Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Idan Adamu Kamilittacen Mutum ne, Me Ya Sa Ya Yi Zunubi?
Adamu yana iya yin zunubi domin Allah ya halicce shi da ’yancin yin zaɓe. Wannan kyautar bata nufin cewa Adamu ba kamili ba ne. Hakika, Allah ne kaɗai kamili cikakke . (Kubawar Shari’a 32:3, 4; Zabura 18:30; Markus 10:18) Babu mutum ko wani abu da ya kamilta baki ɗaya ba. Alal Misali, ana iya yin amfani da wuƙa a yanka nama, amma za ka yi amfani da ita ka sha miya ne? Abu na da cikkaken amfani idan ya cika nufin da ya sa aka ƙera shi.
To, me ya sa Allah ya halicci Adamu? Nufin Allah ne zuriyar yan adam ta kasance da masu basira kuma masu ’yancin yin Zaɓe. Waɗanda suke so su nuna ƙaunarsu ga Allah da kuma hanyoyinsa za su nuna hakan ta wajen yin biyayya ga dokokinsa. Ba a halicci ’yan adam su yi biyayya na dole ba, amma za su yi hakan da son rai. (Kubawar Shari’a 10:12, 13; 30:19, 20) Saboda haka, inda Adamu bai da ’yancin ya zaɓi ko zai yi rashin biyayya, da bai zama cikkake ba, wato da ya zama ajizi mai ’yancin zaɓe. Game da yadda Adamu ya zaɓa ya yi amfani da ’yancin zaɓensa, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya bi matarsa wajen yin rashin biyayya ga dokar Allah game da “itace na sanin nagarta da mugunta.”—Farawa 2:17; 3:1-6.
Amma, Allah ya halicci Adamu ne da wani kumamanci na ɗabi’a da ya sa ya ƙasa yanke shawarwari masu kyau ko ya tsayayya wa jaraba? Kafin rashin biyayya na Adamu, Jehobah Allah ya dubi dukan halittunsa, har da mata da miji na farko, kuma ya tabbata cewa suna “da kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Saboda haka, sa’ad da Adamu ya yi zunubi, Mahaliccinsa bai bukaci ya daidaita wani kuskure a yadda ya halicce sa ba, amma ya ɗaura masa laifi. (Farawa 3:17-19) Adamu ya kasa barin ƙaunar Allah da ta mizanai masu kyau su motsa shi ya yi biyayya ga Allah fiye da kome.
Ka tuna cewa sa’ad da Yesu yake duniya shi ma kamili ne kamar Adamu. Amma Yesu ya bambanta da sauran zuriyar Adamu saboda an yi cikinsa ta ruhu mai tsarki ne kuma bai gaji wani kumammanci da zai sa ya kasa tsayayya wa jaraba ba. (Luka 1:30, 31; 2:21; 3:23, 38) Yesu da son ransa ya kasance da aminci ga ubansa duk da matsi mafi wuya da ya sha. Ta wajen yin amfani da ’yancinsa na zaɓe Adamu yana da hakki na rashin yin biyayya ga dokar Jehobah.
Amma, me ya sa Adamu ya zaɓi ya yi wa Allah rashin biyayya? Yana gani zai kyautata yanayinsa ne? A’a, gama manzo Bulus ya rubuta cewa “ba Adamu aka ruɗe ba.” (1 Timothawus 2:14) Amma, Adamu ya yanke shawarar bin matarsa, wadda ta rigaya ta zaɓi ta ci ’ya’yan itace da aka haramta. Muradinsa na sa ta farin ciki ya fi muradinsa na yi wa Mahaliccinsa biyayya. Hakika, sa’ad da aka ba shi ’ya’yan itacen da aka haramta, da Adamu ya dakata ya yi tunani a kan sakamakon da rashin biyayya zai jawo wa dangantakarsa da Allah. Idan ba shi da ƙauna mai zurfi ga Allah, Adamu yana iya faɗa wa matsi, har da matsi daga matarsa.
Adamu ya yi zunubi kafin ya haifi ’ya’ya, saboda haka, an haifi dukan ’ya’yansa cikin ajizanci. Amma, kamar Adamu, dukan mu muna da ’yancin zaɓe. Bari mu zaɓi mu yi bimbini muna godiya don alherin Jehobah kuma mu gina ƙauna mai zurfi ga Allah, wanda ya cancanci mu yi masa biyayya kuma mu bauta masa. —Zabura 63:6; Matta 22:36, 37.