Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 3 pp. 12-14
  • A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHAWARA DAGA WANDA YA FI MU HIKIMA
  • Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2024
  • Mene Ne Ra’ayinka Game Da Littafi Mai Tsarki?
    Mene Ne Ra’ayinka Game Da Littafi Mai Tsarki?
  • “Masu Tawali’u Za Su Gāji Kasan”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Menene Dukan Waɗannan Abubuwa Ke Nufi?
    Ka Zauna A Faɗake!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 3 pp. 12-14
Wani mutum yana karanta Littafi Mai Tsarki.

A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?

Kamar yadda muka tattauna a baya, mutane sun yi ƙoƙarin more rayuwa ta wurin dogara da ilimi da kuɗi da zama mutanen kirki da kuma neman yin sa’a. Amma wanda yake bin waɗannan hanyoyin don ya more rayuwa, kama yake da mutumin da yake so ya je inda bai taɓa zuwa ba, sai ya tare wanda bai san hanya ba yana tambayarsa inda zai bi. Ba inda za mu sami shawara mai kyau da za ta taimaka mana mu more rayuwa a nan gaba ke nan? A’a!

SHAWARA DAGA WANDA YA FI MU HIKIMA

In muna son mu yi wani abu, mukan nemi shawara daga wanda ya girme mu kuma ya fi mu hikima. A yau ma, za mu sami shawara mai kyau a kan yadda za mu more rayuwa a nan gaba idan muka tuntuɓi wani da ya girme mu kuma ya fi mu hikima. Albishirin shi ne, akwai wani da ya girme mu kuma ya fi mu hikima da zai iya taimaka mana. An rubuta shawarwarin da ya ba mu a wani littafi da ake kira Littafi Mai Tsarki. Littafin nan ya yi wajen shekaru 3,500 yanzu.

Me ya sa za ka iya gaskata Littafi Mai Tsarki? Domin mawallafinsa ya fi kowa daɗewa da hikima a sama da ƙasa. An kira shi “Wanda Yake Tun Dā” da kuma “marar farko marar ƙarshe.” (Daniyel 7:9; Zabura 90:2) Shi ne “Mahaliccin sammai, Allah kaɗai, Mai siffata duniya.” (Ishaya 45:18) Ya gaya mana cewa sunansa shi ne Yahweh ko Jehobah.​—Zabura 83:18.

Littafi Mai Tsarki ba ya fifita wata kabila a kan ta wasu domin littafin ya fito ne daga wanda ya halicci dukan mutane. Shawararsa tana da amfani a koyaushe kuma ta taimaka wa mutane a ƙasashe da yawa. Akwai shi a yaruka da dama kuma yana kusan ko’ina a duniya. Ba wani littafin da aka fassara kuma ya yaɗu kamarsa.a Don haka, mutane a ko’ina za su iya karanta shi kuma ya taimaka musu. Wannan ya tabbatar mana da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa:

“Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”​—AYYUKAN MANZANNI 10:​34, 35.

Kamar yadda iyaye suke taimaka wa yaransu domin suna ƙaunar su, Jehobah yana taimaka mana ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. (2 Timoti 3:16) Za mu iya gaskata da Kalmarsa domin shi ne ya hallice mu kuma ya san abin da ya fi dacewa da mu.

ZA MU IYA DOGARA DA LITTAFI MAI TSARKI

Hotuna: Na 1. Wani mutum a jirgin kasa yana karanta wani abu a wayarsa. Na 2. Ya bude Littafi Mai Tsarki a wayarsa.

Littafi Mai Tsarki abin dogara ne domin ya saba faɗan abubuwan da za su faru kafin su faru. Alal misali, kusan shekaru 2,000 da suka shige, ya annabta cewa abubuwan da muke gani a yau, za su faru.

ABUBUWAN DA ZA SU FARU

“Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi mummunar rawar ƙasa, da yunwa da bala’i a wurare dabam-dabam.”​—LUKA 21:​10, 11.

HALAYEN MUTANE

“Ka sani fa, a kwanakin ƙarshe za a sha wahala sosai. Gama mutane za su zama masu sonkansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, masu riƙe juna a zuciya, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kame kansu, marasa tausayi, masu ƙin nagarta, masu cin amana, marasa hankali, masu cika da ɗaga kai, masu son jin daɗin kansu fiye da son Allah.”​—2 TIMOTI 3:​1-4.

Yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗi waɗannan abubuwan babu kuskure ya burge ka kuwa? Babu shakka za ka yarda da abin da Leung daga ƙasar Hong Kong ya faɗa cewa: “Shekaru da yawa da suka shige ne aka yi annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki. Babu wani ɗan Adam da zai yi waɗannan annabce-annabcen kuma su cika daidai yadda ya faɗa. Hakan ya nuna cewa wanda ya wallafa Littafi Mai Tsarki ya fi mu hikima sosai.”

Akwai ɗarurruwan annabce-annabce a Littafi Mai Tsarki da suka cika.b Hakan ya tabbatar mana da cewa Littafi Mai Tsarki maganar Allah ce. Jehobah ya ce: “Ni ne Allah, babu wani kamar ni. Ina bayyana ƙarshen abu tun daga farkonsa.” (Ishaya 46:​9, 10) Babu shakka, za mu iya dogara da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da nan gaba.

SHAWARA DA ZA TA AMFANE KA YANZU DA KUMA HAR ABADA

Wata mata da mijinta da yaransu sun fita shan iska, dukansu sun rike hannu.

Idan ka bi shawarar da ke Littafi Mai Tsarki, za ka amfana sosai. Ga wasu misalai.

SHAWARA MAI KYAU GAME DA KUƊI DA AIKI

“Gwamma kaɗan a hannu ɗaya cike da kwanciyar rai, da mai yawa a hannu biyu cike da famar aiki, wannan ma ƙoƙarin kamun iska ne.”​—MAI-WA’AZI 4:6.

YADDA IYALI ZA TA ZAUNA LAFIYA

“Duk da haka dai, maganar ta shafe ku ku ma. Bari kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta girmama mijinta.”​—AFISAWA 5:33.

YADDA ZA MU ZAUNA LAFIYA DA MUTANE

“Kada ka bar zuciya ta yi zafi, ko hankalinka ya tashi, kada ka yi fushi, wannan ba ya kawo kome sai mugunta.”​—ZABURA 37:8.

Idan ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki, za ka yi rayuwa mai kyau yanzu da kuma a nan gaba. Allah ya yi alkawari cewa rayuwa za ta yi kyau a nan gaba. Ga wasu abubuwan da ya ce:

ZA A SAMI ZAMAN LAFIYA

“Amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”​—ZABURA 37:11.

KOWA ZAI SAMI ABINCI DA GIDA

“A kwanakin nan, mutane za su gina gidaje, su zauna a cikinsu, za su shuka gonakin inabi, su ci amfaninsu.”​—ISHAYA 65:21.

BA WANDA ZAI YI CIWO KO YA MUTU

“Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace.”​—RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 21:4.

Me za ka yi don ka sami waɗannan albarkun? Za a tattauna hakan a talifi na gaba.

a Don ƙarin bayani a kan yadda aka fassara da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki, ka shiga dandalinmu na www.pr418.com/ha, ka danna KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > TARIHI DA LITTAFI MAI TSARKI.

b Don ka sami ƙarin bayani, ka karanta littafin nan, The Bible​—God’s Word or Man’s? babi na 9, Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Za ka iya samunsa a Turanci a dandalinmu na www.pr418.com. Ka danna LIBRARY > BOOKS & BROCHURES.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba