Bikin Sauke Karatu Na Gilead Aji Na 125 An Ƙarfafa Masu Wa’azi A Ƙasashen Waje Su Zama Kamar Irmiya
“WANNAN ajin na Gilead yana da muhimmanci a tarihi,” in ji Geoffrey Jackson da ke cikin Hukumar Mulki. Yana jawabi ne ga mutane 6,156 da suka halarci bikin sauke karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead, aji na 125 a ranar 13 ga Satumba, 2008. Duk da ɗalibai 56 da suka sauke karatu daga wannan ajin, Makarantar Gilead ta aika masu wa’azi a ƙasashen waje fiye da dubu takwas zuwa “iyakan duniya”!—A. M. 1:8.
Ɗan’uwa Jackson, wanda shi ne mai kujerar sauke karatun, ya yi tambaya, “Yabo zai iya kyautata hidimarku kuwa?” Bayan haka, ya ambata abubuwa huɗu da suke kawo yabo: kasancewa da halin da ya dace, nuna misali mai kyau, koyar da ainihin abin da ke cikin Kalmar Allah, da kuma mai da hankali ga sanar da sunan Jehobah.
David Schafer, wanda yake hidima tare da Kwamitin Koyarwa, ya tattauna jigon nan “Za Ku Fahimci Komai?” Ya tabbatar wa ɗaliban Gilead cewa za su iya ‘fahimtar komai’ da ake bukata a hidimar wa’azi a ƙasashen waje idan suka ci gaba da biɗar Jehobah kuma suka miƙa kai cikin tawali’u ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”—Mis. 28:5; Mat. 24:45.
Bayan haka, John E. Barr da ke cikin Hukumar Mulki ya tattauna jigon nan “Kada Ku Bari Wani Abu Ya Raba Ku da Ƙaunar Allah.” Shawara irin ta mahaifi da ɗan’uwa Barr ya ba da ta sauƙaƙa duk wani tsoro da ɗaliban da kuma iyayensu suke ji game da abubuwan da sababbin masu wa’azi a ƙasashen wajen za su iya fuskanta a inda aka aika su. Ya bayyana cewa, “kasancewa cikin ƙaunar Allah, wuri ne mai kyau na kwanciyar hankali da za mu kasance a rayuwarmu.” Babu abin da zai iya raba masu wa’azi a ƙasashen waje da ƙaunar Allah sai idan sun raba kansu da Allah.
Sam Roberson wanda ke hidima a Sashen Makarantun Hidima ta Allah ya ƙarfafa masu sauraronsa su yafa “tufa mafi kyau.” Ta wajen nazarin abin da Yesu ya yi da kuma yin amfani da shi, masu sauke karatu suna iya “yafa Ubangiji Yesu Kristi.” (Rom. 13:14) Sai William Samuelson, mai kula da Sashen Makarantun Hidima ta Allah ya nanata abin da ke sa mutum ya kasance mai daraja. Ba ra’ayin ’yan adam ba amma ra’ayin Allah ne ke sa mutum ya kasance da daraja.
Michael Burnett, ɗaya cikin malaman, ya gana da ɗaliban su ba da labarin aikinsu na wa’azi a lokacin makarantar. Ko da yake sa’ad da suke Makarantar Gilead a Patterson, New York, an ba yawancin ɗaliban yankin da aka yi wa’azi a kai a kai, sun samu waɗanda suka saurara. Ɗan’uwa Gerald Grizzle na Ofishin Taron Gunduma ya gana da ’yan’uwa maza uku da suka halarci Makarantar Waɗanda suke cikin Kwamitin Reshe. Furcinsu ya taimake waɗanda suke sauke karatu na Gilead su kasance a shirye don abin da za su fuskanta a aikinsu na ƙasashen waje.
David Splane wanda yake cikin Hukumar Mulki da ya sauke karatu a aji na 42 na Gilead ya ba da jawabi mai jigo “Ku Zama Kamar Irmiya.” Ko da yake Irmiya ya ji tsoro game da aikinsa, Jehobah ya ƙarfafa shi. (Irm. 1:7, 8) Allah zai yi hakan ga sababbi masu wa’azi a ƙasashen waje. Ɗan’uwa Splane ya ce: “Idan kuna samun matsala da wani, ku zauna ku rubuta halaye goma da kuke so game da mutumin. Idan ba ku sami goma ba, hakan yana nufin cewa ba ku san mutumin da kyau ba.”
Irmiya ya sadaukar da kansa. Sa’ad da yake son ya daina aikin, ya yi addu’a kuma Jehobah ya kasance tare da shi. (Irm. 20:11) Ɗan’uwa Splane ya ce: “Sa’ad da kuka yi sanyin gwiwa, ku tattauna batun da Jehobah. Za ku yi mamaki yadda Jehobah zai taimake ku.”
A ƙarshen bikin sauke karatun, mai kujere ya tuna wa masu sauraro cewa waɗanda suke sauke karatu sun koyi hanyoyi da yawa da za su sa mutane su yabe su. Sa’ad da mutane suka san za su iya amince da masu wa’azi a ƙasar waje, saƙonsu zai kasance da iko sosai.—Isha. 43:8-12.
[Akwati da ke shafi na 22]
BAYANAI GAME DA ƊALIBAN
Adadin ƙasashen da suka wakilta: 6
Adadin ƙasashen da aka aika su: 21
Adadin ɗalibai: 56
Avirejin shekarunsu: 32.9
Avirejin shekarunsu a cikin gaskiya: 17.4
Avirejin shekarunsu a cikin hidima na cikakken lokaci: 13
[Hotunan da ke shafi na 23]
Aji na 125 na Waɗanda Suka Sauke Karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead
A jerin da ke ƙasa, ana soma ƙirgawa ne daga gaba zuwa baya, kuma an jera sunayen ne daga hagu zuwa dama a kowane layi.
(1) Hodgson, A.; Wall, A.; Beerens, K.; Hortelano, M.; Newman, L.; De Caso, A. (2) Jenkins, J.; Jarzemski, T.; Méndez, N.; Corona, V.; Canalita, L. (3) Fryer, H.; Savage, M.; Tidwell, K.; Erickson, N.; Dyck, E.; McBeath, R. (4) Perez, L.; Puse, L.; Skidmore, A.; Young, B.; McBride, N.; Rondón, P.; Goodman, E. (5) Beerens, M.; Ferguson, J.; Pearson, N.; Chapman, L.; Wardle, J.; Canalita, M. (6) Perez, P.; De Caso, D.; Young, T.; Rondón, D.; Goodman, G.; Jenkins, M.; Dyck, G. (7) Corona, M.; Wall, R.; Puse, S.; Méndez, F.; Jarzemski, S.; Savage, T. (8) Newman, C.; Ferguson, D.; Skidmore, D.; Erickson, T.; McBride, J.; Pearson, M.; Chapman, M. (9) Hodgson, K.; Wardle, A.; McBeath, A.; Tidwell, T.; Fryer, J.; Hortelano, J.