Jehobah “Mai-bayyana Asirai” Ne
“Hakika Allahnka shi ne Allah na allohi, Ubangijin sarakuna kuwa, mai-bayyana asirai.”—DAN. 2:47.
MECE CE AMSARKA?
Waɗanne abubuwa da za su faru a nan gaba ne Jehobah ya bayyana mana?
Mene ne kai na ɗaya zuwa shida na dabbar yake wakilta?
Wace nasaba ce ke tsakanin dabbar da kuma sifar da Sarki Nebuchadnezzar ya gani?
1, 2. Mene ne Jehobah ya bayyana mana, kuma me ya sa ya yi hakan?
WACE mulki ce za ta riƙa sarauta a duniya sa’ad da Mulkin Allah zai kawo ƙarshe ga sarautar ’yan Adam? Mun san amsar domin Jehobah Allah, “Mai-bayyana asirai” ne. Kuma ya bayyana mana wannan asiran ta littattafan da annabi Daniyel da manzo Yohanna suka rubuta.
2 Jehobah ya saukar wa Daniyel da Yohanna wahayi da yawa game da dabbobin. Ya kuma bayyana wa Daniyel ma’anar wani mafarkin da ya yi game da wani babban gunki na ƙarfe. Jehobah ya sa an rubuta kuma an adana waɗannan abubuwan a cikin Littafi Mai Tsarki don amfaninmu. (Rom. 15:4) Ya yi hakan don ya sa mu kasance da bege cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai halaka dukan mulkokin ’yan Adam.—Dan. 2:44.
3. Idan muna son mu fahimci wannan annabcin sosai, mene ne ya kamata mu fara fahimta kuma me ya sa?
3 Annabce-annabcen da Daniyel da kuma Yohanna suka rubuta sun bayyana abubuwa game da sarakai takwas ko kuma sarautar ’yan Adam da kuma yadda za su soma sarauta ɗaya bayan ɗaya. Amma, idan muna son mu fahimci waɗannan annabce-annabcen, wajibi ne mu fahimci ma’anar annabci na farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya da kuma annabce-annabcen da ke cikinsa suna da nasaba da wannan annabcin. Shi ne tushen dukan annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
ZURIYAR MACIJIN DA DABBAR
4. Su wane ne sashen wannan zuriyar kuma mene ne zuriyar za ta yi?
4 Ba da daɗewa ba bayan Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya a gonar Adnin, Jehobah ya yi alkawari cewa wata ‘mace’ za ta haifi ‘zuriya.’a (Karanta Farawa 3:15.) Zuriyar za ta ƙuje kan macijin, wato, Shaiɗan. Daga baya, Jehobah ya bayyana cewa zuriyar za ta taho daga Ibrahim ta al’ummar Isra’ila daga kabilar Yahuda kuma daga iyalin Dauda. (Far. 22:15-18; 49:10; Zab. 89:3, 4; Luk 1:30-33) Kuma Yesu ne ainihin wannan zuriyar. (Gal. 3:16) Ikilisiyar shafaffu ita ce sashe na biyu na wannan zuriyar. (Gal. 3:26-29) Yesu da shafaffu ne suka kafa Mulkin Allah. Kuma Allah zai yi amfani da su wajen halaka Shaiɗan.—Luk 12:32; Rom. 16:20.
5, 6. (a) Gwamnatoci masu iko nawa ne Daniyel da Yohanna suka bayyana? (b) Mene ne kawunan dabbar da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna suke wakilta?
5 A wannan annabci na farko da Jehobah ya ba da a gonar Adnin, ya ce Shaiɗan zai haifi ‘zuriya.’ Zuriyarsa za ta yi magabtaka da zuriyar macen. Su waye ne zuriyar macijin? Dukan waɗanda suka tsane Jehobah kuma suke tsananta wa bayin Allah kamar yadda Shaiɗan yake yi. Da daɗewa, Shaiɗan ya tsara zuriyarsa zuwa gwamnatoci dabam-dabam. (Luk 4:5, 6) Amma dai, ƙalilan ne cikin waɗannan gwamnatocin suka yi tsayayya da mutanen Allah, wato, al’ummar Isra’ila da Kiristoci shafaffu. Hakan ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa wahayin Daniyel da Yohanna suka ambata gwamnatoci takwas masu iko ko da yake sun fi takwas.
6 Yesu ya sauko wa da Yohanna wahayi mai ban mamaki kusan shekara dubu biyu da suka shige. (R. Yoh. 1:1) A ɗaya cikin wahayin, Yohanna ya ga Iblis wanda aka nuna kamar babban maciji yana tsaye a bakin teku. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2.) Yohanna ya kuma ga wata irin dabba tana fitowa daga cikin teku. Tana da kawuna bakwai kuma ta karɓi iko sosai daga wurin Iblis. Daga baya, Yohanna ya ga wata dabba ja wur kuma tana da kawuna bakwai. Wannan ita ce gunkin babbar dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 13:1. Wani mala’ika ya gaya wa Yohanna cewa kawuna bakwai na dabbar ja wur tana nufin “sarakuna bakwai” ko gwamnati. (R. Yoh. 13:1, 14, 15; 17:3, 9, 10) Sa’ad da Yohanna ya rubuta littafin Ru’ya ta Yohanna, sarakuna biyar sun riga sun gama mulkinsu, ɗaya ne yake mulki a lokacin kuma ɗayan da ya rage “bai zo ba tukuna.” Su waye ne waɗannan gwamnatocin? Bari mu tattauna kowane cikin waɗannan kawunan dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna. Za mu kuma koyi abubuwa da yawa game da waɗannan gwamnatocin a littafin Daniyel. Annabce-annabcen Daniyel sun ba da bayani dalla-dalla game da wasu gwamnatoci darurruwan shekaru kafin su soma sarauta.
MASAR CE KAI NA FARKO, NA BIYU KUMA ASSURIYA
7. Mene ne kai na farko yake wakilta kuma me ya sa?
7 Kai na farko na dabbar yana wakiltar ƙasar Masar domin ita ce farkon gwamnatin da ta tsani mutanen Allah. Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa shi ne zai haifi zuriyar macen. Kuma Isra’ilawa ’ya’yan Ibrahim ne. Bayan sun ƙaura zuwa ƙasar Masar kuma suka mamaye ƙasar sosai, Masarawa suka soma wulakanta su. Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya halaka mutanen Allah kafin a haifi zuriyar. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen sa Fir’auna ya yi ƙoƙarin kashe dukan ’ya’ya maza na Isra’ilawa. Amma, Jehobah bai ƙyale hakan ya faru ba kuma ya ’yantar da mutanensa daga ƙasar Masar. (Fit. 1:15-20; 14:13) Daga baya, ya sa Isra’ilawa suka gāji Ƙasar Alkawari.
8. Mene ne kai na biyu yake wakilta kuma me ya yi ƙoƙari ya yi?
8 Kai na biyu na dabbar yana wakiltar ƙasar Assuriya. Wannan gwamnati mai iko sosai ta yi ƙoƙarin halaka mutanen Allah. Jehobah ya yi amfani da Assuriyawa don yi wa ƙabila goma na Isra’ila horo. Ya yi hakan domin Isra’ilawa sun bauta wa gumaka kuma sun yi tawaye da Allah. Amma dai, Assuriyawa suka nemi su halaka Urushalima. Wataƙila Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya halaka iyalan sarakai a Urushalima domin ya san cewa Yesu zai fito daga wannan iyalin. Jehobah ba ya son a halaka Urushalima. Saboda haka, ya halaka rundunar Assuriyawa kuma ya cece mutanensa.—2 Sar. 19:32-35; Isha. 10:5, 6, 12-15.
BABILA CE KAI NA UKU
9, 10. (a) Mene ne Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su yi? (b) Mene ne ya kamata ya faru kafin wannan annabcin ya cika?
9 Kai na uku na dabbar da Yohanna ya gani yana wakiltar mulkin Babila. Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su halaka Urushalima kuma ta kai mutanen birnin bauta. Amma, tun kafin hakan ya faru, Jehobah ya riga ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi cewa hakan zai faru. (2 Sar. 20:16-18) Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa ba zai ƙyale sarakansu su zauna a bisa “kursiyin” Jehobah a Urushalima ba. (1 Laba. 29:23) Amma dai, Jehobah ya sake yin alkawari cewa zuriyar Sarki Dauda, wanda yake da isa zai zo ya yi sarauta.—Ezek. 21:25-27.
10 Wani annabci ya nuna cewa Yahudawa za su riƙa yin bauta a haikali na Urushalima sa’ad da Almasihun da aka yi alkawarinsa zai zo. (Dan. 9:24-27) Kuma kafin a kai Isra’ilawa bauta a Babila, wani annabci ya ce za a haifi Almasihu a Bai’talami. (Mi. 5:2) Idan Yahudawa ba su fita daga Babila ba, sun koma ƙasarsu kuma sun sake gina haikalin, wannan annabcin ba zai cika ba. Amma, haram ne Babiloniyawa su saki waɗanda suka kai bauta a ƙasarsu. Yaya mutanen za su iya koma ƙasarsu? Jehobah ya bayyana wa annabawa amsar.—Amos 3:7.
11. A wace hanyoyi dabam-dabam ne aka bayyana sarautar Babila? (Ka duba hasiya.)
11 Annabi Daniyel yana cikin waɗanda aka kama zuwa Babila. (Dan. 1:1-6) Jehobah ya yi amfani da Daniyel don bayyana cewa akwai wasu gwamnatoci da za su yi sarauta bayan Babila. Jehobah ya yi amfani da alamomi da yawa don annabta abin da zai faru. Alal misali, ya sa Sarkin Babila Nebuchadnezzar ya yi mafarkin wani babbar sifa da aka ƙera ta da abubuwa dabam-dabam. (Karanta Daniyel 2:1, 19, 31-38.) Jehobah ya yi amfani da Daniyel don bayyana cewa sifar da ke da kan zinariya tana wakiltar mulkin Babila.b Ƙirjinta da hannuwanta na azurfa suna wakiltar gwamnatin da za ta yi sarauta bayan faɗuwar Babila. Wace ƙasa ce wannan?
MIDIYA DA FARISA NE KAI NA HUƊU
12, 13. (a) Mene ne Jehobah ya bayyana game da yadda za a ci nasara a kan Babila? (b) Me ya sa za mu iya cewa Midiya da Farisa ce kai na huɗu na dabbar?
12 Shekaru da yawa kafin zamanin Daniyel, Jehobah ya bayyana ta bakin annabi Ishaya game da mulkin da zai ci nasara a kan Babila. Jehobah ya bayyana yadda za a ci nasara a kan Babila da kuma sunan wanda zai ja-goranci waɗannan rundunar. Wannan mai ja-gorar shi ne Sairus, sarkin ƙasar Midiya da Farisa. (Isha. 44:28-45:2) Jehobah ya kuma saukar wa da Daniyel wahayi biyu game da mulkin ƙasar Midiya da Farisa. A wahayi na ɗaya, Daniyel ya ga wata dabba mai kama da bear, wadda gefen jikinta ɗaya ya ɗara ɗayan. Kuma an ce za ta cinye nama da yawa. (Dan. 7:5) A wani wahayi dabam, Daniyel ya ga wani rago mai ƙahoni biyu.—Dan. 8:3, 20.
13 Jehobah ya yi amfani da Midiya da Farisa don ta ci nasara a kan Babila kuma Isra’ilawa su samu damar koma ƙasarsu yadda aka annabta. (2 Laba. 36:22, 23) Amma daga baya, Midiya da Farisa ta yi ƙoƙarin ta halaka mutanen Allah. Littafin Esther ya ba da labarin wani minista na ƙasar Farisa mai suna Haman wanda ya yi ƙulle-ƙulle don ya kashe dukan Isra’ilawa da suke wannan Daular. Haman ya zaɓi kwanan wata kuma ya ba mutanensa umurni cewa su kashe dukan Yahudawa. Amma, Jehobah ya hana zuriyar Shaiɗan su halaka mutanen Allah. (Esther 1:1-3; 3:8, 9; 8:3, 9-14) Saboda haka, za mu iya cewa Midiya da Farisa ita ce kai na huɗu na dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna.
HELLAS CE KAI NA BIYAR
14, 15. Waɗanne bayanai ne Jehobah ya ba da game da mulkin ƙasar Hellas na zamanin dā?
14 Kai na biyar na dabbar da aka kwatanta a littafin Ru’ya ta Yohanna yana wakiltar Hellas. A mafarkin da Daniyel ya bayyana wa sarki Nebuchadnezzar, cikin sifar da cinyoyinta na jangaci suna wakiltar Hellas. Jehobah ya saukar wa da Daniyel wasu wahayi biyu da suka bayyana mulkin ƙasar Hellas da kuma sarkinta.
15 A wahayi guda, Daniyel ya ga damisa mai fukafukai biyu. Kuma wannan damisar tana wakiltar ƙasar Hellas wadda za ta hanzarta wajen halaka al’ummai. (Dan. 7:6) A wani wahayi kuma, Daniyel ya ga wani bunsuru mai babbar ƙaho guda. Kuma nan da nan ya kashe wani rago mai ƙaho biyu wanda ke wakiltar ƙasar Midiya da Farisa. Jehobah ya gaya wa Daniyel cewa bunsurun yana wakiltar Hellas kuma babbar ƙahonsa yana wakiltar ɗaya cikin sarakunan ƙasar. Daniyel ya kuma rubuta cewa za a karya ƙahon kuma ƙahoni huɗu za su yi girma maimakon guda. Dukan abin da aka annabta game da wannan ƙasar ta cika ko da yake an rubuta shi shekaru da yawa kafin ƙasar Hellas ta soma sarauta. Iskandari mai girma ne wannan babbar ƙahon. Shi ne sarki mai iko na ƙasar Hellas ta dā kuma ya halaka ƙasar Midiya da Farisa. An karya wannan ƙahon sa’ad da Iskandari ya mutu. A lokacin, shi ɗan shekara 32 ne kuma yana da iko sosai. Bayan mutuwarsa, aka raba mulkinsa wuri huɗu kuma aka ba wa janarorinsa guda huɗu.—Karanta Daniyel 8:20-22.
16. Mene ne Antiochus na Huɗu ya yi?
16 Bayan ƙasar Hellas ta halaka Farisa, sai ta soma mulki a kan Isra’ila. A lokacin Yahudawa suna zama a Ƙasar Alkawari kuma sun sake gina haikalin da ke Urushalima. Suna bauta wa Jehobah kuma yana amince da bauta da suke yi a haikalin da ke Urushalima. Amma, a ƙarni na biyu kafin zamanin Yesu, Hellas ta kai wa mutanen Allah hari. Hakan ya faru sa’ad da Antiochus na Huɗu, wanda ya gaji ɗaya cikin mulkoki huɗu na Iskandari, ya gina bagadi don bautar gunki a haikalin Urushalima. Kuma ya ce a kashe duk wanda bai bauta wa gunkin ba. A wannan lokacin ma, zuriyar Shaiɗan tana gaba da mutanen Allah. Amma, ba da daɗewa ba bayan haka, aka yi wa ƙasar Hellas juyin mulki. Mene ne zai zama kai na shida na dabbar?
ROMA KAI NA SHIDA “MAI-BAN RAZANA, MAI-IKO” NE
17. Yaya ne Farawa 3:15 ya cika a kan kai na shidan?
17 Ƙasar Roma ce take sarauta sa’ad da aka saukar wa da Yohanna wahayin dabbar. (R. Yoh. 17:10) Ƙasar Roma ce kai na shida na dabbar kuma ta cika wani sashe na annabcin da ke littafin Farawa 3:15. Shaiɗan ya yi amfani da ƙasar Roma don ƙuje “duddugen” zuriyar. Romawa sun ɗauki Yesu a matsayin maƙiyi da ke gaba da sarautar ta. Sun hukunta shi kuma sun kashe shi. (Mat. 27:26) Amma, wannan ƙujewar ba ta daɗe ba domin Jehobah ya ta da Yesu daga matattu.
18. (a) Wace sabuwar al’umma ce Jehobah ya zaɓa kuma me ya sa? (b) Me ya sa zuriyar macijin ta ci gaba da yin gaba da zuriyar macen?
18 Shugabannin addinai na Isra’ila sun haɗa baki da ƙasar Roma don su yi gaba da Yesu. Kuma yawancin Isra’ilawa ba su amince cewa Yesu ne Almasihu ba. Dalilin da ya sa Jehobah ya ƙi da Isra’ilawa ke nan. (Mat. 23:38; A. M. 2:22, 23) Daga baya ya zaɓi sabon al’umma, wato, “Isra’ila na Allah.” (Gal. 3:26-29; 6:16) Wannan sabon al’ummar ita ce ikilisiyar Kiristoci shafaffu wadda ta haɗa da Yahudawa da kuma ’Yan Al’ummai. (Afis. 2:11-18) Har bayan Yesu ya mutu ya kuma tashi daga matattu, zuriyar macijin ta ci gaba da yin gaba da zuriyar macen. Ƙasar Roma ta yi ƙoƙari sau da yawa don ta halaka ikilisiyar Kiristoci gabaki ɗaya, wadda ita ce sashe na biyu na zuriyar macen.c
19. (a) Ta yaya Daniyel ya bayyana mulki na shida da zai yi sarauta bisa duniya? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
19 A mafarkin da Daniyel ya bayyana wa sarki Nebuchadnezzar, ƙasar Roma ce take wakiltar ƙafafu na baƙin ƙarfe. (Dan. 2:33) Daniyel ya sake ganin wahayin da ta bayyana Daular Roma da kuma mulkin da zai yi sarauta bayan ita. (Karanta Daniyel 7:7, 8.) A cikin shekaru da yawa, Roma ta zama ƙasa “mai-ban razana, mai-iko, mai-ƙarfi ƙwarai” ga maƙiyan ta. Amma, wannan annabcin ya nuna cewa wannan daular za ta haifar da “ƙaho goma.” Kuma ɗaya cikinsu zai yi girma kuma ya samu iko sosai. Mene ne waɗannan ƙahoni goma kuma wane ne wannan ƙaramin ƙahon? A wace hanya ce babbar sifar da Sarki Nebuchadnezzar ya gani a mafarkinsa take da nasaba da ƙaramin ƙahon? Talifin da ke shafi na 14 zai ba da amsa ga waɗannan tambayoyin.
[Hasiya]
a Wannan macen tana nufin dukan bayin Jehobah da ke sama. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su kamar matar Jehobah.—Isha. 54:1; Gal. 4:26; R. Yoh. 12:1, 2.
b Kan sifar a littafin Daniyel da kuma kai na uku na babbar dabbar a littafin Ru’ya ta Yohanna suna wakiltar Babila. Ka duba taswirar da ke shafuffuka na 12-13.
c Ko da yake ƙasar Roma ta halaka Urushalima a shekara ta 70 a zamanin Yesu, amma wannan halakar ba ta cika annabcin da ke littafin Farawa 3:15 ba. A lokacin, Allah ya riga ya yasar da al’ummar Isra’ila.