Sashe 24
Bulus Ya Rubuta Wasiƙu ga Ikilisiyoyi
Wasiƙun Bulus sun ƙarfafa ƙungiyar Kirista
SABUWAR ikilisiyar Kirista da aka kafa tana da matsayi mai muhimmanci da za ta cika wajen cika nufin Jehobah. Amma Kiristoci na ƙarni na farko sun fuskanci hari nan da nan. Za su riƙe amincinsu ga Allah kuwa sa’ad da suka fuskanci tsanantawa daga mutanen da ba sa cikin ikilisiya da kuma haɗarurruka daga cikin ikilisiya? Nassosin Helenanci na Kirista sun ƙunshi wasiƙu 21 da suka ba da gargaɗi da ƙarfafawa da ake bukata.
Manzo Bulus ne ya rubuta guda sha huɗu cikin wasiƙun, wato, daga Romawa zuwa Ibraniyawa. An ba wasiƙun sunayen waɗanda aka rubuta wa, wataƙila mutum guda ko waɗanda suke cikin wata ikilisiya. Yi la’akari da wasu batutuwan da aka tattauna a cikin wasiƙun Bulus.
Faɗakarwa game da ɗabi’a. Waɗanda suke yin zina, kwartanci, da sauran mugayen zunubai “ba za su gaji mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5:19-21; 1 Korintiyawa 6:9-11) Dole ne waɗanda suke bauta wa Allah su kasance da haɗin kai ko daga ina suka fito. (Romawa 2:11; Afisawa 4:1-6) Suna bukatan su ba da kansu da son rai don su taimaka wa ’yan’uwansu masu bi da suke da bukata. (2 Korintiyawa 9:7) “Ku yi addu’a ba fasawa,” in ji Bulus. Hakika, an ƙarfafa masu bauta su faɗi abin da ke zukatansu ga Jehobah a addu’a. (1 Tasalonikawa 5:17; 2 Tasalonikawa 3:1; Filibiyawa 4:6, 7) Idan ana son Allah ya ji addu’a, dole ne a yi su cikin bangaskiya.—Ibraniyawa 11:6.
Menene zai taimaka wa iyalai su yi nasara? Magidanta suna bukatan su ƙaunaci matansu kamar jikinsu. Mata suna bukatan su daraja mazansu sosai. Yara suna bukatan su yi biyayya ga iyayensu, domin hakan na faranta wa Allah rai. Iyaye suna bukatan su yi wa yaransu ja-gora kuma su koyar da su cikin ƙauna, ta wajen yin amfani da ƙa’idodin Allah.—Afisawa 5:22–6:4; Kolosiyawa 3:18-21.
Haske ta haskaka a kan manufar Allah. Yawancin fasalolin Dokar Musa an yi su ne don su kāre Isra’ilawa kuma su yi musu ja-gora har sa’ad da Kristi ya bayyana. (Galatiyawa 3:24) Amma Kiristoci ba sa bukatan su bi wannan Dokar don su bauta wa Allah. Sa’ad da yake rubuta wasiƙa zuwa ga Ibraniyawa, Yahudawa Kiristoci, Bulus ya ba da ƙarin haske a kan ma’anar Doka da kuma yadda manufar Allah ta cika a cikin Kristi. Bulus ya bayyana cewa tsari dabam-dabam a ƙarƙashin wannan Dokar annabci ne. Alal misali, hadayar dabbobi tana wakiltar mutuwar hadayar da Yesu zai yi, wadda za ta cim ma ainihin gafarta zunubai. (Ibraniyawa 10:1-4) Ta hanyar mutuwar Yesu, Allah ya kawar da alkawarin Doka, domin ba a bukatan ta.—Kolosiyawa 2:13-17; Ibraniyawa 8:13.
Ja-goranci a kan tsarin da ya dace a cikin ikilisiya. Dole ne mazan da suke son su kasance da hakkoki a cikin ikilisiya su kasance da ɗabi’a mai kyau kuma su cika farillan da ke cikin nassi. (1 Timotawus 3:1-10, 12, 13; Titus 1:5-9) Masu bauta wa Jehobah Allah suna bukatan su riƙa haɗuwa a kai a kai tare da sauran masu bi don su ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Tarurrukan da ake yi na bauta suna bukatan su kasance masu ƙarfafawa kuma masu koyarwa.—1 Korintiyawa 14:26, 31.
A lokacin da Bulus ya rubuta wasiƙa ta biyu a cikin wasiƙu biyu da ya yi zuwa ga Timotawus, manzon ya riga ya koma ƙasar Roma; yana cikin kurkuku, yana jiran a yanke hukunci. Mutane kaɗan masu gaba gaɗi ne kawai suka yi kasadar ziyartarsa. Bulus ya san cewa lokacinsa ya kawo ƙarshe. “Na yi yaƙi mai-kyau,” in ji shi. “Na kure fagen, na kiyaye imani.” (2 Timotawus 4:7) Ba da daɗewa ba, wataƙila an kashe Bulus ne saboda imaninsa. Amma wasiƙun manzon suna yi wa masu bauta ta gaskiya ga Allah ja-gora har yau.
—An ɗauko daga Romawa; Korintiyawa na 1 da 2; Galatiyawa; Afisawa; Filibiyawa; Kolosiyawa; Tasalonikawa na 1 da 2; Timotawus na 1 da na 2; Titus; Filimon; Ibraniyawa.
◼ Wasiƙun Bulus suna ɗauke ne da waɗanne faɗakarwa game da ɗabi’u?
◼ Ta yaya ne Bulus ya ba da ƙarin haske a kan cikar nufin Allah a Kristi?
◼ Wane ja-goranci ne Bulus ya yi tanadinsa a kan tsari mai kyau a cikin ikilisiya?
[Akwati a shafi na 28]
WANENE ZURIYAR DA AKA YI ALKAWARINSA?
Bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, Allah ya yi amfani da yare na alama sa’ad da ya gaya wa macijin: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Farawa 3:15) Nassosi sun bayyana Iblis a matsayin “tsohon macijin nan.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Gane Zuriya da Allah ya yi alkawarinsa, ko kuwa Mai Ceto, asiri ne da aka ci gaba da bayyanawa a hankali daga Littafi Mai Tsarki a cikin ƙarnuka.
Wajen shekaru 2,000 bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi, Jehobah ya nuna cewa Zuriya da aka yi alkawarinsa zai fito ne daga zuriyar Ibrahim. (Farawa 22:17, 18) Ƙarnuka bayan haka, manzo Bulus ya bayyana cewa ainihin sashen farko na wannan Zuriya shi ne Almasihu, Yesu Kristi. (Galatiyawa 3:16) Cikin jituwa da Farawa 3:15, a alamance an ƙuje Yesu a “dudduge” sa’ad da aka kashe shi. Amma, Allah ya ta da Yesu daga matattu, wanda aka “rayar da shi cikin ruhu.”—1 Bitrus 3:18.
Allah kuma ya nufa cewa mutane 144,000 za su zama sashe na biyu na wannan zuriya. (Galatiyawa 3:29; Ru’ya ta Yohanna 14:1) An ta da su zuwa rayuwa ta ruhu a matsayin abokan sarauta tare da Kristi a Mulki ta sama.—Romawa 8:16, 17.
A matsayin Sarki mai iko a sama, ba da daɗewa ba Yesu zai kawar da Iblis da zuriyarsa, wato, mugayen mutane da aljanu da suke bin Shaiɗan. (Yohanna 8:44; Afisawa 6:12) Sarautar Yesu za ta kawo salama da farin ciki ga dukan mutane masu biyayya. A ƙarshe zai ƙuje macijin a ‘kai,’ wato, kawar da shi har abada.—Ibraniyawa 2:14.
[Taswira a shafi na 27]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa ●
1 Korintiyawa ●
2 Korintiyawa ●
Galatiyawa ●
Afisawa ●
Filibiyawa ●
Kolosiyawa ●
1 Tasalonikawa ●
2 Tasalonikawa ●
1 Timotawus ●
2 Timotawus ●
Titus ●
Filimon ●
Ibraniyawa ●
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna
[Taswira a shafi na 28]
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
● Romawa
● 1 Korintiyawa
● 2 Korintiyawa
● Galatiyawa
● Afisawa
● Filibiyawa
● Kolosiyawa
● 1 Tasalonikawa
● 2 Tasalonikawa
● 1 Timotawus
● 2 Timotawus
● Titus
● Filimon
● Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna
[Taswira a shafi na 27]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Wajen shekara ta 50-65 A.Z. Wasiƙun da Bulus Ya Rubuta
● Wuraren da Bulus ya rubuta wasiƙunsa
(?) Babu tabbataccen wurin da ya yi rubutun
ITALIYA
● ROMA
Afisawa
Kolosiyawa
Filimon
Filibiyawa
Ibraniyawa
2 Timotawus
Sicily
MAKIDONIYA
2 Korintiyawa
1 Timotawus
Titus (?)
Filibi
Tasalonika
HELAS
● KORINTI
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
Romawa
Karita
● AFISA
1 Korintiyawa
Kolosi
GALATIYA
● ANTAKIYA
Galatiyawa (?)
Kubrus
Urushalima
MASAR
BAHAR MALIYA