Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 26-27
  • Game da Rayuwar Iyali

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Game da Rayuwar Iyali
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wane ra’ayin aure ne ke sa iyalai farin ciki?
  • Me ya sa yin ƙaunar Allah take sa iyalai farin ciki?
  • Ta yaya miji da mata za su sa juna farin ciki?
  • Menene iyaye za su iya koya daga yadda Yesu ya ɗauki yara?
  • Menene yara za su iya koya daga wurin Yesu?
  • Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Magidanta Ku Yi Koyi Da Shugabancin Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Game da Yadda Za Mu Bi da Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Iyalai Kirista, Ku Bi Misalin Yesu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 26-27

Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu

Game da Rayuwar Iyali

Wane ra’ayin aure ne ke sa iyalai farin ciki?

Aure gami ne mai tsarki. Sa’ad da aka tambaye shi ko ya dace a kashe aure, Yesu ya ce: “Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su, har ya ce, Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne ma matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba. . . . Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi: shi kuma wanda ya auri sakakkiyar, zina ya ke yi.” (Matta 19:4-6, 9) Idan ma’aurata sun bi umurnin Yesu kuma sun kasance da aminci ga juna, kowa a cikin iyalin zai samu kāriya da farin ciki.

Me ya sa yin ƙaunar Allah take sa iyalai farin ciki?

Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.” Waccece kuma doka mafi girma ta biyu? Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka [haɗe da waɗanda suke zama kusa da kai, wato, iyalinka] kamar ranka.” (Matta 22:37-39) Da haka, abin da ke kawo farin ciki a iyali shi ne samun dangantaka da Allah domin yin ƙaunarsa tana motsa mu mu yi ƙaunar juna.

Ta yaya miji da mata za su sa juna farin ciki?

Magidanta suna sa matarsu farin ciki sa’ad da suka bi misalin Yesu. Ya nuna ƙauna ta sadaukar da kai ga matarsa ta alama, ikilisiyar. (Afisawa 5:25) Yesu ya ce: “Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu.” (Matta 20:28) Yesu bai taɓa yin shisshigi ba kuma shi ba matsananci ba ne ga waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsa amma ya sa su kasance da kwanciyar hankali. (Matta 11:28) Ya kamata magidanta su yi amfani da ikonsu a hanya mai kyau da zai amfane kowa a iyalin.

Mata ma za su iya amfana daga misalin Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce, “kan Kristi kuma Allah ne.” Ya kuma ce “kan mace kuma namiji ne.” (1 Korintiyawa 11:3) Yesu bai raina cewa yana ƙarƙashin ikon Allah ba. Yana biyayya sosai ga Ubansa. Yesu ya ce: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:29) Macen da ta yi biyayya ga ikon mijinta domin ƙauna da biyayya ga Allah za ta sa iyalinta farin ciki.

Menene iyaye za su iya koya daga yadda Yesu ya ɗauki yara?

Yesu ya kasance tare da yara kuma ya so ya san tunaninsu da kuma yadda suke ji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yesu ya kirawo su, ya ce, Ku bari yara ƙanƙanana su zo gareni.” (Luka 18:15, 16) Akwai lokacin da, mutane suka yi zargin wasu yara da suka furta imaninsu ga Yesu. Amma Yesu ya ƙarfafa yaran, ya ce wa waɗanda ke neman hana su cewa: “I: ba ku taɓa karantawa ba, Daga cikin bakin jarirai da masu-shan mama ka cika yabo?”—Matta 21:15, 16.

Menene yara za su iya koya daga wurin Yesu?

Yesu ya kafa wa yara misali mai kyau game da abubuwa na ruhaniya. Sa’ad da yake ɗan shekara goma sha biyu, an same shi “cikin haikali, yana zamne a tsakiyar malamai, yana jinsu, yana kuwa yi masu tantambaya.” Da wane sakamako? “Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da magana da ya ke mayarwa.” (Luka 2:42, 46, 47) Duk da hakan, ilimin da Yesu yake da shi bai sa shi girman kai ba. Maimakon hakan, ya sa ya yi biyayya da iyayensa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya ci gaba da “biyayya da su.”—Luka 2:51.

Don ƙarin bayani, ka duba shafi na 14 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba