Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/15 pp. 19-23
  • Iyaye Da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyaye Da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU KEƁE LOKACI DON TATTAUNAWA
  • KU “YI HANZARIN JI”
  • KU “YI JINKIRIN YIN MAGANA”
  • KU “YI JINKIRIN YIN FUSHI”
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • ’Ya’yanmu —Kyauta Ne Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/15 pp. 19-23

Iyaye Da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna

“Kowane mutum ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana, ya yi jinkirin yin fushi.”—YAƘ. 1:19.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa keɓe lokaci don tattaunawa yake da muhimmanci?

  • Ta yaya iyaye za su iya yin amfani da littafin Yaƙub 1:19?

  • Ta yaya yara za su iya yin amfani da littafin Yaƙub 1:19?

1, 2. Yaya iyaye da yara suke ɗaukan juna, kuma wane ƙalubale ne suke fuskanta a wasu lokatai?

AN YI wa yara da yawa a ƙasar Amirka tambayar da ke gaba: “Mene ne za ka so gaya wa iyayenka a yau, idan ka samu labari cewa za su mutu gobe?” Sai yawancinsu suka ce ba za su so su faɗi matsalolinsu ko kuma wata matsalar da suka samu da iyayensu ba, maimakon haka, za su ce musu: “Ku yi haƙuri” da kuma “Ina ƙaunarku sosai.”—Daga littafin nan, For Parents Only, wanda Shaunti Feldhahn da Lisa Rice suka rubuta.

2 Hakika, yara da iyaye suna ƙaunar juna, musamman ma idan su Kiristoci ne. Ko da yake iyaye da yara suna son su kusaci juna, amma tattaunawa yana musu wuya a wasu lokatai. Me ya sa hakan yake faruwa? Me ya sa yake wa iyaye da yara wuya su tattauna game da wasu batutuwa? Mene ne iyaye da yara za su yi don su kyautata yadda suke tattaunawa da juna?

KU KEƁE LOKACI DON TATTAUNAWA

3. (a) Me ya sa yake wa iyalai da yawa wuya su tattauna da juna sosai? (b) Me ya sa ya yi wa iyalai a Isra’ila sauƙi su tattauna da juna?

3 Yana yi wa iyalai da yawa wuya su keɓe lokaci don su riƙa tattaunawa da juna. Amma, ba haka yake a zamanin Isra’ilawa ba. Musa ya ce wa iyaye Isra’ilawa: “Za ka koya wa ’ya’yanka [Kalmar Allah] su da anniya, za ka riƙa faɗinsu sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” (K. Sha 6:6, 7) Yara sukan kasance da mahaifiyarsu a gida ko kuma da mahaifinsu a gona ko wajen aiki. Iyaye suna da isashen lokacin tattaunawa tare da yaransu. Hakan ya sa ya yi wa iyaye sauƙi su san bukatu da sha’awoyi da kuma halayen yaransu. Kuma yara ma sun samu zarafin sanin iyayensu sosai.

4. Me ya sa tattaunawa yake yi wa iyalai da yawa wuya a yau?

4 Rayuwa a yau ta bambanta! A wasu ƙasashe, yara sukan soma makaranta sa’ad da suke ƙanana, a wasu lokatai ma sa’ad da suke ’yan shekara biyu kawai. Iyaye da yawa suna aiki a wurare masu nisa. Kuma sa’ad da iyaye da yara suka dawo gida, sai kallon talabijin ko yin amfani da kwamfuta ko kuma waya ta raba hankalinsu. A cikin iyalai da yawa, iyaye da yara ba su san juna ba sosai. Da kyar suke tattaunawa da juna.

5, 6. Mene ne wasu iyaye suka yi don su samu lokacin kasancewa tare da yaransu?

5 Shin za ka iya keɓe lokaci don ka riƙa kasancewa tare da iyalinka? (Karanta Afisawa 5:15, 16.) Wasu iyalai sun yarda su rage kallon talabijin ko kuma yin amfani da kwamfuta. Wasu kuma sun yi ƙoƙari su riƙa cin abinci tare ko da sau ɗaya ne a kowace rana. Bauta ta iyali zarafi ne mai kyau da zai sa iyaye da yara su san juna sosai, kuma su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Amma, ba a wannan lokacin kaɗai ba ne ya kamata iyalai su kasance tare. Wajibi ne su keɓe lokaci don tattaunawa a kowace rana. Kafin yaranku su tafi makaranta, ya dace ku ɗan faɗi abin da zai ƙarfafa su ko kuma ku tattauna nassin yini ko yi addu’a tare. Yin hakan zai taimaka musu sosai.

6 Wasu iyaye sun yi canje-canje a salon rayuwarsu don su samu lokacin tattaunawa da yaransu. Alal misali, wata mai suna Lauraa da ke da yara biyu, ta yi murabus da aikinta don ta samu lokacin tattaunawa da su. Ta ce: “Da safiya, dukanmu mukan yi shiri da wuri don mu tafi aiki ko kuma makaranta. Sa’ad da na dawo da yamma kuma, sai dai in ga cewa mai reno ta riga ta sa yaran barci. Ko da yake ba ma samun kuɗi sosai don na yi murabus da aikina, amma yanzu na fi sanin halaye da kuma matsalolin yarana. Ina jin abin da suke faɗa sa’ad da suke addu’a don in ja-gorance su da ƙarfafa su da kuma koyar da su.”

KU “YI HANZARIN JI”

7. Wace mafificiyar matsala ce iyaye da yara suke da shi?

7 Bayan wata ganawa da aka yi da matasa da yawa, marubutan littafin nan For Parents Only sun ƙara faɗin abin da yake hana tattaunawa a cikin iyali. Sun ce: “Mafificiyar matsalar yaran game da iyayensu ita ce, ‘Ba sa saurarar mu.’” Abin da iyaye ma suka faɗa game da yaransu ke nan. Idan iyalai suna son su riƙa tattaunawa sosai, wajibi ne su saurari juna da kyau.—Karanta Yaƙub 1:19.

8. Ta yaya iyaye za su saurari yaransu da kyau?

8 Iyaye, shin kuna saurarar yaranku kuwa? Hakan zai iya yin wuya idan kun gaji ko kuma abin da za ku tattauna bai da muhimmanci sosai a gare ku. Amma, abin da kuka ga kamar bai da muhimmanci zai iya zama da muhimmanci a wurin yaranku. Mai “hanzarin ji” yana mai da hankali sosai ga abin da yaransa suke faɗa da kuma yadda suke faɗinsa. Muryar yaronka da kuma yadda yake yi sa’ad da yake gaya maka wani abu zai nuna maka yadda yake ji. Yin tambaya ma yana da muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shawara a cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai-zurfi, amma mutum mai-fahimi za ya jawo ta.” (Mis. 20:5) Kana bukatar basira da kuma fahimi idan kana son ka san yadda yaranka suke ji, musamman ma sa’ad da kuke tattauna wani batun da suke jin kunya ko tsoron faɗa.

9. Me ya sa ya kamata yara su saurari iyayensu?

9 Yara, shin kuna yi wa iyayenku biyayya? Kalmar Allah ta ce: “Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yar da ita.” (Mis. 1:8) Ku tuna cewa, iyayenku suna ƙaunar ku kuma sun damu da ku, shi ya sa yake da muhimmanci ku saurare su kuma ku yi musu biyayya. (Afis. 6:1) Yin biyayya yana da sauƙi idan kuna tattaunawa sosai da iyayenku, kuma idan kuka tuna cewa suna ƙaunarku. Ku gaya wa iyayenku yadda kuke ji, kuma hakan zai sa su fahimce ku. Hakika, ku ma ya kamata ku fahimce su.

10. Mene ne muka koya daga labarin Yerobowam?

10 Ya kamata ku mai da hankali da irin shawarar da kuke karɓa daga matasa tsararku. Kuna iya ji kamar shawararsu ta dace, amma wataƙila ba za ta taimaka muku ba ko kaɗan. Har ila za ta iya jawo muku illa. Matasa ba su da hikima da kuma wayon da tsofaffi suke da shi. Yawancin matasa ba sa tunanin irin illar da shawararsu za ta jawo musu a nan gaba. Ku tuna da misalin Jeroboam, ɗan Sarki Sulemanu. Sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, sai ya bi mummunar shawarar matasa tsararsa, maimakon ya bi na maza tsofaffi. A sakamako, mutane da yawa suka yi tawaye da mulkinsa. (1 Sar. 12:1-17) Kada ku yi koyi da Jeroboam. Amma, ku yi ƙoƙarin tattauna matsalolinku da kuma yadda kuke ji tare da iyayenku. Ku bi shawararsu kuma ku yi koyi da hikimarsu.—Mis. 13:20.

11. Mene ne zai iya faruwa idan yara suna jin kunya ko tsoron tattaunawa da iyayensu?

11 Iyaye, idan kuna so yaranku su karɓi shawararku maimakon na tsararsu, ya kamata ku saki jiki da su don ya yi musu sauƙin tattaunawa da ku. Wata ’yar’uwa matashiya ta ce: “Iyayena suna damuwa sosai duk sa’ad da na yi magana game da namiji. Kuma hakan yana sa in daina maganar.” Wata ’yar’uwa matashiya kuma ta ce: “Matasa da yawa suna son shawarar iyayensu. Amma, idan iyayen ba su ɗauki yaransu da muhimmanci ba, za su nemi shawara a wurin wasu dabam, har ma a wurin marasa hikima.” Idan kuna saurarar duk batutuwan da yaranku suke da su, ba za su ji kunya ko kuma tsoron tattauna matsalolinsu da ku ba, kuma za su riƙa bin shawararku.

KU “YI JINKIRIN YIN MAGANA”

12. Mene ne zai iya sa yara su yi jinkirin tattaunawa da iyayensu?

12 Yadda iyaye suke aikatawa zai iya yi wa yaransu wuya su riƙa tattaunawa da su. Iyaye za su iya fusata nan da nan game da abin da yaransu suka faɗa. Hakika, iyaye Kiristoci suna son su kāre yaransu domin miyagun abubuwa suna faruwa a waɗannan “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1-5) Amma, ba a kowane lokaci ba ne yara suke da ra’ayi ɗaya da iyayensu game da wani abu ba, kuma za su iya ji kamar iyayensu suna matsa musu.

13. Me ya sa ya kamata iyaye su yi hankali don kada su faɗi ra’ayinsu da garaje?

13 Ya kamata iyaye su yi hankali don kada su faɗi ra’ayinsu da garaje. Hakika, yana da wuya iyaye su yi shuru sa’ad da yaransu suka faɗi abin da ya ɓata wa iyayen rai. Amma, yana da muhimmanci ku saurara da kyau kafin ku faɗi wani abu. Sarki Sulemanu ya ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gareshi da kunya.” (Mis. 18:13) Idan kun kwantar da hankalinku kuka saurara, yaranku za su ci gaba da magana. Kafin ku iya taimaka musu, ya dace ku ƙyale su su gaya muku dukan abin da ya faru. Za ku iya fahimtar abin da ya sa ɗanku ya yi “magana da rashin hankali.” (Ayu. 6:1-3) A matsayin iyaye masu ƙauna, ku saurara don ku fahimci yaranku kuma ku faɗi abin da zai taimaka musu.

14. Me ya sa yara suke bukatar su yi jinkirin yin magana?

14 Yara, ku ma kuna bukatar ku “yi jinkirin yin magana.” Ku tuna cewa Allah ya ba iyayenku hakkin renonku, saboda haka, kada ku yi saurin ƙi da abin da suka faɗa muku. (Mis. 22:6) Mai yiwuwa, sun taɓa fuskantar irin matsalolin da kuke ciki a yanzu. Wataƙila, sun yi nadama don kurakuran da suka yi sa’ad da suke matasa, kuma ba za su so ku ma ku yi irin kuskuren da suka yi ba. Iyayenku abokanku ne ba magabtanku ba. Suna son su taimaka muku, ba raunana ku ba. (Karanta Misalai 1:5.) “Ka girmama ubanka da uwarka,” kuma ka nuna musu cewa kana ƙaunarsu kamar yadda suke ƙaunarka. Hakan zai sa ya kasance da sauƙi su “goye ka cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.”—Afis. 6:2, 4.

KU “YI JINKIRIN YIN FUSHI”

15. Mene ne zai taimaka mana mu riƙa haƙuri da iyalinmu?

15 Ba a koyaushe muke haƙuri da mutanen da muke ƙauna ba. A wasiƙar manzo Bulus ga Kiristocin da ke Kolosi, ya ce: “Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali. Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa ’ya’yanku, domin kada su karai.” (Kol. 1:1, 2; 3:19, 21) Bulus ya gaya wa Afisawa cewa: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gare ku.” (Afis. 4:31) Idan muka nuna fannoni dabam-dabam na ’yar ruhun Allah kamar su tsawon jimrewa da nasiha da kuma kamewa, zai yi mana sauƙi mu kasance da haƙuri har ma a yanayi mai wuya.—Gal. 5:22, 23.

16. Ta yaya Yesu ya yi wa almajiransa gyara, kuma me ya sa hakan yake da ban al’ajabi?

16 Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ka yi tunani a kan irin gajiyar da ya yi, bayan sun kammala jibin maraice da ya ci da almajiransa. Yesu ya san cewa ba da daɗewa ba, zai sha azaba sosai kafin ya mutu. Idan ya kasance da aminci, zai ɗaukaka sunan Ubansa, kuma zai ceci ’yan Adam. Amma, a wannan daren ne ‘gardama ta tashi a tsakaninsu [manzanninsa], ko wanene aka maishe shi babba a cikinsu.’ Yesu bai yi musu tsawa da kuma fushi ba. Maimakon haka, ya yi musu gyara cikin haƙuri. Ya tuna musu cewa sun goyi bayansa a mawuyanci lokaci. Ya nuna musu yana da gaba gaɗi cewa za su kasance da aminci ko da Shaiɗan zai gwada su. Kuma ya yi musu alkawari cewa, za su zama sarakuna tare da shi a sama.—Luk 22:24-32.

17. Mene ne zai taimaki yara su natsu?

17 Yara ma suna bukatar su natsu. Musamman ma sa’ad da suke balaga, za su iya ji kamar ja-gorar iyayensu ba zai taimaka musu ba. Za ku iya yin tunani cewa ba su yarda da ku ba. Amma, ku tuna cewa iyayenku suna damuwa da ku domin suna ƙaunarku. Idan kuka saurare su kuma kuka bi ja-gorarsu, za su daraja ku kuma su yarda da ku. Iyayenku kuma za su daɗa ba ku ’yancin yin wasu abubuwa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutum mai natsuwa yana da hikima. Ya ce: “Wawa ya kan furta dukan fushinsa, amma mai-hikima ya kan danne shi ya kwaɓe shi.”—Mis. 29:11.

18. Ta yaya ƙauna za ta taimaka wa iyalai su riƙa tattaunawa da kyau?

18 Iyaye da yara, kada ku yi sanyin gwiwa idan ba ku tattaunawa yadda kuke so. Ku ci gaba da ƙoƙartawa da kuma bin umurnin da ke cikin Kalmar Allah. (3 Yoh. 4) A sabuwar duniya, za mu zama kamiltattu kuma ba za mu samu matsala a yadda muke tattaunawa ba. Amma kafin lokacin, za mu ci gaba da yin kuskure. Saboda haka, kada ku yi jinkirin ba da haƙuri da kuma gafarta wa juna. Kuma ku “zama haɗaɗu cikin ƙauna.” (Kol. 2:2) Ƙauna za ta taimaka muku sosai. Domin ‘ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha. Ba ta jin cakuna. Ba ta yin nukura. Tana jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka.’ (1 Kor. 13:4-7) Za ku kyautata yadda kuke tattaunawa a cikin iyalinku, idan kuka ci gaba da ƙaunar juna. Hakan zai sa iyalinku farin ciki kuma ya ɗaukaka Jehobah.

a An canja sunan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba