Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 pp. 4-9
  • Jimre Baƙin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jimre Baƙin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Baƙin Ciki?
  • Jure Baƙin Ciki
  • Ka Kusaci Allah
  • Begen Tashin Matattu
  • How Can I Live With My Grief?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • ”Ku Yi Kuka Tare da Masu-Kuka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Sa’ad da Aka Mana Rasuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Is It Normal to Feel This Way?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 pp. 4-9

Jimre Baƙin Ciki

“Dukan [’ya’yan Yakubu] maza da mata suka tashi garin su yi masa ta’aziya; amma ya ƙi ta’azantuwa; ya ce, Gama ni zan shiga kabari wurin ɗana ina makoki. Ubansa ya yi kuka dominsa.”—FARAWA 37:35.

YAKUBU uban iyali ya yi kuka sosai domin rashin ɗansa. Ya ce zai yi kuka har ya mutu. Kamar Yakubu, kana iya jin cewa baƙin cikin da ke tattare da mutuwar wanda kake ƙauna ba zai ƙare ba. Irin wannan baƙin cikin yana nufin cewa ba a yi imani ba ne ga Allah? A’a!

Littafi Mai Tsarki ya kira Yakubu mutumi mai bangaskiya. Tare da kakansa Ibrahim da kuma mahaifinsa, Ishaƙu, an yaba wa Yakubu domin fitacciyar bangaskiyarsa. (Ibraniyawa 11:8, 9, 13) Akwai lokacin da ya yi kokawa har kusan wayewar gari da mala’ika don ya sami albarka daga Allah! (Farawa 32:24-30) Babu shakka, Yakubu mutumi ne mai ruhaniya sosai. To, menene za mu iya koya daga baƙin cikin da Yakubu ya yi? Mutum yana iya kasancewa da bangaskiya sosai ga Allah kuma ya yi mugun baƙin ciki da kuka sa’ad da ya yi rashin wanda yake ƙauna. Baƙin ciki da kuka hanya ce ta nuna rashin da muka yi na wanda muke ƙauna.

Menene Baƙin Ciki?

Baƙin ciki yana iya shafanmu a hanyoyi dabam dabam, amma ga yawanci irin wannan tunanin yana shafan motsin zuciyarsu sosai. Ka yi la’akari da abin da Leonardo ya shaida, wanda yake ɗan shekara 14 sa’ad ciwon zuciya da taushewar hanyar numfashi suka kashe mahaifinsa. Leonardo ba zai taɓa mance ranar da ƙanwar mahaifiyarsa ta ba shi labarin ba. Da farko, bai yarda ba cewa gaskiya ne. Ya ga gawar mahaifinsa a wurin jana’iza, amma kamar dai abin ba gaskiya ne ba. Leonardo ya kasa kuka har na tsawon watanni shida. A yawancin lokaci, sai ya ga cewa yana jiran mahaifinsa ya dawo gida daga wurin aiki. Ya ɗauke shi wajen shekara ɗaya kafin ya fahimci cewa mahaifinsa ya mutu. Sa’ad da hakan ya faru, sai ya ji kamar bai da kowa. Wasu abubuwa kamar, komawa gidan da babu kowa, yana tuna masa da mutuwar mahaifinsa. A irin waɗannan lokatai ya kan fashe da kuka. Yayi rashin mahaifinsa sosai!

Kamar yadda labarin Leonardo ya nuna, baƙin ciki yana iya yin tsanani. Abin farin ciki shi ne, za a iya daina wa. Amma, hakan na iya ɗaukan dogon lokaci. Kamar yadda mugun ciwo yake ɗaukan lokaci kafin ya warke, haka ma baƙin ciki. Warwarewa daga baƙin ciki na iya ɗaukan watanni, ’yan shekaru, ko fiye a haka. Amma baƙin cikin da kake yi zai ragu bayan wani ɗan lokaci, kuma rayuwa za ta kasance da ma’ana.

A yanzu, an ce baƙin ciki da kuka sashe ne na warkarwa da kuma koyan yadda za a saba da sabon yanayin. Akwai wani wurin da a dā akwai mutum. Muna bukatar mu daidaita rayuwarmu tun da ba mutumin. Kuka za ta iya taimaka maka ka nuna yadda kake ji. Mu duka muna nuna baƙin cikinmu a hanyoyi dabam dabam. Amma, gaskiyar ita ce: Idan ka danne baƙin cikinka, hakan na iya shafan tunaninka, motsin ranka, da kuma jikinka. Ta yaya za ka iya nuna baƙin cikinka a hanyoyin da suka dace? Littafi Mai Tsarki yana ƙunshe da wasu hanyoyi masu kyau.a

Jure Baƙin Ciki

Yawancin mutanen da suka yi rashi sun ga cewa yin magana yana iya sa a samu sauƙi. Alal misali, yi la’akari da kalaman mutumin nan Ayuba da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wanda ya rasa duka ’ya’yansa goma kuma ya jimre wasu bala’o’i. Ya ce: “Na gaji, duk na gaji da raina. Zan fita da ƙarata a fili; In yi magana cikin ɓācin raina.” (Ayuba 1:2, 18, 19; 10:1) Ka lura cewa Ayuba yana bukatar ya “fita” da abubuwan da ke damunsa. Ta yaya zai yi hakan? Ya ce, zai “yi magana.”

Paulo, wanda ya rasa mahaifiyarsa, ya ce: “Wani abin da ya taimake ni shi ne tattaunawa game da mahaifiyata.” Saboda haka, tattaunawa game da yadda kake ji da abokin da ka amince da shi zai iya sa ka sami sauƙi. (Misalai 17:17) Sa’ad da ta rasa mahaifiyarta, Yone ta roƙi ’yan’uwanta Kirista su riƙa ziyarta a kai a kai. “Yin magana yana rage baƙin cikin,” in ji ta. Kai ma za ga cewa faɗin yadda kake ji da kuma tattauna batun da waɗanda za su saurare ka sosai zai taimaka maka ka magance batun.

Yin rubutu zai iya taimaka a sami sauƙi. Waɗanda faɗin yadda suke ji yana yi musu wuya suna iya rubuta yadda suke ji. Bayan mutuwar Saul da Jonathan, Dauda mutumi mai aminci ya rubuta waƙar baƙin ciki inda ya ambata baƙin cikinsa. Wannan waƙar ta baƙin ciki ta zama sashen littafin Samuila na Biyu da ke Littafi Mai Tsarki.—2 Samuila 1:17-27.

Yin kuka zai iya sa a samu sauƙi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga kowane abu akwai nasa kwanaki, . . . akwai lokacin kuka.” (Mai-Wa’azi 3:1, 4) Babu shakka, mutuwar wanda muke ƙauna ‘lokaci ne na kuka.’ Yin kuka saboda rashi ba abin kunya ba ne. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan maza da mata da yawa masu aminci da suka nuna baƙin cikinsu ta wajen yin kuka. (Farawa 23:2; 2 Samuila 1:11, 12) Yesu Kristi “ya yi kuka” sa’ad da ya kusanci maƙabartar Li’azaru, wanda bai daɗe da mutuwa ba.—Yohanna 11:33, 35.

Jimre wa da baƙin ciki yana ɗaukan lokaci, domin motsin ranka zai ɗinga canjawa. Ka tuna cewa ba ka bukatar jin kunyar hawayenka. Yawancin mutane masu aminci sun ga cewa zubar da hawaye na baƙin ciki sashe ne na samun sauƙi.

Ka Kusaci Allah

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yaƙub 4:8) Ɗaya daga cikin hanyoyi na musamman da za mu iya kusantar Allah ita ce yin addu’a. Kada ka raina tamaninta! Littafi Mai Tsarki ya yi wannan alkawarin mai ƙarfafawa: “Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:18) Ya kuma ba mu wannan tabbacin: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka.” (Zabura 55:22) Ka yi tunanin wannan. Kamar yadda muka ambata ɗazu, yawanci sun ga cewa tattaunawa game da yadda suke ji da abokin da suka gaskata da shi yana taimakawa. Kana ganin ba za ka fi samun taimako ba idan ka gaya wa Allah wanda ya yi alkawarin cewa zai ta’azantar da zukatanmu yadda kake ji ba?—2 Tassalunikawa 2:16, 17.

Paulo, wanda aka ambata ɗazu, ya ce: “Sa’ad da na ji cewa ba zan iya jimre baƙin cikin ba, na kan durƙusa kuma na yi addu’a ga Allah. Na roƙe shi ya taimake ni.” Paulo ya gaskata cewa addu’o’insa sun taimaka masa sosai. Kai ma za ka iya ganin cewa ta wajen nacewa a addu’a, “Allah na dukan ta’aziyya” zai ba ka ƙarfafawa da gaba gaɗin da kake bukata don ka jimre.—2 Korinthiyawa 1:3, 4; Romawa 12:12.

Begen Tashin Matattu

Yesu ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” (Yohanna 11:25) Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a yi tashin matattu.b Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa zai iya ta da matattu. Akwai lokacin da ya ta da wata yarinya ’yar shekara 12. Yaya iyayenta suka ji? Sun “yi mamaki nan da nan da mamaki mai-girma.” (Markus 5:42) A ƙarƙashin sarautar Mulkinsa, Sarki na samaniya Yesu Kristi zai ta da matattu masu yawa zuwa rai a duniya, kuma yanayin zai kasance mai salama da adalci. (Ayukan Manzanni 24:15; 2 Bitrus 3:13) Ka yi tunanin irin farin cikin da mutane za su yi sa’ad da aka ta da matattu kuma suka sake saduwa da ƙaunatattunsu!

Claudete, wadda ɗanta ya mutu a haɗarin jirgin sama, ta ɗaura hoton ɗanta, Renato, a kan firiji. A yawancin lokaci ta kan kalli hoton kuma ta gaya wa kanta, “Za mu sake saduwa a lokacin tashin matattu.” Leonardo ya kan yi tunanin ganin ubansa ya tashi daga matattu a cikin sabuwar duniyar da Allah ya yi alkawari. Hakika, begen tashin matattu yana ƙarfafa su da dukan mutanen da suka yi rashin waɗanda suke ƙauna. Zai iya ƙarfafa ka!

[Hasiya]

a Don ganin yadda za a taimaka wa yara su jimre mutuwar wanda suke ƙauna, ka duba talifin nan “Help Your Child Cope With Grief,” da ke shafi na 18 zuwa 20 na w08-E 07/01 na Turanci.

b Don ƙarin bayani game da begen tashin matattu da ke Littafi Mai Tsarki, ka duba babi na 7 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Box/Hoto a shafi na 7]

“Allah na Dukan Ta’aziyya”

“Albarka ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya.”—2 Korinthiyawa 1:3.

Wannan ayar ta Littafi Mai Tsarki ta nuna cewa Allah zai iya taimaka wa bayinsa masu aminci su jimre duk wata matsala ko ƙalubale da za su fuskanta. Wata hanya da Jehobah zai iya ƙarfafa mutum ita ce ta wajen aboki ko wanda muke ƙauna da mai bi ne.

Leonardo, wanda ya yi rashin mahaifinsa, ya tuna wani abin da ya ƙarfafa shi kuma ya ta’aziyyartar da shi. Ya isa gida, amma sa’ad da ya tuna cewa babu kowa a gidan, sai ya soma kuka ba ji ba gani. Ya tafi wani waje da mutane suke hutawa ya zauna kan benci, kuma ya ci gaba da kuka. Sa’ad da yake kuka, ya roƙi Allah ya taimaka masa. Kwaram, sai wata mota ta tsaya, kuma Leonardo ya lura cewa direban motar ɗan’uwansa ne Kirista. Ɗan’uwan yana son ya kai kaya ne ga masu yin sayayya a wurinsa, kuma ya bi wata hanyar dabam. Kasancewarsa a wurin ya ƙarfafa Leonardo.

A wani lokaci kuma, wani gwauro yana jin kaɗaici kuma yana cike da baƙin ciki. Ya kasa daina kuka domin yana gani kamar dai komi ya ƙare. Ya nemi taimakon Allah. Sa’ad da yake cikin addu’a, sai wayarsa ta soma ƙara. Jikarsa ce ta kira. Ya tuna: “Ɗan tattaunawar da muka yi tare ya ƙarfafa ni sosai. Na gaskata cewa kiran da ta yi shi ne amsar taimakon da na roƙa.”

[Akwati a shafi na 9]

Ƙarfafa Wasu

“[Allah] da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu, har da za mu iya ta’azantarda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci, ta wurin ta’aziyya wadda mu da kanmu muka ta’azantu da ita daga wurin Allah.”—2 Korinthiyawa 1:4.

Kiristoci da yawa sun shaida ma’anar waɗannan kalaman. Ta wajen ta’aziyya sun jimre rashin wanda suke ƙauna, sun ga cewa suna iya ƙarfafa da kuma ta’aziyantar da wasu.

Yi la’akari da misalin Claudete, wadda take ziyartar wasu a kowane lokaci don ta gaya musu abin da ta gaskata da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kafin ta yi rashin ɗanta, tana ziyartar wata matar da cutar daji mai shan jini ya kashe ɗanta. Matar tana jin daɗin ziyarar, amma tana jin cewa Claudete ba za ta taɓa fahimtar baƙin cikin da take ji ba. Amma, ba da daɗewa ba bayan mutuwar ɗan Claudete, matar ta ziyarce ta kuma ta gaya mata cewa ta zo ta gani ne ko har yanzu Claudete tana riƙe da bangaskiyarta. Domin bangaskiyar Claudete ya burge ta, Claudete tana nazarin Littafi Mai Tsarki da wannan matar kuma tana samun ta’aziyya daga Kalmar Allah.

Bayan mutuwar mahaifinsa, Leonardo ya yanke shawarar koyan yaren kurame don ya gaya wa kurame ta’aziyyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ya ga cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcensa na taimaka wa kurame ya amfane shi sosai. Ya ce: “Wani abin da ya taimaka mini na jimre da baƙin cikin shi ne muradi na son taimaka wa kurame su koyi game da Allah. Na keɓe lokaci da kuma ƙarfi mai yawa don na taimaka musu. Baƙin cikin da nike ji ya zama farin ciki sa’ad da na ga ɗalibi na na farko na Littafi Mai Tsarki ya yi baftisma! A gaskiya, tun lokacin da mahaifi na ya rasu, wannan shi ne lokaci na farko da na sami farin ciki sosai.”—Ayukan Manzanni 20:35.

[Hoto a shafi na 5]

Furta yadda kake ji zai iya sa

ka sami sauƙi

[Hoto a shafi na 6]

Yin rubutu zai iya taimaka maka ka furta baƙin cikinka

[Hoto a shafi na 6]

Yin karatu game da begen tashin matattu zai iya ƙarfafawa sosai

[Hoto a shafi na 8]

Yesu ya yi alkawarin tashin matattu ga waɗanda suka yi imani da shi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba