Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 10/1 pp. 8-12
  • Ta Yaya Za Mu Nuna Jin Ƙai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Mu Nuna Jin Ƙai?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Idan Wani Ɗan’uwa Yana Tsiraici’
  • “Idan Kuna Tara”
  • “Hikima Mai Fitowa Daga Bisa . . . [Tana] Cike da Jinƙai”
  • Ka “Gafarta ma Mutane Laifofinsu”
  • Ka Yi “Nagarta Zuwa ga Dukan Mutane”
  • Ka “Bada” Abin da Ka Iya Sadaka
  • “Ubanku Mai-jinƙai Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Muna Bauta wa Allah Mai Yalwar Jinkai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Masu Jinkai Suna Farin Ciki!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 10/1 pp. 8-12

Ta Yaya Za Mu Nuna Jin Ƙai?

“Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.”—GALATIYAWA 6:10.

1, 2. Menene almara na Basamariye ta koya mana game da jin ƙai?

SA’AD da yake magana da Yesu, wani mutum da ya san Doka sosai ya tambaye shi: “Wanene maƙwabcina?” Sai Yesu ya amsa ta wurin ba da almarar da ke gaba: “Wani mutum yana tafiya daga Urushalima zuwa Jericho; ya gamu da mafasa, suka yi masa tsiraici, suka dudduke shi, suka tashi, suka bar shi tsakanin rai da mutuwa. Ya arala fa wani malami yana bin wannan hanya: sa’anda ya gan shi, ya rāɓa ta wancan gefe, ya wuce. Hakanan kuma wani Lawi, sa’anda ya zo wurin, ya gan shi, shi kuma ya rāɓa ta wancan gefe, ya wuce. Amma wani Ba-samariye yana cikin tafiya, ya kawo wurinda shi ke: sa’anda ya gan shi, ya yi juyayi, ya zo wurinsa, ya ɗaure raunukansa, yana zuba masu mai da ruwan anab; ya hawashe shi bisa dabbansa, ya zo da shi wani mashidi, ya yi ɗawainiya da shi. Washegari kuma ya fito da sule biyu, ya ba ubangijin mashidi, ya ce, Ka yi ɗawainiya da shi; abin da za ka ɓatas gaba da wannan, sa’anda na komo, ni mayar maka.” Sai Yesu ya tambayi mai sauraronsa: “A cikin waɗannan uku fa, wa ka aza ya zama maƙwabci ga wanda ya gamu da mafasa?” Mutumin ya amsa: “Wannan da ya nuna masa jinƙai.”—Luka 10:25, 29-37a.

2 Yadda Basamariye ya bi da mutumin da aka ji ma rauni ya kwatanta jin ƙai na gaske! Domin ya nuna jin ƙai ko kuma juyayi, hakan ya motsa Basamariyen ya ɗauki matakin da ya kawo sauƙi ga mutumin da aka ji wa rauni. Bugu da ƙari, Basamariyen bai san mutumin da aka ji ma rauni ba. Ƙasa, addini, ko kuma al’ada ba sa hana mutum ya nuna wa wani jin ƙai. Bayan da ya ba da kwatanci na Basamariyen, Yesu ya ba mai sauraronsa shawara: “Je ka, ka yi hakanan.” (Luka 10:37b) Muna iya bin wannan gargaɗin kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu nuna wa mutane jin ƙai. Ta yaya? Ta yaya za mu iya nuna jin ƙai a rayuwarmu ta yau da kullum?

‘Idan Wani Ɗan’uwa Yana Tsiraici’

3, 4. Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu nuna jin ƙai cikin ikilisiyar Kirista?

3 Manzo Bulus ya ce: “Yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Saboda haka, bari mu fara tattauna yadda za mu yawaita wajen nuna ayyukan jin ƙai ga waɗanda muke cikin imani ɗaya da su.

4 Da yake ƙarfafa Kiristoci na gaskiya su zama masu nuna jin ƙai ga juna, almajiri Yaƙub ya rubuta: “Wanda ba ya nuna jinƙai ba: jinƙai kuma yana fahariya bisa shari’a.” (Yaƙub 2:13) Ayoyin waɗannan hurarrun kalmomi sun gaya mana wasu hanyoyin da za mu ci gaba da yi wa mutane jin ƙai. Alal misalin, Yaƙub 1:27 ta ce: “Addini mai-tsarki marar-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu, shi tsare kansa marar-aibi daga duniya.” Yaƙub 2:15, 16 sun ce: “Idan wani ɗan’uwa ko kuwa wata ’yar’uwa suna tsiraici, kuma sun rasa abincin yini, ɗaya kuwa daga cikinku ya ce masu, Ku tafi lafiya, ku ji ɗumi, ku ƙoshi; ba ku ko ba su bukatar jiki ba; me ya amfana?”

5, 6. Ta yaya za mu yawaita wajen nuna ayyukan jin ƙai a tarayyarmu da ikilisiya?

5 Kula da wasu da kuma taimaka wa mabukata suna cikin abubuwan da ke nuna addinin gaskiya. Domin addininmu, ba zai yi kyau mu yi wa mutane fatar zaman lafiya kawai ba. Maimakon haka, yi wa mutane juyayi mai zurfi zai motsa mu mu taimaka wa mabukata. (1 Yohanna 3:17, 18) Hakika, dafa wa wanda yake ciwo abinci, taimaka wa tsofaffi da aikacen-aikacen gida, yi wa wasu tanadin abin hawa zuwa taro idan bukata ta kama, da kuma yi wa waɗanda suke bukatar taimako alheri suna cikin ayyukan jin ƙai da ya kamata mu yi.—Kubawar Shari’a 15:7-10.

6 Ko da yake yana da kyau a taimaki waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista da ke ƙaruwa a zahiri, ya fi muhimmanci a taimake su a ruhaniya. An gargaɗe mu mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata, [mu] tokare marasa-ƙarfi.” (1 Tassalunikawa 5:14) An ƙarfafa “tsofaffin mata” su zama “masu-koyarda nagarta.” (Titus 2:3) Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kiristoci masu kula: “Mutum kuma za ya zama kamar maɓoya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa.”—Ishaya 32:2.

7. Menene muka koya daga almajirai da ke Suriya ta Antakiya game da jin tausayi?

7 Ban da kula da gwauraye, marayu, da waɗanda suke bukatar taimako da ƙarfafa, ikilisiyoyi na ƙarni na farko sun aika kayan agaji domin masu bi da suke wasu wurare. Alal misali, sa’ad da annabi Agabus ya annabta cewa “za a yi babbar yunwa ko’ina cikin duniya,” dukan almajirai da suke Suriya ta Antakiya sun ba da gwargwadon abin da suka iya, “suka kudurta su aike gudunmuwa ga ’yan’uwa da ke zaune cikin Yahudiya.” An aika wa dattawa da ke wajen “ta hannun Barnaba da Shawulu.” (Ayukan Manzanni 11:28-30) Yau kuma fa? “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya shirya kwamitin kai agaji don su kula da ’yan’uwanmu da tsarar bala’i, kamar su guguwa, girgizar ƙasa ko kuma tsunami ya shafa. (Matta 24:45) Ba da lokacinmu, ƙoƙarinmu, da dukiyarmu da son ranmu don mu ba da haɗin kai da wannan tsarin, hanya ce mai kyau na jin tausayi.

“Idan Kuna Tara”

8. Ta yaya nuna fifiko ke hana tausayi?

8 Sa’ad da yake yin gargaɗi game da halin da ke hana mu jin tausayi da kuma “shari’an nan ba’sarauciya” na ƙauna, Yaƙub ya rubuta: “Idan kuna tara, zunubi ku ke yi, shari’a tana kāshe ku masu-laifi ne.” (Yaƙub 2:8, 9) Yi wa mawadata ko kuma waɗanda suke da matsayi alheri da bai dace ba zai hana mu jin “kukan talaka.” (Misalai 21:13) Nuna fifiko yana hana jin tausayi. Muna jin tausayin mutane ta wurin bi da su ba tare da nuna fifiko ba.

9. Me ya sa yake da kyau a nuna kulawa ta musamman ga waɗanda suka cancanta?

9 Nuna rashin son kai yana nufin cewa ba za mu nuna kulawa ta musamman ga kowa ba ne? A’a. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke Filibbi game da abokin aikinsa Abafroditus: “Ku maida irin wannan abin darajantawa.” Me ya sa? “Sabili da aikin Kristi ya kai kusa da mutuwa, yana kasaida ransa domin shi cika abin da ya tauye wajen hidimarku gareni.” (Filibbiyawa 2:25, 29, 30) Saboda hidimar da ya yi cikin aminci, Abafroditus ya cancanci a nuna masa kulawa ta musamman. Bugu da ƙari, 1 Timothawus 5:17 ta ce: “Dattiɓai waɗanda ke mulki da kyau sai a maishe su sun isa bangirma ninki biyu, balle fa waɗannan da ke aiki cikin kalma da koyarwa.” Ya kuma dace a amince da halaye na ruhaniya masu kyau. Nuna irin wannan kulawar ta musamman ba nuna fifiko ba ne.

“Hikima Mai Fitowa Daga Bisa . . . [Tana] Cike da Jinƙai”

10. Me ya sa ya kamata mu kame harshenmu?

10 Yaƙub ya ce game da harshe: “Mugunta ne shi mara-hutu, cike da guba mai-matarwa. Da shi mu ke albarkata Ubangiji, Uba; da shi kuma mu ke la’antadda mutane, waɗanda an yi su bisa ga kamanin Allah; daga cikin bakin nan ɗaya albarka da la’ana su ke fitowa.” Yaƙub ya daɗa: “Idan kuna da kishi mai-zafi da tsaguwa a cikin zuciyarku, kada ku yi fahariya, kada ku yi ƙarya bisa gaskiya kuma. Wannan hikima ba hikima mai-saukowa daga bisa ba, amma ta duniya ce, ta jiki, ta Shaiɗan. Gama wurinda kishi da tsaguwa su ke, nan akwai yamutsai da kowane irin mugun al’amari. Amma hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, mara-kokanto, mara-riya ce.”—Yaƙub 3:8-10a, 14-17.

11. Ta yaya za mu zama masu jin ƙai a yadda muke amfani da harshenmu?

11 Saboda haka, yadda muke amfani da harshenmu zai nuna ko muna da hikima da take ‘cike da jinƙai.’ Idan saboda kishi ko kuma jayayya muka yi fahariya, ƙarya ko kuma yaɗa gulma fa? Zabura 94:4 ta ce: “Dukan masu-aika mugunta suna ruba.” Kuma baƙar magana na saurin ɓata sunan marar laifi! (Zabura 64:2-4) Bugu da ƙari, ka yi tunanin lahanin da “mai-shaidan zur” da ke yaɗa ƙarya yake jawowa. (Misalai 14:5; 1 Sarakuna 21:7-13) Bayan ya tattauna game da yin amfani da harshe a hanyar da bai dace ba, Yaƙub ya ce: “’Yan’uwana, ba ya kamata waɗannan al’amura su zama haka ba.” (Yaƙub 3:10b) Idan za mu nuna jin ƙai ta gaske muna bukatar mu yi wa mutane magana da hankali, salama, kuma a hanyar da ta dace. Yesu ya ce: “Ina ce muku kuma, Kowacce maganar banza da mutane ke faɗi, a cikin ranar shari’a za su bada lissafinta.” (Matta 12:36) Yana da muhimmanci mu zama masu jin ƙai a yadda muke amfani da harshenmu!

Ka “Gafarta ma Mutane Laifofinsu”

12, 13. (a) Menene muka koya game da jin ƙai daga almarar bawa da ubangijinsa yake bi bashin kuɗi mai yawa? (b) Menene ake nufi da mu gafarta wa ɗan’uwanmu “bakwai bakwai so saba’in”?

12 Almarar Yesu na bawan da ubangijinsa sarki ke binsa bashin talanti dubu goma ya nuna wata hanya da za mu zama masu jin ƙai. Da yake ba zai iya biyan bashin ba, bawan ya yi roƙo a yafe masa bashin. Domin “ya ji juyayi,” ubangijin bawan ya yafe masa bashin. Amma bawan nan ya fita waje kuma ya ga wani bawa da yake bi bashin dinari ɗari kawai kuma ya ƙi gafarta masa ya jefa shi cikin kurkuku. Sa’ad da ubangijinsa ya ji abin da ya faru, ya kira bawan da ya yafe wa bashi, kuma ya ce masa: “Kai mugun bawa, na gafarta maka dukan bashin nan, domin ka roƙe ni: ba ya kamata gareka ba kai kuma ka jiƙan abokin bautanka, kamar yadda ni na jiƙanka?” Da haka ubangijin ya miƙa shi ga ma’aikatan gidan kurkuku. Yesu ya kammala almararsa, yana cewa: “Hakanan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta ma ’yan’uwanku.”—Matta 18:23-35.

13 Wannan almarar ta nuna cewa jin ƙai ya ƙunshi kasancewa a shirye mu gafarta wa mutane! Jehobah ya gafarta mana zunubai masu yawa. Bai kamata mu ma mu “gafarta ma mutane laifofinsu” ba? (Matta 6:14, 15) Kafin Yesu ya ba da almara game da bawa marar jin ƙai, Bitrus ya tambaye shi, “so nawa ɗan’uwana za ya yi mani zunubi, in gafarta masa? har so bakwai?” Yesu ya amsa: “Ban ce maka, Har so bakwai ba; amma, Har bakwai bakwai so saba’in.” (Matta 18:21, 22) Hakika, mutum mai jin ƙai yana shirye ya gafarta “har bakwai bakwai so saba’in,” wato, ba iyaka.

14. In ji Matta 7:1-4, ta yaya za mu nuna jin ƙai kowace rana?

14 Yesu ya nuna wata hanyar da za mu nuna jin ƙai a Huɗubarsa bisa Dutse: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku. Gama da irin shari’a da ku ke shar’antawa, da shi za a shar’anta muku. . . . Don me kuwa ka ke duban ɗan hakin da ke cikin idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke cikin ido naka ba? Ko kuwa ƙaƙa za ka ce ma ɗan’uwanka, Bari in cire ɗan hakin daga cikin idonka; ga shi kuwa, gungume yana cikin ido naka?” (Matta 7:1-4) Saboda haka, za mu nuna jin ƙai kowace rana ta wurin jimrewa da kasawar mutane ba tare da yawan shara’anta su ba.

Ka Yi “Nagarta Zuwa ga Dukan Mutane”

15. Me ya sa ba ’yan’uwanmu masu bi kaɗai ba ne za mu yi wa jin ƙai?

15 Ko da littafin Yaƙub ya nanata jin ƙai tsakanin masu bauta, wannan ba ya nufin cewa waɗanda suke cikin ikilisiya ne kaɗai za mu riƙa nuna wa jin ƙai. “Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane” in ji Zabura 145:9, kuma “jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.” An umurce mu mu “zama fa masu-koyi da Allah” kuma “mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane.” (Afisawa 5:1; Galatiyawa 6:10) Ko da yake ba ma “ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya” muna damuwa da bukatun waɗanda ke cikin duniya.—1 Yohanna 2:15.

16. Waɗanne abubuwa ne ke shafan yadda muke nuna wa mutane alheri?

16 Da yake mu Kiristoci ne, muna shirye koyaushe mu taimaka wa waɗanda ‘sa’a, da tsautsayi’ ya shafe su ko kuma waɗanda suke cikin mugun yanayi. (Mai Hadishi 9:11; LMT) Hakika, abin da za mu iya yi da yawan yadda za mu yi shi ya dangana ne da yanayinmu. (Misalai 3:27) Sa’ad da muke ba da taimako, ya kamata mu mai da hankali don kada alherinmu ya sa mutane ragonci. (Misalai 20:1, 4; 2 Tassalunikawa 3:10-12) Saboda haka, mutumin da ke nuna jin ƙai na gaske na aikatawa cikin juyayi ko tausayi da sanin ya kamata.

17. Wace hanya ce mafi kyau da za mu yi wa waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista alheri?

17 Hanya mafi kyau na nuna wa waɗanda ba sa cikin ikilisiya alheri ita ce ta wajen gaya musu gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Domin yawancin ’yan adam a yau suna cikin duhu na ruhaniya. Da yake ba su san yadda za su bi da matsalolin da suke fuskanta ba, kuma ba su da bege don nan gaba, yawancin mutane “suna nan a warwatse kamar tumaki ba makiyayi.” (Matta 9:36) Saƙon Kalmar Allah zai iya zama ‘fitila ga sawayensu,’ kuma zai taimaka masu su jimre matsaloli na rayuwa. Zai iya zama ‘haske kuma a tafarkinsu’ tun da yake Littafi Mai Tsarki ya annabta ƙudurin Allah don nan gaba, yana ba su dalilin kasancewa da bege mai kyau. (Zabura 119:105) Gata ce ƙwarai mu gaya wa waɗanda suke bukatar wannan saƙon gaskiya mai ban sha’awa! Domin “ƙunci mai-girma” ya kusa, yanzu ne lokacin da za mu yi ƙwazo sosai cikin aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. (Matta 24:3-8, 21, 22, 36-41; 28:19, 20) Ba wani alherin da za mu yi da ya fi wannan.

Ka “Bada” Abin da Ka Iya Sadaka

18, 19. Me ya sa ya kamata mu yi ƙoƙari mu daɗa nuna alheri a rayuwarmu?

18 Yesu ya ce: “Ku bada abin da kun iya sadaka.” (Luka 11:41) Don aikin nagarta ya zama alheri na gaske, zai zama kyauta da aka bayar da zuciya ɗaya cikin ƙauna da son rai. (2 Korinthiyawa 9:7) A cikin duniya da ta cika da zafin rai, son kai, da rashin damuwa game da wahala da matsalolin mutane, irin wannan alheri na da wartsakewa!

19 Bari mu yi aiki tuƙuru don mu ƙara yin jin ƙai a rayuwarmu. Idan muka daɗa zama masu jin ƙai za mu ƙara zama kamar Allah. Wannan zai taimake mu mu yi rayuwa mai ma’ana da gamsarwa.—Matta 5:7.

Menene Ka Koya?

• Me ya sa yake da muhimmanci a ji tausayin ’yan’uwa masu bi?

• Ta yaya za mu nuna jin ƙai cikin ikilisiyar Kirista?

• Ta yaya za mu aikata nagarta ga waɗanda ba sa cikin ikilisiya?

[Hoto a shafi na 8]

Basamariyen ya ji tausayi

[Hotuna a shafi na 9]

Kiristoci sun cika da ayyukan alheri

[Hoto a shafi na 12]

Hanya mafi kyau na nuna wa waɗanda ba sa cikin ikilisiya alheri ita ce ta gaya musu gaskiyar Littafi Mai Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba