Daidai Ne a Ji Haka?
WANI da aka yi masa rasuwa ya rubuta haka: “Kamar yaro cikin Ingila fa, an koya mani kada in nuna jiye-jiyena a cikin jama’a. Na tuna da yadda ubana, wanda soja ne dā, yake mani magana da ɗaurin fuska, ‘Kul kada ka yi kuka!’ sa’anda wani abu ya ɓace mani rai ko. Ban iya tunawa ko uwata ta taɓa sumbace ko kuwa rungume wani cikin mu yaran ba (mu huɗu ne). Shekaru na 56 ne sa’anda ubana ya mutu. Na taɓu ƙwarai da gaske. Duk da haka, a farko, ban iya kuka ba.”
A wasu al’adu fa, mutane sukan nuna jiye-jiyensu a buɗe. Ko suna farinciki ko kuwa baƙinciki, wasu sukan san yadda suke ji. A wata sassa kuma, cikin wasu bangororin duniya fa, musamman a ta arewancin Turai da Britaniya, mutane, musamman mazaje, ana bukatar su ɓoye jiye-jiyensu, su danna juyayinsu, su ƙi nuna sun damu a lokacin azaba kuma nuna jiye-jiye cikin jama’a. Amma yayinda ka yi hasarar wani ƙaunatacce, ashe laifi ne ka nuna baƙincikinka? Minene Littafi Mai-Tsarki ya faɗa?
Waɗanda Suka yi Kuka Cikin Littafi Mai-Tsarki
Ibraniyawa na yankin gabashin Bahar Maliya ne suka rubuta Littafi Mai-Tsarki, mutane masu nuna jiye-jiye ne. Yana kunshe da misalai dayawa na mutane da suka nuna baƙincikinsu a fili. Sarki Dauda ya yi baƙincikin kisan ɗansa Amnon. Hakika fa, ya “yi kuka mai-zafi.” (2 Samuila 13:28-39) Har ma ya yi baƙincikin rashin ɗansa mai-ha’inci Absalom, wanda ya yi ƙoƙarin kwashe sarautancinsa. Labarin Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana haka: “Sai [Dawuda] sarki ya yi juyayi dayawa, ya hau wajen benen da ke kan ƙofa, ya yi ta kuka; yana tafiya, yana cewa, Ya ɗana Absalom, ya ɗana, ɗana Absalom! da ma Allah ya yarda na mutu dominka, ya Absalom, ya ɗana, ɗana!” (2 Samuila 18:33) Dawuda ya yi makoki kamar yadda uba yakan yi. Kuma duba yawan yadda iyaye suna gwammance su mutu maimakon yaransu! Mutuwar yaro kafin mahaifin kamar dai ba abin al’ada ba ne.
Ina yadda Yesu ya mayas da martani ga mutuwar abokinsa Li’azaru? Ya yi kuka yayinda ya kusance kabarinsa. (Yohanna 11:30-38) Nan gaba, Maryamu Magdaliya ta yi kuka yayinda ta kusance kabarin Yesu. (Yohanna 20:11-16) Gaskiya fa, Kirista da ke da ganewar begen Littafi Mai-Tsarki na tashin matattu ba shi baƙinciki gaba da karɓin ta’aziya, kamar yadda wasu suke yi waɗanda basu san imanin Littafi Mai-Tsarki na bangaskiyarsu game da yanayin matattu ba. Amma kamar ɗan-Adam wanda ke da jiye-jiye fa, Kirista na gaskiya, duk da begen tashin matattu, yakan yi baƙinciki da kuma makokin rashin wani ƙaunatacce.—1 Tassalunikawa 4:13, 14.
Yi Kuka ko Kuwa Ƙi Kuka
Me kuma za a ce game da martaninmu ayau? Ashe kana iske shi da wuya ko kuwa kamar abin kunya ne ka nuna jiye-jiyenka? Minene mashawarta suka shawarta? Ra’ayoyinsu na zamani yana furta hurarren hikimar Littafi Mai-Tsarki na dā ne. Sun ce wai mu nuna baƙincikinmu, kada mu danna ta. Wannan ya tunashe mu game da amintattun mutanen dā, kamar su Ayuba, Dawuda, da Irmiya, waɗanda an samu nunin baƙincikinsu cikin Littafi Mai-Tsarki. Ba su kuwa ɓoye jiye-jiyensu ba. Saboda haka, ba abin hikima ba ne ka ware kanka daga mutane. (Misalai 18:1) Hakika kam, akan nuna makoki a hanyoyi dabam dabam cikin al’adu dabam dabam, kuma yana dangana bisa imanin addini da ke ruwan-dare.a
Idan kuma kana jin kamar yin kuka fa? Halin yan-Adam ne su yi kuka. Ka tuna da lokacin mutuwar Li’azaru, lokacinda Yesu “ya ji haushi cikin ruhunsa, . . . ya yi kuka.” (Yohanna 11:33, 35) A ta haka fa ya nuna cewa yin kuka mayas da martani ne da ke daidai ga mutuwar ƙaunatacce na wani.
An goyi bayan wannan da zancen wata uwa, Anne, wadda ta yi rashin ɗiyarta, Rachel ta wurin SIDS (Mutuwa Farat na Jariri). Mijinta ya furta haka: “Abin mamaki duka shine cewa Anne ko kuwa ni ba mu yi kuka a jana’izar ba. Kowa dai kuka yake yi.” Game da wannan fa Anne, ta faɗi haka: “I fa, amma na yi kuka ko sosai a maimakon dukanmu. Na soma shaida jiye-jiyen yan makonni ne bayan masifar, yayinda na kasance kaɗai wata rana cikin gida. Na yi ta kuka dukan yini. Amma na gaskata cewa kuka duk yini ya taimake ni. Na sauƙaƙa bayan haka. Na yi makokin mutuwar jariri ta. Na gaskata sarai ya dace ka ƙyalle mutane masu baƙinciki su yi kuka. Ko da shike abinda wasu sun saɓa yi ne su faɗi cewa, ‘Kada ka yi kuka,’ hakan baya taimakawa sarai.”
Yadda Wasu Suke Mayas da Martani
Ina yadda wasu sun mayas da martani yayinda suka wofinta ta wurin mutuwar wani ƙaunatacce? Bari mu yi la’akari da zancen Juanita. Ta san yadda yake a yi rashin jariri. Ta shaida ɓarin ciki ko sau biyar. Yanzu ta sake yin juna biyu ko. Saboda haka yayinda wani hatsarin mota ya tilasta ta zuwa asibiti fa, ta damu kuwa ƙwarai da gaske. Makonni biyu nan gaba ta haifu—jaririn bai ƙosa ba. Jim kaɗan an haife Vanessa—nauyinta da kaɗan ya shige kilogiram 0.9. “Na yi farinciki,” in ji Juanita. “Kai ni uwa ce yanzu!”
Amma farincikinta na ɗan lokaci ne. Kwanaki biyu nan gaba Vanessa ta mutu. Juanita ta ce: “Na wofinta. An raba ni da zaman uwa ta. Na ji kamar katsattse. Abin zafin rai ne mu dawo gida ga daƙin da muka shirya wa Vanessa da kuma yan rigunan da na saya mata. A sauran watanni da suka biyo, na sauƙaƙa ranar haifuwarta. Bana son in samu wani abinda zan yi da kowa.”
Martani mai-tsananni ne? Zai iya zama da wuya ga wasu su gane, amma ga waɗanda, kamar Juanita, sun taɓa shaida haka fa sun bayyana cewa sun yi makokin jariransu daidai kamar yadda zasu yi ga wani da ya rayu ko da daɗewa. Sun bayyana, da daɗewa kafin haifuwar jariri, iyayen suna ƙaunarsa. Da akwai dangataka na musamman da uwar. Yayinda jaririn nan ya mutu fa, wani ne ya mutu sarai. Kuma abinda wasu suke bukatar ganewa ke nan.
Yadda Fushi da Jin Laifi Zai Iya Taɓe Ka
Wata uwa ta bayyana martaninta yayinda aka gaya mata cewa ɗanta mai-shekaru shidda ya mutu ko farat domin ciwon zuciya mai-tsanani. “Na yi ta mayas da martani dabam dabam—rashin yin magana, ƙin yarda, jin laifi, da kuma fushi da mijina da likitan don kasa gane tsananin yanayinsa.”
Fushi zai iya zama wata alamar baƙinciki. Zai iya zama fushi da likitoci da mataimakansu, jin cewa da sun aika fiye da yadda suka yi don kula da wanda ya mutun. Ko kuwa zai iya zama fushi da abokai ko kuwa dangogi waɗanda, kamar dai, sun faɗi ko kuwa yi abinda ya ƙuskura. Wasu suna fusatawa da wanda ya mutun don kasa kula da lafiyar kansa. Stella ta tuna da haka: “Na tuna na ji fushi da mijina domin na sani cewa da al’amarin ya kasance dabam. Ya yi ta ciwo ko, amma ya yi ta banza da fadakadwar likitar.” A wasu lokutta kuma da akwai fushi game da wanda bashin domin nauyin da mutuwarsa ko kuwa mutuwarta ya kawo bisa waɗanda suke da rai.
Wasu suna jin laifi domin fushi—watau, sukan ba kansu laifi domin sun ji fushin. Wasu sukan ba kansu laifin mutuwar wani ƙaunatacce nasu. “Da bai mutu ba,” sukan tabbatas da kansu, “in da a ce na kai shi wajen likita da sauri” ko kuwa “kai shi wajen wani likita dabam” ko kuwa “sa shi kula da lafiyarsa fiye da haka.”
Ga wasu fa jin laifin yana wuce gaba da haka, musamman idan ƙaunataccensu ya mutu farat ne, babu labari. Sukan soma tuna yawan lokacinda suka fusata wanda ya mutun ko kuwa yawan lokaci da suka yi jayayya da shi. Ko kuwa su a ji cewa basu bada kansu ainun ga wanda ya mutun kamar yadda ya dace ba.
Tsawon lokacin baƙincikin uwaye dayawa ya yarda da abinda yawancin gwanaye suka faɗi, cewa rashin yaro yana jawo ɓacin ran iyaye da daɗewa, musamman uwar.
Yayinda Ka yi Rashin Abokin Aure
Rashin abokin aure shine wani irin baƙinciki, musamman ma idan dukansu suna taimakon juna. Zai iya nufa canji na yayin rayuwa da suka saɓa yi duka ne, na tafiya, aiki, nishaɗi, da kuma danganawa bisa juna.
Eunice ta bayyana abinda ya faru yayinda mijinta ya mutu farat daga ciwon zuciya. “A mako na farkon fa, ina cikin matsayin kurmanci ne, kamar dai na denna rayuwa. Ban iya jin daɗin ɗanɗana ko kuwa sansanawa ba. Duk da haka, azanci na ya kasa jituwa da juna. Domin na zauna da mijina yayinda suke ƙoƙarin tokara shi ta wurin CPR (halin mayas da rai ga zuciya) da magani, ban shaida irin hanin nan ba. Duk da haka dai, da akwai jiye-jiye mai-ƙarfi na ɓacin rai, kamar dai ina kallon mota da ke gangarawa cikin wata kwari kuma babu abinda zan yi game da shi.”
Ta yi kuka? “Hakika fa na yi, musamman yayinda na karanta ɗarurruwan katin ta’aziya da an aiko mani. Nakan yi kuka da ganin kowanne. Yana taimaka mani in iya jurewa a duk yini. Amma babu wani abinda ke taimakawa yayinda sau da sau ake tambaye ni yadda nike ji. Lallai fa, na baƙanta ƙwarai.”
Minene ya taimake Eunice ta iya jure da baƙincikinta? “Ba tare da sani na ba, na tsai da shawara in ci gaba da rayuwa na ba tare da wani ƙoƙari ba,” in ji ta. “Amma dai, abinda ke ɓata mani rai har ila shine yayinda na tuna cewa mijina, wanda yake ƙaunar rai sosai haka, ba shi kuma don ya more shi.”
“Kada Ka Yarda Ma Wasu Su Aza . . .”
Mawallafan Leavetaking—When and How to Say Goodbye sun shawarta haka: “Kada ka yarda ma wasu su aza yadda ya kamata ka aika ko kuwa ji. Halin nuna baƙinciki yana bambantawa da kowa. Wasu su a iya tunani—kuma su nuna maka cewa suna tunani—wai kana baƙinciki ainun ko kuwa baka baƙinciki ainun. Ka gafarta masu kuma manta da shi. Ta wurin tilasta ma kanka ka kasance cikin matsayi da wasu sun yi ko kuwa wata jam’iyya sukutum fa, zaka hana girman iya sabontawar lafiyar jiye-jiyenka.”
Hakika fa, mutane dabam dabam suna kula da baƙincikinsu a hanyoyi dabam dabam. Ba mu a ƙoƙarin faɗin cewa wata hanya ɗaya ta zarce wata ga kowane mutum. Amma dai, haɗari yakan taso yayinda rashin gushewa ya auku, yayinda wanda ke baƙinciki ya kasa yarda da gaskiyar al’amarin. Hakan zai bukace taimako ke nan daga abokai masu juyayi. Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” Don haka kada ka ji tsoron biɗan taimako, yin magana, da kuma yin kuka.—Misalai 17:17.
Baƙinciki martani ne da ya dace don wani rashi, kuma ba mumunar abu ba ne baƙincikinka ya bayanu ga wasu. Amma da akwai ƙarin tambayoyi da suke bukatar amsoshi: ‘Ina yadda zan iya jure da baƙincikina? Shin daidai ne jin laifi da jin fushi? Ina yadda zan yi sha’ani da martanin nan? Minene zai taimake ni in jure da rashin da kuma baƙincikin?’ Sashe na gaba zai amsa waɗannan da kuma wasu tambayoyi.
a Alal misali, Yarabawa na Nijeriya suna da al’adar gaskata da ra’ayin sāke haifuwar kurwa. Saboda haka yayinda uwa ta yi rashin yaro, akan yi baƙinciki na ƙwarai amma na ƙaramar lokaci ne, gama kamar yadda ra’ayin Yarabawa ya sa shi fa: “Ruwa ne kawai ya zuba. Ƙwaryar bata fashe ba.” Bisa ga Yarabawa fa, ƙwaryar da ke ɗauke da ruwan, uwar, zata iya haife wani yaro kuma—watakila sāke haife mataccen. Shaidun Jehovah basu bin wasu al’adu masu tushi bisa camfi da ke fitowa daga ra’ayoyin ƙarya na rashin mutuwar kurwa da kuma na sāke haifa wanda ya mutu, waɗanda basu da tushe cikin Littafi Mai-Tsarki.—Mai-Wa’azi 9:5, 10; Ezekiel 18:4, 20.