Maganar Jehobah Rayayya Ce Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Biyu
MENENE ke jiran waɗanda suke bauta wa Jehobah Allah da waɗanda ba sa bauta masa? Menene zai sami Shaiɗan da aljanunsa a nan gaba? Wace albarka ce ’yan adam masu yin biyayya za su samu a lokacin Sarautar Kristi na Shekara Dubu? An ba da amsoshin waɗannan tambayoyi masu muhimmanci da wasu a Ru’ya ta Yohanna 13:1–22:21.a Waɗannan surori sun ƙunshi wahayi 9 na ƙarshe cikin 16 da manzo Yohanna ya gani a kusan ƙarshen ƙarni na farko.
Yohanna ya rubuta: “Mai-albarka ne shi wanda ke karantawa, da su kuma waɗanda ke jin zantattukan annabcin, suna kuwa kiyaye abin da an rubuta a ciki.” (R. Yoh. 1:3; 22:7) Karanta da kuma yin abin da muka koya daga littafin Ru’ya ta Yohanna za su iya shafan zuciyarmu, su ƙarfafa bangaskiyarmu ga Allah da Ɗansa, Yesu Kristi, su kuma sa mu kasance da bege don nan gaba.b—Ibran. 4:12.
AN ZUBAR DA KASAKE BAKWAI NA FUSHIN ALLAH
(R. Yoh. 13:1–16:21)
Ru’ya ta Yohanna 11:18 ta ce: “Al’ummai kuma suka yi fushi, fushin [Allah] kuma ya zo da lokacin ... hallaka waɗanda ke hallaka duniya.” Don a nuna abin da ya sa Allah ya yi fushi, wahayi na takwas ya nuna ayyukan wani “bisa . . . mai-ƙafo goma da kai bakwai.”—R. Yoh. 13:1.
A wahayi na tara, Yohanna ya ga “Ɗan ragon yana tsaye bisa dutsen Sihiyona” kuma “mutum zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu” suna tare da shi. An fanso su ne “daga cikin mutane.” (R. Yoh. 14:1, 4) Sanarwa na mala’ika ya biyo baya. A wahayi na gaba, Yohanna ya ga “mala’ika bakwai ... da aloba bakwai.” A bayyane yake cewa Jehobah ne da kansa ya ba da umurni ga mala’ikun su zubar da “bakwaiɗin kasake na hasalar Allah” a kan fannoni dabam dabam na duniyar Shaiɗan. Kasake ɗin suna ɗauke da sanarwa da kashedi na hukuncin da Allah zai zartar. (R. Yoh. 15:1; 16:1) Waɗannan wahayi biyu sun ba da bayani dalla-dalla game da hukunci na Mulki da ke tattare da busa ƙaho na bakwai da kuma annoba na uku.—R. Yoh. 11:14, 15.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
13:8—Menene “littafin rai na Ɗan Rago”? Wannan littafi ne na alama da ke ɗauke da sunayen waɗanda suke sarauta da Yesu Kristi a Mulkinsa na samaniya. Ya ƙunshi sunayen Kiristoci shafaffu da har ila suke duniya, da suke da begen samun rai a sama.
13:11-13—Ta yaya bisa mai ƙaho biyu take aikata kamar dragon kuma ta sa wuta ta zubo daga sama? Da yake bisa mai ƙaho biyu, wato, Britaniya da Amirka masu iko da duniya suna magana kamar dragon, ya nuna cewa suna amfani da barazana, matsi, da mugunta don su tilasta wa mutane su amince da sarautarsu. Suna sa wuta ta zubo daga sama don suna yi kamar annabi ta wajen yin da’awa cewa sun sha kan ikon mugunta a yaƙin duniya guda biyu da aka yi a ƙarni na ashirin kuma sun ci nasara bisa Mulkin Kama Karya.
16:17—Menene “sarari” da aka zuba kasko na bakwai a ciki? “Sarari” yana kwatanta tunani na Shaiɗan, wato, “ruhun [tunanin] da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” Duk wanda yake gefen muguwar duniya na Shaiɗan yana shaƙar wannan sarari mai guba.—Afis. 2:2.
Darussa Dominmu:
13:1-4, 18. “Bisa” da ke wakiltar mulkoki na ’yan adam ta fito ne daga cikin “teku,” wato, daga ’yan adam masu yawa da suke kama da ruwa. (Isha. 17:12, 13; Dan. 7:2-8, 17) Wannan bisan, da Shaiɗan ya kafa kuma ya ba shi iko yana da lamba 666, da ke nuna cikakken ajizanci. Fahimtar ko menene wannan dabbar yana taimakonmu domin kada mu bi ta don muna sha’awarta ko kuma mu bauta mata yadda ’yan adam da yawa suke yi.—Yoh. 12:31; 15:19.
13:16, 17. Duk da matsaloli da za mu iya fuskanta sa’ad da muke ayyukanmu na yau da kullum, kamar su ‘saye da sayarwa,’ bai kamata mu yarda a tilasta mana mu ƙyale bisan ta yi wa rayuwarmu ja-gora ba. Amincewa da ‘shaidar wannan bisa a hannunmu ko kuma a goshinmu’ zai nuna cewa mun ƙyale wannan bisar ta ja-goranci ayyukanmu ko kuma ta shafi tunaninmu.
14:6, 7. Sanarwa na mala’ikan yana koya mana cewa ya kamata mu sanar da bisharar Mulkin Allah da aka kafa da gaggawa. Ya kamata mu taimaki ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki su koyi yadda ake jin tsoron Allah da kuma ɗaukaka Jehobah.
14:14-20. Sa’ad da aka kammala girbin “amfanin duniya” wato, girbin waɗanda za su tsira, a lokacin ne mala’ikan zai jefa “kuringar anab ta duniya” cikin “wurin matsewar ruwan anab [babba], na hasalar Allah.” A lokacin ne za a halaka wannan kuringar anab har abada, wato, lalataccen tsarin gwamnatoci na Shaiɗan da muke gani da ke sarautar ’yan adam da kuma ‘nonnansa’ na ’ya’yan mugunta. Ya kamata mu ƙuduri aniya kada kuringar anab na duniya ta rinjaye mu.
16:13-16. “Ƙazaman ruhohi” na nuni ga labarin ƙarya na aljanu don kada zubar da kasakai bakwai na fushin Allah ya rinjayi sarakunan duniya su bi Allah amma don su yi hamayya da Jehobah.—Mat. 24:42, 44.
16:21. Yayin da ƙarshen wannan duniyar ya kusa, shelar hukuncin Jehobah a kan mugun zamani na Shaiɗan zai ƙunshi shela mai tsanani na hukuncin Allah, da wataƙila yake wakiltar ƙanƙara. Duk da haka, yawancin ’yan adam za su ci gaba da saɓa wa Allah.
SARKI DA YA YI NASARA YANA SARAUTA
(R. Yoh. 17:1–22:21)
“Babila Babba,” wato, daular duniya na addinin ƙarya, sashe ne mai ban ƙyama na duniyar Shaiɗan. Wahayi na sha ɗaya ya kwatanta ta da “babbar karuwa” wato, malalaciya da ta “zauna a kan wani bisa, launinsa ja wur.” “Ƙahoni gomaɗin” na bisan da ya ɗauke ta ne zai halaka ta gabaki ɗaya. (R. Yoh. 17:1, 3, 5, 16) Da yake gwada ta da “babban birnin,” wahayi na gaba ya sanar da faɗuwarta kuma ya yi kira na gaggawa ga mutanen Allah cewa su “fito daga cikinta.” Mutane da yawa sun yi makokin faɗuwar babban birnin. Amma, ana murna a sama domin “auren Ɗan rago.” (R. Yoh. 18:4, 9, 10, 15-19; 19:7) A wahayi na 13, mahayin “farin doki” ya yi yaƙi da al’ummai. Ya kawo ƙarshen muguwar duniyar Shaiɗan.—R. Yoh. 19:11-16.
“Tsofon maciji” wanda ake kira “Iblis da Shaitan” kuma fa? Yaushe ne za a “jefarda shi cikin ƙorama ta wuta”? Wannan shi ne batu ɗaya da ke cikin wahayi na sha huɗu. (R. Yoh. 20:2, 10) Wahayi biyu na ƙarshe sun ɗan yi bayani game da rayuwa a lokacin sarauta ta shekara dubu. Yayin da “ru’ya ta Yohanna” ta kusan kammalawa, Yohanna ya ga ‘kogin ruwa na rai yana fitowa daga cikin tsakiyar karabkassa,’ kuma an miƙa gayyata mai al’ajabi ga “mai-jin ƙishi.”—R. Yoh. 1:1; 22:1, 2, 17.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
17:16; 18:9, 10—Me ya sa “sarakunan duniya” suke makoki a kan wadda su da kansu suka halaka? Suna kuka ne don son kai kawai. Bayan halakar Babila Babba, sarakunan duniya babu shakka sun fahimci cewa tana da amfani a gare su. Tana rufe muguntarsu da sunan addini. Babila Babba tana taimakonsu wajen tara matasa domin yaƙi. Bugu da ƙari, tana da matsayi na musamman wajen sa mutane su yi biyayya.
19:12—Ta yaya ne babu wanda ya san sunan Yesu da ba a ambata ba sai shi kaɗai? Wannan sunan kamar na matsayi ne da kuma gata, kamar waɗanda aka ambata a Ishaya 9:6, waɗanda Yesu yake morewa a zamanin Ubangiji. Babu wanda ya san wannan sunan sai shi kaɗai domin wannan hakkin na musamman ne kuma shi kaɗai ne zai iya fahimtar abin da riƙe wannan matsayi mai girma ya ƙunsa. Amma, Yesu ya ba da wasu daga cikin gatan nan ga waɗanda suke cikin rukunin amaryarsa, ta hakan ya rubuta ‘sabon sunan’ nan nasa a kansu.—R. Yoh. 3:12.
19:14—Su waye ne za su bi Yesu a Armageddon? ‘Rundunan waɗanda ke cikin sama’ da za su bi Yesu a yaƙin Allah ya ƙunshi mala’iku da kuma shafaffu da suka ci nasara da sun riga sun samu ladarsu na samaniya.—Mat. 25:31, 32; R. Yoh. 2:26, 27.
20:11-15—Sunayen su wanene aka rubuta cikin “littafin rai”? Wannan littafi ne da ke ɗauke da sunayen dukan waɗanda za su samu rai madawwami, wato, Kiristoci shafaffu, taro mai girma, da bayin Allah masu aminci da za su samu “tashin matattu, na masu-adalci.” (A. M. 24:15; R. Yoh. 2:10; 7:9) Za a rubuta sunayen waɗanda za a dawo da su rai a ‘tashin matattu na marasa adalci’ a “littafin rai” idan sun aikata cikin jituwa da abubuwan “da aka rubuta cikin littattafai” na umurni da aka buɗe a lokacin sarauta na Shekara Dubu. Amma, ba a rubuta sunayen da alƙalami na dindindin ba. Sunayen shafaffu yana zama na dindindin bayan sun nuna amincinsu har mutuwa. (R. Yoh. 3:5) Sunayen waɗanda za su yi rayuwa a duniya har abada zai kasance a cikin littafin rai na dindindin sa’ad da suka jimre wa gwaji na ƙarshe a ƙarshen shakara dubu.—R. Yoh. 20:7, 8.
Darussa Dominmu:
17:3, 5, 7, 16. “Hikima mai-fitowa daga bisa” na taimakonmu mu fahimci “asirin macen, da na bisan [mai launi ja wur] da ke ɗauke da ita.” (Yaƙ. 3:17) Wannan bisa na alama ta soma ne a matsayin Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya kuma daga baya aka farfaɗo da ita a matsayin Majalisar Ɗinkin Duniya. Bai kamata buɗe wannan asirin ya motsa mu mu kasance da himma a shelar bisharar Mulkin Allah da kuma sanar da ranar hukuncin Jehobah?
21:1-6. Muna da tabbaci cewa albarka da aka annabta cewa za a samu a ƙarƙashin Mulki za ta kasance gaskiya. Me ya sa? Domin an faɗa game da su cewa: “Sun tabbata.”
22:1, 17. “Kogin ruwa na rai” yana wakiltar tanadin da Jehobah ya yi don farfaɗo da ’yan adam masu biyayya daga zunubi da mutuwa. Ana samun wannan ruwan sosai a yau. Bari mu yi na’am da gayyatar mu zo mu “ɗiba ruwa na rai kyauta” kuma mu miƙa wa wasu wannan gayyar!
[Hasiya]
a Don bayani game da Ru’ya ta Yohanna 1:1–12:17, ka dubi “Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Ɗaya” Hasumiyar Tsaro na 15 ga Janairu, 2009.
b Don ka sami bayani kan kowace aya na littafin Ru’ya ta Yohanna, ka dubi littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!
[Hotunan da ke shafi na 5]
Yan adam masu biyayya za su samu albarka mai ban al’ajabi a sarautar Mulki!