“Tsohon Alkawari” Yana Da Amfani Har Yanzu?
A SHEKARA ta 1786 wani likita ɗan Faransa ya wallafa wani littafi mai suna Traité d’anatomie et de physiologie (Bayani A Kan Jikin Mutum da Kuma Yadda Yake Aiki). An ce shi ne littafi mafi kyau a zamaninsa da ya yi magana a kan jijiyoyin jiki, kuma ba da daɗewa ba, an sayar da kofi ɗaya na wannan littafin mai wuyar samu sama da dala dubu 27! Duk da haka, majiyyata kaɗan ne kawai za su dogara ga likitan da yake yin aiki da wannan tsohon littafi na magani. Duk da muhimmancin da littafin yake da shi a tarihi, ba zai iya taimaka wa mutumin da ba shi da lafiya ba a yau.
Yadda yawancin mutane suke ji ke nan game da Tsohon Alkawari. Sun ɗauki tarihin Isra’ila da kuma labarai masu daɗi da ke cikinsa da muhimmanci. Duk da haka, suna shakkar ko ya dace su bi shawarar da aka ba da fiye da shekaru 2,400 da suka shige. Ilimin kimiyya, sha’anin kasuwanci, har da rayuwar iyali sun bambanta a yau da yadda suke a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Philip Yancey, wanda shi ne edita a dā na Christianity Today, ya rubuta a cikin littafinsa The Bible Jesus Read cewa: “Tsohon Alkawari ba shi da ma’ana, kuma ɗan sashensa da ke da ma’ana yana ba mutane haushi a yau. Domin wannan da wasu dalilai ya sa a yawancin lokaci mutane ba sa karanta Tsohon Alkawari, wanda shi ne kashi uku cikin huɗu na Littafi Mai Tsarki.” Irin wannan tunanin ba sabon abu ba ne.
Ƙasa da shekara 50 bayan mutuwar manzo Yohanna a kusan shekara ta 100 A.Z., wani matashi mawadaci mai suna Marcion, ya koyar da cewa Kiristoci su daina karanta Tsohon Alkawari. In ji ɗan tarihi na Turanci Robin Lane Fox, Marcion ya faɗi cewa “‘Allahn da ke cikin Tsohon Alkawari ‘mugu ne’ wanda yake goyon bayan waɗanda suke karya doka da kuma ’yan ta’adda kamar Sarki Dauda na Isra’ila. Akasin haka, Kristi ya bayyana Allah mai girma wanda ya bambanta da Allahn da ke cikin Tsohon Alkawari.” Fox ya rubuta cewa wannan imanin ne ya “zama ‘ra’ayin Marcion’ kuma ya ci gaba da jawo mabiya, musamman a Suriya ta Gabas, har zuwa ƙarni na huɗu.” Har yanzu, akwai mutanen da suka manne wa wannan imanin. A sakamakon haka, bayan fiye da shekara 1,600, in ji Philip Yancey, “Kiristoci sun ci gaba da manta abin da ke cikin Tsohon Alkawari kuma ba a bin ilimin gabaki ɗaya a wannan zamanin.”
An canja Tsohon Alkawari ne? Ta yaya za mu iya haɗa fahimtarmu ta “Ubangiji mai-runduna” da ke Tsohon Alkawari da “Allah kuwa na ƙauna da na salama” da ke Sabon Alkawari? (Ishaya 13:13; 2 Korinthiyawa 13:11) Tsohon Alkawari zai amfane ka a yau kuwa?