TALIFIN NAZARI NA 41
Muna Bauta wa Allah Mai Yalwar Jinƙai
“Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.”—ZAB. 145:9, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
WAƘA TA 44 Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Yaya za ka kwatanta mutum mai jinƙai, kuma wane labari ne aka bayar game da wani mutum da ya nuna jinƙai?
IDAN aka ce mutum mai jinƙai ne, za mu iya tunanin mutumin da ya damu da mutane, mai alheri, mai tausayi da kuma mai bayarwa hannu sake. Za mu iya tuna labarin da Yesu ya bayar na wani Basamariye. Mutumin ya nuna ma wani Bayahude da ɓarayi suka yi wa dūka jinƙai. Da Basamariyen ya ga Bayahuden, “sai tausayi ya kama shi” kuma ya sa a kula da Bayahuden. (Luk. 10:29-37) Misalin ya koya mana game da jinƙai, hali mai kyau da Allah yake da shi. Allah yana nuna jinƙai domin yana ƙaunar mu, kuma a kowace rana yana nuna halin nan a hanyoyi da yawa.
2. A wace hanya ce kuma za mu iya nuna jinƙai?
2 Akwai wata hanya dabam da mutum zai iya nuna jinƙai. Mutum mai jinƙai zai iya ƙi ya ba da horo ga wanda ya cancanci a yi masa horo. Hanya da Jehobah yake nuna mana jinƙai ke nan. Wani marubucin zabura ya ce Jehobah ba ya bi da mu “bisa ga zunubanmu.” (Zab. 103:10) Amma a wasu lokuta, Jehobah yakan yi wa masu zunubi horo sosai.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
3 A talifin nan, za mu ga amsoshin tambayoyi uku: Me ya sa Jehobah yake nuna jinƙai? Zai yiwu a yi wa mutum horo sosai kuma a nuna masa jinƙai? Me zai taimaka mana mu nuna jinƙai? Bari mu ga yadda Kalmar Allah ta ba da amsoshin tambayoyin nan.
ME YA SA JEHOBAH YAKE NUNA JINƘAI?
4. Me ya sa Jehobah yake nuna jinƙai?
4 Jehobah yana nuna jinƙai domin shi mai ƙauna ne. Manzo Bulus ya rubuta cewa Allah “mai yalwar jinƙai ne.” A nassin, Bulus yana magana ne game da yadda Allah ya nuna jinƙai ta wajen ba wa bayinsa ajizai begen yin rayuwa a sama. (Afis. 2:4-7, Littafi Mai Tsarki) Amma ba ga shafaffun bayinsa ne kaɗai yake nuna jinƙai ba. Dauda wanda shi ma marubucin zabura ne ya ce: “Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.” (Zab. 145:9, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Da yake Jehobah yana ƙaunar mutane, yana nuna musu jinƙai sa’ad da ya ga dalilin yin hakan.
5. Ta yaya Yesu ya san cewa Jehobah mai jinƙai ne?
5 Yesu ya fi kowa sanin yadda Jehobah yake son nuna jinƙai. Jehobah da Yesu sun yi shekaru da yawa tare kafin Yesu ya zo duniya. (K. Mag. 8:30, 31) Sau da yawa, Yesu ya ga yadda Ubansa ya nuna wa ’yan Adam ajizai jinƙai. (Zab. 78:37-42) A yawancin lokuta, sa’ad da Yesu yake koyarwa, ya yi magana game da wannan hali mai kyau na Ubansa.
Mahaifin bai kunyatar da ɗansa mubazzari ba, amma ya marabce shi (Ka duba sakin layi na 6)c
6. Ta yaya Yesu ya kwatanta yadda Ubansa yake nuna jinƙai?
6 Kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, Yesu ya ba da kwatanci game da ɗa mubazzari domin ya nuna mana yadda Jehobah yake son yin jinƙai. Ɗan ya bar gida kuma ‘ya je ya yi banza da kuɗi cikin iskanci.’ (Luk. 15:13) Daga baya ya tuba, ya daina iskanci, ya ƙasƙantar da kansa kuma ya koma gida. Me babansa ya yi? Yesu ya ce: “Tun [ɗan] yana daga nesa, sai babansa ya gane shi. Tausayi ya kama baban, ya tashi da gudu ya je ya rungumi ɗansa, ya yi ta yi masa sumba.” Baban bai kunyatar da ɗansa ba. Amma nan da nan ya nuna wa yaron jinƙai, ya gafarta masa, kuma ya dawo da shi cikin iyalinsa. Yaron ya yi zunubi mai tsanani, amma da yake ya tuba, babansa ya gafarta masa. Baban da ya nuna jinƙan, yana wakiltar Jehobah. Yesu ya yi amfani da kwatancin don ya nuna mana yadda Jehobah yake a shirye ya gafarta ma waɗanda suka tuba.—Luk. 15:17-24.
7. Ta yaya yadda Jehobah yake nuna jinƙai ya nuna cewa shi mai hikima ne?
7 Jehobah yana nuna jinƙai domin shi mai hikima ne sosai. A kullum, Jehobah yana ɗaukan matakin da zai amfani halittunsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Hikimar nan ta sama . . . mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri,’ ne. (Yak. 3:17, Littafi Mai Tsarki) Kamar uba mai ƙauna, Jehobah ya san cewa bayinsa za su amfana idan ya nuna musu jinƙai. (Zab. 103:13; Isha. 49:15) Da yake Jehobah yana nuna wa bayinsa jinƙai, suna da begen yin rayuwa har abada a nan gaba duk da cewa su ajizai ne. Jehobah yana nuna jinƙai idan ya ga dalilin yin hakan don shi mai hikima ne. Amma Jehobah ya san lokacin da ya kamata ya nuna jinƙai. Saboda hikimarsa, ba ya nuna jinƙai idan yin hakan zai nuna goyon baya ga mai zunubi.
8. Wane mataki ne zai dace a ɗauka a wasu lokuta, kuma me ya sa?
8 A ce wani bawan Allah ya soma yin zunubi da gangan. Me ya kamata mu yi? Jehobah ya sa manzo Bulus ya rubuta cewa ‘kada mu yi tarayya da mutumin.’ (1 Kor. 5:11, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ana yi wa masu zunubi da suka ƙi tuba yankan zumunci. Yin hakan yana da muhimmanci domin a kāre ’yan’uwanmu masu aminci kuma a nuna cewa Jehobah mai tsarki ne. Amma wasu za su iya gani kamar idan aka yi wa mutum yankan zumunci, Jehobah bai nuna wa mutumin jinƙai ba. Hakan gaskiya ne? Bari mu gani.
ME YA SA YANKAN ZUMUNCI HANYA CE TA NUNA JINƘAI?
Za a iya wāre tunkiyar da take rashin lafiya, amma makiyayin zai ci gaba da kula da ita (Ka duba sakin layi na 9-11)
9-10. Bisa ga abin da ke Ibraniyawa 12:5, 6, me ya sa muka ce yankan zumunci hanya ce ta nuna jinƙai? Ka ba da misali.
9 Idan muka ji sanarwa a taro cewa an yi ma wani da muka sani yankan zumunci, hakan yana sa mu baƙin ciki sosai. Za mu iya yin tunani ko ya dace da aka yi masa yankan zumunci. Shin yankan zumunci hanya ce ta nuna jinƙai da gaske? Ƙwarai kuwa. Idan ya dace a yi wa mutum horo, hikima da jinƙai da kuma ƙauna za su sa a yi masa hakan. (K. Mag. 13:24) Shin yankan zumunci zai taimaka wa mutumin da ya ƙi tuba ya canja halayensa? Hakan zai iya faruwa. ’Yan’uwa maza da mata da yawa da suka yi zunubi mai tsanani sun ce, sai da aka yi musu yankan zumunci ne suka fahimci cewa sun yi zunubi mai tsanani, kuma hakan ya taimaka musu su tuba, su canja halayensu kuma su komo ga Jehobah.—Karanta Ibraniyawa 12:5, 6.
10 Ga wani misali da zai taimaka mana mu fahimci wannan batun. A ce wani makiyayi ya lura cewa ɗaya daga cikin tumakinsa tana rashin lafiya. Ya san cewa yana bukatar ya wāre tunkiyar daga sauran tumakin kafin ya yi mata jinya. Idan aka wāre tunkiyar daga sauran tumakin, hankalinta yana iya tashiwa. Amma hakan yana nufin cewa makiyayin mugu ne domin ya wāre tunkiyar? A’a. Ya san cewa idan ya bar tunkiyar tare da sauran, za ta iya yaɗa cutar. Don haka, wāre tunkiyar zai kāre sauran tumakin.—Ka duba misalin da ke Littafin Firistoci 13:3, 4.
11. (a) A waɗanne hanyoyi ne wanda aka yi wa yankan zumunci yake kama da tunkiya mai rashin lafiya? (b) Mene ne waɗanda aka yi musu yankan zumunci za su iya yi, kuma ta yaya za a iya taimaka musu?
11 Kirista da aka yi wa yankan zumunci yana kama da tunkiya mai rashin lafiya, domin dangantakarsa da Jehobah ta ɓace. (Yak. 5:14) Kamar yadda wasu cututtuka sukan yaɗu, haka ma wanda ya yi zunubi zai iya sa wasu su yi abin da bai dace ba. Saboda haka, ya zama dole a yi wa mai zunubi yankan zumunci a wasu lokuta. Wannan horon ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar tumakinsa masu aminci kuma zai iya sa mai zunubin ya tuba. Duk da cewa an yi masa yankan zumunci, zai iya halartan taro, ya ji Kalmar Allah kuma ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Ƙari ga haka, zai iya karɓan littattafai da zai karanta kuma ya kalli shirin Tashar JW. Yayin da dattawa suke ganin yadda yake gyara halinsa, za su iya ba shi shawara da za ta taimake shi ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Hakan zai sa a mai da shi ikilisiya.b
12. Mene ne ƙauna da jinƙai za su sa dattawa su yi wa mutumin da ya ƙi tuba?
12 Yana da muhimmanci mu tuna cewa masu zunubin da suka ƙi tuba ne kawai ake musu yankan zumunci. Dattawa sun san cewa suna bukatar su yi tunani sosai kafin su yanke shawarar yi wa mutum yankan zumunci. Sun san cewa Jehobah yana yin horo “yadda ya kamata.” (Irm. 30:11, New World Translation) Suna ƙaunar ’yan’uwansu kuma ba sa so su yi abin da zai ɓata dangantakar ’yan’uwansu da Jehobah. Amma a wasu lokuta, dattawa za su bukaci su yi wa mai zunubi yankan zumunci don ƙauna da jinƙai.
13. Me ya sa ya dace da aka yi ma wani Kirista a Korinti yankan zumunci?
13 Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya yi game da wani da ya ƙi tuba a ƙarni na farko. Wani Kirista a Korinti yana kwana da matar babansa. Hakan abin ƙyama ne sosai! A zamanin dā, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Mutumin da ya yi jima’i da matar babansa ya ƙasƙantar da babansa ke nan. Dukansu biyu za a kashe su.” (L. Fir. 20:11) Hakika, Bulus bai da ikon gaya wa ikilisiyar su kashe mutumin, amma ya ce su yi masa yankan zumunci. Halin wannan mutumin ya fara shafan wasu a ikilisiya. Wasu sun fara ji kamar abin da ya yi ba zunubi mai tsanani ba ne.—1 Kor. 5:1, 2, 13.
14. Ta yaya Bulus ya yi wa mutumin da aka yi wa yankan zumunci a Korinti jinƙai, kuma me ya sa? (2 Korintiyawa 2:5-8, 11)
14 Da shigewar lokaci, Bulus ya ji cewa mutumin ya canja halinsa. Mai zunubin ya tuba da gaske. Ko da yake mutumin ya ɓata sunan ikilisiyar, Bulus ya ce ba ya so ya yi masa hukunci mai tsanani. Ya umurci dattawa cewa ‘su yafe masa, su kuma yi masa ta’aziyya.’ Ga dalilin da ya sa Bulus ya faɗi hakan, ya ce: ‘Domin kada su bar shi har baƙin ciki ya sha ƙarfinsa.’ Bulus ya ji tausayin mutumin, kuma ba ya so ya yi baƙin ciki har ya daina neman gafara.—Karanta 2 Korintiyawa 2:5-8, 11.
15. Ta yaya dattawa za su yanke hukuncin da ya kamata kuma su nuna jinƙai?
15 Dattawa suna nuna jinƙai domin suna yin koyi da Jehobah. Za su yi wa mai zunubi horo sosai idan da bukata amma za su yi masa jinƙai idan ya kamata. Idan dattawa ba su yi wa mai zunubi horo ba, hakan ba jinƙai ba ne. A maimakon haka, zai nuna cewa sun yarda da laifin da ya yi. Amma dattawa ne kaɗai suke bukatar su nuna jinƙai?
ME ZAI TAIMAKA WA DUKANMU MU RIƘA NUNA JINƘAI?
16. Kamar yadda Karin Magana 21:13 ta nuna, mene ne Jehobah yake yi ma waɗanda suka ƙi nuna jinƙai?
16 Dukan Kiristoci suna ƙoƙari su bi misalin Jehobah na nuna jinƙai. Me ya sa? Domin Jehobah ba zai ji addu’ar waɗanda suka ƙi nuna jinƙai ba. (Karanta Karin Magana 21:13.) Babu wanda zai so Jehobah ya ƙi jin addu’arsa. Don haka, ba zai dace mu ƙi nuna jinƙai ba. Bai kamata mu ƙi taimaka ma ɗan’uwa da ke fama da matsaloli ba. A maimakon haka, ya kamata mu kasance a shirye mu taimaka wa marasa ƙarfi. Zai dace mu riƙa tuna abin da nassin nan ya faɗa cewa: “Allah ba zai nuna jinƙai ga mutum marar jinƙai ba.” (Yak. 2:13) Idan mu ma muka tuna cewa muna bukatar a yi mana jinƙai, za mu nuna jinƙai. Muna bukatar mu nuna jinƙai musamman idan mai zunubi ya tuba kuma ya komo ikilisiya.
17. Ta yaya Sarki Dauda ya nuna jinƙai daga zuciyarsa?
17 Misalan da ke Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu nuna jinƙai. Alal misali, ka yi tunanin Sarki Dauda. Sau da yawa ya nuna wa mutane jinƙai. Duk da cewa Sarki Saul ya yi ƙoƙari ya kashe Dauda, Dauda bai rama ba, amma ya nuna wa sarkin da Allah ya zaɓa jinƙai.—1 Sam. 24:9-12, 18, 19.
18-19. A waɗanne yanayoyi biyu ne Dauda bai nuna jinƙai ba?
18 Amma akwai wasu lokuta da Dauda bai nuna jinƙai ba. Alal misali, wani mutum mai suna Nabal ya zagi Dauda kuma ya ƙi ya ba Dauda da mutanensa abinci, don shi marar tausayi ne. Hakan ya sa Dauda fushi har ya yanke shawarar kashe Nabal da dukan mazan gidansa. Amma Abigail matar Nabal mace mai kirki ce da kuma haƙuri, sai ta ba Dauda abinci nan da nan. Hakan ya sa Dauda bai kashe Nabal da mutanensa ba.—1 Sam. 25:9-22, 32-35.
19 A wani karo kuma, annabi Natan ya gaya wa Dauda game da wani mai arziki da ya kwace tunkiyar wani talaka. Dauda ya yi fushi kuma ya ce: “Na rantse da Sunan Yahweh mai rai, mutumin da ya yi wannan ya isa a kashe shi!” (2 Sam. 12:1-6) Dauda ya san Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa. Dokar ta ce idan aka kama mutumin da ya saci tunkiya, za a sa shi ya biya da tumaki huɗu. (Fit. 22:1) Amma cewa a kashe mai satar hukunci ne mai tsanani! Natan ya yi amfani da kwatancin ne domin ya nuna wa Dauda cewa ya yi zunubi mai tsanani. Jehobah ya nuna wa Dauda jinƙai fiye da yadda Dauda ya nuna jinƙai ga ɓarawon tunkiyar da ke kwatancin Natan.—2 Sam. 12:7-13.
Sarki Dauda bai yi wa mutumin da ke kwatancin Natan jinƙai ba (Ka duba sakin layi na 19-20)d
20. Mene ne za mu iya koya daga misalin Dauda?
20 Ka tuna cewa a lokacin da Dauda yake fushi, ya yanke shawarar kashe Nabal da dukan mazan gidansa. Ban da haka, ya ce a kashe mai arziki na kwatancin Natan. A karo na biyun, za mu iya tunani cewa, ‘Dauda mutumin kirki ne, amma me ya sa ya yanke wa ɓarawon hukunci mai tsanani haka?’ Ka yi tunanin abin da ya faru da Dauda. A lokacin, zuciyarsa na damun sa. Idan mutum yana yanke wa mutane hukunci mai tsanani, mai yiwuwa dangantakarsa da Jehobah ta soma sanyi ne. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi cewa: “Kada ku yanke wa kowa hukunci, domin kada a yanke muku. Gama da irin shari’ar da kuke yi wa mutane, da ita za a yi muku shari’a.” (Mat. 7:1, 2) Saboda haka, bari mu guji yanke wa mutane hukunci mai tsanani, amma mu zama “masu yalwar jinƙai” kamar Allahnmu.
21-22. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yi wa mutane jinƙai?
21 Idan mu masu jinƙai ne, ba tausayin mutane ne kaɗai za mu ji ba. Masu jinƙai suna yin abubuwa da za su taimaka wa mutane. Don haka, dukanmu za mu iya lura don mu ga mutanen da suke bukatar taimako a iyalinmu, da ikilisiyarmu da kuma yankinmu. Hakika, akwai hanyoyi da yawa na yin jinƙai. Akwai wanda yake bukatar ƙarfafa? Shin za mu iya taimaka masa ta wajen yi masa tanadin abinci ko wani abu da zai taimake shi? Idan akwai ɗan’uwa da aka dawo da shi ikilisiya ba da daɗewa ba, shin ɗan’uwan yana bukatar aboki da zai ƙarfafa shi? Za mu iya gaya wa mutane saƙo mai ban ƙarfafa da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Wannan yana cikin hanyoyi mafi kyau na nuna wa mutane jinƙai.—Ayu. 29:12, 13; Rom. 10:14, 15; Yak. 1:27.
22 Idan muna lura don mu ga masu bukata, za mu ga cewa akwai hanyoyi da yawa na yi musu jinƙai. Idan muka yi wa mutane jinƙai, Ubanmu na sama zai yi farin ciki domin shi “mai yalwar jinƙai” ne.
WAƘA TA 43 Addu’ar Godiya
a Jinƙai ɗaya ne daga cikin halayen Jehobah mafi kyau, kuma muna bukatar mu kasance da halin. A wannan talifin, za mu tattauna abin da ya sa Jehobah yake nuna jinƙai, da abin da ya sa za mu iya cewa Jehobah yana nuna jinƙai sa’ad da yake yi wa mutum horo, da kuma yadda za mu iya nuna jinƙai.
b Don samun ƙarin bayani a kan yadda waɗanda aka mayar da su ikilisiya za su iya gyara dangantakarsu da Jehobah, da yadda dattawa za su taimaka musu, ka duba talifin nan, “Yadda Za Ka Gyara Dangantakarka da Jehobah” a mujallar nan.
c BAYANI A KAN HOTO: Daga rufin gidansa, baban ɗa mubazzari ya hango shi yana dawowa gida kuma ya fita a guje ya rungume shi.
d BAYANI A KAN HOTO: A lokacin da zuciyar Sarki Dauda take damun sa, ya yi fushi sosai sa’ad da Natan ya gaya masa kwatancin wani mai arziki kuma Dauda ya ce a kashe mai arzikin.