Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
“Abin da ku ke yi duka, da ƙauna a yi shi.”—1 KORINTHIYAWA 16:14.
1. Yaya ne iyaye suke ji sa’ad da suka haihu?
YAWANCIN mutane za su yarda cewa haihuwa tana cikin abubuwa masu kawo farin ciki. “Sa’ad da na kalli jaririyata, na yi farin ciki ƙwarai da gaske,” in ji wata uwa mai suna Aleah. “Na ɗauka cewa ita ce jaririya mafi kyau da na taɓa gani.” Irin wannan yanayi na farin ciki yana iya jawo damuwa ga wasu iyaye. “Damuwa na,” in ji mijin Aleah, “shi ne ko zan iya shirya ɗiyata don ta iya magance matsalolin da za su iya tasowa a rayuwa.” Yawancin iyaye suna da irin wannan damuwar kuma sun fahimci cewa suna bukatar su koyar da yaransu cikin ƙauna. Amma, iyaye Kiristoci da suke son su koyar da yaransu cikin ƙauna suna fuskantar ƙalubale. Menene wasunsu?
2. Waɗanne ƙalubale ne iyaye suke fuskanta?
2 A yanzu muna zaune ne a ƙarshen wannan zamanin. Kamar yadda aka annabta, rashin ƙauna ta cika ko’ina. Har ma a cikin iyali, mutane sun zama “marasa-ƙauna irin ta tabi’a,” kuma sun zama “marasa-godiya, marasa-tsarki, . . . marasa-kamewa, masu-zafin hali.” (2 Timothawus 3:1-5) Haɗuwa da mutanen da suke nuna irin waɗannan halayen a kullum yana iya shafan yadda iyalan Kirista suke bi da juna. Bugu da ƙari, iyaye suna yin kokawa da ajizancin da suka gada na nuna rashin kamewa, faɗin abin da bai dace ba ba da sane ba, da kuma yanke shawarar da bai dace ba a wasu hanyoyi.—Romawa 3:23; Yaƙub 3:2, 8, 9.
3. Ta yaya ne iyaye za su iya renon yara masu farin ciki?
3 Duk da waɗannan ƙalubalen, iyaye suna iya yin renon yara masu farin ciki kuma masu ruhaniya. Ta yaya? Ta wajen bin shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Abin da ku ke yi duka, da ƙauna a yi shi.” (1 Korinthiyawa 16:14) Hakika, ƙauna “ce magamin kamalta.” (Kolossiyawa 3:14) Bari mu bincika sashe uku na ƙauna da manzo Bulus ya kwatanta a cikin wasiƙarsa ta farko ga Korinthiyawa kuma mu tattauna wasu hanyoyi na musamman da iyaye za su iya yin amfani da wannan halin yayin da suke renon yaransu.—1 Korinthiyawa 13:4-8.
Iyaye Suna Bukatar Su Kasance Masu Haƙuri
4. Me ya sa iyaye suke bukatar su kasance masu haƙuri?
4 Bulus ya rubuta: “Ƙauna tana da yawan haƙuri.” (1 Korinthiyawa 13:4) Furcin nan na Helenanci da aka fassara “yawan haƙuri” yana nufin ƙin yin fushi da wuri. Me ya sa iyaye suke bukatar su kasance masu haƙuri? Babu shakka, yawancin iyaye za su yi tunanin dalilai masu yawa. Ga kaɗan daga ciki. Da wuya yara su roƙi abin da suke so sau ɗaya kawai. Ko da iyayen sun ce a’a, yaron yana iya ci gaba da roƙonsu ko zai yi nasara. Matasa suna iya ba da dalilai masu yawa don a ƙyale su su ɗauki matakin da iyayen suka san cewa wawanci ne. (Misalai 22:15) Kuma kamar dukanmu, yara suna maimaita kurakuran da suka yi.—Zabura 130:3.
5. Menene zai iya taimaka wa iyaye su kasance masu haƙuri?
5 Menene zai taimaka wa iyaye su kasance masu haƙuri da yaransu? Sarki Sulemanu ya rubuta: “Hankalin mutum ya kan sa fushinsa shi yi jinkiri.” (Misalai 19:11) Iyaye za su iya fahimtar halin yaransu idan suka tuna cewa a dā su ma sun taɓa ‘yin magana ta ƙuruciya, ji kamar mai-ƙuruciya, da kuma tunani na ƙuruciya.’ (1 Korinthiyawa 13:11) Iyaye, kun tuna lokacin da kuka dami mama ko babanku don ya ko ta amince da roƙon da kuka yi na yarinta? Sa’ad da kuke matasa, kun taɓa tunanin cewa iyayenku ba su san yadda kuke ji ba? Idan haka ne, ya kamata ku fahimci dalilin da ya sa yaranku suke nuna irin wannan halin, da kuma dalilin da ya sa kuke bukatar ku yi haƙuri sa’ad da kuke tunasar da su a kai a kai game da shawarwarin da kuka yanke. (Kolossiyawa 4:6) Yana da muhimmanci ku lura cewa Jehobah ya gaya wa iyaye Isra’ilawa su “koya ma” yaransu dokokinsa. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Kalmar Ibrananci da aka fassara “koya ma” tana nufin “maimaitawa a kai a kai,” da kuma “cusawa.” Wannan yana nufin cewa wataƙila iyaye suna bukatar su ci gaba da maimaita abin da suke so kafin yaron ya koyi yadda zai yi amfani da dokokin Allah. Ana kuma bukatar a yi amfani da irin wannan maimaitawar don a koyar da wasu darussa a rayuwa.
6. Me ya sa iyaye masu haƙuri ba masu ƙyaliya ba ne?
6 Amma fa, iyaye masu haƙuri ba masu barin a yi abin da Allah ba ya so ba ne. Kalmar Allah ta yi gargaɗi: “Yaro wanda an ƙyale shi za ya jawo ma uwatasa kumya.” Don a guje wa irin wannan aukuwar, littafin misalai ya ce: “Sanda da tsautawa suna bada hikima.” (Misalai 29:15) A wasu lokatai, yara suna iya tunanin cewa iyayensu ba su da ikon horonta su. Amma, iyalan Kirista ba mulkin dimokuraɗiyya ba ce, inda za a ce yaran ne suke da ikon amincewa da dokokin da iyayensu suka kafa. Maimakon haka, Jehobah, Wanda shi ne Shugaban iyali, ya ba iyaye ikon koyar da kuma horanta yaransu a cikin ƙauna. (1 Korinthiyawa 11:3; Afisawa 3:15; 6:1-4) Hakika, horo yana da nasaba na kud da kud da sashe na gaba na ƙauna da Bulus ya ambata.
Yadda Za a Yi Horo Cikin Ƙauna
7. Me ya sa iyaye masu kirki za su yi wa yaransu horo, kuma menene wannan horon ya ƙunsa?
7 Bulus ya rubuta cewa “ƙauna tana da . . . nasiha [ko kirki].” (1 Korinthiyawa 13:4) Iyayen da suke da kirki sosai za su dinga horanta yaransu yadda ya kamata. Suna koyi da Jehobah idan suka yi hakan. Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Wanda Ubangiji ke ƙauna shi ya ke horo.” Don Allah ku lura cewa irin horon da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki ba ya nufin hukunci kawai. Yana nufin koyarwa da kuma ilimantarwa. Menene manufar wannan horon? “Ya kan bada amfani mai-salama-watau na adalci ke nan-ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa,” in ji Bulus. (Ibraniyawa 12:6, 11) Sa’ad da iyaye suka ilimantar da yaransu kamar yadda Allah ya nufa, suna ba su damar zama mutane masu lumana da adalci. Idan yara suka yi na’am da “koyaswar Ubangiji,” za su sami hikima, sani, da fahimi, abubuwan da suka fi azurfa da zinari tamani.—Misalai 3:11-18.
8. Menene ke faruwa a yawancin lokaci sa’ad da iyaye suka ƙi yi wa yaransu horo?
8 A wani ɓangare kuma, rashin ƙauna ce idan iyaye suka ƙi yi wa yaransu horo. Jehobah ya hura Sulemanu ya rubuta: “Wanda ya sauƙaƙa bulalatasa yana ƙin ɗansa ke nan: Amma wanda ya ƙaunace shi ya kan fore shi da anniya.” (Misalai 13:24) Yaran da aka yi renonsu ba tare da horo ba za su iya zama masu son kai kuma marar farin ciki. Akasin haka, an ga cewa yaran da iyayensu ke da tausayi amma masu manne wa abin da suka ce suna yin ƙoƙari sosai a makaranta, sun san yadda ake bi da mutane, kuma suna yin farin ciki. Hakika, iyayen da suke horon yaransu suna nuna masu ne cewa suna ƙaunarsu da gaske.
9. Menene iyaye Kiristoci suke koya wa yaransu, kuma ya ya kamata a ɗauki waɗannan bukatun?
9 Menene yi wa yara horo cikin nasiha da ƙauna ya ƙunsa? Iyaye suna bukatar su tattauna da yaransu ainihin abin da suke bukata daga gare su. Alal misali, tun suna ƙanana ake koya wa yaran da iyayensu Kiristoci ne muhimman mizanai na Littafi Mai Tsarki da kuma bukatar saka hannu a duka fasaloli na bauta ta gaskiya. (Fitowa 20:12-17; Matta 22:37-40; 28:19; Ibraniyawa 10:24, 25) Yara suna bukatar su san cewa waɗannan bukatun ba sa canjawa.
10, 11. Me ya sa iyaye za su iya yin la’akari da abubuwan da yaransu suke so sa’ad suke kafa dokoki a gida?
10 A wasu lokatai, iyaye za su so su tuntuɓi yaransu sa’ad da suke son su kafa dokoki a gida. Idan aka tattauna waɗannan dokokin da yaran, hakan zai iya motsa su su yi biyayya. Alal misali, idan iyaye suna son su kafa dokar hana fitar dare, suna iya zaɓan daidai lokacin da suke son yaransu su dawo gida. Ko kuwa, suna iya ƙyale yaransu su ba da shawarar lokacin da za su dawo gida kuma su faɗi dalilan zaɓan lokacin. Bayan haka, iyayen suna iya faɗin lokacin da suke son yaran su dawo gida kuma su bayyana dalilin da ya sa suka ga cewa hakan ya dace. Menene iyaye za su yi idan ra’ayi ya bambanta? A wasu yanayin, iyaye suna iya yanke shawarar bin ra’ayin yaransu idan hakan bai karya mizanan Allah ba. Wannan yana nufin cewa iyaye sun kasa yin amfani da ikonsu ne?
11 Don a amsa wannan tambayar, yi la’akari da hanyar da Jehobah ya yi amfani da ikonsa cikin ƙauna sa’ad da yake ma’amala da Lutu da iyalinsa. Bayan sun fitar da Lutu, matarsa, da yaransa mata daga Saduma, mala’ikun sun gaya masu: ‘Ku tsira zuwa dutse, domin kada ku hallaka.’ Amma, Lutu ya ce: “Ai, ba haka ba, ya ubangijina.” Sai Lutu ya ba da wata shawarar dabam: “Ga shi, wannan birni kusa ne, in gudu gareshi, ƙanƙane ne kuwa: Ai! ka bari in yi can in tsira, (ba ƙanƙane ba ne?)” Menene Jehobah ya ce? “Ga shi, na amsa maka a kan wannan abu kuma,” in ji shi. (Farawa 19:17-22) Jehobah ya kasa nuna ikonsa ne? A’a! Amma, ya saurari roƙon Lutu kuma ya zaɓi ya nuna masa alheri. Idan ku iyaye ne, akwai lokatan da kuke yin la’akari da abubuwan da yaranku suke so sa’ad da kuke kafa doka a cikin iyali?
12. Menene zai taimaka wa yara su sami kwanciyar hankali?
12 Hakika, yara suna bukatar su san dokoki da kuma sakamakon karya su. Yayin da aka tattauna sakamakon kuma aka fahimce su, ana bukatar a bi dokokin. Iyaye ba za su kyauta ba idan suka ci gaba da yi wa yaransu gargaɗi game da wani horon da ya kamata su yi masu amma suka ƙi. “Saboda ba a aika shari’a da aka hukunta a bisa mugunta da sauri ba, shi ya sa zuciyar ’yan adam ta kan ji ƙarfin aika mugunta,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Mai-Wa’azi 8:11) Hakika, iyaye suna iya ƙin horanta yaro a fili ko kuwa a gaban abokansa, don kada ya ji kunya. Amma, yara sun fi samun kwanciyar hankali kuma suna ƙara daraja da ƙaunar iyayensu idan suka san cewa “I” ɗin iyayensu shi ne i, kuma “A’a” a’a, ko da hakan ya ƙunshi horo.—Matta 5:37.
13, 14. Ta yaya ne iyaye za su iya yin koyi da Jehobah sa’ad da suke koyar da yaransu?
13 Idan horon zai kasance na ƙauna, ya kamata ya dace da yaron. “Yaranmu biyu suna da bukatu dabam dabam idan ya zo ga horo,” in ji Pam. “Abin da ya dace da wannan ba zai dace da wancan ba.” Maigidanta, Larry, ya ce: “Babbar ɗiyarmu tana da taurin kai sosai kuma tana jin magana ne kawai idan aka horanta ta sosai. Amma, ɗiyarmu ƙarama tana jin faɗan baki sosai har da kallon ido.” Hakika, iyaye masu kirki suna iya ƙoƙarinsu su fahimci horon da ya fi dacewa da yaransu ɗaɗɗaya.
14 Jehobah ya kafa wa iyaye misali domin ya san ƙarfi da kumamancin duka bayinsa. (Ibraniyawa 4:13) Bugu da ƙari, sa’ad da yake yin horo, Jehobah ba ya tsanantawa sosai kuma ba ya ƙyaliya. Maimakon haka, Jehobah yana horanta mutanensa “yadda ya kamata.” (Irmiya 30:11;NW) Iyaye, kun san ƙarfi da kumamancin yaranku? Kuna yin amfani da wannan sanin a hanyar da ta dace don ku koyar da su? Idan haka ne, kuna nuna cewa kuna ƙaunar yaranku.
Ku Taimaka wa Yaranku Su Dinga Gaya Maku Gaskiya
15, 16. Ta yaya ne iyaye za su iya ƙarfafa yaransu su faɗi gaskiya, kuma wace irin dabara ce iyaye Kiristoci suka ga cewa ta fi dacewa?
15 Wani sashen kuma na ƙauna shi ne “ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya.” (1 Korinthiyawa 13:6) Ta yaya ne iyaye za su iya koya wa yaransu su ƙaunaci abin da ke da kyau da kuma gaskiya? Mataki mai muhimmanci shi ne su ƙarfafa yaransu su faɗi yadda suke ji, ko da iyayen ba za su so su yarda da abin da yaran suka ce ba. Babu shakka, iyaye suna yin farin ciki sa’ad da yaransu suka faɗi abubuwan da suka jitu da mizanai na gaskiya. A wasu lokatai kuwa, abin da yaro ya faɗa yana iya bayyana tunaninsa na yin abin da bai da kyau. (Farawa 8:21) Menene ya kamata iyaye su yi? Matakin da za su so su fara ɗauka shi ne su horanta yaransu nan da nan domin sun faɗi irin wannan maganar. Idan iyaye suka ɗauki irin wannan matakin, yaran suna iya soma gaya wa iyayen abin da suke son su ji kawai. Ko da yake ya kamata a daidaita furci marar kyau nan da nan, amma akwai bambanci tsakanin koyar da yara yadda za su yi magana da tarbiyya da kuma gaya masu abin da za su faɗa.
16 Ta yaya ne iyaye za su iya ƙarfafa faɗin gaskiya? Aleah, da muka ambata ɗazu ta ce: “Mun kafa yanayi na tattaunawa da juna ta wajen guje wa saurin yin fushi sa’ad da yaranmu suka gaya mana abin da zai ba mu haushi.” Wani uba mai suna Tom ya ce: “Mun ƙarfafa ɗiyarmu ta gaya mana abin da ke zuciyarta, har ma a lokacin da ba ta yarda da namu ra’ayin ba. Mun ga cewa idan muna katse ta a duk lokacin da take magana kuma muka cusa mata ra’ayinmu, za ta ji haushi kuma za ta daina gaya mana abin da ke zuciyarta. Mun ga cewa sauraron abin da take cewa yana motsa ta ta saurare mu.” Hakika, yara suna bukatar su yi biyayya ga iyayensu. (Misalai 6:20) Amma, tattaunawa yana ba iyaye damar taimaka wa yaransu su iya yin tunani. Vincent, wanda yake da yara huɗu, ya ce: “A yawancin lokaci, muna yin magana a kan amfani da rashin amfanin wasu abubuwa domin yaranmu su ga abin da ya fi kyau da kansu. Hakan ya taimaka masu su iya yin tunani sosai.”—Misalai 1:1-4.
17. Wane tabbaci ne ya kamata iyaye su kasance da shi?
17 Hakika, babu iyayen da za su iya yin amfani sarai da shawarar renon yara da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, ku tabbata cewa yaranku za su nuna godiya ƙwarai da gaske game da ƙoƙarin da kuka yi na koyar da su cikin haƙuri, nasiha, da kuma ƙauna. Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenku na yin haka. (Misalai 3:33) Gabaki ɗaya, duka iyaye Kiristoci suna son yaransu su ƙaunaci Jehobah kamar yadda su ma suke yi. Ta yaya ne iyaye za su iya cim ma wannan makasudi mai muhimmanci? A talifi na gaba za a tattauna wasu hanyoyi na musamman.
Ka Tuna?
• Ta yaya nuna fahimi zai taimaka wa iyaye su kasance masu haƙuri?
• Ta yaya ne kirki da horo suke da nasaba?
• Me ya sa tattaunawa tsakanin yara da iyayensu yake da muhimmanci?
[Hotuna a shafi na 23]
Iyaye, za ku iya tuna abin da yaranta ke nufi?
[Hoto a shafi na 24]
Kuna ƙarfafa yaranku su gaya maku gaskiya?