Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 pp. 18-19
  • Ta So Ta Yi Taimako

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta So Ta Yi Taimako
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yarinya Ta Taimaki Jarumi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yara da Suka Faranta wa Allah Rai
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 pp. 18-19

Ku Koyar Da Yaranku

Ta So Ta Yi Taimako

KA SAN wani wanda ba shi da lafiya sosai? Kana fatan da za ka yi wani abu domin ka taimake shi? Idan daga wata ƙasa ko kuma yanki yake fa? Za ka so ka taimake shi? Wata yarinya da ta rayu a ƙasar Isra’ila kusan shekara 3,000 da ta shige ta yi hakan. Bari mu tattauna abin da ya faru a lokacin.

Isra’ila ta dā inda yarinyar take, da kuma ƙasa ta kusa Suriya suna yawan faɗa da juna. (1 Sarakuna 22:1) Wata rana Suriyawa suka zo Isra’ila suka kama yarinyar. Suka ɗauke ta suka kai ta Suriya, ta zama baiwar matar Na’aman, shugaban sojojin Suriya. Na’aman yana da wata muguwar cuta da ake kira kuturta, mai cin jikin mutane.

Yarinyar ta gaya wa matar Na’aman yadda mijinta zai warke. Ta ce: ‘Da a ce Na’aman a Samariya yake, da annabin Jehobah Elisha ya warkar da shi.’ Yadda yarinyar ta yi maganar Elisha ya sa Na’aman ya gaskata cewa annabin da gaske zai iya warkar da shi. Saboda haka, da izinin Ben-Hadad, sarkin Suriya, Na’aman da wasu mataimakansa suka yi doguwar tafiya na ɗarurruwan mil su nemi Elisha.

Da farko, suka tafi wurin Jehoram, sarkin Isra’ila. Sun nuna masa wasiƙar Ben-hadad da ya nemi taimako domin Na’aman. Amma Jehoram ba shi da bangaskiya ga Jehobah ko kuma annabi Elisha. Jehoram yana tsammanin cewa Ben-hadad tsokanarsa yake yi. Sa’ad da Elisha ya sami wannan labarin, ya gaya wa Sarki Jehoram: “Bari shi zo wurina.” Elisha yana so ya nuna cewa Allah yana da ikon warkar da cutar Na’aman.—2 Sarakuna 5:1-8.

Sa’ad da Na’aman ya isa gidan Elisha da dawakai da karusansa, Elisha ya aiki manzonsa ya gaya masa: ‘Je ka, ka yi wanka cikin Urdun so bakwai, namanka za ya komo gareka, za ka tsarkaka.’ Na’aman ya yi fushi. Ya yi tsammanin Elisha zai zo wurinsa ne ya yi amfani da hannunsa ya warkar da kuturtar. Maimakon haka, manzonsa kawai ya gani! Saboda haka, Na’aman ya juya da fushi, yana so ya koma.—2 Sarakuna 5:9-12.

Da a ce kai bawan Na’aman ne da menene za ka yi? Bayin suka tambaye shi: ‘Da a ce wani abu mai wuya Elisha ya ce ka yi, da ba ka yi ba ne? To me zai hana ka yin wannan abu mai sauƙi?’ Na’aman ya saurare su. Ya tafi ya “sabka ya nutsa so bakwai cikin Urdun, . . . namansa kuwa ya komo sai ka ce naman jariri.”

Na’aman ya koma wurin Elisha ya ce: “Ga shi, yanzu na sani babu wani Allah cikin dukan duniya, sai cikin Isra’ila.” Ya yi wa Elisha alkawari cewa ba zai sake “yin hadaya ta ƙonawa, ko kowace hadaya haka ga waɗansu allohi sai ga Ubangiji.”—2 Sarakuna 5:13-17.

Za ka so ka taimaki wani ya koyi game da Jehobah da kuma game da abin da zai yi kamar yadda wannan yarinya ƙarama ta yi? Sa’ad da Yesu yake duniya, wani mutumin da yake da kuturta ya gaskata da shi kuma ya ce: ‘Idan kana so ka taimake ni, zaka iya.’ Ka san abin da Yesu ya ce? “Na yarda.” Yesu ya warkar da shi, kamar yadda Jehobah ya warkar da Na’aman.—Matta 8:2, 3.

Ka taɓa ji game da sabuwar duniya da Jehobah zai yi, wadda a cikinta dukan mutane za su kasance da ƙoshin lafiya kuma za su rayu har abada? (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Hakika za ka so ka gaya wa mutane waɗannan abubuwa masu ban mamaki!

Tambaya:

○ Ta yaya yarinya ƙarama ta taimaki Na’aman wanda mutanensa ne suka kamo ta?

○ Me ya sa da farko Na’aman bai yarda ya yi biyayya ga Elisha ba, amma menene ya canja ra’ayinsa?

○ Menene za ka so ka yi domin ka yi koyi da ƙaramar yarinyar?

○ Menene Yesu yake so ya yi, kuma me ya sa rayuwa za ta kasance da ban sha’awa a sabuwar duniya ta Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba