Domin Matasanmu
Fushin Ɗan’uwa
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda zaka iya mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da kake karanta nassosi, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka ji kamar kana wurin. ◼◼◼
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN.—KA KARANTA FARAWA 4:1-12, Littafi Mai Tsarki.
Ta wajen yin amfani da kwatancin zuci, yaya za ka kwatanta kamanin Kayinu, fuskarsa da kuma halinsa? Habila kuma fa?
․․․․․
Waɗanne “ayyukan jiki” ne Kayinu ya yi, kuma yaya muka san hakan? (Galatiyawa 5:19-21)
․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.—KA SAKE KARANTA FARAWA AYOYI 4-7.
Haɗayun kaɗai ne Jehobah ya karɓa ko ya ƙi karɓa, ko kuwa akwai wasu abubuwa kuma? (Misalai 21:2)
․․․․․
A waɗanne lokatai ne za a iya cewa fushi yana da kyau, amma me ya sa bai dace ba sam Kayinu “ya husata ƙwarai”?
․․․․․
A wane lokaci ne zai dace a yi kishi, amma me ya sa kishin da Kayinu ya yi bai dace ba? (1 Sarakuna 19:10)
․․․․․
Waɗanne matakai ya kamata Kayinu ya ɗauka don ya ‘rinjayi’ fushinsa?
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Fushi.
․․․․․
Kishi.
․․․․․
Yadda za ka ‘rinjayi’ tunani marar kyau.
․․․․․
WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․