Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 7/1 pp. 8-13
  • Iyaye Ku Biya Bukatun Iyalinku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyaye Ku Biya Bukatun Iyalinku
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tanadin Abin Biyan Bukata
  • Tanadi na Ruhaniya
  • Tanadi don Sosuwar Zuciya
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • ’Ya’yanmu —Kyauta Ne Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 7/1 pp. 8-13

Iyaye Ku Biya Bukatun Iyalinku

“Duk wanda bai kula da . . . iyalinsa ba, . . . ya mūsa wa bangaskiya ke nan.”—1 TIMOTI 5:8.

1, 2. (a) Me ya sa abin ƙarfafawa ne a ga iyalai suna halartar taron Kirista tare? (b) Waɗanne abubuwa ne iyalai ke fuskanta don su je taro da wuri?

IDAN ka duba ikilisiyar Kirista kafin a soma taro, za ka ga yara masu tsabta da suka yi ado da kyau suna zaune kusa da iyayensu. Ba abin ban sha’awa ba ne a ga iyalai suna nuna irin wannan ƙaunar—ƙaunar Jehobah da kuma juna? Amma da sauƙi a manta cewa ana bukatar ƙoƙari sosai don iyalai su zo taro a kan lokaci.

2 A yawancin lokaci, iyaye suna da ayyuka da yawa kuma iyalai sun fi shagala a ranar taro. Za a dafa abinci, a yi aikace-aikace na gida, da kuma aikin makaranta da za a yi a gida. Iyaye suna da hakki mai girma, za su tabbata cewa kowa ya yi wanka, ya ci abinci kuma ya shirya a kan lokaci. Hakika, wasu matsaloli sukan taso daga yaran a lokacin da bai dace ba. Babban cikinsu yana iya yaga kayansa sa’ad da yake wasa. Autan kuma ya zubar da abincinsa. Yaran suna iya soma ka-ce-na-ce. (Karin Magana 22:15) Menene sakamakon? Ko da iyayen sun yi shiri da kyau, shirin ba zai kasance yadda suke so ba. Duk da haka, kusan koyaushe iyalin tana Majami’ar Mulki kafin a soma taron. Abin ƙarfafa ne ana ganinsu a taro kowane mako, a dukan shekara yayin da yaran suke girma suna bauta wa Jehobah!

3. Yaya muka sani cewa Jehobah yana daraja iyalai sosai?

3 Ko da yake aikin iyaye yana da wuya wani lokaci, yana gajiyarwa ma, ku tabbata cewa Jehobah yana yaba wa ƙoƙarinku. Jehobah ne ya kafa tsarin iyali. Shi ya sa Kalmarsa ta ce kowace iyali ta sami “suna,” wato, ta kasance daga Jehobah. (Afisawa 3:14, 15) Saboda haka, sa’ad da ku iyaye kuke ƙoƙarin ku cika hakkinku yadda ya dace, kuna ɗaukaka Ubangiji Mamallakin sararin samaniya. (1 Korantiyawa 10:31) Wannan ba gata ba ce mai girma? Saboda haka, ya dace mu yi la’akari da aikin da Jehobah ya ba wa iyaye. A wannan talifin za mu yi magana game da yi wa iyali tanadi. Bari mu maimaita hanyoyi uku da Allah yake son iyaye su yi wa iyalinsu tanadi.

Tanadin Abin Biyan Bukata

4. Wane shiri ne na biyan bukatun yara Jehobah ya yi a cikin iyali?

4 Manzo Bulus ya rubuta: “Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.” (1 Timoti 5:8) Wanene Bulus yake maganarsa sa’ad da ya ce “duk wanda”? Shugaban iyali ne, wato uba. Allah ya kuma ba mata hakki da ya dace, ta zama mataimakiyar mijinta. (Farawa 2:18) A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki mata sau da yawa na taimakon mazansu wajen yi wa iyali tanadi. (Karin Magana 31:13, 14, 16) A yau iyalan iyaye gwauraye suna daɗa ƙaruwa.a Iyaye Kiristoci gwauraye da yawa suna ƙoƙari sosai wajen yi wa iyalinsu tanadi. Hakika, ya fi kyau iyali ta kasance tana da uwa da uba, kuma uban yana shugabanci.

5, 6. (a) Waɗanne ƙalubale ne waɗanda suke wa iyalinsu tanadi suke fuskanta? (b) Kasancewa da wane ra’ayi ne game da aiki zai taimaki Kiristoci masu yin tanadi su nace?

5 Wane irin tanadi ne Bulus yake maganarsa a 1 Timoti 5:8? Mahallin ya nuna cewa yana magana kai tsaye ne game da bukatun rayuwa na iyali. A duniyar yau, da akwai tangarɗa da yawa da shugaban iyali zai fuskanta domin ya biya bukatun iyalinsa. Wahalar tattalin arziki tana ko’ina a duniya, kora daga aiki, ƙaruwar rashin aiki, da tsadar abubuwa. Menene zai taimaki mai yin tanadi ya nace sa’ad da yake fuskantar irin waɗannan ƙalubale?

6 Yana da kyau mai yin tanadi ya tuna cewa yana aikin da Jehobah ya ba shi. Hurarrun kalmomin Bulus sun nuna cewa mutumin da ya ƙi bin wannan umurnin ko da zai iya yin haka, ya yi daidai da wanda ya “mūsa wa bangaskiya.” Kirista zai yi iyakar ƙoƙarinsa ya kaucewa kasancewa hakan a gaban Allahnsa. Abin baƙin ciki, mutane da yawa a duniyar yau “marasa ƙauna” ne. (2 Timoti 3:1, 3) Hakika, ubanni da yawa suna guje wa hakkinsu, ba sa taimaka wa iyalansu. Magidanta Kiristoci ba sa irin wannan mugun hali na guje yi wa iyalansu tanadi. Ba kamar abokan aikinsu da yawa ba, Kiristoci suna iya ɗaukan ƙananan ayyuka da daraja da kuma muhimmanci, ta haka suna faranta wa Jehobah rai, tun da aikin na taimakon su wajen biyan bukatun waɗanda suke ƙauna.

7. Me ya sa ya dace iyaye su yi bimbini a kan misalin Yesu?

7 Shugaban iyali zai sami taimako ta wajen bimbini a kan misalin Yesu. Ka tuna, Littafi Mai Tsarki cikin annabci ya kira Yesu “Uba Madawwami.” (Ishaya 9:6, 7) Da yake Yesu ne “Adamun ƙarshe” ya sake “Mutumin farko, Adamu” sai ya zama uban waɗanda suka ba da gaskiya. (1 Korantiyawa 15:45) Ba kamar Adamu wanda ya zama uba mai son kai ba, Yesu ne uba da ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi: “Yadda muka san ƙauna ke nan, wato ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu.” (1 Yahaya 3:16) Hakika, Yesu da son rai ya ba da ransa don mutane. Kullum yana sa bukatun wasu gaba da nasa. Yana da kyau iyaye su yi koyi da wannan halin sadaukarwa.

8, 9. (a) Menene iyaye za su iya koya daga tsuntsaye game da yi wa yaransu tanadi da rashin son kai? (b) Ta yaya iyaye Kiristoci da yawa suke nuna halin sadaukar da kai?

8 Iyaye za su iya koyan abubuwa da yawa game da ƙauna marar son kai daga kalmomin Yesu ga mutanen Allah masu taurin kai: “Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza ke tattara ’yan tsakinta cikin fikafikanta.” (Matiyu 23:37) A nan Yesu yana kwatanta kaza da take tattara ’yan tsakinta cikin fukafukinta. Hakika, iyaye suna iya koyan abubuwa da yawa daga yadda kaza take tsare ’yan tsakinta, tana sa kanta cikin haɗari don kada wani abu ya same su. Ganin abubuwa da tsuntsaye suke yi kullum abin mamaki ne. Suna kaiwa-da-kawowa wajen neman abinci ba fasawa. Ko ma sun gaji ainun, suna saka abincin a bakin ’yan tsakin, su kuma su cinye suna neman ƙari. Halittun Jehobah da yawa suna da “hikima ƙwarai” a yadda suke kula da bukatun ’ya’yansu.—Karin Magana 30:24.

9 Hakanan ma, iyaye Kiristoci a dukan duniya suna nuna halin sadaukarwa. Za ku so ku wahalar da kanku maimakon wani abu ya sami yaranku. Ƙari ga haka, kuna sadaukarwa kullum da son rai domin ku yi wa iyalinku tanadi. Da yawa cikinku kuna tashi da sassafe ku yi ayyuka masu wuya ko masu gajiyarwa. Kuna aiki tuƙuru domin ku samo wa iyalinku abinci masu gina jiki. Kuna ƙoƙari domin ku tabbata cewa yaranku suna da tufa masu tsabta, wurin kwanciya da ya dace, su kuma sami kyakkyawan ilimi. Kuna waɗannan abubuwa kullum kowace shekara. Babu shakka, irin wannan sadaukarwa da jimiri na faranta wa Jehobah rai! (Ibraniyawa 13:16) Ko da kuna dukan waɗannan abubuwa, ku tuna cewa da hanyoyi mafi muhimmanci da za ku yi wa iyalinku tanadi.

Tanadi na Ruhaniya

10, 11. Menene bukatar ’yan adam da ta fi muhimmanci, kuma menene abu na farko da dole iyaye Kiristoci su yi domin su biya wa yaransu wannan bukata?

10 Tanadi na ruhaniya ya fi tanadin abubuwan biyan bukata muhimmanci. Yesu ya ce: “Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace maganar da ke fitowa daga wurin Allah.” (Matiyu 4:4; 5:3) Iyaye menene za ku iya yi don ku yi tanadi na ruhaniya?

11 Maimaitawar Shari’a 6:5-7 ne ayoyi na Nassosi da ake amfani da su sau da yawa a kan wannan batu. Don Allah ka buɗe naka Littafi Mai Tsarki ka karanta waɗannan ayoyi. Ka lura cewa na farko an gaya wa iyaye su ƙarfafa nasu ruhaniya, su ƙaunaci Jehobah kuma su bi kalmominsa. Hakika, kuna bukatar ku zama masu nazarin Kalmar Allah sosai, kuna karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuna bimbini a kai domin ku fahimci kuma ku ƙaunace hanyoyin Jehobah, da kuma ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ta haka, za ku san gaskiyar Littafi Mai Tsarki mai ban sha’awa da zai motsa ku ku yi murna, ku daraja Jehobah kuma ku ƙaunace shi. Za ku san abubuwa masu kyau da yawa da za ku koya wa yaranku.—Luka 6:45.

12. Ta yaya iyaye za su yi koyi da misalin Yesu sa’ad da suke koya wa yaransu gaskiyar Littafi Mai Tsarki?

12 Iyaye masu ruhaniya sosai suna shirye su yi amfani da gargaɗin da ke Maimaitawar Shari’a 6:7, su “koya” wa yaransu kalmomin Jehobah a kowane zarafi. A ‘koyar’ na nufin a sahinta ta wurin maimaitawa. Jehobah ya san cewa dukanmu —musamman yara—na bukatar maimaitawa domin su koya. Shi ya sa Yesu ya maimaita abubuwan da ya koyar a hidimarsa. Alal misali, sa’ad da yake koyar da almajiransa su kasance masu tawali’u maimakon masu fahariya da gasa, ya nemi hanyoyi dabam dabam don ya maimaita wannan ƙa’ida. Ya koyar ta wurin sa mutane su yi tunani, ya yi kwatanci, ya ma nuna misali. (Matiyu 18:1-4; 20:25-27; Yahaya 13:12-15) Abin ban sha’awa shi ne cewa Yesu mai haƙuri ne sosai. Hakanan ma, iyaye suna bukatar su nemi hanyoyi da za su koya wa yaransu muhimman gaskiya, suna maimaita ƙa’idodin Jehobah cikin haƙuri har sai yaran sun fahimta kuma su yi amfani da abin da aka koya musu.

13, 14. Waɗanne lokatai ne iyaye za su iya koya wa yaransu gaskiyar Littafi Mai Tsarki, waɗanne abubuwan ban taimako za su yi amfani da su?

13 Lokacin nazari na iyali ne ya dace a yi irin wannan koyarwa. Hakika, abu na musamman da ke sa iyali ta kasance da ruhaniya kuma ta yi farin ciki, shi ne nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali mai ban ƙarfafa a kai a kai. Iyalan Kirista a dukan duniya suna farin ciki da irin wannan nazari, suna amfani da littattafai da ƙungiyar Jehobah ke tanadinsu kuma suna gudanar da nazarin yadda zai biya bukatun yaransu. Littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami da kuma Questions Young People Ask—Answers That Work,b kyauta ce na musamman wajen koyar da yara. Amma ba a lokacin nazari na iyali ba ne kaɗai ake koyar da yara.

14 Yadda Maimaitawar Shari’a 6:7 ta nuna, da lokatai da yawa da iyaye za su tattauna abubuwa na ruhaniya da yaransu. Ko kuna tafiya tare, kuna aiki tare, ko kuna hutawa tare, ku nemi zarafi ku biya bukatun ruhaniya na yaranku. Hakika, ba za ku riƙa yi wa yaranku “lacca” ba koyaushe game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Maimakon haka, ku yi ƙoƙari ku sa taɗinku na iyali ya zama da ban ƙarfafa a kan abubuwa na ruhaniya. Alal misali, jaridar Awake! na ɗauke da talifofi a kan batutuwa dabam dabam. Irin waɗannan talifofi game da halittun dabbobi na Jehobah, wurare masu kyau a duniya, da al’adu na ’yan adam dabam dabam da kuma yadda suke rayuwa za su iya zama abin taɗi. Irin wannan taɗin zai iya motsa yara su riƙa karanta littattafan da rukunin amintaccen bawan nan mai hikima ke tanadinsu.—Matiyu 24:45-47.

15. Ta yaya iyaye za su taimaki yaransu su fahimci cewa hidimar Kirista aiki ne mai kyau da ke kawo albarka?

15 Yin taɗi mai ban ƙarfafa da yaranku zai taimake ku ku biya wata bukata ta ruhaniya. Yara Kirista suna bukatar su koyi yadda za su gaya wa mutane game da bangaskiyarsu da kyau. Yayin da kuke magana game da abubuwa da kuka ji daɗin karantawa a Hasumiyar Tsaro ko Awake! ku nemi zarafi ku nuna nasabar batun da wa’azi. Alal misali, kuna iya tambaya: “Kana ganin zai yi kyau idan mutane suka san wannan game da Jehobah? Yaya kake tsammani za mu sa mutum ya so wannan batun?” Irin wannan taɗi zai iya taimakon yara su so su gaya wa wasu abin da suka koya. Idan yaranku suka bi ku wa’azi, za su ga misalin yin amfani da irin wannan taɗi. Za su koyi cewa hidima aiki ne mai kyau da ke kawo farin ciki, yana kawo gamsuwa da albarka.—Ayyukan Manzanni 20:35.

16. Menene yara za su koya ta sauraron addu’ar iyayensu?

16 Iyaye suna biyan bukatun ruhaniya na yaransu sa’ad da suke addu’a. Yesu ya koya wa almajiransa yadda ake addu’a, kuma ya yi addu’a da su a lokatai da yawa. (Luka 11:1-13) Babu shakka, sun koyi abubuwa da yawa ta wajen addu’a tare da Ɗan Jehobah! Hakanan ma, yaranku za su koyi abubuwa da yawa daga addu’o’inku. Alal misali, za su koyi cewa Jehobah yana son mu yi masa magana daga zuciyarmu, mu gaya masa dukan damuwarmu. Hakika, addu’o’inku za su taimaki yaranku su koyi muhimmiyar gaskiya na ruhaniya cewa: Zai yiwu su sami dangantaka da Ubansu na samaniya.—1 Bitrus 5:7.

Tanadi don Sosuwar Zuciya

17, 18. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimmancin ƙaunar yara? (b) Ta yaya ubanni za su yi koyi da Jehobah wajen faɗan suna ƙaunar yaransu?

17 Hakika, yara suna da bukatu masu muhimmanci na sosuwar zuciya. Kalmar Allah ta gaya wa iyaye yadda yake da muhimmanci a biya wannan bukata. Alal misali, an gargaɗi mata masu ƙuruciya su ‘so ’ya’yansu.’ Yin hakan yana da nasaba da sa mata masu ƙuruciya su yi hankali. (Titus 2:4) Hakika yana da kyau a ƙaunaci yaro. Wannan na koya wa yaro ya nuna ƙauna kuma yana kawo fa’idodi na dindindin. A wata sassa, ƙin nuna wa yaro ƙauna wauta ce. Yana kawo baƙin ciki kuma yana nuna ƙin yin koyi da Jehobah, wanda yake ƙaunarmu duk da ajizancinmu.—Zabura 103:8-14.

18 Jehobah ne ma ya soma ƙaunar yaransa na duniya. Yadda 1 Yahaya 4:19 ta ce, “shi ne ya fara ƙaunarmu.” Ya kamata ku ubanni musamman ku yi koyi da misalin Jehobah, ku fara ƙaunar yaranku. Littafi Mai Tsarki ya aririce ubanni kada su ƙuntata wa yaransu, “domin kada su karai.” (Kolosiyawa 3:21) Sanin cewa mahaifi ba ya ƙaunarsu ko kuma daraja su ya fi ƙuntata wa yara. Yana da kyau ubanni da ba sa son nuna yadda suke ji su tuna da misalin Jehobah. Jehobah har ya yi magana daga sama don ya furta amincewarsa da kuma ƙaunarsa ga Ɗansa. (Matiyu 3:17; 17:5) Babu shakka, wannan ya ƙarfafa Yesu! Hakanan ma, yara suna samun ƙarfafa da gabagaɗi idan iyayensu sun furta ƙaunarsu da kuma amincewarsu na gaske.

19. Me ya sa horo yake da muhimmanci, wane irin daidaitawa iyaye Kirista suke ƙoƙari su yi?

19 Hakika, iyaye ba sa nuna ƙaunarsu ga yaransu ta maganar baki kawai. Ana nuna ƙauna musamman ta ayyuka. Iyaye suna nuna suna ƙaunar yaransu ta yin tanadin abubuwan biyan bukata da kuma na ruhaniya, musamman idan iyaye suna hakan a hanyar da ta nuna cewa ƙauna ce ainihi ta motsa su. Ƙari ga haka, iyaye suna ƙaunar yaransu idan suna musu horo. Hakika, “Ubangiji, wanda yake ƙauna, shi yake horo.” (Ibraniyawa 12:6) A wata sassa kuma, iyaye ba sa ƙaunar yaransu idan ba sa yi musu horo! (Karin Magana 13:24) Jehobah koyaushe yana hukunta mutum “yadda ya kamata.” (Irmiya 46:28) Daidaitawa ba koyaushe yake wa iyaye ajizai sauƙi ba. Duk da haka, kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Dagewa wajen yin horo cikin ƙauna na taimakon yaro ya yi girma ya yi rayuwa mai kyau. (Karin Magana 22:6) Ba irin rayuwa da kowane iyaye Kirista yake son ɗansa ya yi ba ke nan?

20. Ta yaya iyaye za su ba yaransu zarafi su “zaɓi rai”?

20 Sa’ad da iyaye suka yi aiki mai muhimmanci da Jehobah ya ba su, wato, yi wa yaransu tanadin abubuwan biyan bukata, na ruhaniya, da bukatu don sosuwar zuciya—suna samun albarka mai yawa. Ta haka kuna ba yaranku zarafin da ya fi kyau su “zaɓi rai” kuma bayan haka su “rayu.” (Maimaitawar Shari’a 30:19) Yaran da suka zaɓi su bauta wa Jehobah kuma suka kasance a hanyar rai sa’ad da suke girma suna sa iyayensu farin ciki matuƙa. (Zabura 127:3-5) Irin wannan farin ciki zai kasance har abada! Amma ta yaya matasa za su yabi Jehobah yanzu? Talifi na gaba zai yi magana a kan wannan batun.

[Hasiya]

a A wannan talifin, mai tanadin zai zama namiji. Amma ƙa’idodin ya shafi mata Kirista waɗanda suke da hakkin yin tanadi.

b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

Yaya Za Ka Amsa?

Menene iyaye za su yi don su yi wa yaransu tanadi

• na abin biyan bukata?

• na ruhaniya?

• don sosuwar zuciya?

[Hoto a shafi na 8]

Tsuntsaye da yawa suna aiki tuƙuru su ciyar da ’ya’yansu

[Hoto a shafi na 10]

Dole iyaye su fara ƙarfafa nasu ruhaniya

[Hotuna a shafuffuka na 10, 11]

Iyaye za su nemi zarafi da yawa su koya wa yaransu game da Mahalicci

[Hoto a shafi na 12]

Yara suna ƙarfafa kuma suna kasancewa da gaba gaɗi idan iyayensu sun amince da su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba