Ku Koya Wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
“Kamar yadda kibawu a hannun ƙaƙarfan mutum, Hakanan ne ’ya’yan ƙuruciya.”—ZABURA 127:4.
1, 2. Ta yaya ne yara suke kama da “kibawu a hannun ƙaƙarfan mutum”?
MAHARBI yana son ya harbi wani abu da kibiya. Ya ɗora kibiyar a kan bakar, sa’an nan ya ja bakar da ƙarfi. Duk da ƙoƙarin da yake yi, ya ɗauki ɗan lokaci don ya saita abin da yake son ya harba. Sai ya saki kibiyar! Kibiyar za ta sami abin da yake son ya harba kuwa? Amsar ta ƙunshi abubuwa masu yawa, har da iyawar maharbin, inda iska take kaɗawa, da kuma yanayin kibiyar.
2 Sarki Sulemanu ya kwatanta yara da “kibawu a hannun ƙaƙarfan mutum.” (Zabura 127:4) Ka yi la’akari da yadda za a iya yin amfani da wannan kwatancin. Maharbin zai ja kibiyar ce kawai na ɗan lokaci. Don ya sami abin da yake son ya harba, dole ne ya sake ta da wuri. Hakazalika, iyaye suna da ɗan gajeren lokaci ne kawai koyar da yaransu su ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarsu. Bayan wasu ’yan shekaru, yaran za su yi girma kuma su bar gida. (Matta 19:5) Za su sami abin da suke son su harba, wato, yaran za su ci gaba da ƙauna da kuma bauta wa Allah bayan sun bar gida? Amsar ta ƙunshi abubuwa masu yawa. Uku daga cikinsu su ne ƙwarewar iyayen, wurin da aka yi renon yaran, da kuma yadda ‘kibiyar,’ ko yaron, ya yi na’am da koyarwar da aka yi masa. Bari mu bincika waɗannan hanyoyin sosai. Na farko, za mu tattauna halayen ƙwararrun iyaye.
Ƙwararrun Iyaye Suna Kafa Misali Mai Kyau
3. Me ya sa ya kamata iyaye su yi abin da suka faɗa?
3 Yesu ya kafa misali ga iyaye domin ya yi abin da yake koya wa mutane. (Yohanna 13:15) A wani ɓangare kuma, ya la’anta Farisawa waɗanda suke “faɗi” amma “ba su kuwa aikatawa.” (Matta 23:3) Don su motsa yaransu su ƙaunaci Jehobah, dole ne abin da iyaye suka faɗa ya jitu da abin da suke yi. Kalaman da aka faɗa da baki kawai ba su da amfani kamar bakar da ba ta da tsirkiya.—1 Yohanna 3:18.
4. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata iyaye su yi wa kansu, kuma don me?
4 Me ya sa ya kamata iyaye su kafa misali mai kyau? Kamar yadda manya za su iya ƙaunar Allah ta wajen bin misalin Yesu, yara suna iya koyan yadda za su ƙaunaci Jehobah ta wajen bin misali mai kyau na iyayensu. Abokan yaro suna iya ƙarfafa shi ko kuma su “ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) A yawancin rayuwar yaro, musamman a lokacin da yake girma, abokai na kud da kud kuma mafi tasiri da yaro yake da shi su ne iyayensa. Saboda haka, zai dace iyaye su tambayi kansu: ‘Wane irin aboki ne ni? Misalin da nike kafawa yana ƙarfafa yarona ya kasance mai halayen kirki? Wane irin misali nike kafawa wajen batutuwa masu muhimmanci a addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki?’
Ƙwararrun Iyaye Suna Yin Addu’a Tare da Yaransu
5. Menene yara za su iya koya daga addu’o’in iyayensu?
5 Yaranku suna iya koyan abubuwa masu yawa ta wajen sauraron addu’o’inku. Idan suka ji kuna gode wa Allah a lokacin cin abinci kuma kuna yin addu’a a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki, menene za su kammala? Wataƙila za su iya koyan cewa Jehobah ne yake tanadin bukatunmu na zahiri, don haka muna bukatar mu gode masa, kuma shi ne ke koya mana gaskiya ta ruhaniya. Waɗannan darussa ne masu kyau.—Yaƙub 1:17.
6. Ta yaya ne iyaye za su iya taimaka wa yara su ga cewa Jehobah yana damuwa da kowannensu ɗaɗɗaya?
6 Amma, idan ka yi addu’a tare da iyalinka a wasu lokatai ba kawai lokacin cin abinci da nazarin Littafi Mai Tsarki ba, kuma idan kuka ambata batutuwa masu muhimmanci da suka shafe ku da yaranku a cikin addu’a, za ku cim ma abubuwa masu yawa. Za ku taimaka wa yaranku su ga cewa Jehobah yana tare da iyalinku, kuma yana kula da kowannenku ɗaɗɗaya. (Afisawa 6:18; 1 Bitrus 5:6, 7) Wani uba ya ce: “Tun lokacin da muka haifi ɗiyarmu, muna yin addu’a tare da ita. Sa’ad da ta girma, mun yi addu’a game da tarayyarta da mutane da kuma sauran batutuwan da suka shafe ta. Kafin ta yi aure, babu ranar da ba ma yin addu’a tare da ita.” Za ku iya yin addu’a da yaranku a kowace rana? Za ku iya taimaka masu su ɗauki Jehobah a matsayin Aboki wanda ba wai kawai yana yi masu tanadin abubuwa na zahiri da kuma na ruhaniya da suke bukata ba, amma wanda yake kula da yadda suke ji?—Filibbiyawa 4:6, 7.
7. Don addu’arsu ta kasance takamaimai, menene iyaye suke bukatar su sani?
7 Hakika, don addu’arku ta zama takamaimai, kuna bukatar ku san abin da yaranku suke fuskanta. Ku yi la’akari da kalaman wani uba wanda ya yi renon yara biyu: “A ƙarshen kowane mako, ina yi wa kai na tambayoyi biyu: ‘Waɗanne abubuwa ne ke damun yarana a wannan makon? Kuma waɗanne abubuwa masu kyau ne suka shaida?’” Iyaye, za ku iya yi wa kanku waɗannan tambayoyin kuma ku sa wasu cikin amsoshin a addu’o’in da za ku yi da ’ya’yanku? Idan kuka yi haka, kuna koya masu ne cewa ba wai kawai za su yi addu’a ga Jehobah, Mai jin addu’a ba, amma suna bukatar su ƙaunace shi.—Zabura 65:2.
Ƙwararrun Iyaye Suna Ƙarfafa Yin Nazari Sosai
8. Me ya sa ya kamata iyaye su taimaka wa yaransu su dinga yin nazarin Kalmar Allah?
8 Ta yaya ne ra’ayin iyaye game da nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya shafan dangantakar yaro da Allah? Idan ana son dangantaka ta ci gaba, waɗanda suke dangantakar suna bukatar su ci gaba da yi wa juna magana kuma su saurari juna. Ɗaya daga cikin hanyoyin da muke sauraron Jehobah ita ce yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta hanyar littattafan da ‘bawan nan mai-aminci’ ke tanadinsu. (Matta 24:45-47; Misalai 4:1, 2) Saboda haka, don su taimaka wa yaransu su kafa dangantaka mai kyau na dindindin da Jehobah, iyaye suna bukatar su ƙarfafa su su yi nazarin Kalmar Allah.
9. Ta yaya ne za a iya taimaka wa yara su soma yin nazari sosai?
9 Ta yaya ne za a iya taimaka wa yara su dinga yin nazari sosai? A nan ma, hanya mafi kyau da iyaye za su iya koya wa yaransu ita ce ta misali. Yaranku suna ganinku a kowane lokaci kuna jin daɗin karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki? Hakika, wataƙila kuna aiki tuƙuru don kula da yaranku, kuma kuna iya mamakin inda za ku sami lokacin yin karatu da kuma nazari. Amma, ku tambayi kanku, ‘Yarana suna ganina ina kallon talabijin a kowane lokaci?’ Idan haka ne, za ku iya yin amfani da wasu daga cikin wannan lokacin ku kafa masu misali mai kyau game da yin nazari?
10, 11. Me ya sa ya kamata iyaye su dinga yin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai?
10 Wata hanya mai kyau kuma da iyaye za su iya taimaka wa yaransu su saurari Jehobah ita ce su dinga yin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai. (Ishaya 30:21) Wasu suna iya cewa, ‘Me ya sa za a yi nazari na iyali da yara tun da iyayensu suna kai su taron ikilisiya a kowane lokaci?’ Akwai kyakkyawan dalilai masu yawa. Jehobah ya ba iyaye ainihin hakkin koyar da yaransu. (Misalai 1:8; Afisawa 6:4) Nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali yana koya wa yara cewa bauta ba abin da ake yi a fili ba ne ba kawai, amma sashe ne na rayuwar iyali.—Kubawar Shari’a 6:6-9.
11 Bugu da ƙari, nazari na iyali da aka yi da kyau zai iya ba iyaye damar sanin irin tunanin da yaransu suke yi game da batutuwa na ruhaniya da ɗabi’a. Alal misali, sa’ad da yara suke ƙanana, iyaye suna iya yin amfani da littattafai kamar Ka Koya Daga Wurin Babban Malami.a A yawancin sakin layin da ke cikin wannan littafin na yin nazarin Littafi Mai Tsarki, an tambayi yara su faɗi ra’ayinsu game da batutuwan da aka tattauna. Ta wajen tattauna nassosin da aka ambata a cikin littafin, iyaye za su iya taimaka wa yaransu su hora hankalinsu don su iya bambanta “nagarta da mugunta.”—Ibraniyawa 5:14.
12. Ta yaya ne iyaye za su daidaita nazari na iyali da bukatun yaransu, kuma menene ka gani ya dace game da wannan?
12 Yayin da yaranku suke girma, ku sa nazarin ya dace da bukatunsu. Ku lura da yadda wata mata da mijinta suka taimaka wa yaransu su yi tunani a kan damar da suke son a ba su don su halarci bikin rawa na makaranta. Uban ya ce: “Mun gaya wa yaranmu cewa a lokacin nazari na iyali na gaba, ni da matata za mu zama yara, kuma yaranmu mata su yi kamar su ne iyaye. Yaran su zaɓi wanda zai zama Uba da Uwa a tsakaninsu, amma yaran suna bukatar su yi aiki tare don su yi bincike a kan batun kuma su yi bayani game da rawa a makaranta.” Menene sakamakon? “Mun yi mamakin yadda yaranmu mata suka bambanta nagarta da mugunta (a gurbin da suka ɗauka na iyaye) sa’ad da suke bayyana mana (a matsayin yara) dalilan da suka samo daga cikin Littafi Mai Tsarki da ya sa bai dace ba a halarci rawan,” in ji uban. “Abin da ya ƙara burge mu shi ne shawarwarin da suka bayar na wasu abubuwa dabam da za a iya yi maimakon wannan. Hakan ya taimaka mana mu san tunaninsu da sha’awoyinsu.” Hakika, ana bukatar nacewa da kuma tunani don a ci gaba da yin nazari na iyali mai amfani, amma kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu.—Misalai 23:15.
Ku sa Yanayin Ya Kasance na Kwanciyar Hankali
13, 14. (a) Ta yaya ne iyaye za su iya sa kwanciyar hankali ta kasance a cikin gida? (b) Wane amfani ne za a iya samu sa’ad da iyaye suka yarda da kuskurensu?
13 Kibiya za ta iya samun abin da ake son a harba ne kawai idan iska ba ta kaɗawa. Hakazalika, yara za su iya koyan yadda za su ƙaunaci Jehobah ne kawai idan akwai kwanciyar hankali a gida. Yaƙub ya rubuta cewa: “Ana shibka ɗiyan adilci cikin salama domin masu-yin salama.” (Yaƙub 3:18) Ta yaya ne iyaye za su iya sa kwanciyar hankali ta kasance a cikin gida? Ma’aurata suna bukatar su kasance da dangantaka mai kyau sosai. Mata da mijin da suke ƙauna da kuma daraja juna, suna da dama mai kyau na koya wa yaransu su ƙaunaci wasu kuma su daraja su, har da Jehobah. (Galatiyawa 6:7; Afisawa 5:33) Ƙauna da daraja suna ɗaukaka salama. Ma’auratan da ke zaune lafiya da juna suna da dama mai kyau na magance matsalolin da za su iya tasowa a cikin iyalin.
14 Hakika, kamar yadda babu auren da ba shi da matsala, haka nan ma, babu iyalai a duniya a yanzu da ba su da matsala. A wasu lokatai, iyaye suna iya ƙin nuna halin ɗiyar ruhu sa’ad da suke ma’amala da yaransu. (Galatiyawa 5:22, 23) Idan hakan ya faru, menene ya kamata iyaye su yi? Idan iyaye suka yarda cewa sun yi kuskure, hakan zai rage darajar da yaran suke ba su ne? Yi la’akari da misalin Bulus. Shi kamar uba ne na ruhaniya ga mutane masu yawa. (1 Korinthiyawa 4:15) Duk da haka, ya amince cewa ya yi kurakurai. (Romawa 7:21-25) Muna daraja shi domin tawali’unsa da sahihancinsa. Duk da kurakuran da ya yi, da gaba gaɗi Bulus ya rubuta wannan wasiƙar ga ikilisiyar Koranti: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Korinthiyawa 11:1) Idan ku ma kuka yarda da kuskuren da kuka yi, yaranku za su iya gafarta maku.
15, 16. Me ya sa ya kamata iyaye su koyar da yaransu su ƙaunaci ’yan’uwansu Kiristoci maza da mata, kuma ta yaya za a iya yin haka?
15 Menene kuma iyaye za su iya yi don kwanciyar hankali ta kasance a inda yaransu za su yi girma su ƙaunaci Jehobah? Manzo Yohanna ya rubuta: “Idan wani ya ce, Ina ƙaunar Allah, shi kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne shi: domin wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yohanna 4:20, 21) Saboda haka, sa’ad da kuke koyar da yaranku su ƙaunaci ’yan’uwansu Kiristoci maza da mata, kuna koya masu ne su ƙaunaci Allah. Ya kamata iyaye su tambayi kansu, ‘Furcin da nike yawan yi game da ikilisiya yana ƙarfafawa ne ko kuwa marar kyau ne?’ Ta yaya za ku sani? Ku saurari abin da yaranku suke cewa sosai game da taro da kuma waɗanda suke cikin ikilisiya. Wataƙila za ku ji abubuwan da kuke cewa a furcinsu.
16 Menene iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaransu su ƙaunaci ’yan’uwansu na ruhaniya? Peter, wanda yake da yara maza biyu, ya ce: “Tun lokacin da yaranmu suke ƙanana, muna gayyato ƙwararrun Kiristoci a kowane lokaci su zo su ci abinci tare da mu kuma mu yi hira tare a gidanmu, kuma muna jin daɗin yin haka. Yaranmu sun girma suna tarayya da mutanen da suke ƙaunar Jehobah, kuma a yanzu sun ga cewa bauta wa Allah ita ce hanya mafi daɗi a rayuwa.” Dennis, wanda yake da yara mata guda biyar, ya ce, “Mun ƙarfafa yaranmu mata su zama ƙawayen tsofaffin majagaba da suke cikin ikilisiya, kuma a duk lokacin da ya yiwu muna nuna karimci ga masu kula masu ziyara da matansu.” Za ku iya taimaka wa yaranku su ɗauki ikilisiya a matsayin wata ɓangare na iyalinku?—Markus 10:29, 30.
Hakkin Yaro
17. Wace shawara ce yara za su yanke wa kansu?
17 Ku sake yin la’akari da misalin maharbin. Ko da yake ƙwararre ne, yana iya ƙin samun abin da yake son ya harba idan kibiyoyin sun riga sun banƙare. Hakika, iyaye za su yi iya ƙoƙarinsu su miƙar da kibiyar da ta banƙare a alamance, ta wajen daidaita tunani marar kyau na yaro. Amma, yara ne za su yanke wa kansu shawarar ko za su yarda wannan duniyar ta banƙarar da su su yi nufinta ko kuwa za su bari Jehobah ‘ya daidaita hanyoyinsu.’—Misalai 3:5, 6; Romawa 12:2.
18. Ta yaya ne abin da yaro ya zaɓa zai iya shafan wasu?
18 Ko da yake iyaye suna da hakki mai girma na yin renon yaransu a “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa,” irin mutumin da zai zama a nan gaba ya rage a hannun yaron. (Afisawa 6:4) Saboda haka, yara ku tambayi kanku: ‘Zan amince da koyarwa mai kyau da iyaye na suke yi mini?’ Idan kuka yi haka, za ku zaɓi hanya mafi kyau a rayuwa. Za ku sa iyayenku su yi farin ciki. Mafi muhimmanci, za ku faranta wa Jehobah rai.—Misalai 27:11.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Ka Tuna?
• Ta yaya ne iyaye za su iya kafa misali mai kyau game da addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki?
• Ta yaya ne iyaye za su iya sa kwanciyar hankali ta kasance a cikin gida?
• Wane irin zaɓi ne yara za su iya yi, kuma ta yaya ne zaɓin da suka yi zai iya shafan wasu?
[Hoto a shafi na 28]
Kuna kafa wa yaranku misali mai kyau game da nazari na kai?
[Hoto a shafi na 29]
Idan akwai kwanciyar hankali a cikin iyali hakan zai daɗa farin ciki