Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”
“Ru’ya ta Yesu Kristi, wanda Allah ya ba shi domin ya bayyana ma bayinsa, al’amura da za su faru ba da daɗewa ba.”—R. YOH. 1:1.
MECE CE AMSARKA?
Wane ɓangaren babbar sifa ne yake wakiltar Mulkin Biritaniya da Amirka?
Ta yaya Yohanna ya kwatanta dangantakar da ke tsakanin Mulkin Biritaniya da Amirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya?
Ta yaya Daniyel da Yohanna suka kwatanta yadda za a kawo ƙarshen mulkin ɗan Adam?
1, 2. (a) Mene ne za mu fahimta idan muka tattauna wahayin Yohanna da na Daniyel? (b) Mene ne kai na ɗaya zuwa shida na dabbar suke wakilta?
ANNABCE-ANNABCEN Daniyel da kuma Yohanna sun sa mun fahimci abubuwan da suke faruwa a yau da waɗanda za su faru a nan gaba. Mene ne za mu koya daga wahayin Yohanna na dabba mai kawuna guda bakwai da kuma daga wahayin Daniyel game da dabba mai ƙahoni guda goma da babbar sifar da Nebuchadnezzar ya yi mafarkinta? Kuma mene ne fahimtar waɗannan annabce-annabcen ya kamata ya motsa mu mu yi?
2 Bari mu tattauna wahayin Yohanna game da dabbar. (R. Yoh., sura ta 13) Mun koyi cewa kai na ɗaya zuwa shida na dabbar suna wakiltar ƙasar Masar da Assuriya da Babila da Midiya-da-Farisa da Hellas da kuma Roma. Shaiɗan ya yi amfani da waɗannan masu mulkin duniya wajen tsananta wa mutanen Allah. (Far. 3:15) Roma ita ce mai mulkin duniya na shida kuma ta ci gaba da kasancewa hakan shekaru da yawa bayan Yohanna ya rubuta wahayinsa. Amma, da shigewar lokaci, kai na bakwai, wato mai mulkin duniya na bakwai zai sauya Roma. Wace ƙasa ce wannan, kuma yaya za ta bi da zuriyar macen?
BIRITANIYA DA AMIRKA SUN SAMU IKO SOSAI
3. Mece ce dabba mai ƙahoni goma mai ban tsoro take wakilta, kuma mene ne ƙahoni guda goma suke wakilta?
3 Za mu gane kai na bakwai na dabbar da aka yi maganarsa a Ru’ya ta Yohanna sura ta 13 idan muka kwatanta wahayin Yohanna da na Daniyel wanda yake maganar wata dabba mai ban tsoro mai ƙahoni goma.a (Karanta Daniyel 7:7, 8, 23, 24.) Wannan dabbar da Daniyel ya gani a wahayinsa tana wakiltar Roma a matsayin mai mulkin duniya. (Duba taswira da ke shafuffuka na 12-13.) A ƙarni na biyar, Sarautar Roma ta fara taɓarɓarewa. Ƙahoni guda goma da Daniyel ya gani suna nufin ƙananan mulkoki da suka fito daga sarautar Roma.
4, 5. (a) Mene ne ƙaramin ƙahon ya yi? (b) Mene ne kai na bakwai na dabbar yake wakilta?
4 A annabcin Daniyel game da dabba mai ƙahoni goma, an ambata cewa wani ƙaramin ƙaho ya fito daga kan dabbar kuma ya sauya ƙahoni uku daga cikin goma. Wannan annabcin ya cika sa’ad da Biritaniya wata ƙasar da Roma take mallaka ta zama mai mulkin kanta. Kafin ƙarni na 17 a zamaninmu, ƙasar Biritaniya ba ta da ƙarfi sosai. Wasu ƙasashe guda uku, wato Sifen da Holan da kuma Faransa sun fi ta iko. Ƙasar Biritaniya ta yaƙe su ɗaya bayan ɗaya kuma ta zama ƙasa mafi iko a cikinsu. A ƙarni na 18 a zamaninmu, Biritaniya tana gab da zama ƙasa mafi iko a duniya amma ba ta zama kai na bakwai na dabbar ba.
5 Ko da yake Biritaniya ta zama ƙasa mafi iko, amma ƙananan ƙasashe da ke ƙarƙashinta a Arewancin Amirka sun yi tawaye kuma suka haɗa kai suka zama ƙasar Amirka. Duk da haka, Biritaniya ba ta hana ƙasar Amirka ci gaba ba, har ta kāre ta da rundunar yaƙi na jiragen ruwa kuma hakan ya sa ƙasar Amirka ta samu ci gaba sosai. Sa’ad da ranar Ubangiji ta soma a shekara ta 1914, Biritaniya, ƙasa mafi iko ta mallaki ƙasashe da yawa a faɗin duniya kuma Amirka ta zama ƙasa mafi samun ci gaba a duniya.b A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Biritaniya ta ƙulla yarjejeniya ta musamman da ƙasar Amirka. Wannan haɗin kai na Biritaniya da Amirka ne ya haifar da Mulkin Biritaniya da Amirka. Ta yaya Mulkin Biritaniya da Amirka ta bi da zuriyar macen?
6. Yaya kai na bakwai na dabbar ya bi da mutanen Allah?
6 Ba da daɗewa ba da ranar Ubangiji ta soma, kai na bakwai na dabbar ya fara kai wa mutanen Allah hari, wato, ’yan’uwan Kristi da suka rage a duniya. (Mat. 25:40) Yesu ya nuna cewa a somawar ranar Ubangiji wato a bayyanuwarsa, zuriyar macen za su riƙa yin aikin da ya ce su yi. (Mat. 24:45-47; Gal. 3:26-29) Mulkin Biritaniya da Amirka sun yaƙe waɗannan tsarkakku. (R. Yoh. 13:3, 7) A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, mulkin ya tsananta wa mutanen Allah, ya hana su buga littattafansu kuma ya jefa wakilan rukunin bawa nan mai-aminci cikin kurkuku. Kai na bakwai na dabbar nan ya kusan sa a daina yin wa’azi gabaki ɗaya a lokacin. Jehobah ya bayyana wa Yohanna a cikin wahayi cewa hakan zai faru. Allah ya ƙara gaya wa Yohanna cewa waɗannan tsarkakkun sashen zuriyar macen za su soma aikin wa’azi kuma. (R. Yoh. 11:3, 7-11) Tarihin Shaidun Jehobah ya nuna cewa waɗannan abubuwa sun faru.
MULKIN BIRITANIYA DA AMIRKA DA KUMA SAWUN ƘARFE DA YUMƁU
7. Wace irin dangantaka ce ke tsakanin kai na bakwai na dabbar da kuma babbar sifar?
7 Wace irin dangantaka ce ke tsakanin kai na bakwai na dabbar da babbar sifar? Biritaniya da Amirka sun fito daga ƙarƙashin Mulkin Roma. Sawayen sifar kuma fa? An kwatanta su a matsayin haɗin ƙarfe da yumɓu. (Karanta Daniyel 2:41-43.) Wannan kwatancin yana maganar lokacin da kai na bakwai na dabbar, wato Mulkin Biritaniya da Amirka zai fara sarauta. Kamar yadda ginin da aka yi da yumɓu da ƙarfe ba zai kai wanda aka yi da ƙarfe zalla ƙarfi ba, hakan ma Mulkin Biritaniya da Amirka ba zai kai Roma ƙarfi ba. Ta yaya hakan ya faru?
8, 9. (a) Ta yaya mai mulkin duniya na bakwai ya nuna iko da ke kama da ƙarfe? (b) Mene ne sawayen sifar suke nufi?
8 A wasu lokatai, mulkin Biritaniya da Amirka ya nuna cewa yana da ƙarfi kamar ƙarfe. Alal misali, ya yi hakan ta wajen samun nasara a Yaƙin Duniya na ɗaya. Kuma a Yaƙin Duniya na biyu ya sake samun nasara.c A wasu lokatai bayan yaƙin, kai na bakwai na dabbar yana nuna ƙarfinsa da ke kamar ƙarfe. Amma, daga lokacin da Mulkin Biritaniya da Amirka ya fara sarauta, an garwaya ƙarfen da yumɓu.
9 Da daɗewa bayin Jehobah sun yi ƙoƙari su fahimci abin da sawayen sifar suke nufi. Littafin Daniyel 2:41 ya kwatanta ƙarfe da ke garwaye da yumɓu a matsayin “mulki” ɗaya ba mulkoki dabam-dabam ba. Yumɓun yana nufin wani abin da ke rage ƙarfin Mulkin Biritaniya da Amirka kuma hakan ya sa Mulkin Roma wanda ƙarfe ne zalla ya fi shi ƙarfi. Annabcin Daniyel ya ce yumɓun yana nufin “zuriyar mutane” ko kuma talakawa. (Dan. 2:43) A Mulkin Biritaniya da Amirka, jama’a sun tashi tsaye a kan neman ’yancinsu, sun yi hakan ta yin zanga-zanga cikin lumana, ta ƙungiyar ƙwadago kuma ƙasashe sun nemi ’yanci kai. Waɗannan abubuwa da mutane suke yi suna sa ya yi wa Mulkin Biritaniya da Amirka wuya ya yi ƙarfi kamar ƙarfe. Mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da siyasa. Kuma sa’ad da wani ya ci zaɓe da ƙarin ƙuri’o’i kaɗan, ba ya samun isashen iko ya aiwatar da abubuwan da ya yi alkawarinsu. Daniyel ya annabta cewa: “Mulkin za ya kasance, rabi da ƙarfi, rabi mara-ƙarfi.”—Dan. 2:42; 2 Tim. 3:1-3.
10, 11. (a) Mene ne zai faru da ‘sawayen’ a nan gaba? (b) Mene ne za mu iya kammala game da adadin yatsun sifar?
10 A zamaninmu, Biritaniya da Amirka sun ci gaba da ƙawanci, sau da yawa suna haɗa kai kuma su saka hannu a al’amuran duniya. Annabcin babbar sifar da kuma dabbar sun nuna cewa ba wani mulki da zai sauya Mulkin Biritaniya da Amirka, shi ne mulki na ƙarshe. Ko da yake, wannan mulkin ba shi da ƙarfi kamar mulkin Roma, wato, ƙafar ƙarfen, ba zai ragargaje da kanta ba.
11 Adadin yatsun sifar yana da wata ma’ana ne? A wasu wahayi, Daniyel ya ambata adadin abubuwa, alal misali, adadin ƙahoni da ke kan dabbobi dabam-dabam. Waɗannan adadin suna da muhimmanci. Amma, sa’ad da Daniyel yake kwatanta sifar, bai ambata adadin yatsun ba. Wannan ya nuna cewa adadin yatsun bai da wani muhimmanci, matsayinsu ɗaya ne da adadin hannuwan da yatsun da ƙafafuwan da kuma sawayen. Amma, Daniyel ya ambata cewa yatsun za su kasance na ƙarfe da yumɓu. A nan za mu fahimta cewa Mulkin Biritaniya da Amirka ne zai riƙa mulkin duniya sa’ad da ‘dutsen,’ wato Mulkin Allah zai rugurguje sawayen sifar.—Dan. 2:45.
MULKIN BIRITANIYA DA AMIRKA DA KUMA DABBA MAI ƘAHONI BIYU
12, 13. Mece ce dabba mai ƙahoni biyu take wakilta, kuma me ta yi?
12 Ko da yake Mulkin Biritaniya da Amirka haɗin ƙarfe da yumɓu ne, wahayin da Yesu ya nuna wa Yohanna ya bayyana cewa wannan mulkin zai yi abu mai muhimmanci a kwanaki na ƙarshe. Ta yaya zai yi hakan? Yohanna ya ga wahayin wata dabba mai ƙahoni biyu mai magana kamar dragon. Mene ne wannan dabba mai ban tsoro take wakilta? Tana da ƙahoni biyu, wato ƙasashe guda biyu da suka haɗa kai a yin sarauta. Wannan dabbar tana wakiltar Mulkin Biritaniya da Amirka amma tana yin wani abu na musamman.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 13:11-15.
13 Wannan dabbar tana gaya wa jama’a su ƙera sifar dabbar da ke da kawuna bakwai. Yohanna ya rubuta cewa sifar dabbar za ta bayyana kuma ta ɓace, daga baya ta sake bayyana. Hakan ya faru da wata ƙungiyar da Biritaniya da Amirka suke ja-gora, burin wannan ƙungiyar shi ne ta haɗa kan dukan gwamnatocin duniya kuma ta wakilce su.d Wannan ƙungiyar ta bayyana bayan Yaƙin Duniya na ɗaya, ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta dā. Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na biyu, wannan ƙungiyar ta daina aiki. A lokacin wannan yaƙin, mutanen Allah sun bayyana cewa ƙungiyar za ta sake tasowa kamar yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya annabta. Kuma hakan ya faru, ta taso a matsayin Majalisar Ɗinkin Duniya ta yanzu.—R. Yoh. 17:8.
14. Me ya sa Yohanna ya kira sifar dabbar sarki “na takwas”?
14 Yohanna ya kwatanta sifar dabba mai kawuna bakwai a matsayin sarki “na takwas.” Me ya sa ya kira shi sarki? Bai bayyana a matsayin kai na takwas na ainihin dabbar ba. Ya bayyana ne a matsayin sifarta. Tana samun ikonta daga ƙasashen da Majalisar Ɗinkin Duniya ke wakiltar su ne, musamman daga Mulkin Biritaniya da Amirka. (R. Yoh. 17:10, 11) Yohanna ya ce sarki ne don yana samun ikon yin abubuwan da zai shafi dukan duniya.
SIFAR DABBAR TA HALAKA KARUWAR
15, 16. Mene ne karuwar da Yohanna ya gani a wahayinsa take wakilta kuma mene ne yake faruwa da addinai a yau?
15 Yohanna ya sake kwatanta wata karuwa da take zaune a kan wata dabba ja wur. Sunanta “Babila Babba.” (R. Yoh. 17:1-6) Wannan karuwar tana nufin dukan addinan ƙarya, kuma a cikin waɗannan addinan ƙarya, Kiristendam ne ta fi rinjaya. Addinai sun goyi bayan Majalisar Ɗinkin Duniya na dā da na yanzu kuma suna ƙoƙarin yi mata ja-gora.
16 An ce Babila Babba tana zaune a kan ‘ruwa.’ Wannan ruwan yana nufin jama’an da suke goyon bayanta. Amma a ranar Ubangiji, goyon bayan da suke yi mata ya ragu sosai. (R. Yoh. 16:12; 17:15) Alal misali, lokacin da sifar dabbar ta bayyana da farko, coci na Kiristendam suna da iko sosai a ƙasashe da yawa. Amma a yanzu jama’a ba sa daraja coci da limamanta kamar yadda suke yi a dā. Mutane da yawa sun tabbata cewa addini ne yake haddasa tashin hankali a wurare da yawa a duniya. Wasu suna so a kawo ƙarshen dukan addinai.
17. Mene ne zai faru da addinan ƙarya nan ba da daɗewa ba, kuma me ya sa?
17 Ba za a kawo ƙarshen addinan ƙarya da sannu-sannu ba. Karuwar za ta ci gaba da kasancewa da iko kuma ta riƙa sa sarakuna su aikata nufinta har sai Allah ya sa cikin zuciya masu mulki su yi nufinsa. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:16, 17.) Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi amfani da gwamnatocin ’yan Adam wanda Majalisar Ɗinkin Duniya na yanzu take wakilta don ya kai wa addinan ƙarya hari. Karuwar ba za ta sake iya rinjayar waɗannan gwamnatoci ba kuma za ta rasa dukan dukiyoyinta. Shekaru ashirin ko talatin da suka wuce, mutane da yawa ba su taɓa tsammani cewa wannan abin zai iya faruwa ba. Amma a yau, abubuwa sun fara canjawa, duk da haka karuwar ba za ta faɗo daga kan dabbar ja wur a hankali ba. Za a halaka ta ne nan take.—R. Yoh. 18:7, 8, 15-19.
AN HALAKA DABBOBIN
18. (a) Mene ne dabbar za ta yi, kuma mene ne sakamakon? (b) Waɗanne mulkoki ne littafin Daniyel 2:44 ya ce Mulkin Allah zai halaka? (Duba akwatin da ke shafi na 17.)
18 Bayan an halaka addinan ƙarya, Shaiɗan zai sa dabbar, wato gwamnatocin da ke ƙarƙashin ikonsa ta kai hari ga Mulkin Allah. Tun da sarakunan duniya ba za su iya kai hari ga Mulkin Allah a sama ba, za su yi yaƙi da waɗanda suke goyon bayan Mulkin Allah a nan duniya. Sakamakon haka shi ne yaƙin ƙarshe da Allah zai yi da su. (R. Yoh. 16:13-16; 17:12-14) Daniyel ya bayyana abin da zai faru a wannan yaƙin. (Karanta Daniyel 2:44.) Za a halaka dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 13:1 da sifarta da kuma dabba mai ƙahoni biyu.
19. Wane tabbaci ne muke da shi, kuma yanzu ne lokacin yin mene ne?
19 Muna zama ne a kwanakin kai na bakwai na dabbar. Ba za a sake yin wani kai kafin a halaka wannan dabbar ba. Mulkin Biritaniya da Amirka zai riƙa sarauta a lokacin da za a halaka addinan ƙarya. Dukan annabce-annabcen Daniyel da na Yohanna sun cika daidai yadda aka rubuta. Bari mu kasance da gaba gaɗi cewa za a halaka addinan ƙarya nan ba da daɗewa ba. Allah ya bayyana mana waɗannan abubuwa tun da wuri. Amma, za mu yi biyayya da gargaɗin da ke cikin waɗannan annabcin ne? (2 Bit. 1:19) Yanzu ne ya kamata mu yi biyayya ga Jehobah kuma mu goyi bayan Mulkinsa.—R. Yoh. 14:6, 7.
[Hasiya]
a A cikin Littafi Mai Tsarki goma yana nufin cikakke. Wato wannan ƙahoni goma suna nufin dukan sarautar da suka fito daga ƙarƙashin Sarautar Roma.
b Ko da yake fasalolin Mulkin Amirka da Biritaniya sun bayyana tun ƙarni na 18, Yohanna ya annabta cewa za su fara sarauta a matsayin Mulki guda a somawar ranar Ubangiji. Hakika, wahayin Yohanna annabci ne da ke cika a “ranar Ubangiji.” (R. Yoh. 1:10) A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya ne Biritaniya da Amirka suka haɗa kai a matsayin masu mulkin duniya.
c Kamar yadda Daniyel ya annabta, Mulkin Biritaniya da Amirka ya yi “hallakaswa da ban mamaki.” (Dan. 8:24) Alal misali, Amirka ta jefa bama-bamai na atam guda biyu da suka halaka abubuwa sosai a ƙasar da ke gaba Mulkin Biritaniya da Amirka.
d Duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax at Hand!, shafuffuka na 240 da 241 da kuma 253 na Turanci.
[Akwati a shafi na 17]
SU WAYE NE ‘DUKAN WAƊANNAN MULKOKIN’?
Annabcin da ke littafin Daniyel 2:44 ya ce Mulkin Allah ‘za ya farfashe dukan waɗannan mulkokin.’ Wannan annabcin yana maganar mulkoki da babbar sifar take wakilta ne kawai.
Sauran Gwamnatocin ’yan Adam kuma fa? Annabcin da ke Ru’ya ta Yohanna da ya yi magana game da wannan batun ya ba da ƙarin haske. Ya nuna cewa “sarakunan dukan duniya” za su haɗa kai don su yaƙi Jehobah a “babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (R. Yoh. 16:14; 19:19-21) Saboda haka, ba mulkokin da sifar take wakilta ba ne kawai za a halaka a Armageddon, amma dukan gwamnatocin ’yan Adam.