Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/15 pp. 23-27
  • An Kawar da Mutuwa, Maƙiya ta Ƙarshe

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Kawar da Mutuwa, Maƙiya ta Ƙarshe
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • GARGAƊI MAI KYAU
  • YADDA MUTANE SUKA SOMA MUTUWA
  • AN KAWAR DA ZUNUBI DA KUMA MUTUWA
  • Mutuwar Yesu da Kuma Tashinsa Daga Mutuwa​—⁠Yadda Za Su Iya Amfanar Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Mutane Suke Tsufa da Mutuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Idan Adamu Kamilittacen Mutum ne, Me Ya Sa Ya Yi Zunubi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/15 pp. 23-27

An Kawar da Mutuwa, Maƙiya ta Ƙarshe

“Maƙiyi na ƙarshe da za a kawar, mutuwa ne.”—1 KOR. 15:26.

MECE CE AMSARKA?

  • Wace muhimmiyar doka ce Jehobah ya ba Adamu?

  • Ta yaya ’yan Adam suka soma mutuwa?

  • Yaushe ne za a kawar da ‘maƙiya ta ƙarshe,’ wato mutuwa?

1, 2. Wane yanayi ne Adamu da Hawwa’u suka shaida da farko, kuma waɗanne tambayoyi ne hakan ya jawo?

SA’AD DA aka halicci Adamu da Hawwa’u, ba su da maƙiya. Su kamilai ne kuma suna zama a cikin aljanna. Suna da dangantaka ta kud da kud da mahaliccinsu kuma suna kamar ’ya’ya ne a wajensa. (Far. 2:7-9; Luk 3:38) Umurnin da Allah ya ba su ya nuna irin rayuwar da za su yi. (Karanta Farawa 1:28.) Zai daɗe kafin ‘su riɓu, su mamaye duniya.’ Amma idan Adamu da Hawwa’u suna so su ci gaba da mallakar ‘kowane abu mai-rai,’ wajibi ne su yi rayuwa har abada.

2 Me ya sa rayuwa ta canja haka a yau? Me ya sa abubuwa da yawa suke hana ’yan Adam farin ciki, musamman ma maƙiyar nan mutuwa? Mene ne Allah zai yi don ya halaka waɗannan maƙiyan? Yayin da muke tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da hakan, za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin da kuma wasu a ciki.

GARGAƊI MAI KYAU

3, 4. (a) Wace doka ce Allah ya ba wa Adamu da Hawwa’u? (b) Mene ne muhimmancin bin wannan dokar?

3 Ko da yake Adamu da Hawwa’u za su iya rayuwa har abada, wajibi ne su yi wasu abubuwa don su ci gaba da rayuwa. Alal misali, suna bukatar sheƙar iska, yin barci da kuma ci da sha. Mafi muhimmanci ma, suna bukatar su ƙulla dangantaka da Allah domin shi ya ba su rai. (K. Sha 8:3) Idan sun bi ja-gorar Allah, za su ji daɗi kuma za su ci gaba da rayuwa. Jehobah ya bayyana wa Adamu hakan tun kafin ya halicci Hawwa’u. Ta yaya ya yi hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji Allah kuma ya dokaci mutumin, yana cewa, An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.”—Far. 2:16, 17.

4 “Itace na sanin nagarta da mugunta” yana wakiltar ikon da Allah yake da shi na gaya wa mutane abin da ke nagarta da mugunta. Babu shakka, Adamu ya san abin da ya dace da abin da bai dace ba domin Allah ya halicce shi cikin kamaninsa kuma yana da lamiri. Itacen zai riƙa tuna wa Adamu da Hawwa’u cewa suna bukatar ja-gorar Jehobah a koyaushe. Idan sun ci ’ya’yan itacen, hakan zai nuna cewa suna neman ’yancin kansu, kuma zai jawo musu da kuma ’ya’yansu matsaloli sosai. Dokar da Allah ya bayar da kuma hukuncin ya nuna cewa cin ’ya’yan itacen yana tattare da mugun sakamako.

YADDA MUTANE SUKA SOMA MUTUWA

5. Ta yaya aka yaudari Adamu da Hawwa’u su yi rashin biyayya?

5 Bayan Allah ya halicci Hawwa’u, Adamu ya gaya mata dokar da Allah ya bayar. Ta san dokar sosai, domin ta kusan maimaita dokar kalma bayan kalma. (Far. 3:1-3) Ta yi hakan a lokacin da take magana da wani halitta da ya yi amfani da maciji. Wannan halittan shi ne Shaiɗan Iblis, ya bar son iko da neman ’yancin kai su sha kansa. (Gwada Yaƙub 1:14, 15.) Don ya cim ma wannan mugun burin, ya ce Allah maƙaryaci ne kuma ya gaya wa Hawwa’u cewa idan ta sami ’yancin kai, ba za ta mutu ba, amma za ta zama kamar Allah. (Far. 3:4, 5) Hawwa’u ta saurare shi kuma ta nemi ’yancin kai ta wajen cin ’ya’yan itacen, ta kuma rinjayi Adamu shi ma ya ci. (Far. 3:6, 17) Ƙarya ce Iblis ya yi. (Karanta 1 Timotawus 2:14.) Duk da haka, Adamu ya saurari ‘muryar matarsa.’ Ko da yake, macijin ya yi kamar yana ƙaunarsu, amma Iblis ne ainihin wanda yake maganar. Shi wani maƙiyi marar tausayi ne kuma ya san cewa shawarar da ya ba Hawwa’u zai haifar da mugun sakamako.

6, 7. Ta yaya Jehobah ya bi da Adamu da Hawwa’u sa’ad da yake yanke musu hukunci?

6 Adamu da Hawwa’u sun bi ra’ayinsu kuma sun yi watsi da Wanda ya ba su rai da sauran abubuwan da suka mallaka. Jehobah ya san dukan abin da ya faru. (1 Laba. 28:9; karanta Misalai 15:3.) Ya ba waɗannan halittunsa uku dama su bayyana ra’ayinsu game da shi. Da yake Jehobah yana kamar Uba a gare su, abin da suka yi ya ɓata masa rai sosai. (Gwada Farawa 6:6.) Amma ya mai da kansa Alƙali, ya gudanar da shari’a kuma ya yanke hukunci bisa ga dokar da ya ba su.

7 Allah ya riga ya ba da wannan umurnin ga Adamu: ‘A ranar da ka ci [itace na sanin nagarta da mugunta] za ka mutu lalle.’ Wataƙila Adamu ya fahimci cewa wannan ranar mai tsawon sa’o’i 24 ne. Bayan ya ƙi bin umurnin Allah, mai yiwuwa ya ɗauka cewa Jehobah zai ɗauki mataki kafin yamma ta yi. Jehobah ya zo wajen waɗannan ma’auratan “da sanyin yamma.” (Far. 3:8) A matsayin alƙali, ya ba Adamu da Hawwa’u dama su furta ra’ayinsu kuma bisa ga amsar da suka bayar, ya fahimci gaskiyar lamarin. (Far. 3:9-13) Ya yanke musu hukunci. (Far. 3:14-19) Da a ce ya hallakar da Adamu da Hawwa’u nan da nan, da nufinsa game da su da kuma ’ya’yansu ba zai cika ba. (Isha. 55:11) Ko da yake ya riga ya zartar da hukuncin mutuwa kuma sakamakon zunubi ya soma bayyana nan take, ya bar Adamu da Hawwa’u su haifi ’ya’yan da za su iya amfana daga wasu tanadodi da Zai yi. Saboda haka, daga ranar da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi, sun zama matattu a gaban Allah. Ƙari ga haka, da yake shekara 1,000 rana ɗaya ce a gaban Jehobah, sun mutu a ‘ranar.’—2 Bit. 3:8.

8, 9. Ta yaya zunubin da Adamu ya yi ya shafi ’ya’yansa? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

8 Shin abin da Adamu da Hawwa’u suka yi zai shafi yaransu ne? Hakika. Littafin Romawa 5:12 ta ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” Habila ne mutumi na farko da ya soma mutuwa. (Far. 4:8) Bayan haka, wasu ’ya’yan Adamu sun tsufa kuma suka mutu. Shin su ma sun gāji zunubi da kuma mutuwa ne? Manzo Bulus ya ba da amsar cewa ‘ta wurin kangarar [mutum] ɗaya masu-yawa suka zama masu zunubi.’ (Rom. 5:19) Ta hakan ne zunubi da mutuwa da muka gāda daga Adamu suka zama maƙiyan da ’yan Adam ba za su iya guje musu ba. Ko da yake ba za mu iya fahimtar yadda ’ya’yan Adamu suka gāji zunubi daga wajen Adamu ba, amma muna ganin sakamakon hakan.

9 Ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta zunubi da kuma mutuwa da muka gāda kamar “labule, wanda ya rufe dukan dangogi, da luluɓi wanda an shimfiɗa a kan dukan al’ummai.” (Isha. 25:7) Wannan labulen ko kuma lulluɓin ya mamaye dukan ’yan Adam kamar tarko. Sakamakon hakan shi ne “cikin Adamu duka suna mutuwa.” (1 Kor. 15:22) Tambayar da mutum zai iya yi ita ce irin wanda Bulus ya yi cewa: ‘Wane ne zai tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa?’ Akwai wani kuwa da zai iya yin hakan?a—Rom. 7:24.

AN KAWAR DA ZUNUBI DA KUMA MUTUWA

10. (a) Waɗanne ayoyin Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa Jehobah zai kawo ƙarshen mutuwa? (b) Mene ne waɗannan ayoyin suka nuna game da Jehobah da kuma Ɗansa?

10 Hakika, Jehobah zai iya ceton Bulus. Bayan da Ishaya ya ambaci “labule,” ya ce: “Ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” (Isha. 25:8) Kamar yadda uba yake cire duk wani abin da zai sa yaransa su sha wahala kuma ya share musu hawaye, Jehobah yana marmarin kawo ƙarshen mutuwa! Ƙari ga haka, akwai wanda yake ba wa Allah haɗin kai a wannan batun. Littafin 1 Korintiyawa 15:22 ta ce: “Kamar yadda cikin Adamu duka suna mutuwa, haka nan cikin Kristi duka za su rayu.” Hakazalika, bayan da Bulus ya yi wannan tambayar ‘Wane ne zai tsamo ni?’ Sai ya ƙara da cewa: “Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Rom. 7:25) Babu shakka, tawayen da Adamu da Hawwa’u suka yi bai sa Allah ya daina ƙaunar ’yan Adam ba. Ƙari ga haka, wanda ya yi aiki da Jehobah wajen halittar ma’aurata na farko bai daina ƙaunar ’yan Adam ba. (Mis. 8:30, 31) Amma ta yaya za a ceci ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa?

11. Wane tanadi ne Jehobah ya yi don ya taimaka wa ’yan Adam?

11 Sa’ad da Adamu ya yi zunubi, Jehobah ya yanke musu hukuncin kisa. A sakamakon haka, dukan ’yan Adam sun gāji zunubi da kuma mutuwa. (Rom. 5:12, 16) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci.” (Rom. 5:18, Littafi Mai Tsarki) Mene ne Jehobah zai yi don ya kawar da wannan hukuncin ba tare da ƙetare ƙa’idodinsa ba? Furucin da Yesu ya yi ya ba da amsar: “Ɗan mutum ya zo . . . shi ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Wanda Jehobah ya fara halitta, wato Yesu da aka haife shi kamili a nan duniya ne ya ba da fansa. Ta yaya wannan fansar za ta daidaita al’amarin?—1 Tim. 2:5, 6.

12. Wace fansa ce ta yi daidai da abin da Adamu ya ɓatar?

12 Da yake Yesu kamiltaccen mutum ne, yana da irin begen da Adamu yake da shi kafin ya yi zunubi. Nufin Jehobah shi ne Adamu ya haifi ’ya’ya kamiltattu da za su mamaye duniya. Da yake Yesu yana ƙaunar Ubansa da kuma ’yan Adam, ya ba da ransa abin fansa. Hakika, Yesu ya ba da kamiltaccen ransa da ya yi daidai da abin da Adamu ya ɓatar. Bayan haka, Jehobah ya tayar da Ɗansa zuwa sama a matsayin ruhu. (1 Bit. 3:18) Jehobah ya amince da hadayar da wannan kamiltaccen mutum, wato Yesu ya yi. Hadayar ta fanshi ’yan Adam kuma sun sake kasancewa da begen yin rayuwa har abada. A taƙaice, Yesu ya ɗauki matsayin Adamu. Bulus ya bayyana cewa: “Haka kuma an rubuta, mutum na fari Adamu ya zama rayayyen rai. Adamu na ƙarshe ya zama ruhu mai-rayarwa.”—1 Kor. 15:45.

13. Ta yaya “Adamu na ƙarshe” zai taimaka wa waɗanda suka mutu?

13 Lokaci yana zuwa da “Adamu na ƙarshe” zai zama “ruhu mai-rayarwa” ga ’yan Adam gaba ɗaya. Za a ta da yawancin ’yan Adam daga mutuwa. Me ya sa? Don sun riga sun mutu. Saboda haka, suna bukatar a sake ta da su daga matattu domin su yi rayuwa a duniya.—Yoh. 5:28, 29.

14. Mene ne Jehobah zai yi amfani da shi wajen kawo ƙarshen ajizanci da ’yan Adam suka gāda?

14 Ta yaya ’yan Adam za su sami ’yanci daga ajizanci? Jehobah ya kafa Mulkin da ya ƙunshi “Adamu na ƙarshe” da abokan sarautarsa da aka zaɓa daga cikin ’yan Adam. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.) Waɗannan da za su kasance tare da Yesu a sama kuma za su zama kamiltattu. Sarautar da za su yi na shekara dubu ɗaya zai taimaka wa waɗanda suke duniya, kuma zai sa su sami ’yanci daga ajizanci da ya zama musu kamar ƙashi a wuya.—R. Yoh. 20:6.

15, 16. (a) Mece ce ‘maƙiya ta ƙarshe,’ wato mutuwa, kuma a yaushe ne za a kawar da ita? (b) Bisa ga 1 Korintiyawa 15:28, mene ne Yesu zai yi da shigewar lokaci?

15 A ƙarshen sarautar Yesu na shekara dubu ɗaya, mutane masu biyayya za su sami ’yanci daga dukan maƙiyan da Adamu ya jawo saboda rashin biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kamar yadda cikin Adamu duka suna mutuwa, haka nan cikin Kristi duka za su rayu. Amma kowane cikin jeruwarsa: Kristi ’ya’yan fari; kāna su da ke na Kristi, [abokan sarautarsa] cikin zuwansa. Bayan wannan sai matuƙa, sa’anda zai ba da mulki ga Allah, Uba; sa’anda ya rigaya ya kawar da dukan hukunci, da dukan sarauta, da dukan iko. Gama shi dole za ya yi mulki, har ya sa dukan maƙiyansa ƙarƙashin sawayensa. Maƙiyi na ƙarshe da za a kawar, mutuwa ne.’ (1 Kor. 15:22-26) Hakika, za a kawar da wannan “labule,” wato mutuwa da muka gāda daga Adamu kuma ba za ta sake addabar ’yan Adam ba.—Isha. 25:7, 8.

16 Manzo Bulus ya kammala hurarren bayaninsa da waɗannan kalaman: “Sa’ad da an gama an sarayar da dukan kome ƙarƙashin mulkinsa, sa’an nan shi Ɗan da kansa kuma za ya sarayu ga wannan wanda ya sarayar da dukan kome a ƙarƙashin mulkinsa, domin Allah ya zama duka cikin duka.” (1 Kor. 15:28) A lokacin, sarautar Yesu ta riga ta cim ma abubuwan da ya sa aka kafa ta. Sa’an nan cikin gamsuwa, zai mayar da sarautar da kuma kamiltattun mutane ga Jehobah.

17. Wane hukunci ne za a yi wa Shaiɗan a ƙarshe?

17 Me zai faru da Shaiɗan da ya jawo wa ’yan Adam wahala da suke fama da ita? Ru’ya ta Yohanna 20:7-15 sun ba da amsar. A lokacin gwaji na ƙarshe, za a saki Shaiɗan don ya gwada mutane. Bayan haka, za a halaka shi da dukan waɗanda suka goyi bayansa kuma ba za su sake rayuwa ba. Wannan ita ce “mutuwa ta biyu.” (R. Yoh. 21:8) Ba za a kawar da wannan mutuwar ba domin mutanen da ta addaba ba za su sake rayuwa ba. Saboda haka, “mutuwa ta biyu” ba maƙiyar mutanen da suke ƙaunar Mahaliccinsu kuma suna bauta masa ba.

18. Ta yaya za a cika wannan umurnin da Allah ya ba wa Adamu?

18 A lokacin, mutane za su kasance kamiltattu kuma Jehobah zai ba su rai na har abada. Ƙari ga haka, ba za su sake kasancewa da maƙiya ba. Za a cika umurnin da aka ba Adamu duk da cewa ba zai kasance a wurin ba. Duniya za ta cika da ’ya’yansa kuma za su ji daɗin kula da duniya da kuma dabbobi. Bari mu ci gaba da nuna godiya ga tanadin da Jehobah ya yi cikin ƙauna don ya kawar da maƙiya ta ƙarshe, wato mutuwa!

a Littafin nan Insight on the Scriptures ya yi bayani a kan ƙoƙarin da ’yan kimiyya suka yi don su gano dalilin da ya sa ake tsufa da kuma mutuwa, ya ce: “Sun manta cewa Mahalicci ne da kansa ya zartar wa iyayenmu na farko hukuncin mutuwa. Ƙari ga haka, Allah ya yi hakan a hanyar da mutane ba za su iya fahimtar lamarin gaba ɗaya ba.”—Littafi na 2, shafi na 247.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba