Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba!
Wataƙila a wani lokaci, ka taɓa tambayar kanka, ‘Me ya sa ake wahala?’ Mutane sun sha wahala sosai na shekaru dubbai daga yaƙe-yaƙe, talauci, masifu, aikata laifi, rashin gaskiya, rashin lafiya, da kuma mutuwa. Mutane sun wahala sosai a shekaru ɗarurruwa da suka wuce fiye da dā. Dukan wahala za ta ƙare kuwa?
Amsa mai ƙarfafawa ita ce, e, kuma ba zai daɗe ba! Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ta ce: “Mugaye za su shuɗe. . . . Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama.” Har yaushe? “Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, su gāje ta har abada.”—Zabura 37:10, 11, 29.
Bayan Allah ya kawar da mugunta da kuma wahala, zai mai da duniya ta zama aljanna. Mutane za su zauna har abada cikin ƙoshin lafiya da farin ciki. Kalmar Allah ta ce: “[Allah] zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”—Wahayin Yahaya 21:4.
A wannan sabuwar duniya, za a ta da matattu zuwa rai domin su ma su more waɗannan albarkatu: “Za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Shi ya sa Yesu Kristi ya gaya wa wani mugu da ya tuba kuma ya ba da gaskiya a gare shi cewa: “Za ka kasance tare da ni a [Aljanna].”—Luka 23:43.
Me Ya sa Aka Soma Wahala?
Tun da nufin Allah ne cewa mutane su sami rayuwa mai kyau, me ya sa ya ƙyale wahala ta soma? Me ya sa ya ƙyale ta daɗe haka?
Sa’ad da Allah ya halicci Adamu da Hauwa’u, Ya halicce su kamiltattu. Ya saka su a cikin lambu a aljanna kuma ya ba su aiki mai kyau da za su yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Da a ce sun yi biyayya ga Allah, da sun haifi ’ya’ya kamiltattu. Kuma da duniya ta zama aljanna, wurin da mutane za su zauna har abada cikin salama da farin ciki.
Allah ya ba Adamu da Hauwa’u ikon yin zaɓi a matsayinsu na mutane. Kuma su ba ’yar tsana ba ne. Amma farin cikinsu za ta ci gaba ne kawai idan suka yi amfani da ’yancinsu na zaɓe a hanyar da ta dace—ta yin biyayya ga dokokin Allah. Kamar yadda Allah ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.” (Ishaya 48:17) Yin amfani da ’yancin zaɓe a yadda bai dace ba, zai jawo haɗari, domin ba a halicci mutane ba su yi nasara ba tare da taimakon Allah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Al’amuran mutum ba a hannunsa suke ba, ba mutum ne ke kiyaye takawarsa ba.”—Irmiya 10:23.
Abin baƙin ciki, iyayenmu na farko sun yi zaton cewa za su iya ’yantar da kansu daga Allah kuma su yi nasara. Amma sa’ad da suka ƙi sarautar Allah, sun yi hasarar kamiltacciyar rayuwarsu. Daga nan sai suka fara suƙuƙucewa, daga ƙarshe suka tsufa kuma suka mutu. Domin mu ’ya’yansu ne, mun gaji wannan ajizancin da kuma mutuwa.—Romawa 5:12.
Ainihin Batun Ikon Mallaka
Me ya sa Allah bai halaka Adamu da Hauwa’u kuma ya halicci wasu mutane ba? Dalili shi ne, an ƙalubalanci ikon mallaka na Allah. Tambaya ita ce, Wanene yake da ikon yin sarauta, kuma sarautar waye ce ta fi dacewa? Saboda haka, mutane za su iya yin nasara kuwa ba tare da mulkin Allah ba? Ta wajen ba su isashen lokaci da kuma ’yanci su gwada sarautar kansu, Allah zai tabbatar da ko za su fi jin daɗi a ƙarƙashinsa ko kuma a sarautar kansu. Lokacin da ya ba mutane ya ishe su su gwada dukan fannonin siyasa, zaman jama’a, tattalin arziki, da kuma tsarin addinai da ba sa ƙarƙashin ja-gorar Allah.
Menene sakamakon haka? Tarihin mutane na shekaru dubbai ya nuna cewa wahala sai ƙaruwa take yi. A ƙarnukan da suka wuce, mutane sun fuskanci wahala da ta fi kowace. An kashe miliyoyi a Yaƙin Duniya na II. An kashe fiye da miliyan 100 a yaƙe-yaƙe. Aikata laifi da mugunta sun zama ruwan dare. Shan miyagun ƙwayoyi sai ƙaruwa yake yi. Cuta da ake samu ta wajen jima’i sai yaɗuwa take yi. Miliyoyi suna mutuwa kowace shekara domin yunwa da cuta. Rayuwar iyali da tarbiyya sai ƙara muni suke yi a ko’ina. Babu gwamnatin mutane da za ta iya magance waɗannan matsaloli. Babu wadda ta taɓa magance tsufa, rashin lafiya, da mutuwa.
Yanayin mutane a yau ya yi daidai da yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta. Kalmar Allah ta bayyana cewa muna ‘ƙarshen’ wannan zamanin, sa’ad da “za a sha wuya ƙwarai.” Kuma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, sai ƙara muni suke yi.’—2 Timoti 3:1-5, 13.
Wahala ta Kusa Ƙarewa
Duka waɗannan tabbaci sun nuna cewa muna ƙarshen wannan lokaci na baƙin ciki da mutane suka ’yantar da kansu daga Allah. An nuna sarai cewa mulkin mutane idan ba na Allah ba, ba zai taɓa yin nasara ba. Mulkin Allah ne kawai zai iya kawo salama, farin ciki, ƙoshin lafiya, da rai madawwami. Saboda haka, ƙarshen mugunta da wahala da Jehobah ya ƙyale ta kusa. Nan ba da daɗewa ba, Allah zai sa hannu a al’amuran mutane ta wajen halaka wannan zamani.
Annabcin Littafi Mai Tsarki ya ce: “A kwanakin waɗannan sarakuna [mulkin mutanen da ke sarauta], Allah na Sama zai kafa wani mulki [a sama] wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, . . . zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki [sarauta ta yanzu], ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.” (Daniyel 2:44) Kunita ikon mallaka na Jehobah, ikonsa na yin mulki, ta wurin Mulkinsa na sama, shi ne muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da yake bayyana wata alama ta “ƙarshen zamani,” Yesu ya ce: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”—Matiyu 24:14.
Sa’ad da ƙarshen ya zo, waye zai tsira? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: “Mutane adalai masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu. Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar.” (Karin Magana 2:21, 22) Adalai su ne waɗanda suka koyi nufin Jehobah kuma suke yin sa. Yesu ya ce: “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.” (Yahaya 17:3) Hakika, “duniyar kuwa tana shuɗewa . . . amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.”—1 Yahaya 2:17.
Sai ko an ba da alama, an ɗauko dukan Nassosi daga Littafi Mai Tsarki ne kuma an yi amfani da haruffan zamani.