Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/15 pp. 7-11
  • Iyalai Kirista, Ku Bi Misalin Yesu!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyalai Kirista, Ku Bi Misalin Yesu!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Maigida Zai Girmama Matarsa
  • Yadda Mace Za Ta Yi wa Mijinta Ladabi Sosai
  • Misalin Yesu ga Iyaye
  • Yara, Menene Zai Taimake Ku Ku Bi Misalin Yesu?
  • Abin da Zai Kawo Farin Ciki a Iyali
  • Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Magidanta Ku Yi Koyi Da Shugabancin Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/15 pp. 7-11

Iyalai Kirista, Ku Bi Misalin Yesu!

“Kristi [ya] bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.”—1 BIT. 2:21.

1. (a) Wane aiki ne Ɗan Allah ya yi a halitta? (b) Yaya Yesu yake ji game da ’yan adam?

SA’AD da Allah ya halicci sama da ƙasa, Ɗansa na fari yana tare da shi a matsayin “gwanin mai-aiki.” Ɗan Allah ya haɗa hannu da Ubansa Jehobah sa’ad da ya tsara ya kuma halicci dabbobi da shuke-shuke iri-iri a nan duniya da kuma sa’ad da ya kafa Aljanna da za ta zama gidan ’yan adam da aka halicce su cikin surar Jehobah. Ɗan Allah da ya zama Yesu, yana ƙaunar ’yan adam sosai. ‘Daularsa tana wurin yan adam.’—Mis. 8:27-31; Far. 1:26, 27.

2. (a) Menene Jehobah ya ba ’yan adam ajizai don ya taimake su? (b) A wace hanya ɗaya ta rayuwa ce Littafi Mai Tsarki ya yi tanadin ja-gora?

2 Bayan da ’yan adam na farko suka yi zunubi, ceton ’yan adam masu zunubi ya zama sashe na musamman a nufin Jehobah. Jehobah ya yi tanadin hadayar fansa na Kristi don ceto ya yiwu. (Rom. 5:8) Ƙari ga haka, Jehobah ya yi tanadin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, wadda take yi wa ’yan adam ja-gora a yadda za su jimre da ajizancin da suka gada. (Zab. 119:105) A cikin Kalmarsa, Jehobah ya yi tanadin ja-gora don ya taimaki mutane su samu iyalai masu ƙarfi da farin ciki. Littafin Farawa ya ce game da aure, namiji zai “manne ma matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.”—Far. 2:24.

3. (a) Menene Yesu ya koyar game da aure? (b) Menene za mu bincika a wannan talifin?

3 Sa’ad da yake hidima a duniya, Yesu ya nanata cewa ana son aure ya zama gami na dindindin. Ya koyar da ƙa’idodin da idan aka yi amfani da su za su taimaki waɗanda suke cikin iyali su guji halayen da za su yi wa aurensu ko kuma farin ciki iyalinsu barazana. (Mat. 5:27-37; 7:12) Wannan talifin zai tattauna yadda koyarwar Yesu da misalin da ya kafa sa’ad da yake duniya, za su iya taimaka wa magidanta, mata, iyaye, da yara su yi rayuwa ta farin ciki kuma mai gamsarwa.

Yadda Maigida Zai Girmama Matarsa

4. Wane kamanni yake tsakanin hakkin Yesu da na magidanta Kiristoci?

4 Allah ya naɗa maigida ya zama shugaban iyalinsa, kamar yadda Yesu ne Shugaban ikilisiyar. Manzo Bulus ya ce: “Miji kan mata yake, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne, shi da kansa fa mai-ceton jiki ne. Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afis. 5:23, 25) Hakika, yadda Yesu ya bi da mabiyansa misali ne ga yadda maza Kirista suke bukatar su bi da matansu. Bari mu bincika wasu hanyoyi da Yesu ya yi amfani da ikon da Allah ya ba shi.

5. Ta yaya Yesu ya yi amfani da ikonsa a kan almajiransa?

5 Yesu “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya.” (Mat. 11:29) Mutum ne mai aikata abu nan da nan. Kuma ya cika hakkinsa sosai. (Mar. 6:34; Yoh. 2:14-17) Yana ba almajiransa gargaɗi da ake bukata sau da yawa a kan batu ɗaya. (Mat. 20:21-28; Mar. 9:33-37; Luk 22:24-27) Duk da haka, Yesu bai tsauta musu ba ko kuma wulakanta su, kuma bai sa su tunanin ba ya ƙaunarsu ko kuma ba za su iya yin abin da yake koya musu ba. Maimakon haka, ya yaba wa almajiransa kuma ya ƙarfafa su. (Luk 10:17-21) Shi ya sa almajiran Yesu suka ba shi ladabi domin ya bi da su cikin ƙauna da juyayi!

6. (a) Menene miji zai koya daga yadda Yesu ya bi da almajiransa? (b) Wane gargaɗi ne Bitrus ya ba magidanta?

6 Misalin Yesu ya koya wa magidanta cewa shugabanci na Kirista ba matsayi ba ne na zalunci. Maimakon haka, ladabi ne da ƙauna ta sadaukar da kai. Manzo Bitrus ya ƙarfafa magidanta su yi koyi da hanyoyin da Yesu yake nuna ƙauna, ta wajen ‘zama’ da matansu, suna ‘ba su girma.’ (Karanta 1 Bitrus 3:7.) To, ta yaya miji zai yi amfani da ikonsa kuma har ila ya bi da matarsa a matsayin wadda ta cancanci a girmama ta?

7. A wace hanya ce miji zai girmama matarsa? Ka ba da misali.

7 Hanya ɗaya da miji zai girmama matarsa ita ce ta wajen yin la’akari da ra’ayinta da yadda take ji kafin ya tsai da shawarwari da za su shafi iyalin. Wataƙila za a tsai da shawara game da ƙaura zuwa wani wuri ko kuma canja aiki ko kuma game da al’amura na yau da kullum, kamar inda za a tafi hutu ko kuma yadda za a rage kuɗin da iyalin take kashewa sa’ad da abubuwa suka yi tsada. Tun da yake shawarar za ta shafi iyalin, yana da kyau maigida ya yi la’akari da ra’ayin matarsa, mai yiwuwa hakan zai taimake shi ya tsai da shawara mai kyau, kuma zai wa matar sauƙi ta tallafa masa. (Mis. 15:22) Magidanta da suke girmama matansu za su sa matansu su ƙaunace su kuma su ba su ladabi, mafi muhimmanci ma za su samu amincewar Jehobah.—Afis. 5:28, 29.

Yadda Mace Za Ta Yi wa Mijinta Ladabi Sosai

8. Me ya sa za a guji misalin Hauwa’u?

8 Yesu ya kafa wa mace Kirista misali mafi kyau na yin biyayya ga iko. Ra’ayinsa game da iko ya bambanta da halin da matar aure ta farko ta nuna! Hauwa’u ba misali mai kyau ba ce da mata za su bi. Tana da shugaba da Allah ya naɗa, wanda ta wurinsa Jehobah ya ba su umurni. Duk da haka, Hauwa’u ba ta nuna ladabi ga wannan tsarin ba. Ta ƙi bin umurnin da Adamu ya ba ta. (Far. 2:16, 17; 3:3; 1 Kor. 11:3) Hakika, an ruɗi Hauwa’u; duk da haka ya kamata ta tambayi mijinta ko ya dace ta bi maganar wanda ya yi da’awar gaya mata abin da “Allah ya sani.” Maimakon haka, ta ja-goranci mijinta.—Far. 3:5, 6; 1 Tim. 2:14.

9. Wane misali ne wajen miƙa kai Yesu ya kafa?

9 Akasin haka, Yesu ya kafa misali mafi kyau wajen miƙa kai ga shugabansa. Halinsa da tafarkin rayuwarsa sun nuna cewa bai “maida kasancewarsa daidai da Allah abin raini ba.” Maimakon haka, “ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa.” (Filib. 2:5-7) A yau, a matsayin Sarki da ke sarauta, Yesu ya ci gaba da nuna irin wannan halin. Yana miƙa kai ga Ubansa da tawali’u a dukan abubuwa kuma yana tallafa wa shugabancinsa.—Mat. 20:23; Yoh. 5:30; 1 Kor. 15:28.

10. Ta yaya mace za ta tallafa wa shugabancin mijinta?

10 Yana da kyau mace Kirista ta yi koyi da Yesu ta wajen tallafa wa shugabancin mijinta. (Karanta 1 Bitrus 2:21; 3:1, 2.) Ka yi la’akari da wani yanayin da za ta samu zarafin yin haka. Ɗansu ya nemi izini daga wajenta don ya yi wani abu da yake bukatar izinin iyayensa. Domin iyayen ba su tattauna batun dā ba, zai dace uwar ta tambaye shi, “Ka gaya wa babanka?” Idan yaron bai yi hakan ba, ya kamata ta tattauna batun da mijinta kafin a tsai da shawara. Ƙari ga haka, bai kamata mata Kirista ta ƙi ra’ayin mijinta ko kuma ta ƙalubalance shi a gaban yaransu ba. Idan ba ta yarda da wani abu da mijinta ya faɗa ba, za ta tattauna da shi sa’ad da suke su kaɗai.—Afis. 6:4.

Misalin Yesu ga Iyaye

11. Wane misali ne Yesu ya kafa wa iyaye?

11 Ko da yake Yesu bai yi aure ba kuma ba shi da yara, shi misali ne mafi kyau ga iyaye Kirista. Ta yaya? Ya koya wa almajiransa ta furcinsa da misali cikin ƙauna da haƙuri. Ya nuna musu yadda za su yi aikin da ya ba su. (Luk 8:1) Yadda Yesu ya bi da almajiransa da kuma halinsa ya koya musu yadda za su bi da juna.—Karanta Yohanna 13:14-17.

12, 13. Menene ake bukata idan iyaye za su yi renon yara masu tsoron Allah?

12 Yara suna bin misalin iyayensu ko mai kyau ne ko marar kyau. Saboda haka, iyaye ku tambayi kanku: ‘Menene muke koya wa yaranmu ta misalinmu sa’ad da ya zo ga yawan lokacin da muke kallon talabijin da kuma nishaɗi, da yawan lokaci da muke ba da wa ga nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma fita hidimar fage? Waɗanne abubuwa ne suke kan gaba a iyalinmu? Muna nuna misali mai kyau ta wajen mai da hankali da kuma tsai da shawara bisa bauta ta gaskiya?’ Dole ne dokar Allah ta fara kasancewa cikin zuciyar iyaye idan za su yi renon yara masu jin tsoron Allah.—K. Sha 6:6.

13 Idan iyaye suna ƙoƙari su yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a harkokinsu na kowace rana, yaransu za su lura da hakan. Yaran za su yi dukan abubuwa da iyayen suka gaya musu. Amma, idan yaran suka fahimci cewa iyayen ba sa bin mizanan da suka kafa musu, suna iya kammala cewa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba su da muhimmanci ko amfani. A sakamakon haka, yaran za su iya faɗa wa matsi na duniya.

14, 15. Waɗanne ƙa’idodi ne ya kamata iyaye su sa yaransu su yi sha’awarsu, kuma wace hanya ɗaya ce za su iya yin hakan?

14 Iyaye Kiristoci sun fahimci cewa renon yaro ya wuce biyan bukatarsa ta zahiri kawai. Saboda haka, ba shi da kyau idan aka koya wa yaro ya biɗi makasudai na zahiri kawai da yake gani zai amfane shi. (M. Wa. 7:12) Yesu ya koya wa almajiransa su fara biɗan Mulki da adalcinsa. (Mat. 6:33) Saboda haka, wajen yin koyi da Yesu, ya kamata iyaye Kiristoci su yi ƙoƙari su sa yaransu su yi sha’awar biɗan makasudai na ruhaniya.

15 Hanya ɗaya da iyaye za su iya yin hakan ita ce ta neman zarafin da yaransu za su yi tarayya da waɗanda suke hidima na cikakken lokaci. Ka yi tunanin irin ƙarfafawar da matasa za su samu idan suka san majagaba ko kuma mai kula da da’ira da matarsa. Masu wa’azi a ƙasashen waje da suka kawo ziyara, waɗanda suke hidima a Bethel, da masu yin aikin gine-gine a ƙasashe dabam dabam sukan yi magana game da farin cikinsu wajen bauta wa Jehobah. Babu shakka irin waɗannan baƙi suna da labarai masu kyau da za su ba da. Misalinsu na sadaukar da kai yana iya taimakon yaranku sosai su tsai da shawara mai kyau, su kafa makasudai na ruhaniya, kuma su je makarantar da ta dace don su tallafa wa kansu a hidima ta cikakken lokaci.

Yara, Menene Zai Taimake Ku Ku Bi Misalin Yesu?

16. Yaya Yesu ya girmama iyayensa na duniya da Ubansa na samaniya?

16 Yara, Yesu ya kafa muku misali mafi kyau. Yusufu da Maryamu ne suka yi renon Yesu, kuma ya yi musu biyayya. (Karanta Luka 2:51.) Ya fahimci cewa duk da ajizancinsu, Allah ne ya ba su hakkin kula da shi. Saboda haka, zai girmama su. (K. Sha 5:16; Mat. 15:4) A lokacin da ya girma, a kullum, Yesu yana yin abubuwan da suke faranta wa Ubansa na samaniya rai. Hakan yana nufin yin tsayayya da gwaji. (Mat. 4:1-10) A wani lokaci, ana iya gwada ku matasa ku yi rashin biyayya ga iyayenku. Saboda haka, menene zai taimake ku ku bi misalin Yesu?

17, 18. (a) Wane matsi ne matasa suke fuskanta a makaranta? (b) Tuna menene zai taimaki matasa su jimre gwaji?

17 Mai yiwuwa, yawancin abokan makarantarku ba sa daraja mizanai na Littafi Mai Tsarki. Suna iya matsa muku ku yi ayyukan da ba su da kyau kuma su yi maku ba’a idan kuka ƙi. Abokan makarantarku sun taɓa ba ku suna domin kun ƙi yin wasu ayyuka tare da su? Idan haka ne, me kuka yi? Kun san cewa idan kuka ji kunya kuma kuka bi su za ku sa iyayenku da Jehobah baƙin ciki. Menene zai faru idan kuka bi abokan makarantarku? Wataƙila ka kafa wa kanka wasu makasudai, kamar zama majagaba ko bawa mai hidima, yin hidima a yankin da ake bukatar masu shelar Mulki sosai, ko kuma zama wanda yake hidima a Bethel. Yin tarayya da abokan makarantarku zai taimake ku ku cim ma makasudanku?

18 Matasa da ke cikin ikilisiyar Kirista, kun taɓa samun kanku cikin yanayin da aka gwada bangaskiyarku? Menene kuka yi? Ku yi tunanin Yesu, wanda kuke bin misalinsa. Ya ƙi faɗa wa gwaji kuma ya yi tsayin daka don abin da ya san daidai ne. Tuna wannan zai ƙarfafa ku ku gaya wa abokan makarantarku sarai cewa ba ku son ku bi su ku yi abin da kuka san ba shi da kyau. Kamar Yesu, ku mai da hankali ga begen yin rayuwa na yin hidima na farin ciki da yin biyayya ga Jehobah.—Ibran. 12:2.

Abin da Zai Kawo Farin Ciki a Iyali

19. Wane tafarki ne a rayuwa zai kawo farin ciki na gaske?

19 Jehobah Allah da Yesu Kristi suna son abu mafi kyau ga ’yan adam. Ko a yanayinmu na ajizanci, zai yiwu mu more farin ciki daidai gwargwado. (Isha. 48:17, 18; Mat. 5:3) Yesu ya koyar da gaskiya na addini da zai sa ’yan adam farin ciki, amma ba wannan kaɗai ya koya wa almajiransa ba. Yesu ya kuma koyar da hanyar rayuwa mafi kyau. Ƙari ga haka, ya kafa misali mai kyau na yin rayuwa da aka tsara da kyau da kuma ra’ayin da ya dace. Dukanmu, ko menene matsayinmu a iyali, za mu iya amfana ta wajen bin misalinsa. Saboda haka, magidanta, mata, iyaye da yara ku bi misalin Yesu! Bin  koyarwar Yesu da yin koyi da misalinsa abubuwa ne da za su sa mu more rayuwar iyali mai gamsarwa da kuma na farin ciki.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya ya kamata magidanta su yi amfani da ikon da Allah ya ba su?

• Ta yaya mace za ta yi koyi da misalin Yesu?

• Menene iyaye za su iya koya daga yadda Yesu ya bi da almajiransa?

• Menene matasa za su iya koya daga misalin Yesu?

[Hotunan da ke shafi na 8]

Kafin ya tsai da shawara da za ta shafi iyalinsa, menene miji mai ƙauna zai yi?

[Hotunan da ke shafi na 9]

Wane yanayi ne zai ba mata zarafin tallafa wa shugabancin mijinta?

[Hotunan da ke shafi na 10]

Yara suna yin koyi da halin iyayensu masu kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba