Sashe 25
Shawara a Kan Bangaskiya, Ɗabi’a, da Ƙauna
Yaƙub, Bitrus, Yohanna, da Yahuda sun rubuta wasiƙu don su ƙarfafa ’yan’uwa masu bi
YAƘUB da Yahuda ’yan’uwan Yesu ne. Bitrus da Yohanna suna cikin manzanni 12 na Yesu. Waɗannan mazaje huɗu sun rubuta wasiƙu guda bakwai da za a iya samu a cikin Nassosin Helenanci na Kirista. Kowace wasiƙa tana ɗauke ne da sunan marubucin. An shirya hurarren gargaɗi da ke cikin waɗannan wasiƙu don su taimaka wa Kiristoci su riƙe amincinsu ga Allah da kuma Mulkinsa.
Nuna bangaskiya. Yin da’awar cewa mutum yana da bangaskiya bai isa ba kawai. Bangaskiya ta gaske tana kai ga ɗaukan mataki. Yaƙub ya rubuta: “Haka nan kuma bangaskiya ba tare da ayyuka mataciya ce.” (Yaƙub 2:26) Kasancewa da bangaskiya sa’ad da ake fuskantar jarrabobi yana sa a jimre. Don ya yi nasara, Kirista yana bukatan ya roƙi Allah ya ba shi hikima, kuma ya kasance da tabbaci cewa Allah zai ba shi. Jimrewa tana kai ga samun amincewar Allah. (Yaƙub 1:2-6, 12) Idan mai bauta ya riƙe amincinsa da bangaskiya, Jehobah Allah zai amsa. “Ku kusato ga Allah,” in ji Yaƙub, “shi kuwa za ya kusato gare ku.”—Yaƙub 4:8.
Dole ne bangaskiyar Kirista ta kasance mai ƙarfi sosai don ta taimake shi ya guji jarrabobi da lalata. Mahallin ɗabi’a da ya taɓarɓare ya motsa Yahuda ya aririci ’yan’uwansa masu bi su “yi yaƙi domin imani.”—Yahuda 3.
Ka kasance da ɗabi’a mai kyau. Jehobah yana son masu bauta masa su kasance da tsarki, wato, su kasance da tsabta a komi. Bitrus ya rubuta: “Ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi; domin an rubuta, Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni [Jehobah] mai-tsarki ne.” (1 Bitrus 1:15, 16) Akwai misali mai tamani da Kiristoci za su bi. Bitrus ya ce: “Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bitrus 2:21) Ko da yake Kiristoci suna iya shan wahala domin sun manne wa mizanan Allah, suna kasancewa da “lamiri mai-kyau.” (1 Bitrus 3:16, 17) Bitrus ya aririci Kiristoci su yawalta cikin hali da ayyuka masu tsarki da suke nuna ibada yayin da suke jiran ranar Allah ta hukunci da kuma sabuwar duniya da aka yi alkawarinta inda “adalci yake zaune.”—2 Bitrus 3:11-13.
Nuna ƙauna. Yohanna ya rubuta: “Allah ƙauna ne.” Manzon ya bayyana cewa Allah ya nuna ƙaunarsa mai girma ta wajen aiko Yesu ya “biya hakin zunubanmu.” Menene ya kamata Kiristoci su yi? Yohanna ya bayyana: “Masoya, idan Allah ya ƙaunace mu haka nan, ya kamata mu kuma mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yohanna 4:8-11) Hanya ɗaya da za mu nuna irin wannan ƙaunar ita ce nuna alheri ga ’yan’uwa masu bi.—3 Yohanna 5-8.
Amma, yaya ne masu bauta wa Jehobah za su nuna masa ƙaunarsu? Yohanna ya amsa: “Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3; 2 Yohanna 6) Waɗanda suka yi biyayya ga Allah suna da tabbaci cewa Allah zai ci gaba da ƙaunarsu, za su kuma samu “rai na har abada.”—Yahuda 21.
—An ɗauko daga Yaƙub; Bitrus na 1 da na 2; da Yohanna na 3; Yahuda.
◼ Ta yaya ne Kirista zai iya nuna bangaskiya?
◼ Wane irin ɗabi’a ne Allah yake son masu bauta masa su nuna?
◼ Ta yaya ne mutum zai nuna cewa yana ƙaunar Allah da gaske?
[Bayanin da ke shafi na 29]
“Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.”—Yaƙub 4:8
[Taswira a shafi na 29]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub ●
1 Bitrus ●
2 Bitrus ●
1 Yohanna ●
2 Yohanna ●
3 Yohanna ●
Wasiƙa ta Yahuda ●
Ru’ya ta Yohanna