Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 17-19
  • Za Ka Iya Kyautata Rayuwarka Yadda Suka Yi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Kyautata Rayuwarka Yadda Suka Yi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka More Duniya Amma Ba Sosai Ba
  • “Mun Kusanci Jehobah Fiye da dā”
  • ‘Ina da Abin Biyan Bukata, Amma ba na Farin Ciki’
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • “Za Ka Iya Zama Majagaba Mai Kyau!”
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—⁠a Kasar Gana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Hidimar Majagaba Tana Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 17-19

Za Ka Iya Kyautata Rayuwarka Yadda Suka Yi?

MARC, wani ɗan’uwa a ƙasar Kanada, yana aiki da wani kamfanin da ke ƙera wata irin na’urar da masu zuwa sararin samaniya suke amfani da ita. Yana aiki na ɗan lokaci kuma shi majagaba ne na kullum. Sai wani a cikin shugabanninsa ya ce zai yi wa Marc ƙarin girma zuwa aiki na cikakken lokaci kuma za a ba shi albashi mai tsoka. Menene Marc ya yi?

Amy, wata ’yar’uwa a ƙasar Philippines ta yi hidima na majagaba na kullum sa’ad da take gab da kammala makarantarta na sakandare. Bayan haka, an ba ta wani aiki na cikakken lokaci wanda zai ɗauki lokacinta amma za ta sami kuɗi. Wane zaɓi ne Amy ta yi?

Marc da Amy sun yanke shawara dabam dabam, kuma sakamakon zaɓin da suka yi ya nuna amfanin shawarar da aka ba Kiristocin da ke Koranti na dā. Manzo Bulus ya rubuta: “[Bari] waɗanda su ke moron duniya, [su yi] kamar ba su cika moriyatata ba.”—1 Kor. 7:29-31.

Ka More Duniya Amma Ba Sosai Ba

Kafin mu tattauna abin da ya sami Marc da Amy, bari mu ɗan duba ma’anar furcin nan “duniya” (ko, koʹsmos a Helenanci) da Bulus ya yi amfani da shi a cikin wasiƙarsa ga Korinthiyawa. A wannan ayar ta Littafi Mai Tsarki, koʹsmos tana nufin tsarin duniyar da muke ciki, wadda ta haɗa da bukatun rayuwa na yau da kullum, kamar su wurin kwana, abinci, da sitira.a Dole ne mu yi aiki don samun waɗannan bukatu na yau da kullum. Kuma muna bukatar mu yi amfani da duniya don mu cika hakkinmu da ke cikin Nassi na yi wa kanmu da iyalinmu tanadi. (1 Tim. 5:8) Amma kuma ya kamata mu fahimci cewa “duniya ma tana wucewa.” (1 Yoh. 2:17) Saboda haka, muna amfani da duniya yadda ya kamata amma ba ma “cika moriyatata.”—1 Kor. 7:31.

Domin sun bi shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce kada su cika moriyar duniya, yawancin ’yan’uwa sun sake bincika yanayinsu, sun rage lokacin da suke amfani da shi a wajen aikinsu, kuma sun sauƙaƙa salon rayuwarsu. Bayan sun yi hakan, sun ga cewa sun kyautata rayuwarsu domin a yanzu suna da isashen lokaci na kasancewa da iyalinsu da kuma na yi wa Jehobah hidima. Bugu da ƙari, rayuwarsu da suka sauƙaƙa ta sa sun dogara sosai ga Jehobah. Kai ma za ka iya yin hakan, wato, za ka iya sauƙaƙa rayuwarka don ka sami ƙarin lokaci wajen yin abin da Jehobah yake so?—Mat. 6:19-24, 33.

“Mun Kusanci Jehobah Fiye da dā”

Marc, wanda muka ambata a gabatarwa ya bi shawarar Littafi Mai Tsarki na ƙin cika moriyar duniya. Ya ƙi amincewa da ƙarin girman da ake son a ba shi. Bayan wasu ’yan kwanaki, shugaban Marc ya ce zai ba shi albashi mai tsoka sosai don ya amince da sabon aikin da aka ba shi. Marc ya ce: “Wannan jarraba ce, amma na ƙi amincewa.” Ya bayyana dalilin da ya sa: “Ni da matata Paula, muna son mu bauta wa Jehobah sosai da rayuwarmu yadda ya kamata. Shi ya sa muka yanke shawarar sauƙaƙa rayuwarmu. Mun yi addu’a ga Jehobah don samun hikima na cim ma makasudinmu, kuma muka kafa ainihin ranar da za mu soma yi wa Jehobah hidima yadda ya kamata.”

Paula ta ce: “A sati ina yin aiki na kwana uku a matsayin sakatariya na asibiti kuma ina karɓan albashi mai tsoka. Kuma ina hidima na majagaba na kullum. Amma kamar Marc, ina son in ba da kaina don in bauta wa Jehobah a duk inda ake bukatar masu shelar Mulki. Duk da haka, a lokacin da na ba da takardar ajiye aiki, sai shugabana ta ce na cancanci samun damar da ta buɗe na zama babbar sakatariya. Wannan shi ne aikin sakatariya da aka fi samun kuɗi a asibitin, amma na manne wa shawarata na ajiye aikin. Sa’ad da na gaya wa shugabana dalilin da ya sa ba zan karɓi matsayin ba, ta yaba mini domin bangaskiya ta.”

Ba da daɗewa ba, Marc da Paula suka sami damar yin hidima na majagaba na musamman a wata ƙaramar ikilisiya da ke wani keɓaɓɓen wuri a ƙasar Kanada. Menene sakamakon ƙaurar da suka yi? Marc ya ce: “Bayan na bar aikin da na yi kusan rabin rayuwata ina yi, kuma ina samun isashen kuɗi, na ɗan yi shakkar yadda rayuwarmu za ta kasance a gaba, amma Jehobah ya albarkaci hidimarmu. Mun sami farin cikin taimaka wa mutane su bauta wa Allah. Hidima na cikakken lokaci ya kyautata aurenmu. Abubuwan da muke tattaunawa abubuwa ne masu muhimmanci sosai, wato, batutuwa na ruhaniya. Mun kusanci Jehobah fiye da dā.” (A. M. 20:35) Paula ta daɗa: “Idan ka bar aikin da ka ke yi da kuma gidanka, dole ne ka dogara ga Jehobah gaba ɗaya. Mun yi hakan, kuma Jehobah ya albarkace mu. ’Yan’uwanmu da suke sabuwar ikilisiyarmu sun nuna cewa suna ƙaunarmu kuma suna bukatarmu. Ƙarfin da nike amfani da shi a dā wajen aikina, a yanzu ina amfani da shi wajen taimaka wa mutane su bauta wa Allah. Yin wannan hidimar ta sa ni farin ciki sosai.”

‘Ina da Abin Biyan Bukata, Amma ba na Farin Ciki’

Amy, da muka ambata ɗazu ta zaɓi wani tafarkin dabam. Ta karɓi aiki mai kyau na cikakken lokaci da aka ba ta. Amy ta ce: “A shekara ta farko, na ci gaba da nuna ƙwazo a hidimata amma sai na ga cewa rayuwata ta kauce daga yi wa Allah hidima zuwa samun ƙarin girma. Da na sami damar samun ƙarin girma sai na soma nuna ƙwazo sosai don samun matsayi mafi girma. Yayin da ayyuka na a wajen aiki suka ƙaru, hakan ya sa ba ni da isashen lokacin yin hidima. Daga baya, sai na daina yin wa’azi gaba ɗaya.”

Sa’ad da ta tuna wannan lokacin, Amy ta ce: “Ina da kuɗi sosai. Ina yawan tafiye-tafiye kuma na more darajar da nike samu domin matsayina. Duk da haka, ba na farin ciki. Duk da cewa ina da kuɗi, ina da matsaloli masu yawa. Na yi mamakin abin da ke faruwa. Sai na fahimci cewa matsayin da nike nema a wannan duniyar ne ya sa na kusan ‘ratse daga imani.’ Domin haka, kamar yadda Kalmar Allah ta ce, na yi ‘baƙinciki mai-yawa.’”—1 Tim. 6:10.

Menene Amy ta yi? Ta ce: “Na gaya wa dattawa su taimaka mini na sake samun dagantaka da Allah kuma na soma halartar taro. A lokacin da ake wata waƙa, sai na soma kuka. Na tuna irin farin cikin da nike da shi a shekaru biyar da na yi ina majagaba duk da cewa ba ni da kuɗi a lokacin. Na san cewa ina bukatar in daina ɓata lokacina wajen neman kuɗi kuma ina bukatar in saka batutuwa na Mulki abin farko a rayuwata. Na sa a rage matsayina a wurin aiki, hakan na nufin cewa zan rasa kashi hamsin na albashi na, sai na soma yin wa’azi.” Cikin farin ciki Amy ta ce: “Na sami farin cikin yin hidima na majagaba na ɗan shekaru. A yanzu na sami gamsuwa irin wanda ban taɓa samu ba a lokacin da nike ɓata lokaci na wajen yi wa duniya aiki.”

Kana iya canja yanayinka kuma ka sauƙaƙa rayuwarka? Idan ka yi amfani da lokacin da ka ke da shi wajen faɗaɗa ayyukan Mulki, kai ma za ka kyautata rayuwarka.—Mis. 10:22.

[Hasiya]

a Dubi Insight on the Scriptures, Volume 2, pages 1207-8.

[Bayanin da ke shafi na 19]

Za ka iya canja yanayinka kuma ka sauƙaƙa salon rayuwarka?

[Box/Hoto a shafi na 19]

“Ina Jin Daɗinsa Sosai!”

David, wani dattijo Kirista da ke zaune a ƙasar Amirka yana son ya shiga hidima na cikakken lokaci kamar matarsa da ’ya’yansa. Ya nemi aiki na ɗan lokaci a kamfanin da yake aiki, kuma ya zama majagaba na cikakken lokaci. Canjin ya kyautata rayuwarsa kuwa? Bayan wasu watanni, David ya rubuta wa abokinsa cewa: “Babu abin da ya fi gamsar da ni kamar bauta wa Jehobah sosai tare da iyali na. Na ɗauka cewa zan daɗe kafin na saba da hidimar majagaba, amma ina jin daɗinsa sosai! Yana wartsakarwa sosai.”

[Hoto a shafi na 18]

Marc da Paula a hidimar fage

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba