Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 pp. 30-31
  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ta So Ta Yi Taimako
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yarinya Ta Taimaki Jarumi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yara da Suka Faranta wa Allah Rai
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 pp. 30-31

Ku Koyar Da Yaranku

Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya

KA TAƁA yin taurin kai kuma ka ƙi yin biyayya?—a Mai yiwuwa ka kalli wani shiri a talabijin wanda mamarka ko babanka ya hana ka kallo. Amma daga baya ka yi tunani kuma ba ka ji daɗin rashin biyayyar da ka yi ba. Wani mutumin da ya taɓa yin taurin kai shi ne Na’aman. Bari mu ga yadda aka taimake shi don ya daina taurin kai.

A ce muna raye ne shekaru sama da 3,000 da suka shige. Na’aman babban kwamandan sojoji ne a ƙasar Siriya. Ya saba gaya wa sojojinsa abin da za su yi kuma suna yi masa biyayya. Amma Na’aman yana da wata mummunar cuta da ake kira kuturta. Wannan cutar ta sa ya yi muni, kuma wataƙila ma tana yi masa zafi sosai.

Matar Na’aman tana da wata ƙaramar yarinya ’yar Isra’ila wadda baiwa ce. Wata rana yarinyar ta gaya wa uwar ɗakinta labarin wani mutumin da ke ƙasarsu mai suna Elisha. Ta ce zai iya warkar da Na’aman. Sa’ad da Na’aman ya samu wannan labarin, nan da nan ya shirya ya tafi wurin Elisha. Ya riƙe kyauta mai yawa kuma ya tafi da sojojinsa zuwa Isra’ila. Ya je wurin sarkin Isra’ila don ya bayyana masa dalilin zuwansa.

Elisha ya ji hakan kuma ya aika saƙo ga sarkin cewa ya bar Na’aman ya zo wurinsa. Sa’ad da Na’aman ya isa gidan Elisha, Elisha ya tura bawansa ya gaya wa Na’aman cewa ya je ya yi wanka sau bakwai a cikin Kogin Urdun. Elisha ya ce yin hakan zai sa Na’aman ya warke. Yaya Na’aman ya ji sa’ad da aka gaya masa hakan?—

Ya ji haushi. Saboda haka ya yi taurin kai kuma ya ƙi yin biyayya ga annabin Allah. Ya gaya wa sojojinsa cewa: ‘Kogunan garinmu sun fi na Isra’ila kyau.’ Na’aman ya fara tafiya. Amma ka san abin da sojojinsa suka tambaye shi?— ‘In da abu mai wuya ne annabin ya gaya maka ka yi, da ba ka yi ba? To me ya sa ba za ka yi biyayya ba ga abu mai sauƙi da ya ce ka yi?’

Na’aman ya saurara kuma ya yi abin da sojojinsa suka gaya masa. Ya nitse sau shida cikin kogin. Da ya nitse na bakwai ɗin kuma ya fito daga cikin ruwan, Na’aman ya yi mamaki domin cutar ta warke! Nan da nan ya koma gidan Elisha mai nisan mil wajen 30 don ya gode masa. Yana son ya ba Elisha kyauta mai tsada amma annabin ya ƙi karɓa.

Don haka, Na’aman ya roƙi Elisha wani abu. Ka san abin?— ‘Ka bari in tafi gida da kayan alfadari biyu na ƙasa.’ Ka san dalilin da ya sa yake son ya yi hakan?— Na’aman ya ce yana son ya yi hadaya ne ga Allah a kan ƙasar mutanen Allah, wato, Isra’ila. Sa’an nan ya yi alkawari cewa ba zai sake bauta wa wani alla ba sai Jehobah! Ya daina yin taurin kai kuma ya soma yin biyayya ga Allah na gaskiya.

Ka ga yadda za ka iya yin koyi da Na’aman?— Idan kana da taurin kai kamar Na’aman, za ka iya canjawa. Za ka iya karɓan shawara kuma ka daina yin taurin kai.

Ka karanta wuraren nan a cikin naka Littafi Mai Tsarki

2 Sarakuna 5:1-19

Luka 4:27

[Hasiya]

a Idan kana karatun da yaro ne, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba