Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 6/15 pp. 18-22
  • Ka Amince Da Ikon Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Amince Da Ikon Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ra’ayinmu Game da Iko
  • Koyar da Hankalinmu
  • Shaiɗan Yana Neman Ya Ƙasƙantar da Ikon Allah
  • Ka Guji Halin Neman ’Yancin Kai
  • Muhimmancin Tawali’u
  • Me Ya Sa Za a Girmama Hukuma?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Me Ya Sa Biyayya ga Masu Iko—Ke Da Muhimmanci?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Me Ya Sa Ya Dace Mu Rika Yin Biyayya?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ku Girmama Waɗanda Suke Da Iko Bisa Kanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 6/15 pp. 18-22

Ka Amince Da Ikon Jehobah

“Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” —1 YOH. 5:3.

1, 2. (a) Me ya sa mutane da yawa a yau ba sa son su kasance a ƙarƙashin ikon wani? (b) Da gaske ne cewa waɗanda suka ce ba sa son su kasance a ƙarƙashin iko suna da ’yanci? Ka bayyana.

MUTANE da yawa a yau ba sa so su kasance a ƙarƙashin ikon wani. Ra’ayin irin waɗannan mutanen shi ne, “Babu wanda ya isa ya gaya mini abin da zan yi.” Da gaske ne cewa ba sa ƙarƙashin ikon kowa? Da kyar! Yawancinsu suna bin misalin mutane da yawa da suka “kamantu bisa ga kamar wannan zamani.” (Rom. 12:2) Maimakon su kasance ’yantattu, ta wajen yin amfani da kalaman manzo Bitrus, su “bayin zamba ne.” (2 Bit. 2:19, LMT) Suna yin abubuwa “bisa ga zamanin wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama,” wato, Shaiɗan Iblis.—Afis. 2:2.

2 Wani mawallafi ya ce: Ba na yarda iyayena ko firist ko shugabannin coci ko malamin addinin Hindu ko Littafi Mai Tsarki su tsai da mini shawara a kan abin da ya dace ba.” Hakika, wasu mutane sun lalata ikonsu kuma mai yiwuwa ba za su cancanci mu yi musu biyayya ba. Amma ƙin ja-goranci ne zai magance matsalar? Kallon kawunan labaran da ke cikin jarida yana ba da amsa marar daɗin ji. Abin baƙin ciki ne cewa a lokacin da mutane suke bukatar ja-gora sosai, yawanci ba sa son a yi musu ja-gora.

Ra’ayinmu Game da Iko

3. Ta yaya ne Kiristoci na ƙarni na farko suka nuna cewa ba duka abin da mutane masu iko suka ce su yi ba ne za su yi?

3 Matsayin da mu Kiristoci muka ɗauka ya bambanta da ta duniya. Ba wai za mu yi duk wani abin da aka ce mu yi ba ne ba tare da yin tambaya ba. Akasin haka, a wasu lokatai dole ne mu ƙi yin abin da wasu mutane suka faɗa ko da suna da iko. Abin da Kiristoci na gaskiya a ƙarni na farko suka yi ke nan. Alal misali, sa’ad da aka gaya wa manzanni su daina yin wa’azi, ba su bi umurnin babban firist da sauran manya-manya masu iko da suke cikin ’Yan Majalisa ba. Ba su ƙi hali mai kyau don su miƙa wuya ga ikon mutane ba.—Ka karanta Ayukan Manzanni 5:27-29.

4. Waɗanne misalai ne daga Nassosin Ibraniyawa suka nuna cewa mutanen Allah masu yawa ba su bi tafarkin da yawancin mutane suke bi ba?

4 Bayin Allah masu yawa da suka rayu kafin lokacin Kirista su ma sun yanke irin wannan ƙudurin. Alal misali, Musa “ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna; yana gwammace a wulakance shi tare da mutanen Allah,” duk da cewa yin hakan zai jawo “hasalar sarki.” (Ibran. 11:24, 25, 27) Yusufu ya ƙi tayin da matar Fotifar take ta yi masa, duk da cewa tana da ikon ramawa kuma ta sa a yi masa lahani. (Far. 39:7-9) Daniyel “ya yi ƙuduri a zuciyatasa ba za ya ɓāta kansa da abincin sarki” ba, duk da cewa yana da wuya sarkin fadan Babila ya yarda da hakan. (Dan. 1:8-14) Daga tarihi, waɗannan misalan sun nuna cewa mutanen Allah sun manne wa gaskiya ko da menene zai kasance sakamakon hakan. Ba su yi biyayya ga mutane ba don su sami amincewarsu ba, kuma bai kamata mu ma mu yi haka ba?

5. Ta yaya ne yadda muka ɗauki iko ya bambanta da na duniya?

5 Bai kamata a ɗauki gaba gaɗinmu a matsayin taurin kai ba; kuma mu ba kamar wasu ’yan tawaye ba ne da suke son su nuna cewa ba su amince da irin siyasar da ake yi ba. Maimakon haka, mun ƙudurta cewa za mu amince da ikon Jehobah fiye da na mutane. Sa’ad da dokar mutane ta saɓa da dokar Allah, matakin da za mu ɗauka bai da wuya. Kamar manzanni a ƙarni na farko, za mu yi biyayya ga Allah a matsayin mai sarauta ba mutane ba.

6. Me ya sa ya kamata mu yi biyayya ga umurnin Jehobah?

6 Menene ya taimakemu mu amince da ikon Allah? Mun yarda da abin da ke cikin Misalai 3:5, 6: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” Mu yarda cewa dukan abin da Allah yake bukata a gare mu don amfaninmu ne. (Ka karanta Kubawar Shari’a 10:12, 13.) Hakika, Jehobah ya kwatanta kansa ga Isra’ilawa cewa shi ne ‘wanda ya ke koya musu zuwa amfaninsu, wanda yana bishe su ta hanyar da za su bi.’ Ya kuma daɗa: “Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Isha. 48:17, 18) Mun gaskata da waɗannan kalaman. Mun tabbata cewa yin biyayya ga umurnin Allah don amfaninmu ne.

7. Me ya kamata mu yi idan ba mu fahimci dokokin da ke cikin Kalmar Allah sosai ba?

7 Za mu iya amince da ikon Jehobah kuma mu yi masa biyayya idan ma ba mu fahimci dalilin wasu ka’idodi a cikin Kalmarsa ba. Hakan ba imani marar tushe ba ne; gaskatawa ne. Yin hakan yana tabbata mana cewa Jehobah ya san abin da zai amfane mu. Biyayyarmu tana nuna ƙaunarmu, gama manzo Yohanna ya rubuta: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yoh. 5:3) Amma akwai wani fasalin biyayya da bai kamata mu manta da shi ba.

Koyar da Hankalinmu

8. Ta yaya ne koyar da “hankalinmu” ya daidaita da amincewa da ikon Jehobah?

8 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu koyar da ‘hankulanmu . . . bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.’ (Ibran. 5:14) Amma, makasudinmu ba shi ne mu yi biyayya ga dokokin Allah ba tare da mun yi tunani a kansu ba; maimakon haka, ya kamata mu ‘raba nagarta da mugunta’ bisa ga mizanan Jehobah. Muna so mu ga hikimar nufin Jehobah, don mu ce kamar mai zabura: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.”—Zab. 40:8.

9. Ta yaya za mu iya yin abubuwa da suka jitu da mizanin Jehobah, kuma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci?

9 Don mu fahimci dokar Allah kamar yadda mai zabura ya yi, ya kamata mu yi bimbini a kan abin da muka karanta daga cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, idan muka koyi wata bukatar Jehobah, za mu iya tambaya: ‘Me ya sa wannan doka ko ka’ida take da kyau? Me ya sa zan amfana idan na yi biyayya? Menene sakamakon waɗanda suka ƙi su bi umurnin Allah game da wannan batu?’ Sa’ad da muka yarda da nufin Jehobah a wannan batu, za mu iya yin shawara da ta jitu da nufinsa. Za mu iya fahimtar “abin da ke nufin Ubangiji” kuma mu yi biyayya. (Afis. 5:17) Hakan ba shi da sauƙi.

Shaiɗan Yana Neman Ya Ƙasƙantar da Ikon Allah

10. Ta wace hanya ce kuma Shaiɗan yake so ya ƙasƙantar da ikon Allah?

10 Da daɗewa Shaiɗan yana so ya ƙasƙantar da ikon Allah. Ya nuna ikonsa na ’yancin kai a hanyoyi da yawa. Alal misali, rashin yin biyayya ga tsarin da Allah ya kafa na aure. Wasu sun fi so su zauna tare ba sai sun yi aure ba, wasu kuma suna neman hanyar da za su kashe aurensu. Waɗanda suke da irin wannan ra’ayi za su yarda da abin da wata sananniyar ’yar wasa ta ce: “Bai dace na miji ya auri mata ɗaya ba ko kuma na mace ta auri miji ɗaya kawai ba.” Ta daɗa: “Ban taɓa ganin mata ko mijin da suka taɓa kasancewa da aminci da juna ba ko kuma waɗanda suke son su yi hakan ba.” Sa’ad da ya tuna da dangantakarsa da ta rushe, wani sanannen ɗan wasa ya ce: “Ban tabbata ba cewa an yi mu don mu zauna da mutum ɗaya kawai a rayuwarmu ba.” Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Na amince da umurnin Jehobah game da aure, ko kuma ra’ayin duniya game da aure ya shafi tunani na ne?’

11, 12. (a) Me ya sa zai iya yi wa matasa wuya su amince da ikon Jehobah? (b) Ka ba da labarin da ya nuna cewa wawanci ne a ƙi bin dokokin Jehobah da ka’idodinsa.

11 Kai matashi ne a ƙungiyar Jehobah? Idan haka ne, Shaiɗan yana so ka yi tunani cewa ikon Jehobah ba zai amfane ka ba. “Sha’awoyin ƙuruciya” tare da matsi daga wajen abokanka za su iya sa ka kammala cewa dokokin Allah suna da wuya. (2 Tim. 2:22) Kada ka bar hakan ya faru. Ka yi ƙoƙarin ganin amfanin mizanan Allah. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce ka “guje ma fasikanci.” (1 Kor. 6:18) A nan kuma, ka yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘Me ya sa wannan dokar take da muhimmanci? Ta yaya ne biyayya a wannan batun zai amfane ni?’ Wataƙila ka san wasu da suka ƙi bin dokar Allah kuma suka sha wahala sosai domin wannan zunubin. Suna farin ciki yanzu? Suna jin daɗin rayuwa fiye da lokacin da suke tarayya da ƙungiyar Jehobah kuwa? Sun sami wasu asirin farin cikin wanda sauran bayin Allah suka rasa ne?—Ka karanta Ishaya 65:14.

12 Ka yi la’akari da abin da wata Kirista mai suna Sharon ta ce: “Saboda na ƙi bin dokar Jehobah, na kamu da cutar ƘANJAMAU. A koyaushe ina tuna da farin cikin da na samu shekaru da yawa sa’ad na ke bauta wa Jehobah.” Ta fahimci cewa wauta ce a taka dokokin Jehobah kuma da ta ɗauke su da muhimmanci. Jehobah ya ba mu dokokinsa ne don su kāre mu. Sharon ta rasu bayan sati bakwai da rubuta waɗannan kalaman. Kamar yadda mugun abin da ya same ta ya nuna, Shaiɗan ba shi da wani abu mai kyau da zai ba waɗanda suke yin sha’ani da wannan mugun zamanin. Da yake shi “uban ƙarya” ne, yana yin alkawura da yawa, amma ba ya cika su kamar yadda ya yi wa Hauwa’u. (Yoh. 8:44) Hakika, yana da kyau mu amince da ikon Jehobah.

Ka Guji Halin Neman ’Yancin Kai

13. A wane ɓangare ne muke bukatar mu guji neman ’yancin kai?

13 Don mu amince da ikon Jehobah, muna bukatar mu guji halin neman ’yancin kai. Girman kai zai iya sa mu ga cewa ba ma bukatar ja-gora daga kowa. Alal misali, za mu iya ƙin shawarar da dattawa suka ba mu. Allah ya tsara yadda bawan nan mai aminci mai hikima zai yi mana tanadin abinci na ruhaniya a kan kari. (Mat. 24:45-47) Da tawali’u, ya kamata mu fahimci cewa wannan ita ce hanyar da Jehobah yake kula da mutanensa a yau. Ka bi misalin manzanni masu aminci. Sa’ad da wasu almajirai suka daina binsa, Yesu ya tambayi manzannin: “Ku kuma kuna so ku tafi?” Bitrus ya amsa masa, ya ce, “Ubangiji, a wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada.”—Yoh. 6:66-68.

14, 15. Me ya sa ya kamata mu bi gargaɗin da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

14 Kasance a ƙarƙashin ikon Jehobah ya ƙunshi yin abubuwan da suka jitu da umurnin da ke cikin Kalmarsa. Alal misali, rukunin bawan nan mai aminci mai hikima yana ci gaba da yi mana gargaɗi cewa mu “zauna a faɗake, da natsuwa.” (1 Tas. 5:6, LMT.) Irin wannan gargaɗin yana da muhimmanci sosai a waɗannan kwanaki na ƙarshe inda mutane da yawa suka “zama masu-son kansu, masu-son kuɗi.” (2 Tim. 3:1, 2) Irin waɗannan halayen da suka zama gama gari za su iya shafanmu kuwa? Ƙwarai kuwa. Makasudan da ba na ruhaniya ba za su iya sa mu daina mai da hankali ga dangantakarmu da Jehobah, ko kuwa mu soma neman abin duniya. (Luka 12:16-21) Saboda haka, abu ne mai muhimmanci sosai mu bi gargaɗin da Littafi Mai Tsarki ya yi kuma mu guji hanyar rayuwa ta son kai da ta zama gama gari a duniyar Shaiɗan!—1 Yoh. 2:16.

15 Ana aika da abinci na ruhaniya da ake samu daga rukunin bawan nan mai aminci mai hikima zuwa ikilisiyoyi ta hanyar dattawa da aka naɗa. Littafi Mai Tsarki ya umurce mu: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan mara-anfani ne gareku.” (Ibran. 13:17) Wannan yana nufin cewa dattawan ikilisiya ba sa kuskure ne? A’a. Allah yana ganin ajizancinsu sosai fiye da mutane. Duk da haka, ya ce mu yi musu biyayya. Ba da haɗin kai ga dattawa duk da cewa su ajizai ne, zai nuna cewa mun amince da ikon Jehobah.

Muhimmancin Tawali’u

16. Ta yaya za mu iya nuna daraja ga Yesu a matsayin Shugaban ikilisiyar Kirista?

16 A kowane lokaci, ya kamata mu dinga tuna cewa Yesu ne ainihin Shugaban ikilisiya. (Kol. 1:18) Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa muke bin ja-gorancin dattawan da aka naɗa da tawali’u, kuma mu “ga kwarjininsu ƙwarai da gaske.” (1 Tas. 5:12, 13) Hakika, su ma dattawan ikilisiya za su iya nuna biyayya ta wajen gaya wa ikilisiya saƙon Allah, ba nasu ra’ayin ba. Ba sa “zarce abin da an rubuta” don su ɗaukaka ra’ayinsu.—1 Kor. 4:6.

17. Me ya sa kasancewa da dogon buri yake da haɗari?

17 Dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna bukatar su mai da hankali da ɗaukaka kansu. (Mis. 25:27) Wannan shi ne tarkon da wani almajirin da manzo Yohanna ya haɗu da shi ya faɗa. Ya rubuta: “Diyoturifis, wanda ya ke so ya sami shugabanci a cikinsu, ba shi karɓanmu. Ni fa, idan na zo, sai in tuna da ayukansa da ya ke aika, miyagun zantattukan da ya ke ambatonmu da su.” (3 Yoh. 9, 10) Akwai darasin da za mu koya a yau. Muna da dalili mai kyau na kawar da duk wani dogon burin da muke da shi. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Bayan girman kai sai halaka, faɗuwa kuma tana biye da tada hanci.” Dole waɗanda suka amince da ikon Allah su guji fahariya, saboda ƙin yin hakan zai kai ga cin mutunci.—Mis. 11:2; 16:18.

18. Menene zai taimake mu mu amince da ikon Jehobah?

18 Hakika, ka ƙudurta guje wa ruhun duniya na neman ’yancin kai kuma ka amince da ikon Jehobah. Ka ci gaba da yin bimbini a kan gata mai girma da kake da shi na bauta wa Jehobah. Da yake kana cikin mutanen Allah ya nuna cewa shi ne ya jawo ka ta wurin ruhunsa mai tsarki. (Yoh. 6:44) Kada ka yi wasa da dangantakarka da Allah. Ka yi iya ƙoƙarinka a dukan fasalolin rayuwa ka nuna cewa ba ka son ’yancin kai kuma ka amince da ikon Jehobah.

Ka Tuna?

• Menene amincewa da ikon Jehobah yake nufi?

• Ta yaya ne koyar da “hankalinmu” ya jitu da amincewa da ikon Jehobah?

• A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan yake ƙoƙarin ya ƙasƙantar da ikon Allah?

• Me ya sa tawali’u yake da kyau a wajen amincewa da ikon Allah?

[Hoto a shafi na 18]

“Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”

[Hoto a shafi na 20]

Yana da muhimmanci mu bi mizanan Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba