Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 8/15 pp. 30-32
  • An Kwatanta Masu Wa’azi A Ƙasashen Waje Da Fari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Kwatanta Masu Wa’azi A Ƙasashen Waje Da Fari
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 8/15 pp. 30-32

Bikin Sauke Karatu Na Gilead Aji Na 124

An Kwatanta Masu Wa’azi A Ƙasashen Waje Da Fari

KOWANE watanni shida, Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead tana yin bikin sauke karatu da ake gayyatar dukan iyalin Bethel na Amirka. A ranar 8 ga Maris, 2008, baƙi daga fiye da ƙasashe 30 sun haɗu da iyalin Bethel don bikin sauke karatu na aji na 124 na Makarantar Gilead. Duka mutane 6,411 da suka halarta sun taya ɗaliban murna a ranarsu ta musamman.

Mai kujera na tsarin ayyukan, Stephen Lett da ke cikin Hukumar Mulki ya soma tsarin ayyukan da jawabi mai jigo “Ku Tafi da Fari ta Alama na Jehobah.” Ru’ya ta Yohanna 9:1-4 ta kwatanta ƙaramin rukuni na shafaffu Kiristoci da suka farfaɗo daga rashin aiki na ruhaniya a shekara ta 1919 zuwa rundunar fari da suka soma aiki nan da nan. An tuna wa ɗaliban cewa da yake suna cikin “waɗansu tumaki,” sun haɗa kansu tare da wannan rundunar fari na alama.—Yohanna 10:16.

Lon Schilling, wanda yake cikin Kwamitin Reshe na Amirka ya ba da jawabi mai jigo “Ku Zama Masu Taimakon Juna.” Jawabin bisa misalin Littafi Mai Tsarki ne na Akila da Biriskilla, ma’aurata na Kirista a ƙarni na farko. (Rom. 16:3, 4) Ma’aurata 28 ne suke cikin ajin Gilead. An tuna musu cewa idan za su yi nasara a aikinsu na masu wa’azi a ƙasashen waje, suna bukatar su ƙarfafa aurensu. Littafi Mai Tsarki ba ya maganar Akila ba tare da ya ambata matarsa, Biriskilla ba. Saboda haka, manzo Bulus da ikilisiyar sun ɗauke su masu haɗin kai. Hakazalika, ya kamata ma’aurata a yau masu wa’azi a ƙasar waje su zama masu haɗin kai, su yi bauta tare, kuma su bi da kalubalen hidima na ƙasar waje tare, ta yin hakan suna taimakon juna.—Far. 2:18.

Guy Pierce, da yake cikin Hukumar Mulki ya ba da jawabi na gaba, mai jigo “Ka Amince da Nagartar Jehobah.” Ɗan’uwa Pierce ya ba da bayani cewa zama nagari ya ƙunshi fiye da ƙin yin abin da ba shi da kyau. Mutum nagari yana yin abu mai kyau don ya amfani wasu. Jehobah Allah nagari ne da babu kamarsa. (Zech. 9:16, 17) Nagartar Allah zai iya motsa mu mu yi wa mutane abubuwa masu kyau. Da yake yaba wa ɗaliban, Ɗan’uwa Pierce ya kammala da cewa: “Kuna aiki mai kyau. Mun tabbata cewa za ku ci gaba da bin nagartar Allah ta wajen yin abu mai kyau a duk wani aiki da Jehobah Allah ya ba ku a nan gaba.”

Sai Michael Burnett, mai wa’azi na ƙasan waje a dā da ba da daɗewa ba ya zama mai jawabi a makarantar Gilead, ya ba da jawabi mai jigo “Ku Saka shi a Matsayin Tālilai a Tsakanin Idanunka.” Kamar suna yafe da “talilai” a tsakanin idanunsu, Isra’ilawa za su tuna mu’ujizar da Jehobah ya yi a Masar don ya cece su. (Fit. 13:16) An gargaɗi ɗaliban su riƙa tuna koyarwa da aka yi musu a Makarantar Gilead kamar suna yafe da shi a matsayin talilai a tsakanin idanunsu. Ɗan’uwa Burnett ya nanata cewa suna bukatar su kasance masu tawali’u da kuma filako kuma su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke sasanta matsala tsakanin ’yan’uwansu masu wa’azin a ƙasar waje da kuma wasu.—Mat. 5:23, 24.

Mark Noumair, da ya daɗe yana koyarwa a makarantar Gilead, ya ba da jawabi “Wace Waƙa Za a Rera Game da Ku?” A zamanin dā, ana rera waƙa idan aka ci nasara a yaƙi. Wata waƙa da aka yi ta fallasa ƙabilun Reuben, Dan, and Asher masu son jiki, amma an yabi ƙabilar Zebulun don halinsu na sadaukar da kai. (Alƙa. 5:16-18) Kamar kalmomin waƙar, ayyukan kowanne Kirista ya zama sananne ga mutane. Mutum zai faranta wa Jehobah rai don ƙwazonsa a aikin Allah da kuma aminci ga tsarinsa kuma zai kasance misali mai kyau ga ’yan’uwansa. Idan wasu a cikin ikilisiya suka ga ƙoƙarinmu hakan zai motsa su su yi koyi da misalinmu mai kyau.

Sa’ad da Ɗaliban makarantar Gilead na aji na 124 suke makaranta, sun yi awoyi 3,000 a aikin wa’azi. A jigon nan “Ku bi Shugabancin Ruhu Mai Tsarki,” ɗaliban sun nanata wa Sam Roberson da ke sashe na makaranta na Allah, abubuwan da suka fuskanta a hidimarsu, sun kuma sake nuna yadda abin ya faru. Waɗannan labarai masu ƙarfafawa sun biyo bayan ganawa, wanda Patrick LaFranca da ke kwamitin reshe na Amirka da wasu da suka sauke karatu a makarantar Gilead da suke hidima a ƙasashe dabam dabam ne suka ɗauki nauyin wannan. Ɗaliban sun yi farin cikin shawarar da waɗannan ’yan’uwa suka ba su.

Anthony Morris da ke cikin Hukumar Mulki ya ba da jawabi na ƙarshe “Ku Tuna, Abubuwan da Kuke Gani Masu Wucewa Ne.” Nassosi sun gargaɗe mu mu dogara ga albarkatun Jehobah maimakon wani ƙunci mai wucewa da wataƙila muke yanzu. (2 Kor. 4:16-18) Talauci, rashin gaskiya, zalunci, cuta, da kuma mutuwa za su iya safe mu a yau. Masu-wa’azi na ƙasashen waje za su iya fuskantar irin waɗannan mugun yanayin. Amma idan muka tuna cewa waɗannan abubuwan masu wucewa ne za su taimake mu mu riƙe ruhaniyarmu da begenmu.

An ƙarshen wannan tsarin ayyuka ɗaliban suna kan dakalin magana suna saurarar Ɗan’uwa Lett yana jawabinsa na ƙarshe. Ya ƙarfafa su ka da su kasala kuma ya ce: “Ko wane irin jaraba muke fuskanta, za mu iya jimrewa kuma mu riƙe amincinmu idan Jehobah yana taimakon mu.” Ya aririce sababbin masu-wa’azi na ƙasashen waje su zama kamar fari, su ci gaba a hidimar Jehobah kuma su ci gaba da ƙwazo, da aminci da kuma biyayya har abada.

[Akwati a shafi na 30]

BAYANAI GAME DA ƊALIBAN

Adadin ƙasashen da suka wakilta: 7

Adadin ƙasashen da aka aika su: 16

Adadin ɗalibai: 56

Avirejin shekarunsu: 33.8

Avirejin shekarunsu a cikin gaskiya: 18.2

Avirejin shekarunsu a cikin hidima na cikakken lokaci: 13.8

[Hoto a shafi na 31]

Aji na 124 na Waɗanda Suka Sauke Karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead

A jerin da ke ƙasa, ana soma ƙirgawa ne daga gaba zuwa baya, kuma an jera sunayen ne daga hagu zuwa dama a kowane layi.

(1) Nicholson, T.; Main, H.; Senge, Y.; Snape, L.; Vanegas, C.; Pou, L. (2) Santana, S.; Oh, K.; Lemaitre, C.; Williams, N.; Alexander, L. (3) Woods, B.; Stainton, L.; Huntley, E.; Alvarez, G.; Cruz, J.; Bennett, J. (4) Williamson, A.; González, N.; Zuroski, J.; Degandt, I.; May, J.; Diemmi, C.; Tavener, L. (5) Lemaitre, W.; Harris, A.; Wells, C.; Rodgers, S.; Durrant, M.; Senge, J. (6) Huntley, T.; Vanegas, A.; Pou, A.; Santana, M.; Bennett, V.; Tavener, D.; Oh, M. (7) Zuroski, M.; Rodgers, G.; Diemmi, D.; Nicholson, L.; Alvarez, C.; Snape, J. (8) Harris, M.; González, P.; Main, S.; Woods, S.; Stainton, B.; Williamson, D.; Durrant, J. (9) Cruz, P.; Degandt, B.; Williams, D.; Wells, S.; Alexander, D.; May, M.

[Hoto a shafi na 32]

Makarantar Gilead tana nan a Cibiyar Koyarwa ta Watchtower

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba