Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp24 Na 1 pp. 6-9
  • Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MUNA BUKATAR JA-GORANCIN ALLAH
  • LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊI ABIN DA ALLAH YAKE SO MU YI
  • A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Wajibi Ne Ka Zabi Irin Shawarwarin da Za Ka Yanke
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2024
  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwata?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ka Bi Umurnin Allah A Dukan Abu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2024
wp24 Na 1 pp. 6-9

Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki

Idan muka yanke shawara bisa ga raꞌayinmu da na wasu kawai, ba za mu kasance da tabbaci cewa zaɓinmu zai kawo mana sakamako mai kyau ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya sa. Ban da haka ma, yana ɗauke da shawarwarin da za su taimaka mana a rayuwa, kuma hakan zai sa mu yi farin ciki.

MUNA BUKATAR JA-GORANCIN ALLAH

A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobaha Allah ya bayyana cewa yana so ꞌyan Adam su nemi taimakon daga wurinsa, maimakon su ja-goranci kansu. (Irmiya 10:23) Shi ya sa ya ba da shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Yana ƙaunar ꞌyan Adam kuma ba ya so mu yanke shawarwarin da za su sa mu baƙin ciki kuma mu sha wahala a rayuwa. (Maimaitawar Shariꞌa 5:29; 1 Yohanna 4:8) Ban da haka, shi ne Mahaliccinmu, yana da hikima kuma ya san abin da zai fi amfanar mu. (Zabura 100:3; 104:24) Duk da haka, Allah ba ya tilasta wa mutane su bi ƙaꞌidodinsa.

Jehobah ya ba mata da miji na farko, wato Adamu da Hauwaꞌu duk abin da suke bukata da zai sa su farin ciki. (Farawa 1:​28, 29; 2:​8, 15) Kuma ya ba su umurni da ya so su bi. Amma, ya ba su ꞌyanci su zaɓa ko za su bi umurninsa ko aꞌa. (Farawa 2:​9, 16, 17) Abin baƙin ciki shi ne, Adamu da Hauwaꞌu sun zaɓi su bi nasu raꞌayin maimakon na Allah. (Farawa 3:6) Mene ne sakamakon? Shin mutane suna farin ciki don suna yin duk abin da suke gani ya dace? Aꞌa. A cikin shekarun da suka shige, mun gano cewa ƙin bin ƙaꞌidodin Allah ba ya kawo farin ciki da kwanciyar hankali na dindindin.—Mai-Waꞌazi 8:9.

Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarar da muke bukata don yanke shawarwari masu kyau da za su taimaka mana ko a ina ne muke da zama ko daga ina ne muka fito. (2 Timoti 3:​16, 17; ka duba akwatin “Littafi Don Dukan Mutane.”) Ka ga yadda Littafi Mai Tsarki yake hakan.

Ka ƙara koyan dalilin da ya sa ya dace da aka kira Littafi Mai Tsarki “kalmar Allah.”—1 Tasalonikawa 2:13. Ka kalli bidiyon Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki? a dandalin jw.org/ha.

LITTAFI DON DUKAN MUTANE

Mahaliccinmu mai hikima da ƙauna ya tabbata cewa dukan mutane sun sami damar sanin ƙaꞌidodinsa. Ka yi laꞌakari da waɗannan abubuwa game da Littafi Mai Tsarki:

Mutane da suka fito daga kasashe dabam-dabam suna karanta Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki kala-kala a gaban mutanen.
  • 3,500+ Adadin harsuna da aka wallafa wani sashen Littafi Mai Tsarki, hakan ya sa ya zama littafin da aka fi fassarawa a duniya.

  • 5,000,000,000+ Adadin Littafi Mai Tsarki da aka buga, wannan ya sa ya zama littafin da aka fi rarrabawa a dukan duniya.

Littafi Mai Tsarki ba ya ɗaukaka wata ƙasa ko kabila ko kuma alꞌada ba. Hakan ya nuna cewa littafi ne don dukan mutane.

Ka karanta Littafi Mai Tsarki (cikin harsuna fiye da 250) a dandalin jw.org

Wani mutum yana bin abin da yake karantawa a Littafi Mai Tsarki da yatsansa.

WASU SUNA GANIN LITTAFI MAI TSARKI BA ZAI TAIMAKA MUSU BA

Wasu mutane suna ganin ba za su iya samun shawara mai kyau a Littafi Mai Tsarki ba. Suna iya faɗin waɗannan abubuwa.

Wani zai iya ce: “Ayoyin Littafi Mai Tsarki ba su jitu da juna ba.”

Gaskiyar: Da farko, wani zai iya gani kamar akwai ayoyin da ba su jitu da juna ba. Amma, idan ka lura da yadda aka rubuta su da kuma lokacin da aka rubuta su, za ka ga cewa a gaskiya sun jitu.

Don ka ga wasu misalai, ka karanta talifin nan “Akwai Ayoyi a Cikin Littafi Mai Tsarki da Ba Su Jitu da Juna Ba?” da ke dandalin jw.org/ha.

Wani zai iya ce: “Mutanen da suke cewa suna bin Littafi Mai Tsarki, su ma suna yin abubuwa marasa kyau, don haka ba ya taimakawa.”

Gaskiyar: Bai kamata a gan laifin Littafi Mai Tsarki don mugun halayen waɗanda ba sa bin koyarwarsa ba. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane da yawa har da shugabannin addini da suke cewa suna bin Littafi Mai Tsarki ba sa yin abubuwan da ya faɗa. Ya kuma ce hakan zai sa a “rena” koyarwarsa.”—2 Bitrus 2:​1, 2.

Don ka ga wani misali game da yadda shugabannin addini da yawa ba sa bin koyarwar Littafi Mai Tsarki, ka karanta talifin nan “Is Religion Just Another Big Business?” da ke dandalin jw.org.

Wani zai iya ce: “Mutanen da suke bin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba sa daraja wasu da ba sa yin hakan.”

Gaskiyar: Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa mu mu daraja mutane. Ba ya son mu riƙa. . .

  • ganin kamar mun fi wasu.—Filibiyawa 2:3.

  • rena mutanen da ba sa bin abubuwan da muka yi imani da su.—1 Bitrus 2:17.

  • tilasta wa mutane su amince da raꞌayinmu.—Matiyu 10:14.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya damu da mutane, shi ya sa yake nuna musu alheri da adalci, kuma yana so mu riƙa yi wa mutane hakan.—Romawa 9:14.

Don samun ƙarin bayani, ka karanta talifin nan “Yin Hakuri da Mutane​—Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Mana” da ke dandalin jw.org/ha.

LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊI ABIN DA ALLAH YAKE SO MU YI

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da dangantakar Jehobah da ꞌyan Adam tun daga farko. Abin da ke cikinsa ya taimaka mana mu fahimci abin da ya dace a gaban Allah da abin da bai dace ba. Ban da haka, za mu fahimci abin da zai amfane mu da kuma abin da zai jawo mana lahani. (Zabura 19:​7, 11) Za mu koyi ƙaꞌidodin da za mu yi amfani da su a kowane lokaci kuma za su taimaka mana mu yi zaɓi masu kyau a rayuwa.

Alal misali, ka yi laꞌakari da shawara da ke Karin Magana 13:20: “Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai lalace.” Wannan shawarar ta dace da zamanin nan, kamar yadda take a dā. Littafi Mai Tsarki yana cike da irin waɗannan ƙaꞌidodi masu kyau.—Ka duba akwatin “Littafi Mai Tsarki Yana da Amfani a Koyaushe.”

Amma kana iya yin tunani, ‘Ta yaya zan tabbata cewa shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mini a yau?’ A talifi na gaba za a tattauna misalan wasu mutane.

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.—Zabura 83:18.

LITTAFI MAI TSARKI YANA DA AMFANI A KOYAUSHE

Ko da yake an kammala rubutun Littafi Mai Tsarki cikin shekaru 2,000 da suka shige, shawarwarinsa suna da amfani har wa yau. Har ila mutane suna so su kasance da farin ciki kuma su yi rayuwa mai kyau. (Mai-Waꞌazi 1:9) Shawarwarin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu cim ma hakan.

Faɗin Gaskiya

  • “Nufinmu shi ne mu aikata abin da yake daidai cikin ayyukanmu duka.”—Ibraniyawa 13:18.

  • “Kada mai sata ya ƙara yin sata. A maimakon haka sai ya yi aikin gaskiya.”—Afisawa 4:28.

Dangantaka da Mutane

  • “Kada ka yi wa kanka kaɗai abu mai kyau, amma ka yi wa ɗanꞌuwanka.” —1 Korintiyawa 10:24.

  • “Kuna ta yin haƙuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa.”—Kolosiyawa 3:13.

Yadda Za Mu Yanke Shawarwari

  • “Marar tunani yakan gaskata kome, amma mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.”—Karin Magana 14:15.

  • “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.”—Karin Magana 22:3.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba