Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/1 pp. 12-14
  • Shirya Matasa Su Zama Manya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shirya Matasa Su Zama Manya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙuruciya, Lokaci Mai Muhimmanci a Rayuwar Matasa
  • Hanyoyin Yin Nasara
  • Sa’ad da Ɗanka Matashi Ya Fara Shakkar Addinin da Kake Bi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Tattaunawa da Matasa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Tarbiyyatar da Matasanku don Su Bauta wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/1 pp. 12-14

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Shirya Matasa Su Zama Manya

“A dā ina jin daɗin tattaunawa da yarana. Suna kasa kunne ƙwarai ga abin da nake cewa, kuma suna yin abin da na ce nan da nan. Amma yanzu da suka zama samari, muna yin jayayya bisa komi. Har ba sa son hidimar da muke yi ta bauta. Sukan tambaye ni, ‘Wai dole ne sai mun yi magana game da Littafi Mai Tsarki?’ Kafin ’ya’yana su balaga, ban taɓa yin zaton cewa hakan zai sami iyalina ba, ko da yake na ga hakan ya faru da wasu.”—Reggie.a

KANA da yaro matashi? Idan haka ne, kana ganin abubuwa dabam-dabam masu ban sha’awa yayin da ɗanka ke girma. Kuma yana iya kasancewa mafi wuyan gaske. Kana ganin yanayin da ke gaba?

▪ Sa’ad da ɗanka yake ɗan ƙarami, yana kamar kwalekwalen da aka ɗaure a wurin da jirgin ruwa ke tsayawa, wato, kai. Amma yanzu da ya zama matashi, yana neman ya tsinke igiyar, ya yi tafiyarsa, kuma kana jin kamar baya son ka bi shi.

▪ Sa’ad da ’yarka take ƙarama, takan gaya maka komi. Amma yanzu da ta zama budurwa, ta ƙafa ‘ƙungiya’ da ƙawayenta, kuma ka ji kamar ba a son ka shiga ƙungiya.

Idan irin wannan abu yana faruwa a gidanka, kada ka yi saurin kammala cewa ɗanka ya fara zama gagararre da ba zai gyaru ba. Menene ke damun su? Don amsa wannan tambayar, bari mu duba matsayi na musamman da balaga take da shi sa’ad da ɗanka yake girma.

Ƙuruciya, Lokaci Mai Muhimmanci a Rayuwar Matasa

Tun daga lokacin da aka haife su, duk abin da yara suka yi shi ne na farko a rayuwarsu, wato, soma yin tafiya, magana ta farko da ya yi, ranarsa ta farko a makaranta, da sauransu. Iyaye suna yin farin ciki sa’ad da yaransu suka kai wannan lokacin. Abin da suka cim ma ya nuna alamun abin da suke ɗokin gani, wato, girma.

Ƙuruciya abu ne na musamman, ko da yake wasu iyaye suna shan wahala sosai a wannan lokaci. Tsoron da suke ji daidai ne. Wane uba ko uwa ce za su so su ga ɗansu da ke ba da haɗin kai a dā ya zama marar walwala? Duk da haka, ƙuruciya lokaci ne na musamman sa’ad da aka balaga. A wace hanya?

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa bayan wani lokaci “mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa.” (Farawa 2:24) Amfanin balaga shi ne ya shirya ɗanka ko ’yarka don abubuwan da za su fuskanta a nan gaba, wato masu daɗi da marar daɗi. A lokacin, ɗanka za ya furta waɗannan kalami kamar manzo Bulus: “Sa’anda ina yaro, ni kan yi magana ta ƙuruciya, ni kan ji kamar mai-ƙuruciya, tunanina na ƙuruciya ne: amma yanzu da na zama namiji, na kawarda al’amuran ƙuruciya.”—1 Korintiyawa 13:11.

A ainihi, abin da ɗanku ko ’yarku take yi kenan a lokacin da suke balaga, wato, suna zubar da halayen yara kuma suna koyon halayen da zai sa su zama mutanen da suka san abin da ya kamata, da za su iya yanke shawara da kansu, kuma su soma zaman kansu. Hakika, da baƙin ciki wani littafin bincike ya kwatanta ƙuruciya da yin “doguwar ban kwana.”

Hakika, a yanzu yin tunanin cewa “ƙaramin” ɗanka ko ’yarka za su soma zaman kansu zai iya soma ba ka tsoro. Za ka iya tambaya:

▪ “Ɗana da ya kasa kula da ɗakinsa a yanzu, ta yaya zai kula da gida mai girma?”

▪ “’Yata da ba ta dawowa gida a daidai lokacin da muka ba ta, yaya za ta yi idan ta sami aiki?”

Idan kana fama da irin waɗannan tunanin, ka tuna cewa: ’Yanci ba ɗan ƙaramin abu ba ne, hanya ce da ɗanka ko ’yarka za ta yi shekaru tana bi. A yanzu, daga abubuwan da ka sani, ka san cewa “wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro,” ko yarinya.—Misalai 22:15.

Da ja-gora mai kyau, ɗanka ko ’yarka wataƙila za su girma su zama mutanen da suke yin abin da ya kamata da “hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—Ibraniyawa 5:14.

Hanyoyin Yin Nasara

Don taimaka wa matashi sa’ad da ya manyanta, kana bukatan ka taimake shi ya gina ‘ingancin tunani’ don ya iya yanke shawara mai kyau da kansa.b (Romawa 12:1, 2) Mizanan Littafi Mai Tsarki da ke gaba za su taimake ka ka cim ma hakan.

Filibbiyawa 4:5: “Ku bari jimrewarku ta sanu ga dukan mutane.” Ɗanka matashi ya tambaye ka wani abu, wataƙila yana son ka ba shi ƙarin lokacin yin hira a waje. Sai ka ƙi amincewa. Sai ɗanka matashi ya soma gunaguni, “Kana bi da ni kamar ɗan ƙaramin yaro!” Kafin ka ce, “Ai, kana yi kamar ɗan ƙaramin yaro,” ka yi la’akari da wannan: Matasa sukan nemi a ba su ’yanci fiye da yadda ya kamata, amma wataƙila iyaye sun ƙi su ba su ’yanci yadda ya kamata. Ƙila kana bukatar ka ɗan yi sassauci a lokaci-lokaci. Ya kamata ka ɗan yi la’akari da abin da ɗanka yake bukata.

GWADA WANNAN: Ka rubuta hanyoyi ɗaya ko biyu da za ka iya daɗa wa ɗanka matashi ’yanci. Ka bayyana masa cewa ka ba shi wannan ’yancin ne don ka gwada shi. Idan ya yi amfani da shi yadda ya kamata, a nan gaba za ka daɗa masa. Idan bai yi amfani da shi ba sosai, za ka daɗa yanke ’yancin da ka ba shi.—Matta 25:21.

Kolossiyawa 3:21: “Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa ’ya’yanku, domin kada su karai.”—Littafi Mai Tsarki. Wasu iyaye suna juya yaransu a dukan abin da suke yi fiye da yadda ya kamata. Don su san halayensa da abin da yake yi, suna sa masa ido. Sukan zaɓan masa abokai kuma su saurari dukan wayar da yake yi. Amma irin wannan halin zai iya kawo sakamako marar kyau. Ƙin ba shi ’yanci zai sa ya so ya gudu daga gida; zagin abokansa zai sa ya daɗa so su; saurarar duk wayar da ya samu zai iya tilasta masa ya nemi wasu hanyoyin tattaunawa da abokansa a ɓoye. Yayin da kake ƙoƙarin son juya shi yadda kake so, zai iya bijire maka. Hakika, idan ɗanka matashi bai koyi yadda zai yanke shawara da kansa ba sa’ad da yake gida, yaya zai iya yin hakan idan ya bar gida?

GWADA WANNAN: Sa’ad da kake son ka tattauna da ɗanka matashi a nan gaba, ka sa ya yi tunani a kan yadda shawararsa za ta iya shafansa. Alal misali, maimakon ka suki abokansa, ka ce: “Idan an kama [suna] saboda ya taka doka fa? Wane irin kallo za a yi maka? Ka taimaka wa ɗanka ya ga yadda shawararsa za ta sa ya ƙara yin suna mai kyau ko kuma ya ɓata sunansa.—Misalai 11:17, 22; 20:11.

Afisawa 6:4: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” Ma’anar kalmar nan “gargaɗi” ta wuce bayyana zance kawai. Tana nufin yin abin da zai sa yaron ya samu ɗabi’a mai kyau, kuma hakan ya shafi abubuwan da yake yi. Hakan yana da muhimmanci sosai musamman sa’ad da yaron ya balaga. Wani uba mai suna Andre ya ce, “Yayin da ɗanka yake ƙara girma, kana bukatan ka daidaita yadda kake bi da shi, kuma kana bukatan ka tattauna da shi.”—2 Timotawus 3:14.

GWADA WANNAN: Idan wani abu ya faru, ka sauya matsayinku. Ka tambayi ɗanka shawarar da zai ba ka a ce kai ne ɗansa. Ka sa ya yi bincike don ya samu dalilan da za su sa ya yarda da tunaninsa ko kuma ya ƙi amincewa da shi. Ka sake tattauna batun a cikin mako ɗaya.

Galatiyawa 6:7: “Iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” Za a iya koyar da yaro ta hanyar horo, wataƙila ta korar shi zuwa ɗakinsa ko kuma hana shi yin wani abin da yake sha’awar yi. Ya kamata ka yi tunanin sakamakon abin da matashi ya yi.—Misalai 6:27.

GWADA WANNAN: Kada ka biya basussukan da ake bin shi ko kuma kāre shi a gaban malaminsa game da jarabawa da ya faɗi. Ka ƙyale shi ya ga sakamakon abin da ya yi, ba zai taɓa mance darassin da ya koya ba.

A matsayin iyaye, za ka so lokacin balagar ɗanka har zuwa lokacin da ya manyanta ya kasance marar matsala. Amma dai, hakan ba shi da sauƙi. Duk da haka, lokacin da ɗanka yake ƙuruciya, hakan zai ba ka zarafin koya wa “yaro cikin hanya da za shi bi.” (Misalai 22:6) Mizanan da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne ainihin abin da zai taimaka maka ka samu farin ciki a iyali.

[Hasiya]

a An canja sunan.

b Sa’ad da muka ambata ɗa namiji, mizanan da aka tattauna sun shafi maza da mata.

KA TAMBAYI KANKA . . .

Sa’ad da ɗana ko ɗiyata ya ko ta bar gida, zai iya yin abubuwan da ke gaba?

▪ riƙe tsarin ayyuka na ruhaniya a kullum

▪ yin zaɓi da shawarwari masu kyau

▪ tattaunawa da mutane yadda ya kamata

▪ kula da lafiyar jikinsa

▪ kashe kuɗi yadda ya kamata

▪ tsabtace ɗakinsa ko gidansa

▪ yanke shawara da kansa

[Hotunan da ke shafi na 14]

Idan ɗanka matashi ya nuna hali mai kyau, za ka iya daɗa masa ’yanci?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba