Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 p. 29
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Za Ka Iya Kyautata Rayuwarka Yadda Suka Yi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Taimaka wa Makafi Su San Jehobah
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Yesu Kristi​—⁠Jariri Ne ko Kuma Sarki Mai Iko?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 p. 29

Ka Tuna?

Ka ji daɗin karatun Hasumiyar Tsaro na baya bayan nan? To, ka yi ƙoƙari ka ga ko za ka iya amsa waɗannan tambayoyi:

• Yaushe ne masanan taurari suka ziyarci Yesu?

Wani bugu na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shefunan nan ba su ziyarci Yesu sa’ad da yake cikin sakarkari a daren da aka haife shi ba kamar yadda makiyaya suka yi. Sun ziyarce shi ne bayan watanni.” Sa’an nan Yesu ‘yaro’ ne yana zama a gida. (Mat. 2:7-11) Da a ce an ba Yesu kyautar zinariya da kuma wasu abubuwa masu tamani a daren da aka haife shi, da Maryamu ba ta ba da hadayar tsuntsaye biyu ba kawai bayan kwanaki 40 sa’ad da ta kai Yesu haikali a Urushalima ba?—1/1, Shafi na 31.

• Menene mutane da yawa za su yi don su kyautata rayuwarsu?

Wani zai iya tambaya, ‘Zan iya canja yanayi na kuma in sauƙaƙa rayuwata kuwa?’ Amy ta yi hakan. Tana da kuɗi amma ba ta farin ciki. Ta fahimci cewa biɗan arziki a wannan duniya ya sa ta kusa ratse daga imani. Saboda haka, ta tsai da shawara cewa za ta sa abubuwa na Mulki ya zama abu na farko a rayuwarta kuma hakan ya sa ta yi hidima na majagaba na ɗan lokaci. Amy ta ce: “Yanzu na sami gamsuwa irin wanda ban taɓa samu ba a lokacin da nike ɓata lokaci na wajen yi wa duniya aiki.”—1/15, shafi na 19.

• Wace “tsara” ce Yesu yake nufi a Matta 24:34?

Yesu yakan yi amfani da kalmar nan “tsara” sa’ad da yake magana game da mugayen mutane. Amma bai ambata hakan ba sa’ad da yake magana game da almajiransa, waɗanda za a shafa su da ruhu mai tsarki. Sune za su iya bayyana abin da ke cikin Matta 24:32, 33. Saboda haka za mu iya cewa Yesu yana nufin shafaffun mabiyansa ne na ƙarni na farko da kuma na zamaninmu.—2/15, shafofi na 23-4.

• Yaya ne Shari’a ta zama mai tsaro, kamar yadda aka ambata a Galatiyawa. 3:24?

Sau da yawa a zamani dā, mai tsaro amintaccen bawa ne wanda yake kula da yaro kuma ya tabbata cewa yaron ya yi abin da mahaifinsa ke so. Akasarin haka, shari’ar tana ƙare Yahudawa daga lalata, kamar auratayya da kafirai. Amma kamar mai tsaron yaron, shari’ar za ta kasance da ɗan lokaci ne har sai Kristi ya zo.—3/1 shafofi na 18-21 na Turanci.

• Game da abin da ke cikin Yaƙub 3:17, wane hali ne ya kamata mu kasance da shi?

Idan muna son mu kasance da tsarki, dole ne mu guji miyagun abubuwa nan take. (Far. 39:7-9) Ya kamata kuma mu kasance masu zaman lafiya, mu guji abubuwan da za su kawo rashin zaman lafiya. Saboda haka, kowannenmu ya tambayi kansa: ‘An san ni da zaman lafiya ko kuma mai son tashin hankali? In yawan jayayya da mutane? Ina da saurin fushi, ko kuma Ina da yawan ɓata wa wasu rai? Ko kuma Ina saurin gafartawa, kuma ba na nacewa sai an bi ra’ayi na?’—3/15, shafofi 24-5.

• Me ya sa Yesu ya warkar da makaho da sannu sannu? (Markus 8:22-26)

Littafi Mai Tsarki bai ba da ainihin bayani ba. Amma wataƙila dalilin shi ne, Yesu ya warƙar da makahon sannu sannu don ya ba shi lokaci ya daidaita da sabon mahallinsa. Hakan ya nuna cewa Yesu yana ƙaunar wannan mutumin.—4/1, shafofi na 21.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba