Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 20-24
  • Sun Cancanci Samun Mulki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Cancanci Samun Mulki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Kira Zuriyar Ibrahim Masu Adalci
  • Cika Adadin da Aka Annabta
  • Gwamnatin Allah ta Sama ta Kusan Cika
  • Ruhun Allah Yana Ba Mu Tabbaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Za Mu Tafi Tare da Ku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ruhu Mai Tsarki Yana Shaida Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • “Za Mu Tafi Tare da Ku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 20-24

Sun Cancanci Samun Mulki

“Ainihin shaida ke nan ta shari’a mai-adalci ta Allah; da nufin a maishe ku kun cancanta ga mulkin Allah.”—2 TAS. 1:5.

1, 2. Menene nufin Allah game da shari’a, kuma wanene zai yi shari’ar?

KUSAN shekara 50 A.Z., manzo Bulus yana Atina. Don ya damu da yadda ake yawan bauta wa gunki a wajen, hakan ya sa ya ba da shaida mai kyau. Ya kammala jawabinsa da maganar da ta jawo hankalin arnan da suke sauraronsa. Ya ce: “Yanzu [Allah] yana umurtan mutane dukansu cikin kowane wuri su tuba: da shi ke ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara; wannan fa ya bada shaidarsa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.”—A. M. 17:30, 31.

2 Abu ne mai muhimmanci mu yi tunani sosai domin Allah ya kafa wata rana nan gaba da zai hukunta ’yan adam! Wanda Bulus bai ambata ba a jawabinsa a Atina, wato Yesu Kristi wanda aka ta da daga matattu ne zai yi hukuncin. Hukuncin Yesu zai kai ga rai ko kuma mutuwa.

3. Me ya sa Jehobah ya yi alkawari da Ibrahim, kuma wanene yake da matsayi na musamman wajen cika shi?

3 Ranar Shari’ar za ta kai tsawon shekaru 1,000. Yesu zai yi shari’ar cikin sunan Jehobah da yake shi ne Sarkin Mulkin Allah, amma ba zai yi hakan shi kaɗai ba. Jehobah ya zaɓi wasu daga cikin ’yan adam su yi sarauta da Yesu kuma su yi shari’a a lokacin sarautarsa na shekara dubu. (Ka gwada da Luka 22:29, 30.) Kusan shekaru 4,000 da suka shige, Jehobah ya kafa tushen wannan Ranar Hukunci sa’ad da ya yi alkawari da Ibrahim bawansa mai aminci. (Ka karanta Farawa 22:17, 18.) An soma wannan alkawarin a shekara ta 1943 K.Z. Hakika, Ibrahim bai da cikakken fahimi na yadda wannan alkawarin zai shafi ’yan adam. Amma mu a yau mun ga cewa bisa alkawarin, zuriyar Ibrahim yana da matsayi na musamman wajen cika nufin Allah na hukunta ’yan adam.

4, 5. (a) Wanene ainihin sashen zuriyar Ibrahim, kuma menene ya faɗa game da Mulkin? (b) Yaushe ne begen zuwa sama don yin Mulki ya buɗu?

4 Yesu ne ya zama ainihin sashen zuriyar Ibrahim, wanda a shekara ta 29 A.Z., aka shafa shi da ruhu mai tsarki kuma ya zama Almasihu ko Kristi da aka yi alkawarinsa. (Gal. 3:16) Yesu zai yi shekara uku da rabi yana wa’azin bishara na Mulkin ga al’ummar Yahudawa. Bayan da aka tsare Yohanna mai baftisma, Yesu ya nuna cewa wasu za su kasance cikin Mulkin sa’ad da ya ce: “Daga zamanin Yohanna Mai-yin baftisma har yanzu kuma mulkin sama yana shan guggurmaya, masu guggurmaya kuwa su kan ci shi da ƙarfi.”—Matta 11:12.

5 Kafin ya yi maganar waɗanda za su yi ‘guggurmayar’ shiga Mulkin sama, Yesu ya ce: “Hakika ina ce maku, A cikin waɗanda an haifa daga wajen mata ba wanda ya tashi wanda ya fi Yohanna Mai-yin baptisma girma: duk da haka, wanda shi ke ƙanƙani a cikin mulkin sama ya fi shi girma.” (Matta 11:11) Me ya sa? Domin begen zama sashen Mulkin bai buɗu ba ga mutane masu aminci sai a lokacin da aka zuba ruhu mai tsarki a kansu a ranar Fentikos ta 33 K.Z. A lokacin, Yohanna mai Baftisma ya riga ya mutu.—Ayukan Manzanni 2:1-4.

An Kira Zuriyar Ibrahim Masu Adalci

6, 7. (a) Ta yaya zuriyar Ibrahim za ta zama “kamar taurarin sama”? (b) Wace albarka ce Ibrahim ya samu, kuma wace irin albarka ce zuriyarsa ta samu?

6 An gaya wa Ibrahim cewa zuriyarsa za ta yi yawa kuma ta zama “kamar taurarin sama” da kuma yashin da ke bakin teku. (Far. 13:16; 22:17) A wata sassa, a zamanin Ibrahim ba zai yiwu ba ’yan adam su san yawan mutanen da za su kasance cikin wannan zuriyar ba. Amma, a ƙarshe an bayyana ainihin adadin zuriyarsa na ruhaniya. Ban da Yesu, akwai mutane 144,000.—R. Yoh. 7:4; 14:1.

7 Game da bangaskiyar Ibrahim, Kalmar Allah ta ce: “[Ibrahim] ya fa bada gaskiya ga Ubangiji; shi kuma ya lissafta wannan adalci ne gareshi.” (Far. 15:5, 6) Hakika, babu ɗan adam ɗin da adali ne sarai. (Yaƙ. 3:2) Duk da haka, domin bangaskiyar Ibrahim na musamman, Jehobah ya bi da shi kamar shi adali ne, har ya kira shi amininsa. (Isha. 41:8) An kira waɗanda suke cikin zuriya ta ruhaniya na Ibrahim tare da Yesu adilai, kuma wannan ya kawo musu albarka mai yawa da ya fi wanda Ibrahim ya samu.

8. Waɗanne albarkatai ne waɗanda suke cikin zuriyar Ibrahim za su samu?

8 An kira Kiristoci shafaffu masu adalci domin sun ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu. (Rom. 3:24, 28) A gaban Jehobah, sun kuɓuta daga zunubi kuma za a iya shafa su da ruhu mai tsarki su zama ’ya’yan Allah na ruhaniya, wato, ’yan’uwan Yesu Kristi. (Yoh. 1:12, 13) Sun shiga cikin sabon alkawari kuma sun kafa sabuwar al’umma, wato,“Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16; Luk. 22:20) Wannan ba ƙaramin gata ba ne ba! Domin waɗannan abubuwa da Allah ya yi dominsu, shafaffun Kiristoci ba su da begen zama har abada a duniya. Sun bar wannan begen don farin cikin da babu na biyunsa na yin tarayya da Yesu a lokacin Ranar Hukunci da kuma yin sarauta tare da shi a sama.—Ka karanta Romawa 8:17.

9, 10. (a) Wane lokaci ne aka fara shafa Kiristoci da ruhu mai tsarki, kuma menene ke gabansu? (b) Wane taimako ne shafaffun Kiristoci suka samu?

9 A Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an ba rukunin ’yan adam masu aminci zarafin kasancewa cikin waɗanda za su yi sarauta da Yesu a Ranar Hukunci. Almajiran Yesu kusan 120 ne suka sami ruhu mai tsarki kuma ta haka suka zama shafaffu Kiristoci na farko. Amma, wannan somawa ne kawai. Tun daga wannan lokacin, suna bukatar su nuna amincinsu ga Jehobah duk da gwajin da Shaiɗan zai kawo a kansu. Idan suna son su sami kambin rayuwa a sama suna bukatar su kasance da aminci har mutuwa.—R. Yoh. 2:10.

10 Saboda haka, Jehobah ya yi wa shafaffun Kiristoci tanadin gargaɗi da kuma ƙarfafawar da suke bukata ta Kalmarsa da kuma ikilisiyar Kirista. Alal misali, manzo Bulus ya rubuta wa shafaffun Kiristoci da ke Tassaluniki: “Kamar uba da ’ya’yan kansa, muna yi maku gargaɗi, muna ba ku ƙarfinzuciya, muna shaida, domin ku yi tafiya wadda za ta cancanta ga Allah, wanda ya kira ku zuwa cikin nasa mulki da daraja.”—1 Tas. 2:11, 12.

11. Wane rubutaccen tanadi ne Jehobah ya yi wa waɗanda suke cikin “Isra’ila na Allah”?

11 Shekaru da yawa bayan da aka zaɓi waɗanda suke cikin ikilisiyar shafaffun Kiristoci, Jehobah ya ga cewa ya dace a samu tarihi na dindindin na hidimar Yesu a duniya da kuma sha’aninsa da Kiristoci shafaffu da kuma gargaɗin da ya yi musu. Ta haka, Jehobah ya daɗa Nassosin Helenanci na Kiristoci ga Nassosin Ibrananci da ake da shi dama. Da farko an rubuta Nassosin Ibrananci ne domin al’ummar Isra’ila na dā a lokacin da suke da dangantaka na musamman da Allah. An rubuta Nassosin Helenanci ne ainihi don “Isra’ila na Allah,” waɗanda aka shafa su a matsayin ’yan’uwan Kristi da ’ya’yan Allah na ruhaniya. Hakika, wannan ba ya nufin cewa waɗanda ba Isra’ilawa ba ne ba za su iya amfana sosai daga nazarin Nassosin Ibrananci ba. Hakanan ma, Kiristocin da ba a shafa su ba da ruhu mai tsarki sun amfana sosai daga yin nazari da kuma yin rayuwar da ta dace da shawarar da ke cikin Nassosin Helenanci.—Ka Karanta 2 Timothawus 3:15-17.

12. Menene Bulus ya tuna wa Kiristoci shafaffu?

12 An kira Kiristoci na ƙarni na farko masu adalci kuma an shafa su da ruhu mai tsarki don su sami gadōnsu na samaniya. Shafa su da aka yi da ruhu bai fifita su su zama sarki bisa ’yan’uwansu shafaffu ba sa’ad da suke duniya. Babu shakka, wasu Kiristoci na farko sun mance da hakan kuma suka soma biɗar matsayin da bai dace ba tsakanin ’yan’uwansu cikin ikilisiya. Saboda haka, Bulus ya ce: “Ko yanzu kun rigaya kun ƙoshi, kun rigaya kun zama mawadata, kun yi mulki ba tare da mu ba: ni kuwa, da ma kun yi mulki, har da za mu yi mulki kuma tare da ku.” (1 Kor. 4:8) Saboda haka, Bulus ya tuna wa shafaffu na zamaninsa: “Ba sarauta mu ke yi bisa bangaskiyarku ba, amma mataimaka ne na farinzuciyarku.”—2 Kor. 1:24.

Cika Adadin da Aka Annabta

13. Ta yaya aka samu cin gaba wajen zaɓan shafaffu bayan shekara ta 33 A.Z.?

13 Ba duka Kiristoci shafaffu 144,000 ba ne aka zaɓa a ƙarni na farko ba. An ci gaba da zaɓan su har bayan mutuwar manzanni, daga baya kuma aka ɗan zaɓi wasu kaɗan. Amma an ci gaba da yin haka cikin ƙarnuka har zuwa zamaninmu. (Mat. 28:20) Daga bisani, abubuwa sun ci gaba sosai bayan da Yesu ya soma sarauta a shekara ta 1914.

14, 15. Menene ya faru a zamaninmu game da zaɓan shafaffu?

14 Da farko, Yesu ya kawar da dukan wani abin da zai yi hamayya ga sarautar Allah. (Ka Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:10, 12.) Bayan haka, ya mai da hankalinsa ga tattara sauran waɗanda za su kasance cikin Mulkinsa don cika adadi na 144,000. A tsakiyar shekara ta 1930 wannan aikin ya kusa ƙarewa kuma mutane da yawa da suke sauraron aikin wa’azi ba su da sha’awar zuwa sama. Ruhun bai shaida musu cewa su ’ya’yan Allah ba ne. (Ka gwada da Romawa 8:16.) Maimakon haka, sun fahimci cewa su “waɗansu tumaki” ne waɗanda suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya har abada. (Yoh. 10:16) Saboda haka, bayan shekara ta 1935 sai aka soma mai da hankali wajen tattara “taro mai-girma,” waɗanda manzo Yohanna ya gani a wahayi waɗanda kuma za su tsira wa “babban tsananin.”—R. Yoh. 7:9, 10, 14.

15 Amma, tun daga shekara ta 1930 an zaɓi mutane kaɗan don zuwa sama. Me ya sa? A wasu lokutta, wataƙila suna sauya mutanen da aka zaɓa a dā su je sama amma sai suka yi rashin aminci. (Ka gwada da Ru’ya ta Yohanna 3:16.) Bulus ya yi magana game da mutanen da ya sani da suka bar gaskiya. (Filib. 3:17-19) Su wanene Jehobah zai zaɓa su sauya waɗannan mutanen? Hakika, shi ne zai tsai da wannan shawarar da kansa. Duk da haka, zai dace mu san cewa ba zai zaɓi sababbi ba, sai dai irin almajiran da Yesu a lokacin da ya kafa Tuna mutuwarsa ya ce sun kasance da aminci.a—Luk. 22:28.

16. Me ya sa muke godiya game da shafaffu, kuma menene za mu iya gaskata da shi?

16 Amma kamar dai ba dukan waɗanda aka zaɓa su je sama tun shekara ta 1930 ba ne suka sauya waɗanda suka bar gaskiya ba. Babu shakka Jehobah ya tabbatar da cewa shafaffun Kiristoci za su kasance tsakaninmu a kwanaki na ƙarshe har sai an halaka “Babila Babba.”b (R. Yoh. 17:5) Muna da tabbaci cewa adadin 144,000 zai cika a lokacin da Jehobah ya ga ya dace kuma kowannensu zai yi sarauta a Mulkin sama. Mun kuma gaskata da Kalmar annabcin da ta ce rukunin taro mai girma da ke ƙaruwa zai ci gaba da kasancewa da aminci. Nan ba da daɗewa ba za su “fito daga cikin babban tsananin” da duniyar Shaiɗan za ta fuskanta kuma za su shiga sabuwar duniya ta Allah cike da farin ciki.

Gwamnatin Allah ta Sama ta Kusan Cika

17. In ji 1 Tassalunikawa 4:15-17 da Ru’ya ta Yohanna 6:9-11, menene ya faru da shafaffun Kiristocin da suka mutu da aminci?

17 Tun shekara ta 33 A.Z., dubban shafaffu Kiristoci sun nuna cikakkiyar bangaskiya kuma sun jimre cikin aminci har mutuwarsu. Waɗannan sun riga sun cancanci samun Mulki kuma babu shakka sun samu ladarsu ta zuwa sama tun somawar bayyanuwar Kristi.—Ka karanta 1 Tassalunikawa 4:15-17; Ru’ya ta Yohanna 6:9-11.

18. (a) Wane tabbaci ne shafaffu da suka rage a duniya suke da shi? (b) Ta yaya waɗansu tumaki suke ɗaukan ’yan’uwansu shafaffun Kiristoci?

18 Shafaffu da suka rage a duniya suna da tabbaci cewa idan sun kasance da aminci ba da daɗewa ba za su sami ladar tafarkinsu na aminci. Sa’ad da suke tunani game da bangaskiyar ’yan’uwansu shafaffu, miliyoyin waɗansu tumaki sun yarda da kalmomin manzo Bulus, wanda ya ce game da shafaffun da ke Tassaluniki: “Mu da kanmu muna fahariya domin ku cikin ikilisiyai na Allah, saboda hanƙurinku da bangaskiyarku cikin dukan tsanani naku da kuncin da kuke jimrewa da shi; ainihin shaida ke nan ta shari’a mai-adalci ta Allah; da nufin a maishe ku kun cancanta ga mulkin Allah, wanda ku ke shan wahala dominsa.” (2 Tas. 1:4, 5) A duk lokacin da mutum na ƙarshe cikin shafaffu ya mutu, gwamnatin Allah a sama za ta cika. Wannan abin farin ciki ne a sama da kuma duniya!

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1992, shafi na 20, sakin layi na 17 na Turanci.

b Ka duba “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Mayu, 2007, na Turanci.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Menene Allah ya bayyana wa Ibrahim game da Ranar Shari’a?

• Me ya sa aka ce Ibrahim mai adalci ne?

• Menene zuriyar Ibrahim suka samu domin amincinsu?

• Wane tabbaci ne dukan Kiristoci suke da shi?

[Hoto a shafi na 20]

Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su nace ga samun Mulki

[Hoto a shafi na 21]

Jehobah ya soma zaɓan waɗanda suke cikin zuriyar Ibrahim ta biyu a Fentakos ta 33 A.Z.

[Hotuna a shafi na 23]

Waɗansu tumaki suna godiya cewa shafaffu Kiristoci suna tare da su a wannan kwanaki na ƙarshe

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba