gamsuwa ta wajen sanin cewa muna wahala saboda yin nufin Jehobah da kuma bin tafarkin Yesu. Alal misali, a ƙarni na farko, an saka wasu manzanni cikin kurkuku kuma aka kawo su gaban babban kotu na Yahudawa kuma aka hukunta su domin suna wa’azi game da Yesu Kristi. An yi musu bulala sai aka sake su. Menene suka yi? Littafi Mai Tsarki ya ce “suka fita fa daga gaban majalisa, suna murna da aka maishe su sun isa su sha ƙanƙanci sabili da Sunan.” (Ayukan Manzanni 5:17-41) Ba su yi farin ciki saboda bulalar da aka yi musu da kuma zafin bulalar da suka sha ba. Amma sun yi farin ciki ne saboda sun fahimci cewa hakan ya faru ne saboda sun riƙe amincinsu ga Jehobah kuma don sun bi tafarkin Yesu.—Ayukan Manzanni 16:25; 2 Korinthiyawa 12:10; 1 Bitrus 4:13.
15. Ta yaya jimre wahala yanzu zai amfane mu a nan gaba?
15 Idan muka jimre hamayya da kuma tsanani a hanya mai kyau, hakan na iya sa mu kasance masu jimiri. Hakan kuma zai sa mu jimre wahalar da ke zuwa a gaba. Mun karanta: “’Yan’uwana, kadan jarabobi masu-yawa sun same ku, ku maishe shi abin farinciki sarai; kun sani gwadawar bangaskiyarku tana jawo haƙuri.” (Yaƙub 1:2, 3) Hakan nan ma, Romawa 5:3-5 sun ce: “Mu yi farinciki kuma cikin ƙuncinmu: muna sane ƙunci yana faradda haƙuri; haƙuri kuma, gwadawa; gwadawa kuma, bege: bege kuma ba ya kunyatarwa.” Idan muka jimre wa gwaji saboda halinmu na Kirista, hakan zai shirya mu mu jimre wa gwaji na wannan mugun zamani.
Jehobah Zai Albarkaci Waɗanda Suka Yi Hasara
16. Wane lada ne Jehobah zai ba sarakuna da firistoci na nan gaba domin wahalar da suka sha?
16 Idan mun yi hasarar abin duniya saboda hamayya ko kuma tsanani da muke sha don muna bin hanyar Kirista, za mu yi farin cikin sanin cewa Jehobah zai albarkace mu sosai. Alal misali, manzo Bulus ya rubuta wa waɗanda suke da begen zuwa sama su yi sarauta a Mulkin Allah cewa: “Kuka yi . . . farin ciki kuka sha wason dukiyarku, kuna sane ku da kanku kuna da dukiya mafiya kyau, matabbaciya kuwa.” (Ibraniyawa 10:34) Ka yi tunanin farin cikin da za su yi sa’ad da a ƙarƙashin ja-gorancin Jehobah da Kristi suka kasance cikin masu yi wa mazaunan sabuwar duniya albarka. Kalmar manzo Bulus ga amintattun Kiristoci za ta kasance da gaske: “Ga ganina, raɗaɗar na wannan zamani ba su isa a gwada su da daraja wadda za a bayyana zuwa garemu.”—Romawa 8:18.
17. Menene Jehobah zai yi wa waɗanda suke da begen zama a duniya da suke bauta masa da aminci yanzu?
17 Hakazalika, ko menene waɗanda suke da begen zama a duniya suka yi hasararsa ko kuma suka bari saboda hidimar Jehobah, zai albarkace su sosai da abin da zai yi a nan gaba. Zai ba su kamilin rayuwa ta har abada a aljannar duniya. A sabuwar duniyar, Jehobah zai “share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Wannan alkawari ne mai ban al’ajabi! Ba abin da muka bari da son ranmu ko kuma ba da son ranmu ba don Jehobah a wannan duniya da zai yi daidai da rayuwa mai kyau a nan gaba, wanda zai ba amintattun bayinsa da suka jimre wahala.
18. Wane alkawari ne mai ban ƙarfafa Jehobah ya yi mana a Kalmarsa?
18 Duka wahalar da za mu jimre ba za ta shafi farin cikin mu na rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah ba. Yanayi mai kyau na sabuwar duniya zai canja dukan wannan. Ishaya 65:17, 18 sun ce: “Ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa.” Saboda haka, ya dace da Yaƙub ɗan’uwan Yesu ya ce: “Waɗanda suka jimre muna ce da su masu-albarka.” (Yaƙub 5:11) Hakika, idan muka jimre wahala, za mu sami albarka yanzu da kuma nan gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya ne ’yan adam suka soma fuskantar wahala?
• Wace albarka ce waɗanda za su yi sarauta bisa duniya da kuma mazauna duniya za su samu domin wahalar da suka sha?
• Me ya sa za mu yi farin ciki yanzu ko idan muna wahala?
[Hoto a shafi na 13]
Iyayenmu na farko suna da rayuwa mai kyau a gabansu
[Hoto a shafi na 15]
Wahalar da Yesu ya gani ta sa ya zama Sarki nagari da Babban Firist
[Hoto a shafi na 17]
Manzanni sun yi ‘murna da aka maishe su sun isa su sha ƙanƙanci sabili da bangaskiyarsu’