Ka Sani?
A yaushe ne masanan taurari suka ziyarci Yesu?
A Linjilar Matta, an gaya mana cewa wasu ‘masanan taurari daga gabas’ sun ziyarci Yesu suka kuma ba shi kyauta. (Matta 2:1-12) Ba a bayyana ko masanan taurari, ko kuma “shefuna” nawa ne suka ziyarci Yesu sa’ad da yake yaro ba, kuma babu wani abu takamaimai da ya nuna cewa su uku ne; kuma ba a faɗi sunansu ba a cikin Littafi Mai Tsarki.
New International Version Study Bible ya yi wannan kalami game da Matta 2:11: “Ba kamar yadda aka saba faɗi ba, Shefunan nan ba su ziyarci Yesu sa’ad da yake cikin sakarkari a daren da aka haife shi ba kamar yadda makiyaya suka yi. Sun ziyarce shi ne bayan watanni masu yawa sa’ad da yake ‘yaro’ a ‘gidansu.’” Hakan ya tabbata ne domin sa’ad da Hirudus ya nemi ya kashe yaron, ya ba da umurni a kashe dukan yara maza daga masu shekara biyu zuwa ƙasa a dukan Bai’talami da kuma gundumominta. Ya zaɓi waɗannan tsara ne “bisa ga lissafin kwanakin da ya sami labari a hankali daga wurin shefunan nan.”—Matta 2:16.
Da a ce waɗannan masanan taurari sun ziyarci Yesu a daren da aka haife shi kuma suka ba da kyautar zinariya da kuma wasu abubuwa masu tamani, da Maryamu ba ta ba da hadayar tsuntsaye biyu ba kawai bayan kwanaki 40 sa’ad da ta kai Yesu haikali a Urushalima. (Luka 2:22-24) Wannan tsari ne a Dokar domin matalauta waɗanda ba za su iya ba da hadayar ɗan rago ba. (Leviticus 12:6-8) Amma, wataƙila wannan kyauta mai tamani ta taimaka wajen biyan bukatar iyalin Yesu a ƙasar Masar.—Matta 2:13-15.
Me ya sa Yesu ya yi kwana huɗu kafin ya isa kabarin Li’azaru?
Kamar dai Yesu ne ya shirya tafiyarsa ta kasance haka. Me ya sa muka ce haka? Dubi labarin da aka rubuta a Yohanna sura 11.
Sa’ad da Li’azaru abokin Yesu wanda ke da zama a Bait’anya ya kwanta ciwo mai tsanani, ’yan’uwansa mata suka sanar da Yesu. (Ayoyi na 1-3) A wannan lokacin, zai ɗauki Yesu kwanaki biyu daga inda yake kafin ya kai Bait’anya. (Yohanna 10:40) Kamar dai Li’azaru ya mutu a daidai lokacin da Yesu ya sami wannan saƙon. Menene Yesu ya yi? Sai ya sake “kwana biyu a wurinda ya ke,” kafin ya nufi Bait’anya. (Ayoyi na 6, 7) Domin ya sake kwana biyu ya kuma yi tafiyar kwana biyu, ya isa kabarin kwanaki huɗu bayan mutuwar Li’azaru.—Aya ta 17.
A dā, Yesu ya ta da mutane biyu daga matattu, na farkon an ta da shi ne nan da nan bayan mutuwarsa, ɗayan kuma wataƙila an ta da shi ne bayan wani ɗan lokaci a ranar da ya mutu. (Luka 7:11-17; 8:49-55) Shin zai iya ta da mutumin da ya yi kwanaki huɗu da mutuwa wanda gangar jikinsa ta soma ruɓewa? (Aya ta 39) Abin sha’awa, wani bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce wasu Yahudawa sun gaskata cewa “idan mutum ya yi kwana huɗu a mace, mutumin ba zai iya tashi ba; domin jikinsa zai fara ruɓewa, kuma kurwar da aka ce tana zagaya jiki na kwana uku ta riga ta tafi.”
Idan da wanda ke shakka a cikin mutanen da suka taru a kabarin, ya yi kusan ganin ikon Yesu bisa mutuwa. Yesu ya tsaya a gaban kabarin ya yi kira: “Li’azaru, ka fito.” Sai “shi wanda ya mutu ya fito.” (Ayoyi na 43, 44) Tashin matattu, shi ne bege na gaskiya ga matattu, ba ra’ayin nan na ƙarya ba cewa kurwa tana ci gaba da rayuwa bayan mutuwa.—Ezekiel 18:4; Yohanna 11:25.