Ka Kusaci Allah
Tabbaci Mafi Girma na Ƙaunar Allah
Farawa 22:1-18
IBRAHIM ya ƙaunaci Allah. Wannan uban iyali mai aminci ya ƙaunaci Ishaƙu, ɗan da ya haifa sa’ad da ya tsufa. Amma lokacin da Ishaƙu ya kai wataƙila shekara 25 da haihuwa, Ibrahim ya fuskanci gwaji mai wuya, wato Allah ya ce ya ba da ɗansa don hadaya. Labarin bai ce Ishaƙu ya rasu ba. Kafin Ibrahim ya ba da hadayan ɗansa, Allah ya aiko da mala’ika. Wannan labari na Littafi Mai Tsarki da ke cikin Farawa 22:1-18, ya annabta mana irin ƙauna mai girma da Allah yake yi mana.
Aya 1 ta ce: “Allah ya gwada Ibrahim.” Ibrahim mutum ne mai bangaskiya, amma yanzu za a gwada bangaskiyarsa yadda ba a taɓa yi ba. Allah ya ce: “Sai ka ɗauki ɗanka, tilonka, wanda ka ke ƙaunassa, watau Ishaƙu, . . . ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a bisa ɗayan duwatsu wanda zan fada maka.” (Aya 2) Ka tuna, Allah ba zai yarda a gwada bayinsa ya fi ƙarfinsu ba. Wannan gwajin ya nuna cewa Allah ya amince da Ibrahim.—1 Korinthiyawa 10:13.
Ibrahim ya yi biyayya babu ɓata lokaci. Mun karanta: “Ibrahim fa ya yi sammako, ya yi ma jakinsa sirdi, ya ɗauki guda biyu cikin majiya-ƙarfinsa tare da shi, da Ishaƙu ɗansa; ya faskare itace domin hadaya ta ƙonawa, ya tashi, ya je wurin.” (Aya 3) Hakika Ibrahim bai gaya wa kowa abin da gwajin ya ƙunsa ba.
Tafiya na kwana uku da suka yi ya ba shi zarafin yin bimbini sosai. Amma ƙudurin Ibrahim bai raunana ba. Kalaman da ya yi sun nuna bangaskiyarsa. Da ya hangi tsaunin da aka ce ya je daga nesa, sai ya ce wa bayinsa: “Ku zauna daganan . . . da ni da sarmayin za mu tafi can; mu yi sujada, kāna mu komo wurinku.” Sa’ad da Ishaƙu ya yi tambaya ina ɗan ragon da za su yi hadayar da shi, Ibrahim ya ce: “Allah za ya tanada wa kansa ɗan rago.” (Ayoyi 5, 8) Ibrahim ya gaskata cewa za ya dawo tare da ɗansa. Me ya sa? Saboda “Ya amince cewa ko daga matattu Allah yana da iko ya ta da mutum.”—Ibraniyawa 11:19; LMT.
A kan tsaunin, sa’ad da Ibrahim ya ɗauki “wuƙa domin shi yanka ɗansa,” wani mala’ika ya dakatar da hannunsa. Sai Allah ya yi tanadin rago, a cikin sarƙaƙiya, da Ibrahim zai yi hadaya da shi “maimakon ɗansa.” (Ayoyi 10-13) A gaban Allah, kamar ya riga ya yi hadaya ne da Ishaƙu. (Ibraniyawa 11:17) Wani masani ya bayyana cewa “A gaban Allah, da yake Ibrahim ya yi niyar ya yi hadaya da ɗansa, daidai yake da yin hadaya da shi.”
Amincin Jehobah ga Ibrahim ya ɗaukaka. Kuma an bai wa Ibrahim lada domin amincinsa ga Jehobah, saboda Allah ya sake yi wa Ibrahim alkawari cewa zai albarkaci dukan al’ummai.—Ayoyi 15-18.
A ƙarshe, Allah ya hana Ibrahim ya yi hadaya da ɗansa, amma daga baya Allah ya yi hadaya da ɗansa. Miƙa Ishaƙu da Ibrahim ya yi da son ransa ya nuna yadda Allah zai miƙa makaɗaicin Ɗansa, Yesu, don zunubanmu. (Yohanna 3:16) Haɗayar Kristi shi ne tabbaci mafi girma da ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu. Tun da Allah ya yi mana wannan hadayar, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Wace hadaya ce zan so na yi don in farantawa Allah rai?’