Bikin Sauƙe Karatu Na Gilead Aji Na 123
An Aririci Waɗanda Suka Sauƙe Karatu Daga Makarantar Gilead “Su Soma Haƙawa”
A RANAR Asabar, 8 ga Satumba, 2007, mutane 6,352 daga ƙasashe 41 ne suka taru a wajen bikin sauƙe karatu na aji na 123 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. Da ƙarfe 10:00 na safe, mai kujeran taron, Anthony Morris wanda yana ɗaya daga cikin Hukumar Mulki ne ya marabci masu sauraro. Bayan ya yi wasu kalamai na buɗe taron, ya gabatar da mai jawabi na farko Gary Breaux wanda yana cikin Kwamitin Reshe na ƙasar Amirka.
Ɗan’uwa Breaux ya tabbatar wa ɗaliban cewa ko yaya siffarsu take, waɗanda suke yin nufin Jehobah ne kawai suke da kyau a idanunsa. (Irm. 13:11) Ya aririci ɗaliban su ci gaba da kasancewa da irin wannan kyaun. Bayan haka, Gerrit Lösch wanda yana cikin Hukumar Mulki ya nanata cewa yana da kyau mu sa rai cewa za mu sami lada sa’ad da muka bauta wa Jehobah. (Ibran. 11:6) Amma ya kamata muradinmu ya kasance na ƙauna marar son kai.
Bayan haka, William Samuelson wanda shi ne ke kula da Sashen Makarantu na Tsarin Allah, ya aririci ɗaliban su manne wa aiki mai tamani da aka ba su na yin shelar Sarkin da ke mulki kuma su ci gaba da nuna darajarsu ta wajen halinsu mai kyau.a Sam Roberson, mataimakin mai kula da Sashen Makarantu na Tsarin Allah, ya ƙarfafa ɗaliban su mai da hankali ga halaye masu kyau na mutane. Hakan zai taimaka wa ɗaliban su ‘ƙaunaci [dukan] ’yan’uwa.’—1 Bit. 2:17.
Bayan waɗannan jawaban masu motsawa, malamin makarantar Gilead Mark Noumair ya gana da yawancin ɗaliban waɗanda suka ambata abubuwan da suka shaida a hidimar fage a lokacin makarantar ta Gilead. Dukan masu sauraro sun ga cewa ɗaliban suna son hidima kuma suna da muradin taimaka wa mutane. Kent Fischer wanda ke Ofishin Bethel na Patterson ya gana da Kwamitin Reshe na ƙasashe guda uku waɗanda suke da masu wa’azi a ƙasashen waje. Kalaman waɗannan ’yan’uwan sun tabbatarwa masu sauraro waɗanda suka haɗa da iyayen yawancin ɗaliban da ke sauƙe karatu, cewa ana kula da sababbin masu wa’azi na ƙasashen waje a wuraren da suke wa’azi. Bayan haka, Izak Marais wanda ke Sashen Taimakon Masu Fassara ya gana da wasu da suka daɗe suna wa’azi a ƙasashen waje, waɗanda labaransu ya nuna wa masu sauƙe karatun irin farin cikin da za su shaida.
Jigon ainihin jawabin da ke cikin tsarin ayyukan da Geoffrey Jackson wanda ke cikin Hukumar Mulki ya bayar shi ne “Bayan Dukan Abubuwan da Kuka Ji, Menene Za Ku Yi? Ɗan’uwa Jackson, wanda ya yi shekaru 25 yana hidima a ƙasar Pasifik ta Kudu ne ya tattauna sashe na ƙarshe na Huɗuba Bisa Dutse. A wannan jawabin, Yesu ya yi magana game da mutane biyu da suka gina gidaje, ɗaya yana da hikima ɗayan kuma wawa ne. Mai jawabin ya ambata cewa wataƙila gidajen biyu suna yanki ɗaya ne. Amma, shi wawan ya gina gidansa ne a kan yashi, shi kuwa mai hikima ya haƙa ƙasa sosai har sai da ya tad da dutse wanda zai iya yin gini a kai. Sa’ad da aka yi mugun ruwa da iska, gidan da aka gina a kan dutse bai faɗi ba, amma wanda aka gina a kan yashi ya rushe.—Mat. 7:24-27; Luka 6:48.
Yesu ya bayyana cewa wawan yana kama ne da waɗanda suka saurari koyarwar Yesu kawai. Mutum mai hikima yana kama ne da waɗanda suka saurari Yesu kuma suka yi amfani da abin da suka ji. Ɗan’uwa Jackson ya gaya wa masu sauƙe karatun, “Idan kuka yi amfani da abubuwan da kuka koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki a ƙasar da za ku je wa’azi, za ku zama kamar mutumin nan mai hikima.” A ƙarshe, ya aririci ɗaliban da suka sauƙe karatu “su soma haƙawa” a ƙasashen da aka aika su yin wa’azi.
A ƙarshe, ɗaliban da suka sauƙe karatu sun karɓi satifiket da kuma wuraren da za su wa’azi, kuma Ɗan’uwa Morris ya ba da shawara na ƙarshe. Ya ƙarfafa dukan ɗaliban su ci gaba da bin Yesu kuma kada su daina dogara ga Jehobah don samun ƙarfi. Sai aka kammala bikin sauƙe karatun.
[Hasiya]
a Sashen Makarantu na Tsarin Allah, wanda yake ƙarƙashin kulawar Kwamitin Koyarwa, yana kula ne da makarantar Gilead, makarantar Kwamitin Reshe, da kuma makarantar masu kula masu ziyara.
[Akwati a shafi na 31]
BAYANAI GAME DA ƊALIBAN
Adadin ƙasashen da aka wakilta: 10
Adadin ƙasashen da aka aika su: 24
Adadin ɗalibai: 56
Avirejin shekarunsu: 33.5
Avirejin shekarunsu a cikin gaskiya: 17.9
Avirejin shekarunsu a cikin hidima na cikakken lokaci: 13.8
[Hoto a shafi na 32]
Aji na 123 na Waɗanda Suka Sauƙe Karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead
A jerin da ke ƙasa, ana soma ƙirgawa ne daga gaba zuwa baya, kuma an jera sunayen ne daga hagu zuwa dama a kowane layi.
(1) Esparza, E.; Papaya, S.; Bilal, A.; Suárez, M.; Evers, E.; Dimichino, K. (2) Rosa, M.; Fujii, R.; Ratey, O.; Leveton, J.; Van Leemputten, M. (3) Boscaino, A.; Beck, K.; Budanov, H.; Braz, C.; Peltz, K.; Siaw, A. (4) Leveton, S.; Santikko, H.; Conte, S.; Wilson, J.; Rylatt, J.; Pierce, S.; Fujii, K. (5) Rosa, D.; Boscaino, M.; Austin, V.; Rodiel, P.; Bilal, P.; Dimichino, P. (6) Ratey, B.; Czyzyk, D.; Clarke, C.; Riedel, A.; Esparza, F.; Siaw, P.; Van Leemputten, T.(7) Rodiel, J.; Evers, J.; Green, J.; Czyzyk, J.; Santikko, M.; Rylatt, M. (8) Peltz, L.; Austin, D.; Riedel, T.; Beck, M.; Pierce, W.; Conte, S.; Green, S. (9) Suárez, J.; Clarke, J.; Papaya, S.; Budanov, M.; Wilson, R.; Braz, R.