Ka Bi Umurnin Allah A Dukan Abu
“Gama wannan Allah Allahnmu ne har abada abadin: Za ya zama ja gabanmu har zuwa mutuwa.”—ZAB. 48:14.
1, 2. Me ya sa ya kamata mu bi umurnin Jehobah maimakon mu dogara ga hikimarmu, kuma waɗanne tambayoyi ne za a tattauna?
SA’DA DA muke tunani a kan abubuwan banza ko kuma masu la’ani, babu wuya mu yaudari kanmu. (Mis. 12:11) Sa’ad da muke so lalle mu yi abin da bai dace da Kirista ya yi ba, zuciyarmu za ta iya ba mu kyawawan dalilan yin haka. (Irm. 17:5, 9) Domin haka, mai zabura ya nuna hikima sa’ad da ya yi addu’a ga Jehobah: “Ka aiko da haskenka da gaskiyarka; su bishe ni.” (Zab. 43:3) Maimakon ya dogara ga na sa hikima ya dogara ga Jehobah, kuma ya yi masa ja-gora. Ya kamata mu dogara ga Allah kamar yadda mai zabura ya yi, don ya ja-gorance mu.
2 Me ya sa ya kamata mu dogara ga umurnin Jehobah fiye da dukan wani umurni? Yaushe ya kamata mu biɗi umurni? Wani hali ne ya kamata mu nuna don mu amfana daga umurnin, kuma yaya Jehobah yake ja-gorarmu a yau? Za a tattauna waɗannan tambayoyi masu muhimmanci a wannan talifi.
Me Ya Sa Ya Kamata Mu Dogara ga Umurnin Jehobah?
3-5. Me ya sa ya kamata mu dogara ga umurnin Jehobah?
3 Jehobah shi ne Ubanmu na samaniya. (1 Kor. 8:6) Ya san kowannen mu sosai kuma yana ganin zuciyarmu. (1 Sam. 16:7; Mis. 21:2) Sarki Dauda ya ce wa Allah: “Zamana da tashina ka sani, kā fahimci tunanina tun daga nesa. Gama babu wata magana da ke bakina, Sai dai, ka san ta duk, ya Ubangiji.” (Zab. 139:2, 4) Tun da Jehobah ya san mu sosai kada mu yi shakka cewa ya san abin da zai amfane mu. Ban da ma haka, Jehobah ya fi kowa hikima. Yana ganin kome, yana ganin fiye da duk wani ɗan adam, kuma ya san ƙarshen kowane abu daga farkonsa. (Isha. 46:9-11; Rom. 11:33) ‘Allah kaɗai ne mai-hikima.’—Rom. 16:27.
4 Bugu da ƙari, Jehobah yana ƙaunarmu kuma koyaushe yana son abin da ya fi mana kyau. (Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:8) A matsayinsa na Allah mai ƙauna, yana yi mana karimci. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana sabkowa daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙ. 1:17) Waɗanda suka bi umurnin Allah za su amfana sosai daga karimcinsa.
5 Daga bisani, Jehobah shi ne Maɗaukaki. Saboda haka ne mai zabura ya ce: “Mai-zama cikin sitirar Maɗaukaki, za ya dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka. Zan ce da Ubangiji, shi ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareshi ni ke dogara.” (Zab. 91:1, 2) Idan muka bi umurnin Jehobah, muna neman mafaka ne a wajen Allah da ba zai taɓa kasawa ba. Idan ma muka fuskanci hamayya, Jehobah zai taimakemu. Bai zai bashe mu ba. (Zab. 71:4, 5; Ka karanta Misalai 3:19-26.) Hakika, Jehobah ya san abin da ya fi mana kyau, yana son abin da ya fi mana kyau, kuma yana da ikon ya yi mana tanadin abin da ya fi mana kyau. Wauta ce mu ƙi bin umurninsa! Amma, a yaushe muke bukatar wannan umurni?
A Yaushe Muke Bukatar Umurni?
6, 7. Yaushe muke bukatar umurnin Jehobah?
6 Hakika, muna bukatar umurni daga Allah koyaushe a rayuwarmu, daga kuruciyarmu har zuwa tsufa. Mai zabura ya ce: “Wannan Allah Allahnmu ne har abada abadin: Za ya zama ja gabanmu har zuwa mutuwa.” (Zab. 48:14) Kamar mai zabura, Kiristoci masu hikima suna neman umurni daga Allah.
7 Hakika, da akwai lokacin da muke bukatar taimako da gaggawa. A wani lokaci muna fuskantar “ƙunci,” wataƙila saboda tsanani da muke fuskanta, cuta mai tsanani, ko kuma rashin aiki dare ɗaya. (Zab. 69:16, 17) A wannan lokaci, yana da kyau mu dogara ga Jehobah, da tabbaci cewa zai ƙarfafamu mu jimre kuma zai taimakemu mu yanke shawara mai kyau. (Ka karanta Zabura 102:17.) Har ila, muna bukatar taimakonsa a wasu abubuwa. Alal da misali, idan za mu yi wa maƙwabtanmu wa’azi game da bisharar Mulkin, muna bukatar taimakon Jehobah don bishararmu ya amfana. Kuma idan muna da shawara da za mu yanke ko game da nishaɗi, sa tufafi da kuma kwalliya, abokantaka, aiki, ilimi, da wasu abubuwa, za mu kasance masu hikima idan muka bi umurnin Jehobah. Hakika, muna bukatar umurni a dukan fasalolin rayuwanmu.
Haɗarin Ƙin Bin Umurnin Allah
8. Menene cin ’ya’yan itace da aka haramta da Hauwa’u ta yi yake nufi?
8 Ka tuna, cewa muna bukatar mu nuna muna son mu bi umurnin Jehobah. Allah ba zai tilasa mana ba idan ba ma so. Wadda ta fara ƙin bin umurnin Jehobah ita ce Hauwa’u, kuma abin da ta yi ya nuna cewa irin wannan shawara ba shi da kyau. Ka yi tunanin manufar abin da ta yi. Hauwa’u ta ci ’ya’yan itace da aka haramta saboda tana so ta ‘zama kamar Allah, ta san nagarta da mugunta.’ (Far. 3:5) Da ta yi haka, ta ɗaura kanta ne a matsayin Allah, tana so ta yanke wa kanta shawara game da abin da ke nagarta da mugunta maimakon ta bi umurnin Jehobah. Da haka, ta ƙi bin ikon mallakar Jehovah. Tana so ta zama mai ikon kanta. Mijinta Adamu ma ya bi wannan tafarki na tawaye.—Rom. 5:12.
9. Idan muka ƙi bin umurnin Jehobah, menene muke nuna wa, kuma me ya sa hakan wauta ce ƙwarai?
9 Idan ba mu bi umurnin Jehobah ba yau, mu ma muna nuna cewa bai isa ya ba mu umurni ba. Alal da misali, ka yi tunanin wani da yake son kallon hotunan batsa. Idan yana zuwa taron Kirista, ya san umurnin Jehobah game da wannan abu. Kada a ambata kalaman banza, balle ma a zuba musu ido da sha’awa. (Afis. 5:3) Ta wajen ƙin umurnin Jehobah, wannan mutumin yana ƙin ikon mallakar Jehovah ne, kuma yana ƙin shugabancinsa. (1 Kor. 11:3) Hakan wauta ce ƙwarai, tun da Irmiya ya ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irm. 10:23.
10. Me ya sa ya kamata mu yi amfani da ’yancin da muke da shi na zaɓe a hanya da ta dace?
10 Wasu za su ƙi yarda da abin da Irmiya ya ce, suna ganin cewa tun da Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓe, bai kamata ya zarge mu idan muka ƙi yin amfani da shi ba. Amma, kada ka mance cewa wannan ’yancin zaɓen hakki ne kuma kyauta ce. Za mu ba da lissafin abubuwan da muke furtawa da kuma abubuwan da muke yi. (Rom. 14:10) Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” Ya kuma ce: “Daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha.” (Mat. 12:34; 15:19) Hakika, kalamanmu da ayyukanmu suna nuna yanayin zuciyarmu. Suna nuna ainihi irin mutane da muke. Shi ya sa Kirista mai hikima yakan bi umurnin Jehobah a dukan abubuwa. A haka, Jehobah ya ga cewa shi mutumi ne mai ‘zuciyar kirki’ kuma zai ‘kyautata’ shi—Zab. 125:4.
11. Menene muka koya daga tarihin Isra’ilawa?
11 Ka tuna da tarihin Isra’ilawa. Sa’ad da wannan al’ummar ta bi dokokin Jehobah, Jehobah ya kāre ta. (Josh. 24:15, 21, 31) Amma a kai a kai ba su yi amfani da ’yancinsu na zaɓe a hanyar da ta dace ba. A zamanin Irmiya Jehobah ya ce musu: “Ba su kula ba, ba su kuwa karkata kunne ba, amma suka bi nasu shawara da taurin zuciyassu mai-mugunta, suka yi baya baya, ba su yi gaba ba.” (Irm. 7:24-26) Abin baƙin ciki ne! Saboda taurin kai ko kuma don son ra’ayinmu, kada mu ƙi umurnin Jehobah mu bi na mu shawarar don hakan zai sa mu yi ‘baya baya, ba gaba ba’!
Menene Ake Bukata Don a Bi Umurnin Allah?
12, 13. (a) Menene ya sa muke so mu bi umurnin Jehobah? (b) Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci?
12 Ƙaunarmu ga Jehobah ce take sa mu bi umurninsa. (1 Yoh. 5:3) Amma, Bulus ya ambata wani abu da muke bukata sa’ad da ya ce: “Bisa ga bangaskiya mu ke tafiya ba bisa ga gani ba.” (2 Kor. 5:6, 7) Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci? Jehobah yana bishe mu “cikin hanyoyin adilci,” amma waɗannan hanyoyin ba sa nufin samun arziki ko kuma mukami a wannan duniya. (Zab. 23:3) Saboda haka, ya kamata mu kasance da bangaskiya sosai don albarkar da Jehobah zai ba wa masu bauta masa. (Ka karanta 2 Korinthiyawa 4:17, 18.) Kuma bangaskiya tana taimakonmu mu gamsu da abu na biyan bukata da muke da su.—1 Tim. 6:8.
13 Yesu ya nuna cewa bauta ta gaskiya ta ƙunshi sadaukarwa, kuma hakan na bukatar kasancewa da bangaskiya. (Luk 9:23, 24) Wasu amintattu masu bauta sun sadaukar da kai sosai, sun jimre talauci, zalunci, nuna bambanci, har da tsanantawa mai tsanani. (2 Kor. 11:23-27; R. Yoh. 3:8-10) Bangaskiya mai ƙarfi ne za ta sa su jimre da farin ciki. (Yaƙ. 1:2, 3) Bangaskiya mai ƙarfi ne ta sa muka tabbata cewa bin umurnin Jehobah a koyaushe ne ya fi kyau. Domin amfaninmu ne a koyaushe. Muna da tabbaci cewa albarkar da waɗanda suka jimre za su samu ya fi wahalar da suke fuskanta yanzu.—Ibran. 11:6.
14. Me ya sa dole Hajaratu ta nuna tawali’u?
14 Ka yi la’akari kuma da muhimmancin tawali’u a wajen bin umurnin Jehobah. Labarin Hajaratu baiwar Saratu ya nuna hakan. Sa’ad da Saratu ta ga ba za ta haihu ba, sai ta ba Ibrahim Hajaratu, kuma Hajaratu ta sami ciki daga Ibrahim. Sai Hajaratu ta fara yi wa uwargijiyarta wulakanci. A sakamakon haka, Saratu “ta yi mata ƙanƙanci,” har ta gudu. Wani mala’ikan Jehobah ya ce wa Hajaratu: “Ki koma wurin uwargijiyarki, ki kwantadda kanki a hannunta.” (Far. 16:2, 6, 8, 9) Wataƙila Hajaratu da ba wannan shawarar za ta so ba. Saboda idan tana son ta bi umurnin mala’ikan, dole ne ta daina girman kai. Duk da haka, Hajaratu ta ƙaskantar da kanta ta yi abin da mala’ikan ya ce, kuma ta haifi ɗanta Isma’ilu a gidan babansa.
15. Ka kwatanta wasu yanayi da ya sa bin umurnin Jehobah yake bukatar kasancewa da tawali’u a gare mu a yau?
15 Bin umurnin Jehobah yana nufin dole muma mu nuna tawali’u. Dole ne wasu su yarda cewa Jehobah ba ya son irin nishaɗi da suke so. Mai yiwuwa wani Kirista ya ɓata wa wani rai kuma yana bukatar ya nemi gafara. Ko kuma ya yi wani kuskure kuma yana bukatar ya amince da hakan. Idan wani ya yi zunubi mai tsanani fa? Ya kamata ya ƙaskantar da kansa ya sanarwa dattawa zunubin da ya yi. Wataƙila an yi wa wani yankan zumunci. Idan yana son a dawo da shi a cikin ikilisiya, dole ne ya ƙaskantar da kansa ya nuna ya tuba kuma ya canja halayensa. Kalaman Misalai 29:23 suna ƙarfafawa a irin waɗannan yanayin ne da kuma wasu, ta ce: “Girman kai na mutum za ya ƙasƙantadda shi: Amma mai-tawali’u za ya sami girma.”
Ta Yaya ne Jehobah Yake Mana Ja-gora?
16, 17. Ta yaya za mu amfana da kyau daga Littafi Mai Tsarki da ya ƙunshi ja-gora daga Allah?
16 Wani tushen ja-gora mafi girma shi ne daga Littafi Mai Tsarki, wato, hurarren Kalmar Allah. (Ka karanta 2 Timothawus 3:16, 17.) Don mu amfana daga Kalmar Allah, kada mu jira sai muna cikin yanayi mai wuya kafin mu nemi taimako daga Nassosi. Maimakon haka, ya kamata mu kasance masu karatun Littafi Mai Tsarki a kowace rana. (Zab. 1:1-3) A haka, za mu fahimci abubuwan da suke cikin Kalmar Allah. Za mu kasance da ra’ayin Allah, kuma za mu kasance a shirye mu fuskanci matsaloli da za su zo.
17 Bugu da ƙari, yana da kyau mu yi bimbini bisa abin da muka karanta a cikin Nassosi kuma mu yi addu’a game da shi. Sa’ad da muka yi bimbini bisa ayoyin Littafi Mai Tsarki, muna yin tunanin yadda za mu yi amfani da su a kowane yanayi. (Zab. 77:12) Idan muka fuskanci matsaloli masu tsanani, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah, mu roƙe shi ya taimakemu mu sami irin ja-gorar da muke bukata. Ruhun Jehobah zai taimakemu mu tuna da ƙa’idodi na Nassi da muka taɓa karantawa a cikin Littafi Mai Tsarki ko kuma a cikin littattafai da suke bayani a kan Littafi Mai Tsarki.—Ka karanta Zabura 25:4, 5.
18. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake amfani da ’yan’uwancinmu na Kirista don yi mana ja-gora?
18 ’Yan’uwancinmu na Kirista shi ma wata hanya ce da za mu iya neman ja-gorar Jehobah. Wani fanni ’yan’uwancinmu mai muhimmanci shi ne “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da wakilinsa Hukumar Mulki, wanda yake yin tanadin abinci na ruhaniya a cikin littattafai da kuma ayyukan tsari a taro na ikilisiyoyi da kuma mayan taro. (Mat. 24:45-47; gwada da A. M. 15:6, 22-31.) Bugu da ƙari, a cikin ikilisiyar Kirista akwai dattawa waɗanda suka ƙware wajen taimako da kuma shawara daga Nassi. (Isha. 32:1) Matasa a cikin iyalin Kirista suna da ƙarin gata mai muhimmanci. Iyayensu masu bi hanya ne da Allah ya ba su domin su sami ja-gora kuma ana ƙarfafa su a kullum su bi wannan.—Afis. 6:1-3.
19. Wace albarka ce muke more wa saboda da mun ci gaba da bin umurnin Jehobah?
19 Hakika, Jehobah yana yi mana ja-gora a hanyoyi dabam dabam, kuma ya kamata mu yi ƙoƙari mu amfana da su. Sa’ad da Isra’ila suka kasance da aminci, Sarki Dauda ya ce: “Ubanninmu suka dogara gareka: Suka yi dogara, ka kuwa cece su. Suka tada murya gareka, suka tsira: Suka dogara gareka, ba su kumyata ba.” (Zab. 22:3-5) Idan muka dogara ga umurnin Jehobah, mu ma ba za mu ji ‘kunya ba.’ Ba za mu yi sanyin gwiwa a begen da muke da shi ba. Idan muka ‘danƙa ma Ubangiji tafarkinmu,’ maimakon mu dogara ga hikimarmu, za mu sami albarka masu kyau yanzu. (Zab. 37:5) Idan muka yi biyayya ga Allah kuma muka jimre don ƙaunarsa, za mu amfana daga albarkar nan har abada. Sarki Dauda ya rubuta: “Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba; ana kiyaye su har abada: . . . Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zab. 37:28, 29.
Za Ka Iya Bayani?
• Me ya sa muka dogara ga umurnin Jehobah?
• Menene muke nufi idan muka ƙi bin umurnin Jehobah?
• A waɗanne yanayi ne Kirista yake bukata ya kasance da tawali’u?
• Ta yaya ne Jehobah yake yi mana ja-gora a yau?
[Hotuna a shafi na 8]
Kana bin ja-gorar Jehobah a dukan rayuwarka?
[Hoto a shafi na 9]
Hauwa’u ta ƙi bin umurnin Jehobah
[Hoto a shafi na 10]
Wane hali ne ya kamata Hajaratu ta kasance da shi idan tana son ta bi umurnin mala’ikan?