Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp19 Na 3 pp. 8-9
  • Me Ya Sa Mutane Suke Tsufa da Mutuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Mutane Suke Tsufa da Mutuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA YA SA ADAMU DA HAUWA’U SUKA MUTU
  • ABIN DA YA SA MUKA ZAMA AJIZAI
  • Mutuwar Yesu da Kuma Tashinsa Daga Mutuwa​—⁠Yadda Za Su Iya Amfanar Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • An Kawar da Mutuwa, Maƙiya ta Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
wp19 Na 3 pp. 8-9
Adamu ya ci ’ya’yan itacen da aka hana shi ci; Adamu a lokacin da ya tsufa; mutane suna tsaye a kabarin Adamu

Me Ya Sa Mutane Suke Tsufa Da Mutuwa?

BA NUFIN Allah ba ne cewa ’yan Adam su riƙa mutuwa. Allah ya halicci iyayenmu na farko, wato, Adamu da Hauwa’u da jiki marar aibi, saboda haka, da sun so da suna raye har wa yau. Dokar da Allah ya ba wa Adamu game da wani itace a lambun Adnin ya nuna sarai cewa Allah ya ba su damar yin rayuwa har abada.

Allah ya gaya wa Adamu cewa: “A ranar da ka ci daga itacen nan lallai za ka mutu.” (Farawa 2:17) Da a ce tun asali, an halicci Adamu don ya tsufa kuma ya mutu ne, da Allah bai ba shi wannan dokar ba. Adamu ya san cewa idan bai ci ’ya’yan itacen nan ba, ba zai mutu ba.

BA NUFIN ALLAH BA NE ’YAN ADAM SU RIƘA MUTUWA

Ba rashin abinci ne ya sa Adamu da Hauwa’u suka ci ’ya’yan itacen ba, domin akwai itatuwa da yawa da suke ba da ’ya’ya a lambun. (Farawa 2:9) Da a ce ba su ci ’ya’yan itacen da Allah ya hana su ci ba, da sun nuna biyayyarsu ga Wanda ya ba su rai. Kuma da hakan ya nuna sun yarda cewa Allah ne ya kamata ya riƙa gaya musu abin da za su yi.

ABIN DA YA SA ADAMU DA HAUWA’U SUKA MUTU

Kafin mu fahimci abin da ya kai ga mutuwar Adamu da Hauwa’u, wajibi ne mu bincika wata hirar da aka yi da ta shafi dukanmu a yau. Shaiɗan ya tabka wata ƙarya sa’ad da yake magana da Hauwa’u ta wurin maciji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maciji kuwa ya fi kowace dabbar daji da Yahweh Allah ya yi wayo. Maciji ya ce wa macen, ‘Allah ya ce, lallai ba za ku ci daga kowane itacen da yake . . . gonar ba?’”​—Farawa 3:1.

Sai Hauwa’u ta amsa ta ce: “Muna da ’yanci mu ci daga ’ya’yan itatuwan da suke . . . gonar. Amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga ’ya’yan itacen da yake . . . tsakiyar gonar ba. Kada ku ci ko ku taɓa shi, domin kada ku mutu.’” Macijin kuwa ya ce mata: “Ko kaɗan, ba za ku mutu ba. Gama Allah ya sani cewa a ranar da kuka ci daga ’ya’yan itacen nan, idanunku za su buɗe. Za ku kuwa zama kamar Allah, masu sanin nagarta da mugunta.” Da haka, Shaiɗan ya kira Jehobah Allah maƙaryaci, wanda ya hana wa iyayenmu na farko abu mai kyau.​—Farawa 3:​2-5.

Hauwa’u ta yarda da ƙaryar. Sai ta soma kallon itacen da marmari kuma ta ga cewa yana da ban sha’awa sosai! Da haka, ta tsinka ’ya’yan itacen ta soma ci. Littafi Mai Tsarki ya ce, daga baya “ta kuma ba mijinta [sa’ad da] yake tare da ita, shi ma ya ci.”​—Farawa 3:6.

Allah ya gaya wa Adamu cewa: “A ranar da ka ci daga itacen nan lallai za ka mutu.”​—FARAWA 2:17

Babu shakka, Allah ya yi baƙin ciki sosai da ya ga bayinsa da yake ƙauna suna masa tawaye! Mene ne ya yi? Jehobah ya ce wa Adamu: “Za ka . . . koma ƙasa. Gama daga wurin ka fito, kai ƙurar ƙasa ne, ga ƙura kuwa za ka koma.” (Farawa 3:​17-19) A ƙarshe, Adamu ya yi “shekara . . . ɗari tara da talatin (930), sai ya mutu.” (Farawa 5:5) Da Adamu ya mutu, bai je sama ba, kuma bai ci gaba da rayuwa a wani wuri ba. Kafin Jehobah ya halicce Adamu da ƙasa, Adamu ba ya ko’ina. Saboda haka, sa’ad da ya mutu, Adamu ya zama ƙasa, kuma ya daina wanzuwa. Wannan ba ƙaramar hasara ba ce!

ABIN DA YA SA MUKA ZAMA AJIZAI

Rashin biyayyar da Adamu da Hauwa’u suka yi da gangan, ya sa sun rasa gatar yin rayuwa har abada. Zunubin ya canja su gabaki ɗaya, sun zama ajizai. Amma ba su kaɗai ba ne zunubin da suka yi ya shafa. Duk ’ya’yan da suka haifa sun zama ajizai, masu zunubi kamar su. Littafin Romawa 5:12 ta ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [wato, Adamu], zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam, gama kowa ya yi zunubi.”

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta zunubi da mutuwa a matsayin “abin da ya rufe idon dukan kabilu,” da kuma “zanen da ya rufe dukan al’umman duniya.” (Ishaya 25:7) Zunubi da mutuwa sun mamaye dukan mutane kamar hayaƙin da ba wanda zai iya kauce masa. Hakika, kowa yana ‘mutuwa saboda Adamu.’ (1 Korintiyawa 15:22) Amma, tambayar da manzo Bulus ya yi ita ce: “Wane ne zai cece ni daga jikin nan mai kai ga mutuwa?” Akwai wanda zai iya cetonmu kuwa?​—Romawa 7:24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba