Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Game da Yadda Za Mu Bi da Mutane
Me ya sa za ka kasance da Alheri?
Kana kasancewa da alheri har sa’ad da mutane suka yi maka rashin alheri? Idan muna so mu yi koyi da Yesu, muna bukatar mu kasance da alheri har ma ga waɗanda ba sa ƙaunarmu. Yesu ya ce: “In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu. . . . Amma ku yi ƙaunar magabtanku. . . , za ku zama ’ya’yan Maɗaukaki, gama shi mai-alheri ne ga marasa-godiya da miyagu.”—Luka 6: 32-36; 10:25-37.
Me ya sa za ka gafarta?
Sa’ad da muka yi kuskure, muna so Allah ya gafarta mana. Yesu ya koyar da cewa ya dace mu yi addu’a mu nemi gafara daga wurin Allah. (Matta 6:12) Amma, Yesu ya ce Allah zai gafarta mana idan mun gafarta wa mutane. Ya ce: “Gama idan kuna gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku na sama kuma za ya gafarta muku. Amma idan ba ku gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofi ba.”— Matta 6:14, 15.
Ta yaya iyalai za su kasance da farin ciki?
Ko da yake Yesu bai taɓa yin aure ba, za mu iya koyon abubuwa masu yawa daga wurinsa game da yadda iyali za ta kasance da farin ciki. Ta wajen kalmominsa da kuma ayyukansa ya bar mana tafarki da za mu bi. Ka yi la’akari da batutuwa uku na gaba:
1. Ya kamata maigida ya ƙaunaci matarsa kamar kansa. Yesu ya kafa wa magidanta misali. Ya ce wa almajiransa: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna.” Yaya zurfin ƙaunar? “Kamar yadda ni na ƙaunace ku,” in ji shi. (Yohanna 13:34) Littafi Mai Tsarki ya faɗi yadda wannan mizanin ya shafi magidanta, ya ce: “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta. . . Hakanan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyarda shi ya kan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya.”—Afisawa 5:25, 28, 29.
2. Ma’aurata suna bukatar su kasance da aminci ga juna. Yin jima’i da wani da ba abokin aure ba zunubi ne ga Allah kuma yana raba iyalai. Yesu ya ce: “Ba ku karanta ba. . . Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne ma matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba. . . Ni ma na ce muku, Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.”—Matta 19: 4-9.
3. Tilas yara su yi wa iyayensu biyyaya. Ko da yake Yesu kamili ne kuma iyayensa ajizai ne, duk da hakan ya yi musu biyyaya. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu sa’ad da yake ɗan shekara 12: “Ya tafi tare da su, ya zo Nazarat; yana biyayya da su.”—Luka 2:51; Afisawa 6:1-3.
Me ya sa za ka yi amfani da waɗannan mizanan?
Game da darussa da ya koya wa mabiyansa, Yesu ya ce: “Idan kun san waɗannan abu, masu-albarka ne idan kun yi su.” (Yohana 13:17) Domin mu zama Kiristoci na gaske, tilas ne mu yi amfani da shawarar da Yesu ya bayar game da yadda za mu bi da mutane. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohana 13:35.
Domin ƙarin bayani, ka dubi Shafi na 14 na littafi nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne Suka Wallafa.
[Hoto a shafi nas 18, 19]
Almara da Yesu ya yi game da ɗa mai ɓarna ya koya mana muhimmancin alheri da gafartawa.—Luka 15:11-32
[Hoto a shafi na 19]
Ma’aurata suna bukatar su kasance da aminci ga juna