Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Wasiƙun Yohanna da Yahuda
WATAƘILA an rubuta wasiƙun ne a shekara ta 98 A.Z., a Afisa, wasiƙu uku na manzo Yohanna suna cikin littattafai na ƙarshe da ke cikin Nassosi da aka hure. Wasiƙu biyu na farko sun ƙarfafa Kiristoci su ci gaba da tafiya cikin haske kuma su ƙi ridda. A wasiƙa ta uku, Yohanna ya yi maganar tafiya cikin gaskiya kuma ya ƙarfafa Kiristoci su kasance da haɗin kai.
A cikin wasiƙar da ya rubuta a Falasɗinu, wataƙila a shekara ta 65 A.Z., Yahuda ɗan’uwan Yesu, ya gargaɗi Kiristoci ’yan’uwa game da miyagu da suka shigo cikin ikilisiya, kuma ya ba da shawarar yadda za su ƙi mugun tasiri. Mai da hankali ga saƙon wasiƙu uku na Yohanna da kuma wasiƙar Yahuda zai taimaka mana mu kasance da ƙarfi cikin bangaskiya duk da matsaloli.—Ibran. 4:12.
KA CI GABA DA YIN TAFIYA CIKIN HASKE DA ƘAUNA DA KUMA BANGASKIYA
(1 Yoh. 1:1–5:21)
Ko da yake an rubuta wasiƙun don dukan ikilisiyoyi da suke tarayya da Kristi, wasiƙar Yohanna ta farko ta ba da gargaɗi mai kyau da zai taimaka wa Kiristoci su ƙi ridda kuma su manne wa gaskiya da kuma adalci. Ya nanata cewa muna bukatar mu ci gaba da yin tafiya cikin haske da ƙauna da kuma bangaskiya. Yohanna ya rubuta: “Idan muna tafiya cikin haske, kamar yadda [Allah] shi ke cikin haske, muna zumunta da junanmu.” Kuma tun da yake Allah ne Tushen ƙauna, manzon ya ce: “Mu yi ƙaunar junanmu.” Ko da yake “ƙaunar Allah” tana motsa mu “mu kiyaye dokokinsa,” muna yin nasara da duniya ta wurin “bangaskiyarmu” ga Jehobah Allah, Kalmarsa, da kuma Ɗansa.—1 Yoh. 1:7; 4:7; 5:3, 4.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:2; 4:10—Ta yaya Yesu ya zama “hadayar sulhu”? Sulhu na nufin a “lallashi,” ko kuma “sanyaya zuciya.” Yesu ya ba da ransa a matsayin hadayar sulhu, ta yin hakan, ya gamsar da abin da cikakken adalci yake bukata. Domin wannan hadayar, Allah yana yin jin ƙai, kuma yana iya gafarta zunuban waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu.—Yoh. 3:16; Rom. 6:23.
2:7, 8—Wace doka ce Yohanna yake kiran “tsofuwa” da kuma “sabuwa”? Yohanna yana maganar doka game da ƙaunar ’yan’uwa ta sadaukar da kai. (Yoh. 13:34) Ya kira ta “tsofuwa” domin Yesu ya ba da dokar fiye da shekara sattin kafin Yohanna ya rubuta hurarriyar wasiƙarsa ta farko. Saboda haka, an ba masu bi wannan dokar “tun daga farko” na rayuwarsu a matsayin Kiristoci. Dokar “sabuwa” ce kuma domin ba kawai ‘mutum ya yi ƙaunar maƙwabcinsa kamar kansa’ ba amma ya nuna ƙauna ta sadaukar da kai.—Lev. 19:18; Yoh. 15:12, 13.
3:2—Menene ba a “bayana ba tukuna” ga shafaffu Kiristoci, kuma wanene za su gani “kamar yadda shi ke”? Ba a bayyana musu yadda za su zama sa’ad da aka ta da su daga matattu zuwa sama da jikuna na ruhu ba. (Filib. 3:20, 21) Amma abin da suka sani shi ne “kadan am bayana shi [Allah], [su] za [su] zama kamansa; gama za [su] gan shi kamar yadda shi ke,” wato, “ruhun.”—2 Kor. 3:17, 18.
5:5-8—Ta yaya ruwa, jini, da ruhu suke ba da shaida cewa “Yesu Ɗan Allah ne”? Ruwa ya ba da shaida domin sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma a ruwa, Jehobah da kansa ya furta cewa yana farin ciki da Ɗansa. (Mat. 3:17) Jinin Yesu, ko kuma ransa, wanda ya ba da “fansar dukan mutane” ya kuma nuna cewa Yesu Ɗan Allah ne. (1 Tim. 2:5, 6) Ruhu mai tsarki ya kuma tabbatar da cewa Yesu Ɗan Allah ne sa’ad da ya sauka a kansa a lokacin baftismarsa, wannan ya taimaka masa “ya riƙa zagawa yana aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis, ya matsa wa.”—Yoh. 1:29-34; A. M. 10:38.
Darussa Dominmu:
2:9-11; 3:15. Idan Kirista ya ƙyale wani abu ko kuma wani mutum ya sa ya daina ƙaunar ’yan’uwansa, yana tafiya ne cikin duhu na ruhaniya, bai san inda ya nufa ba.
KA CI GABA DA YIN “TAFIYA CIKIN GASKIYA”
(2 Yohanna 1-13)
Yohanna ya soma wasiƙarsa ta biyu yana cewa: “Dattijon zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da ’ya’yanta.” Yana farin ciki sa’ad da ya ga “waɗansu daga cikin ’ya’yan[ta] suna tafiya cikin gaskiya.”—2 Yoh. 1, 4.
Bayan ya ƙarfafa a riƙa nuna ƙauna, Yohanna ya rubuta: “Ƙauna ke nan, mu yi tafiya bisa ga dokokinsa.” Yohanna ya kuma yi gargaɗi game da ‘mai ruɗewa da magabcin Kristi.’—2 Yoh. 5-7.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1, 13—Wacece “uwargida zaɓaɓɓiya”? Mai yiwuwa Yohanna yana maganar wata mata ce da aka kira Kyria, kalmar da ke nufin “mace” a Helenanci. Ko kuma wataƙila ya yi amfani da fasahar magana ce don ya yi wa wata ikilisiya magana domin ya rikitar da ’yan hamayya. Idan haka ne, yaranta za su zama waɗanda suke cikin wannan ikilisiya kuma “’ya’yan ’yar’uwar[ta]” za su zama waɗanda suke cikin wata ikilisiya.
7—Wane ‘zuwan’ Yesu ne Yohanna yake magana a nan, kuma ta yaya masu ruɗin mutane “ba su shaida” shi ba? Wannan ba ‘zuwan’ Yesu da ba za a gani a nan gaba ba ne. Maimakon haka, zuwansa na jiki ne da kuma naɗa shi a matsayin Kristi. (1 Yoh. 4:2) Masu ruɗin mutane ba su gaskata da wannan zuwa na jiki ba. Wataƙila sun yi musun cewa Yesu ya taɓa rayuwa ko kuma sun ƙi cewa an shafa shi da ruhu mai tsarki.
Darussa Dominmu:
2, 4. Sanin “gaskiya,” wato, dukan koyarwa ta Kirista da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma yin abubuwa da ya faɗa suna da muhimmanci don mu sami ceto.—3 Yoh. 3, 4.
8-11. Idan ba ma son mu yi rashin “alheri, da jinƙai, da salama . . . , daga wurin Allah Uba, da Yesu Kristi, Ɗan,” da kuma cuɗanya da ’yan’uwa masu bi, ya kamata mu “lura” da kanmu don mu tabbata muna da ruhaniya kuma mu ƙi waɗanda ba sa “lizima cikin koyarwar Kristi ba.”—2 Yoh. 3.
KU ZAMA “ABOKAN AIKI TARE DA GASKIYA”
(3 John 1-14)
Yohanna ya rubuta wasiƙarsa ta uku zuwa ga abokinsa Gayus. Ya rubuta: “Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.”—3 Yoh. 4.
Yohanna ya yaba wa Gayus don yin “aikin aminci” wajen taimaka wa ’yan’uwa da suke ziyara. Manzon ya ce: “Ya kamata fa mu yi ma irin waɗannan maraba, domin mu zama abokan aiki tare da gaskiya.”—3 Yoh. 5-8.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
11—Me ya sa wasu suke yin abin da ba shi da kyau? Domin ba su da ruhaniya, wasu ba sa ganin Allah da idanunsu na fahimi. Tun da yake ba za su iya ganinsa da idanunsa na zahiri ba, suna yin abubuwa kamar ba ya ganinsu.—Ezek. 9:9.
14—Su Waye ake kira ‘abokai’ a nan? Kalmar nan ‘abokai’ a nan ba waɗanda suke dangantaka na kud da kud da juna ba ne ba kawai. Yohanna ya yi amfani da ita ce ga ’yan’uwa gabaki ɗaya.
Darussa Dominmu:
4. ’Yan’uwa da suka manyanta a cikin ikilisiya suna farin ciki sosai sa’ad da suka ga matasa “suna tafiya cikin gaskiya.” Iyaye suna murna da babu kamarta sa’ad da suka yi nasara wajen taimaka wa yaransu su zama masu bauta wa Jehobah!
5-8. Masu kula masu ziyara, masu wa’azi a ƙasashen waje, waɗanda suke hidima a Bethel ko kuma ofishin reshe, da kuma majagaba suna cikin waɗanda suke aikin tuƙuru domin ’yan’uwansu don suna ƙaunarsu da kuma Jehobah. Yana da kyau a yi koyi da bangaskiyarsu, kuma sun cancanci mu tallafa musu.
9-12. Ya kamata mu yi koyi da misalin Dimitiriyus mai aminci amma ba na Diyoturifis mai yin miyagun zantattuka ba, wanda matsegunci ne.
“KU TSARE KANKU CIKIN ƘAUNAR ALLAH”
(Yahu. 1-25)
Yahuda ya kwatanta waɗanda suke shiga cikin ikilisiya don su ɓata ta da “masu-gunaguni . . . , masu-ƙunƙuni, suna bin sha’awoyin ransu.” Suna “furtadda manyan ruba, suna tara.”—Yahu. 4, 16.
Ta yaya Kiristoci za su ƙi mugun tasiri? Yahuda ya rubuta: “Masoya, ku tuna da zantattukan da manzannin Ubangijinmu Yesu Kristi suka faɗi tun dā.” Ya daɗa: “Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah.”—Yahu. 17-21.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
3, 4—Me ya sa Yahuda ya aririci Kiristoci su “yi yaƙi domin imani”? Domin ‘mutane masu fajirci sun shigo cikin ikilisiya.’ Waɗannan mutanen suna ‘kaɓantad da alherin Allah zuwa wajen lalata.’
20, 21—Ta yaya za mu “tsare [kanmu] cikin ƙaunar Allah”? Za mu iya yin haka a hanyoyi uku: (1) ta wajen ƙarfafa kanmu bisa ‘bangaskiyarmu maficin tsarki’ ta yin nazarin Kalmar Allah sosai da kuma sa hannu a aikin wa’azi; (2) ta yin addu’a “cikin ruhu mai-tsarki” ko kuma cikin jituwa da rinjayarsa; da kuma (3) ta ba da gaskiya ga abin da ke sa a sami rai madawwami, wato, hadayar fansa ta Yesu Kristi.—Yoh. 3:16, 36.
Darussa Dominmu:
5-7. Miyagu za su iya tsira ne daga hukuncin Jehobah? Bisa ga misalai uku da Yahuda ya tsara, hakan ba zai yiwu ba.
8-10. Ya kamata mu bi misalin Mika’ilu, shugaban mala’iku kuma mu nuna daraja ga waɗanda Jehobah ya ba iko.
12. ’Yan ridda da suka yi kamar suna nuna mana ƙauna suna da lahani ga bangaskiyarmu kamar yadda duwatsu da ke ƙarƙashin ruwa suke da lahani ga jirage ko kuma masu iyo. Malaman ƙarya suna iya yin kamar suna mana alheri, amma suna kama ne da hadari da ba a yi ruwa ba domin ba su da ruhaniya. Irin waɗannan sun yi kama da matattun itatuwa da ba sa ’ya’ya a lokacin kaka. Za a halaka su, kamar itatuwa da aka tuge. Za mu kasance masu hikima idan muka guji ’yan ridda.
22, 23. Kiristoci na gaskiya suna ƙin abin da ba shi da kyau. Ta yin ƙoƙari a ceci ‘waɗanda ke shakka’ daga wutar halaka ta har abada, waɗanda suka manyanta a cikin ikilisiya, musamman dattawa suna ba da taimako na ruhaniya.