Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 21-25
  • Menene Yake Sa Rayuwa Ta Kasance Da Ma’ana?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Yake Sa Rayuwa Ta Kasance Da Ma’ana?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Cin Iska”
  • Biɗan Nishaɗi Zai Iya Samu Farin Ciki Ne?
  • Mallakar Abin Duniya Zai Sa Mu Gamsu Kuwa?
  • Wane Irin Aiki ne Yake Kawo Gamsuwa?
  • “Ka Aika da Abincinka”
  • Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 21-25

Menene Yake Sa Rayuwa Ta Kasance Da Ma’ana?

“Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa.” —M.-WA. 12:13.

1, 2. Ta yaya za mu amfana daga yin nazari na littafin Mai-Wa’azi?

YI TUNANIN wani mutum wanda kamar dai ba abin da ba shi da shi. Sananne ne, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fi arziki a duniya, kuma ya fi kowa hikima a zamaninsa. Duk da abin da ya mallaka, ya tambayi kansa, ‘menene yake sa rayuwa ta kasance da ma’ana?

2 Wannan mutumin ya rayu shekaru dubu uku da suka shige. Sunansa Sulemanu, kuma ya nuna mana yadda ya nemi gamsuwa a littafin Mai-Wa’azi. (M. Wa. 1:13) Akwai abubuwa da yawa da za mu koya daga labarin Sulemanu. Hakika, hikimar da ke cikin littafin Mai-Wa’azi za ta iya taimakonmu mu kafa makasudai da za su sa mu yi rayuwa mai ma’ana.

“Cin Iska”

3. Wace gaskiya ce game da rayuwar mutum dukan mu za mu fuskanta?

3 Sulemanu ya bayyana cewa Allah ya halicci abubuwa da yawa masu kyau a duniya, wato abubuwa masu ban sha’awa masu ban mamaki da ba za mu daina moran su ba. Amma, ba za mu iya bincika dukan halittar Allah ba saboda rayuwarmu ba ta da tsawo. (M. Wa. 3:11; 8:17) Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, kwanakinmu kaɗan ne kuma suna shigewa da sauri. (Ayu. 14:1, 2; M. Wa. 6:12) Wannan gaskiya ya kamata ya motsa mu mu yi amfani da rayuwarmu a hanya da ta dace. Hakan ba shi da sauki, tun da duniyar Shaidan za ta iya rinjayar mu mu bi hanyar da bai dace ba.

4. (a) Menene kalmar nan “banza” take nufi? (b) Waɗanne abubuwa ne na rayuwa za mu tattauna?

4 Don ya nanata haɗarin lalata rayuwarmu, Sulemanu ya yi amfani da wannan kalmar “banza” kusan sau 30 a cikin littafin Mai-Wa’azi. Kalmar Ibrananci da aka fassara “banza” tana nufin abin da ba shi da amfani, ko kuma wofi. (M. Wa. 1:2, 3) Wani lokaci Sulemanu yana yin amfani da kalmar nan “banza” daidai da furcin nan “cin iska.” (M. Wa. 1:14; 2:11) Hakika, duk wani ƙoƙari a kama iska duk banza ne. Duk wanda yake yin ƙoƙari ya yi hakan baya samun kome. Biɗan makasudai da ba su dace ba duk banza ne. Rayuwa a wannan zamani ba ta da tsawo da za mu lalata ta da abubuwan da za su ƙyale mu hannu banza. Don mu guji yin kuskure, bari mu tattauna wasu misalai da Sulemanu ya ba da game da biɗan abin duniya. Da farko za mu tattauna game da biɗan nishaɗi da kuma abin duniya. Bayan haka, za mu tattauna muhimmancin aiki.

Biɗan Nishaɗi Zai Iya Samu Farin Ciki Ne?

5. A ina ne Sulemanu ya nemi gamsuwa?

5 Kamar mutane da yawa a yau, Sulemanu ya yi ƙoƙari ya nemi gamsuwa ta wurin rayuwar jin daɗi. Ya ce: “Ban hana ma raina kowane abin marmari” ba. (M. Wa. 2:10) A ina ne ya nemi nishaɗi? Mai-Wa’azi sura 2 ta ce, ya ‘ji ma jikinsa daɗi da ruwan anab,’ kuma ya kame kansa, ya yi aiki kamar su gwaje-gwajen fili, zane-zane fada, sauraran waƙoƙi, da kuma cin abinci masu ɗanɗano.

6. (a) Me ya sa ba laifi ba ne a more wasu abubuwan masu kyau na rayuwa? (b) Menene ya kamata a yi game da nishaɗi?

6 Littafi Mai Tsarki ya hana jin daɗi da abokane ne? A’a. Alal misali, Sulemanu ya lura cewa cin abinci bayan aiki kyauta ce daga Allah. (Ka karanta Mai-Wa’azi 2:24; 3:12, 13.) Amma, Jehobah da kansa ya ce matasa su yi ‘murna kuma su bari zuciyarsu ta yi fari’ a hanya da ta dace. (M. Wa. 11:9) Muna bukatar nishaɗi mai kyau. (Gwada da Markus 6:31.) Amma, kada nishaɗi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Maimakon haka, nishaɗi ya kamata ya zama kamar kayan zaƙi da ake sha bayan an gama cin abinci, amma ba ainihin abinci ba. Za ka yarda cewa komin son da ka ke yi wa kayan zaƙi da ake sha bayan an gama cin abinci, za su ishe ka idan su kaɗai ka sha, kuma ba za su ba ka abubuwa na gina jiki ba. Hakazalika, Sulemanu ya fahimci cewa rayuwar nishaɗi kawai “cin iska” ne.—M. Wa. 2:10, 11.

7. Me ya sa ya kamata mu zaɓi nishaɗi da za mu yi?

7 Bugu da ƙari, ba kowane nishaɗi ne yake da kyau ba. Da yawa suna da lahani, ga ruhaniya da kuma ɗabi’a. Miliyoyin mutane sun saka rayuwarsu cikin matsala don suna ‘son su ji daɗin rayuwa,’ sun soma shan kwayoyi, yawan shan giya, ko kuma yin caca. Jehobah ya yi mana gargaɗi cewa idan muka yarda zuciyarmu ko kuma idanunmu suka rinjaye mu mu yi abubuwa marasa kyau, za mu sami sakamakon haka.—Gal. 6:7.

8. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi bimbini a kan rayuwar?

8 Bugu da ƙari, nishaɗi da ba a daidaita ba zai hana mu kula da abubuwa masu muhimmanci. Ka tuna, rayuwa tana wucewa da wuri, kuma babu tabbaci cewa ba za mu yi ciwo ba kuma ba za mu fuskanci matsaloli ba a wannan rayuwa marar tsawo. Shi ya sa Sulemanu ya sake lura ce wa, za mu sami albarka mai girma inda muka je wajen jana’iza musamman na ɗan’uwa Kirista ko kuma ’yar’uwa da suka kasance da aminci fiye da zuwa “gidan dariya.” (Ka karanta Mai-Wa’azi 7:2, 4.) Me ya sa? Idan muka saurari jawabi na jana’iza kuma muka yi bimbini a kan rayuwar wannan amintaccen bawan Jehobah da ya rasu, zai motsa mu mu bincika rayuwarmu. A sakamakon haka, za mu ga cewa ya kamata mu gyara makasudanmu don mu yi amfani da sauran rayuwanmu da kyau.—M. Wa. 12:1.

Mallakar Abin Duniya Zai Sa Mu Gamsu Kuwa?

9. Menene Sulemanu ya fahimta game da mallakar dukiya?

9 Sa’ad Sulemanu ya rubuta littafin Mai-Wa’azi yana ɗaya daga cikin masu arziki na duniya. (2 Laba. 9:22) Yana da kuɗin da zai sayi duk abin da yake so. Ya rubuta: “Dukan abin da idona ke sha’awa ban hana masa ba.” (M. Wa. 2:10) Duk da haka, ya fahimci cewa mallakar abubuwan duniya ba sa kawo gamsuwa. Ya kammala da cewa: “Wanda ya ke ƙaunar azurfa ba za ya ƙoshi da azurfa ba; wanda ya ke neman yalwa kuma ba za ya ƙoshi da ƙaruwa ba.”—M. Wa. 5:10.

10. Menene zai kai ga samun gamsuwa da dukiya ta gaske?

10 Ko da yake abubuwan duniya masu shuɗewa ne, dukiya tana iya rinjayar mutane. A wani bincike da aka yi a Amirka, kashi 75 cikin dari na dukan daliɓan da suke shekarar su ta farko a jami’a sun ce makasudinsu a rayuwa shi ne “yin arziki.” Idan har suka cim ma makasudinsu, za su sami farin ciki kuwa? Ba lalle ba ne. ’Yan bincike sun lura cewa biɗan abubuwan duniya yakan hana samun farin ciki da gamsuwa. Da daɗewa Sulemanu ya faɗi haka. Ya rubuta: “Na tattaro azurfa da zinariya da taskokin sarakuna . . . Ga shi kuwa, duk banza ne, cin iska kawai.”a (M. Wa. 2:8, 11) Akasin haka, idan muka yi amfani da rayuwarmu muka bauta wa Jehobah da zuciyarmu ɗaya kuma muka sami albarkarsa, za mu sami dukiya ta gaske.—Ka karanta Zabura 10:22.

Wane Irin Aiki ne Yake Kawo Gamsuwa?

11. Menene Nassosi ta ce game da muhimmancin aiki?

11 Yesu ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.” (Yoh. 5:17) Babu shakka Jehobah da Yesu sun sami gamsuwa daga aiki. Littafi Mai Tsarki ya nuna gamsuwar Jehobah da aikin da ya yi na halitta sa’ad da ya ce: “Allah kuma ya duba kowane abin da ya yi, ga shi kuwa, yana da kyau ƙwarai.” (Far. 1:31) Mala’iku “suka yi sowa don farinciki” sa’ad da suka ga dukan abin da Allah ya yi. (Ayu. 38:4-7) Hakazalika Sulemanu yana son aiki mai muhimmanci.—M. Wa. 3:13.

12, 13. (a) Yaya ne mutane biyu suka nuna irin gamsuwa da suka samu a yin aiki tuƙuru? (b) Me ya sa aikin duniya wani lokaci yakan jawo takaici?

12 Mutane da yawa sun san muhimmancin aiki mai kyau. Alal misali, José, wani ƙwararen mai zane ya ce: “Idan ka yi irin fenti da zuciyarka take so kan yadi, za ka yi farin ciki sosai.” Miguel,b wani ɗan kasuwa, ya ce: “Aiki yana ba da gamsuwa saboda yana sa ka yi wa iyalinka tanadi. Kuma yana sa ka cim ma abubuwa.”

13 A wani ɓangare, a wasu ayyuka da yawa abu iri ɗaya ake yi yau da gobe kuma ba sa ba mutum zarafin yin wasu sababbin abubuwa. Wani lokaci wajen aiki kansa yakan jawo takaici kuma mutane suna fuskantar rashin adalci. Kamar yadda Sulemanu ya nuna, sai a ba rago ladan aikin wanda ya yi aiki tuƙuru wataƙila domin alaƙarsa da masu sarauta. (M. Wa. 2:21) Akwai wasu abubuwa da za su sa mutum ya yi takaici. Kasuwanci da ya soma da kyau, jarin ya karye saboda hannu ya faɗi ko kuma tsautsayi. (Ka karanta Mai-Wa’azi 9:11.) Sau da yawa, mutumin da ya yi aiki sosai don ya yi nasara, yakan ƙare da fushi da takaici, don ya fahimci cewa “dukan aikinsa banza ne.”—M. Wa. 5:16.

14. Wane aiki ne yake kawo gamsuwa ta gaske?

14 Akwai wani irin aiki da ba zai taɓa sa mutum takaici ba? José, mai yin zane-zane da aka ambata a baya, ya ce: “Bayan shekaru masu yawa, fentin zai iya ɓata ko kuma ya halaka. Amma ba haka yake da abubuwan da muke yi a hidimar Allah ba. Ta wajen yi wa Jehobah biyayya a shelar bishara, na taimaki waɗansu su zama Kiristoci masu tsoron Allah, kuma hakan ya taimake su sosai. Hakan na da muhimmanci ƙwarai.” (1 Kor. 3:9-11) Miguel ya kuma ce yin wa’azin Mulki ya kawo masa gamsuwa fiye da aiki na duniya. “Babu abin da zai fi ba da farin cikin da ka ke samu sa’ad da ka gaya wa wani gaskiyar Nassi kuma ka lura cewa ta motsa zuciyarsa,” in ji sa.

“Ka Aika da Abincinka”

15. Menene ainihi yake sa rayuwa ta kasance da ma’ana?

15 A ƙarshe, menene yake sa rayuwa ta kasance da ma’ana? Za mu sami gamsuwa idan muka yi amfani da rayuwarmu marar tsawo a wannan zamanin muka yi ayyuka masu kyau kuma muka faranta wa Jehobah rai. Za mu iya kafa dangantaka na kud da kud da Allah; za mu iya koya wa ’ya’yanmu abubuwan na ruhaniya; za mu iya taimakawa wasu su san Jehobah; kuma za mu iya kafa dangantaka mai ƙarfi da ’yan’uwanmu. (Gal. 6:10) Dukan irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce suna da amfani na dindindin kuma za su kawo albarka ga waɗanda suka same su. Sulemanu ya yi kwatanci mai kyau don ya nuna amfanin yin abubuwa masu kyau. Ya ce: “Ka aike da abincinka a bisa ruwaye: gama za ka same shi bayan kwanaki dayawa.” (M. Wa. 11:1) Yesu ya aririce almajiransa: “Ku bayar, za a ba ku.” (Luk 6:38) Bugu da ƙari, Jehobah ya yi alkawari zai albarkaci waɗanda suka yi wa wasu alheri.—Mis. 19:17; Ka karanta Ibraniyawa 6:10.

16. Yaushe ne ya kamata mu tsai da shawara game da rayuwarmu?

16 Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu yanke shawara mai kyau game da yadda za mu yi amfani da rayuwarmu sa’ad da muke da sauran ƙarfi. Idan muka yi haka, za mu iya guje wa matsaloli a nan gaba. (M. Wa. 12:1) Abin baƙin ciki ne idan muka yi amfani da rayuwarmu a wajen neman abin duniya, sai daga baya muka fahimci cewa duk banza ne.

17. Menene zai taimake mu mu zaɓi rayuwa mai kyau?

17 Kamar uba mai ƙauna, Jehobah yana son ka mori rayuwa, ka yi abubuwa masu kyau, kuma ka guje wa matsaloli. (M. Wa. 11:9, 10) Menene zai taimake ka ka cim ma hakan? Ka kafa makasudai na ruhaniya kuma ka yi ƙoƙari don ka cim ma su. Shekara 20 da suka wuce, Javier ya yi zaɓi tsakanin zama likita da hidima na cikakken lokaci. Ya ce: “Ko da yake aikin likita yana da gamsarwa, babu abin da zai kai farin cikin da na samu sa’ad da na taimaki mutane da yawa su san gaskiya. Hidima na cikakken lokaci ya taimake ni in ji daɗin rayuwa. Abin baƙin ciki shi ne, ban soma da wuri ba.”

18. Me ya sa rayuwar Yesu a duniya ya kasance mai ma’ana?

18 Menene ne abu mafi kyau da ya kamata mu yi ƙoƙari mu samu? Littafin Mai Wa’azi ya ce: “Nagarin suna ya fi mai mai-tamani; kuma ranar mutuwa ta fi ranar haifuwa.” (M. Wa. 7:1) Babu abin da ya bayyana hakan da kyau fiye da rayuwar Yesu. Hakika ya yi suna mai kyau a wurin Jehobah. Sa’ad da Yesu ya mutu cikin aminci, ya ɗaukaka ikon mallaka na Ubansa kuma ya yi hadayar fansa, wanda hakan ya kai mu ga ceto. (Mat. 20:28) A lokacin da yake duniya, Yesu ya nuna mana misali mai kyau wanda ya kamata mu yi ƙoƙari mu bi gurbinsa, wato, na yin rayuwa mai ma’ana.—1 Kor. 11:1; 1 Bit. 2:21.

19. Wace shawara ce mai kyau Sulemanu ya bayar?

19 Muma za mu iya yin suna mai kyau a wajen Allah. Yin suna mai kyau a wajen Jehobah ya fi muhimmanci fiye da samun arziki. (Ka karanta Matta 6:19-21.) Koyaushe ya kamata mu nemi zarafin yin abubuwa masu kyau da Jehobah yake so, yin hakan zai kyautata rayuwarmu. Alal misali, za mu iya yi wa wasu wa’azi, mu ƙarfafa aurenmu da iyalinmu, kuma mu ƙarfafa ruhaniyarmu ta wurin yin nazari na kai da kuma halartar taro. (M. Wa. 11:6; Ibran. 13:16) Saboda haka, kana son ka more rayuwa mai ma’ana? To, ka ci gaba da bin umurnin Sulemanu: “Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.”—M. Wa. 12:13.

[Hasiya]

a Sulemanu yana samun talanti 666 (wato, fiye da awo 50,000) na azurfa a kowace shekara.—2 Laba. 9:13.

b Ana canja sunan.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene ya zai motsa mu mu yi tunani sosai game da makasudan mu a rayuwa?

• Menene ra’ayinmu game da nishaɗi da biɗan abin duniya?

• Wane irin aiki ne zai kawo gamsuwa na dindindin?

• Wane abu ne mai muhimmanci ya kamata mu biɗa?

[Hoto a shafi na 23]

Yaya nishaɗi ya kamata ya kasance a rayuwarmu?

[Hoto a shafi na 24]

Menene ya sa aikin wa’azi yana da gamsuwa sosai?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba