Laifi Ne A Kira Sunan Allah?
ACIKIN rubutu na ainihi na nassosin Ibrananci, da ake yawan kira “Tsohon Alkawari,” sunan Allah ya bayyana kusan sau 7,000 kamar haka יהוה (ana karanta wa daga dama zuwa hagu.) Wannan yana nufin cewa ana rubuta sunan Allah da baƙaƙe huɗu na Ibrananci Yohdh, He, Waw, da He, wanda ake rubutawa YHWH.
Da daɗewa, Ibraniyawa sun yi camfi cewa laifi ne a kira sunan Allah. Saboda haka, suka ƙi furta sunan, suka kuma fara sake sunan da wasu furci. Yawancin waɗanda suka fassara Littafi Mai Tsarki, suna rubuta sunan “Yahweh,” ko “Jehobah.” Ɗaya daga cikin fassara da suka yi haka shi ne Catholic Jerusalem Bible. In ji wannan fassarar, sa’ad da Musa ya tambayi Allah yaya zai amsa idan Isra’ilawa suka tambaye shi, wa ya aike shi gare su, Allah ya ce: “Ka gaya wa ’ya’yan Isra’ila, Yahweh, Allah na ubanninku, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub, ya aike ni gareku: wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.”—Fitowa 3:15.
Sa’ad da yake addu’a, Yesu ya ce game da yadda ya yi amfani da sunan Allah: “Na kuma sanar masu da sunanka, zan kuma sanarda shi.” A kuma addu’ar da aka fi sani da Addu’ar Ubangiji, Yesu ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.”—Yohanna 17:26; Matta 6:9.
Saboda haka zai kasance abin mamaki, a fahimci cewa a littafinsa na baya bayan nan Jesus of Nazareth, (Yesu Banazare), Paparoma Benedict na XVI ya faɗi haka game da yin amfani da sunan Allah: “Abin da Isra’ilawa suka yi . . . daidai ne da suka ƙi furta wannan sunan na Allah, da ake rubuta wa YHWH, don a guji lalata sunan har ya yi daidai da sunan allolin arna. Kuma saboda haka, waɗanda suka fassara Littafi Mai Tsarki a baya bayan nan ba su kyauta ba da suka rubuta sunansa, wanda Isra’ilawa suka ɗauke shi gaibi ne wanda ba a furta wa.”
Me kake tsammani? Daidai ne ko ba daidai ba ne a kira sunan Allah? Idan Jehobah da kansa ya ce: “Wannan sunana ne a dukan lokaci; da wannan suna za a kira ni daga zamani zuwa zamani,” akwai wanda ya isa ya ce ba haka ba ne?
[Hoto a shafi na 30]
Yesu ya yi amfani da sunan Allah a addu’a