’Ya’yanmu —Kyauta Ne Mai Tamani
“ ’Ya’ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, albarka ce ta musamman.”—ZABURA 127:3.
1. Ta yaya aka kai ga haifan ɗan mutum na farko?
KA YI la’akari da aikin mu’ujiza da Jehobah Allah ya yi sa’ad da ya halicci mata da miji na farko. Baba, Adamu, da mama, Hauwa’u, suka ba da gudummawa daga jikinsu da ya girma a cikin Hauwa’u ya zama sabon mutum—ɗan mutum na farko. (Farawa 4:1) Har wa yau, ɗaukan ciki da kuma haifar yaro suna ba mu mamaki har waɗansu suka ce mu’ujiza ne.
2. Me ya sa za ka ce abin da yake faruwa a cikin mace mai ciki mu’ujiza ce?
2 A cikin kwanaki 270, ƙwayar halitta da ke cikin uwar saboda saduwa da ta yi da uban ta girma ta zama jariri da ƙwayoyin halitta biliyoyi. A cikin wannan ƙwayar ta farko da umurnai da take bukata domin ta ba da wasu ƙwayoyi iri dabam dabam har 200. Bayan waɗannan umurnai masu ban sha’awa da suka fi gaban fahimtar mutum, waɗannan ƙwayoyin masu wuyar ganewa suke girma a daidai bisa tsari da kuma hanyar da ta dace domin su zama sabon mutum rayayye!
3. Me ya sa mutane da yawa masu tunani suka yarda cewa Allah ne ke halittar jariri?
3 Waye za ka ce ainihi ya halicci jaririn? Hakika Wanda ya halicci rai tun farko ne. Mai zabura na Littafi Mai Tsarki ya rera waƙa a Zabura 100:3: “Kada fa a manta cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne.” Iyaye, kun dai sani cewa ba domin basirar ku ne kuka haifi jariri ba. Allah ne kawai mai hikima marar iyaka zai iya halittar sabon mutum rayayye. Cikin shekaru aru-aru da suka shige mutane masu tunani sun ce Mahalicci ne ya halicci yaro a cikin uwarsa. Kai ma ra’ayinka ke nan?—Zabura 139:13-16.
4. Wane laifi na mutane ne ba za a taɓa ɗora wa Jehobah ba?
4 To, Jehobah Mahalicci ne kawai marar ƙauna wanda ya kafa hanyar da mata da maza za su riƙa haifan ’ya’ya? Wasu mutane ba su da ƙauna amma Jehobah ba haka yake ba. (Zabura 78:38-40) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana a Zabura 127:3: “ ’Ya’ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, albarka ce ta musamman.” Bari yanzu mu bincika abin da ake nufi da kyauta, da kuma abin da take tabbatarwa.
Kyauta da Kuma Albarka
5. Me ya sa ’ya’ya kyauta ce?
5 Kyauta bayarwa ce. Iyaye suna ba da himma ƙwarai domin su bar wani abu ga ’ya’yansu. Yana iya zama kuɗi, kayayyaki, ko kuma wataƙila wani abu mai tamani da aka mallaka. Ko yaya dai, ya nuna ƙauna ta iyaye. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya ba wa iyaye ’ya’yansu kyauta. ’Ya’yan kyauta ne domin ƙaunarsa. Idan kana da ’ya’ya, za ka iya cewa abin da kake yi yana nuna cewa kana ɗaukan ’ya’yanka tamkar kyautar da Mahaliccin kome da kowa ya yi maka?
6. Menene nufin Allah na ƙyale mutane su sami ’ya’ya?
6 Manufar wannan kyauta da Jehobah ya bayar domin duniya ta cika ne da ’ya’yan Adamu da Hauwa’u. (Farawa 1:27, 28; Ishaya 45:18) Jehobah bai halicci kowane mutum ɗaiɗai kamar yadda ya halicci mala’iku ba. (Zabura 104:4; Wahayin Yahaya 4:11) Maimakon haka, Allah ya zaɓi ya halicci mutum da iya haihuwa domin ya haifi ’ya’ya da za su yi kama da shi a hanyoyi da za a iya ganewa. Wannan gāta ce mai ban sha’awa ga iyaye maza da mata su haifa kuma su kula da waɗannan sababbin mutane! Iyaye, kuna yi wa Jehobah godiya kuwa da ya sa ya yiwu muku ku more wannan kyautar mai tamani?
Ku Koya Daga Misalin Yesu
7. Akasarin wasu iyaye, ta yaya Yesu ya nuna ƙauna da juyayi ga “ ’yan adam”?
7 Abin baƙin ciki, ba dukan iyaye ba ne suke ɗaukan ’ya’ya albarka. Da yawa ba sa nuna juyayi ga ’ya’yansu. Irin waɗannan iyaye ba sa nuna irin hali na Jehobah da kuma Ɗansa. (Zabura 27:10; Ishaya 49:15) Akasarin wasu iyaye, ka yi la’akari da yadda Yesu yake ƙaunar yara. Kafin ma Yesu ya zama mutum ya zo duniya—sa’ad da yake halittar ruhu mai iko a samaniya—Littafi Mai Tsarki ya ce yana “murna da ’yan adam.” (Karin Magana 8:31) Ƙauna da yake yi wa ’yan adam tana da ƙarfi da ta sa ya ba da ransa fansa da son ransa domin mu sami rai madawwami.—Matiyu 20:28; Yahaya 10:18.
8. Ta yaya Yesu ya kafa misali mai kyau ga iyaye?
8 Sa’ad da yake duniya, Yesu ya kafa misali na musamman ga iyaye. Ka yi la’akari da abin da ya yi. Ya ba da lokaci ga yara, har a lokacin da ma yake da aiki mai yawa kuma yake fama da matsi. Ya lura da su sa’ad da suke wasa a kasuwa kuma ya yi amfani da halinsu wajen koyarwarsa. (Matiyu 11:16, 17) A tafiyarsa ta ƙarshe zuwa Urushalima, Yesu ya sani cewa zai wahala kuma za a kashe shi. Sa’ad da mutane suka kawo masa yara su gan shi, almajiran Yesu suka yi ƙoƙarin su hana yaran zuwa wataƙila domin suna kāre Yesu daga ƙarin matsi. Amma Yesu ya gargaɗi almajiransa. Wajen nuna ‘murnarsa’ da waɗannan yara, ya ce: “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su.”—Markus 10:13, 14.
9. Me ya sa abin da muka yi zai fi ma abin da muka ce muhimmanci?
9 Muna iya yin koyi da misalin Yesu. Sa’ad da yara suka zo gare mu, yaya muke yi—har a sa’ad da muke fama da aiki? Kamar yadda Yesu ya yi? Abin da yara suke bukata, musamman daga wurin iyayensu, shi ne Yesu ya ba su—lokaci da kuma kula. Hakika, irin waɗannan kalmomi kamarsu “ina ƙaunarka” suna da muhimmanci. Duk da haka, aikatawa ya fi maganar baki. Ƙaunarka za ta bayyana ba daga abin da ka ce ba kawai amma fiye da haka ta abin da kake yi. Tana bayyana daga lokaci, kula da kuma so da kake nuna wa ’ya’yanka. Yin wannan duka, ba zai ba da abin da kake bukata ba, musamman ma da sauri kamar yadda kake bukata. Ana bukatar haƙuri. Za mu koyi haƙuri idan muka yi koyi da yadda Yesu ya bi da almajiransa.
Haƙuri da Ƙauna na Yesu
10. Ta yaya Yesu ya koyar da almajiransa darassi na tawali’u, ya yi nasara ne da farko?
10 Yesu yana sane da gasa ta ɗaukaka da take tsakanin almajiransa. Wata rana bayan ya iso Kafarnahum da almajiransa, ya yi tambaya: “Muhawarar me kuka yi a hanya?” Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wanene babbansu.” Maimakon ya tsawata musu, Yesu cikin haƙuri ya koya musu tawali’u da kwatanci. (Markus 9:33-37) Sun mai da hankali ne ga abin da ya koyar? Ba nan take ba. Bayan kamar wata shida, Yakubu da Yahaya suka sa mamarsu ta roƙar musu matsayi masu girma a Mulkinsa. A nan ma Yesu ya yi musu gyara cikin haƙuri.—Matiyu 20:20-28.
11. (a) Wane aiki ne na al’ada manzannin Yesu suka ƙi su yi bayan sun isa ɗaki na bene tare da Yesu? (b) Menene Yesu ya yi, kuma ya yi nasara kuwa a wannan lokaci?
11 Ba da daɗewa ba lokacin bikin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z., ya yi, kuma Yesu da manzanninsa suka taru su kaɗai. Da suka iso ɗakin bene, babu ɗaya cikin manzanni 12 da yake so ya wanke ƙafafu masu ƙura na wasu—aikin bawa ko kuwa mace a gida. (1 Sama’ila 25:41; 1 Timoti 5:10) Lalle zai dami Yesu ƙwarai ya ga almajiransa sun ci gaba da nuna cewa suna bukatar matsayi! Saboda haka Yesu ya wanke ƙafafunsu da ɗai ɗai kuma ya aririce su su bi misalinsa na yi wa wasu hidima. (Yahaya 13:4-17) Sun yi haka ne? Littafi Mai Tsarki ya ce bayan an jima kaɗan “sai musu ya tashi tsakaninsu a kan kowanene babbansu.”—Luka 22:24.
12. Ta yaya iyaye za su yi koyi da Yesu a ƙoƙarin su yi tarbiyyar da ’ya’yansu?
12 Sa’ad da yaranku suka ƙi bin gargaɗinku, iyaye kuna fahimtar yadda Yesu ya ji kuwa? Ku lura cewa Yesu bai daina ƙoƙari ba ya taimaki manzanninsa ko da yake ba sa ɗaukan gyara da sauri. Wannan haƙuri a ƙarshe ya cim ma burinsa. (1 Yahaya 3:14, 18) Iyaye, ku yi ƙoƙari ku yi koyi da ƙauna da kuma haƙuri na Yesu, kada ku daina ƙoƙarin tarbiyyar da ’ya’yanku.
13. Me ya sa bai kamata iyaye su kori yaro da yake da tambaya ba?
13 Yara suna bukatar su fahimci cewa iyayensu suna ƙaunarsu kuma sunan son su. Yesu yana so ya san abin da almajiransa suke tunani a kai, saboda haka yana sauraransu sa’ad da suke da tambaya. Yana tambayarsu ra’ayinsu game da wasu batutuwa. (Matiyu 17:25-27) Hakika, koyarwa mai kyau ya haɗa da sauraro da kyau. Bai kamata iyaye su kori yaro da yake da tambaya ba su yi masa tsawa: “Tafi ka ba ni wuri! Ba ka ga ina aiki ba ne?” Idan da gaske iyayen suna aiki, su gaya wa yaron za su tattauna batun an jima. Kuma iyayen su tabbata an tattauna batun. A wannan hanyar yaron zai fahimci cewa iyayensa da gaske suna ƙaunarsa, kuma ba zai yi masa wuya ya yi magana da iyayensa ba.
14. Menene iyaye za su koya daga wurin Yesu game da nuna ƙauna ga yara?
14 Daidai ne iyaye su nuna ƙaunarsu ta wajen ɗora wa ’ya’yansu hannu suna kuma rungumarsu? A nan, iyaye za su iya koya daga wurin Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce “ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.” (Markus 10:16) Me kake tsammani yaran suka yi? Hakika sun yi farin ciki, kuma sun matsa kusa da Yesu! Idan da ƙauna ta gaskiya tsakaninku iyaye da ’ya’yanku ƙanƙanana, za su bi horon da kuke musu babu wuya.
Batun Yawan Lokaci
15, 16. Menene ya kawo ra’ayi da ya samu karɓuwa game da renon yara?
15 Wasu suna shakkar ko da gaske yara suna bukatar lokaci mai yawa daga iyayensu da kuma kula. Wani ra’ayi game da reno da aka yaɗa cikin basira ana kiransa kyakkyawan lokaci. Masu irin wannan ra’ayin sun yi da’awar cewa yara ba sa bukatar lokaci mai yawa daga iyayensu idan ɗan lokaci da suka kasance da su mai ma’ana ne, wanda aka shirya aka tsara. Wannan ra’ayin kyakkyawan lokaci yana da kyau kuwa, an kirkiro shi ne da tunanin kyautata wa yara?
16 Wani marubuci da ya yi magana da yara da yawa ya ce “abin da suke bukata matuƙa daga wurin iyayensu shi ne lokaci,” tare da “kula sosai.” Wani shehun malami ya lura cewa: “Wannan furcin [kyakkyawan lokaci] an samo shi ne domin iyaye sun fahimci cewa ba sa cika hakkinsu. Iyaye suna ba wa kansu izinin su ba da ɗan lokaci ga ’ya’yansu.” Yaya yawan lokaci da iyaye ya kamata su ba wa ’ya’yansu?
17. Menene yara suke bukata daga iyayensu?
17 Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Amma, an aririci iyaye Yahudawa su yi magana da ’ya’yansu sa’ad da suke gida, sa’ad da suke tafiya a hanya, sa’ad da suka kwanta, da kuma sa’ad da suka tashi. (Maimaitawar Shari’a 6:7) Wannan ya nuna cewa iyaye suna bukatar su riƙa hulɗa kowace rana da ’ya’yansu suna koya musu a kai a kai kowace rana.
18. Ta yaya Yesu ya yi amfani da dukan zarafi domin ya koyar da almajiransa, kuma menene iyaye za su iya koya daga wannan?
18 Yesu ya yi nasara wajen koyar da almajiransa sa’ad da yake cin abinci tare da su, sa’ad da suke tafiya tare har da sa’ad da suke hutawa. Saboda haka ya yi amfani da dukan zarafi domin ya koya musu. (Markus 6:31, 32; Luka 8:1; 22:14) Haka nan, ya kamata iyaye Kiristoci su riƙa kula, su yi amfani da dukan zarafi su kafa sadawa mai kyau da ’ya’yansu domin su tarbiyyar da su cikin tafarkin Jehobah.
Abin da Za a Koyar da Kuma Yadda Za a Koyar
19. (a) Me ake bukata ƙari ga ba da lokaci ga yara? (b) Menene iyaye suke bukatar su koya wa ’ya’yansu?
19 Kashe lokaci tare da yara har ma da koya musu ba shi kenan ba ga renonsu cikin nasara. Wani abu mai muhimmanci, shi ne abin da za a koyar. Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya nanata da ya kamata a koyar. “Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau,” ya ce , “sai ku koya wa ’ya’yanku.” Menene “waɗannan kalmomi” da ake bukata a koya wa yara? Hakika, sune kalmomin da aka faɗa kafin wannan, wato: “Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.” (Maimaitawar Shari’a 6:5-7) Yesu ya ce wannan ita ce doka mai muhimmanci a dukan umurnan Allah. (Markus 12:28-30) Ainihi iyaye suna bukatar su koya wa ’ya’yansu game da Jehobah, suna yi musu bayanin abin da ya sa shi ne kawai ya cancanci ƙaunarmu da dukan zuciya da bauta.
20. Menene Allah ya umurci iyaye na dā su koya wa ’ya’yansu?
20 Bugu da ƙari, “waɗannan kalmomi” da aka aririci iyaye su koya wa ’ya’yansu ya ƙunshi fiye da kawai su ƙaunaci Allah da dukan ransu. A sura na baya na Maimaitawar Shari’a, za ka lura cewa Musa ya sake maimaita dokokin da Allah ya rubuta a kan allunan dutse—Dokoki Goma. Waɗannan dokoki sun ƙunshi umurni irinsu, kada ka yi ƙarya, kada ka yi sata, kada ka yi kisa, da kuma kada ka yi zina. (Maimaitawar Shari’a 5:11-22) Saboda haka an tabbatar wa iyaye na zamanin bukatar tarbiyyar da ’ya’yansu ɗabi’a mai kyau. Iyaye Kiristoci suna bukatar su yi wa ’ya’yansu irin wannan tanadin umurni idan suna so su taimake su su yi farin ciki a nan gaba a rayuwarsu.
21. Menene Allah yake nufi da umurnan nan a “koya” wa yara umurnansa?
21 Ka lura an gaya wa iyaye yadda za su koyar da “waɗannan kalmomi,” ko umurnai ga ’ya’yansu: “Ku koya wa ’ya’yanku su da himma.” Kalmar nan “koya” tana nufin “sa a haddace abu ta wajen maimaitawa, ƙarfafawa ko riƙewa a zuciya.” Wato Allah yana gaya wa iyaye ne su tsara tsarin koyar da Littafi Mai Tsarki da nufin cusa batutuwa na ruhaniya a zukatan ’ya’yansu.
22. Menene aka gaya wa iyaye Isra’ilawa su yi don su koyar da ’ya’yansu, kuma menene wannan yake nufi?
22 Irin wannan tsarin koyarwa yana bukatar himmar iyaye. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za ku ɗaura su [“waɗannan kalmomi,” ko dokokin Allah] a hannunku da goshinku don alama. Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.” (Maimaitawar Shari’a 6:8, 9) Wannan ba ya nufin cewa iyaye su rubuta dokokin Allah a zahiri a ƙofofinsu, ko su ɗaura a hannun ’ya’yansu, kuma su ɗaura ɗaya a goshinsu. Maimakon haka, abin da ake nufi a nan shi ne cewa ya kamata iyaye su riƙa tuna wa ’ya’yansu koyarwar Allah. Ya kamata su riƙa yin irin wannan koyarwar a kai a kai, a hanyar da kamar koyarwar Allah tana goshin su ne a dukan lokaci.
23. Menene za a tattauna a darasi na mako mai zuwa?
23 Waɗanne abubuwa ne na musamman iyaye suke bukata su koyar da ’ya’yansu? Me ya sa yake da muhimmanci a yau a koyar a kuma tarbiyyar da yara domin su kāre kansu? Waɗanne taimako iyaye za su iya samu domin su koyar da ’ya’yansu da kyau? Wannan da kuma wasu tambayoyi da suke damun iyaye za a tattauna su a talifi na gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa ya kamata iyaye su ɗauki ’ya’yansu da tamani?
• Menene iyaye da wasu za su koya daga Yesu?
• Yaya yawan lokaci da iyaye za su ba wa ’ya’yansu?
• Menene ya kamata a koya wa ’ya’ya kuma yaya za a koyar?
[Hoto a shafi na 22]
Menene iyaye za su koya a hanyar koyarwar Yesu?
[Hotuna a shafi na 23]
Yaushe kuma a wace hanya iyaye Isra’ilawa za su koyar da ’ya’yansu?
[Hotuna a shafi na 24]
Ya kamata iyaye su ɗaura koyarwar Allah a goshin ’ya’yansu