Abubuwan da Ke Kawo Farin Ciki a Iyali
Sa’ad da Ɗanka Matashi Ya Fara Shakkar Addinin da Kake Bi
Sa’ad da suke girma, matasa da yawa sukan rungumi addinin iyayensu. (2 Timotawus 3:14) Amma wasu kuma ba sa yin hakan. Mene ne ya kamata ka yi sa’ad da ɗanka matashi ya fara shakkar addinin da kake bi? Wannan talifin zai tattauna abin da Shaidun Jehobah suke yi sa’ad da hakan ya faru.
“Na gaji da bin addinin iyayena.”—Cora, ’yar shekara 18.a
KA TABBATA cewa addinin da kake bi yana koyar da gaskiya game da Allah. Ka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki yana sa mutane su yi rayuwa mafi inganci. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa kana son ɗanka ya bi addinin da kake bi. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Amma me za ka yi idan ɗanka ya soma sanyin gwiwar bin addininka yayin da yake girma?b Idan ya soma shakkar abubuwan da ya amince da su sa’ad da yake yaro fa?—Galatiyawa 5:7.
Idan hakan ya faru, kada ka kammala cewa ba ka yi aikinka a matsayin mahaifi Kirista ba. Wataƙila akwai wasu dalilan da suka jawo hakan, kamar yadda za mu tattauna a gaba. Amma, ka yi la’akari da wannan: Yadda ka bi da yanayin zai iya sa ɗanka ya bi addinin da kake bi ko kuma ya janye daga bin addinin. Idan ka yi fito-na-fito da ɗanka a kan wannan batun, ba za ka yi nasara ba.—Kolosiyawa 3:21.
Zai dace ka bi gargaɗin da manzo Bulus ya ba da. Bulus ya ce: “Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri.” (2 Timotawus 2:24, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya za ka nuna cewa kai ‘gwani’ ne wajen koyarwa sa’ad da ɗanka matashi ya soma shakkar addinin da kake bi?
Ka Kasance Mai Fahimi
Da farko, ka ƙoƙarta ka fahimci abubuwan da mai yiwuwa suka sa ɗanka matashi ya kasance da irin wannan ra’ayin. Alal misali:
▪ Yana ganin ba shi da abokai ne a cikin ikilisiya? “Na yi abota da ’yan makarantarmu da dama kuma hakan ya sa na yi shekaru ban ƙulla dangantaka da Allah ba. Na daina sha’awar duk wani abin da ke da alaƙa da bautar da nake yi domin sha’anin da na yi da abokan banza, kuma yanzu ina da-na-sani.”—Lenore, ’yar shekara 19.
▪ Yana jin tsoron tattaunawa game da imaninsa ne? “Sa’ad da nake makaranta, ina jin kunyar yi wa abokan ajinmu magana game da imanina. Ina tsoron cewa za su yi mini ba’a kuma su kira ni da sunaye iri-iri. Ana mai da duk wani ɗalibin da halinsa ya bambanta da na sauran, saniyar ware, kuma ba na son hakan ya faru da ni.”—Ramón, ɗan shekara 23.
▪ Yana ganin ba zai iya cika farillai da ke tattare da zama Kirista ba ne? “A ganina, alkawarin da Littafi Mai Tsarki ya yi na yin rayuwa har abada tamkar allura ce a cikin ruwa, kuma samun ta zai yi mini wuya. Tsoron da nake ji na shiga ruwan ne ya sa na yi tunanin daina bin addinin da nake ciki.”—Renee, ’yar shekara 16.
Ka Tattauna da Ɗanka don Ka San Abin da Yake Zuciyarsa
Mene ne wataƙila ya sa ɗanka ya kasance da wannan ra’ayin? Hanya mafi inganci na sanin hakan shi ne ka tambaye shi! Amma ka mai da hankali, kada tattaunawar ta zama gardama. A maimakon haka, ka bi gargaɗin da ke Yaƙub 1:19, wadda ta ce kowane mutum “ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana, ya yi jinkirin yin fushi.” Ka bi shi da haƙuri. Ka yi amfani da “iyakacin jimrewa da koyarwa,” yayin da kake tattaunawa da ɗanka, kamar yadda za ka yi ga wanda ba ya cikin iyalinka.—2 Timotawus 4:2.
Alal misali, idan ɗanka matashi ba ya son zuwa taron Kirista, ka bincika ko akwai wani abin da ke damunsa. Amma ka yi hakan cikin haƙuri. Kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba a tattaunawar da mahaifin da ke gaba ya yi da ɗansa.
Ɗa: Ba na son zuwa taro ne kawai.
Mahaifi: [da fushi] Me kake nufi da ba ka son zuwa taro?
Ɗa: Na gaji ne kawai da zuwa taron!
Mahaifi: Yadda kake ji game da Allah ke nan? Kana nufin ya gundure ka, ko ba haka ba? Kaito! Muddin kana zama tare da mu a gidan nan, ko ka ƙi ko ka so, dole ne ka riƙa zuwa taro tare da mu!
Allah ya umurci iyaye su koya wa yaransu game da shi kuma yara su yi wa iyayensu biyayya. (Afisawa 6:1) Amma ba wai za ka tilasta masa ya riƙa zuwa taron Kirista ba. Amma abin da kake son ya sani shi ne yana bukatar ya riƙa zuwa taron Kirista domin hakan zai taimaka masa kuma zai nuna cewa yana ƙaunar Jehobah.
Za ka iya cim ma hakan idan ka fahimci dalilan da ya sa yake nuna irin waɗannan halayen. Saboda haka, ka lura da yadda mahaifin da aka ambata a baya ya kamata ya bi da yanayin.
Ɗa: Ba na son zuwa taro ne kawai.
Mahaifi: [da hankali] Me ya sa?
Ɗa: Na gaji ne kawai da zuwa taron!
Mahaifi: Zama wuri guda har tsawon awa ɗaya ko biyu zai iya gajiyar da mutum. Wane abu ne game da taron ya zama maka ƙalubale?
Ɗa: Ina ganin kasancewa a wani wuri dabam zai fi dacewa.
Mahaifi: Ra’ayin abokanka ke nan?
Ɗa: Matsalar ke nan! Ba ni da aboki ko guda. Tun lokacin da abokina na kud da kud ya ƙaura, ji nake kamar kome ya zo ƙarshe! Kowa yana harkarsa. An bar ni ni kaɗai!
Domin ya ƙyale ɗansa matashi ya faɗi abin da ke zuciyarsa, mahaifin nan a misali na sama ya gano abin da ke ci ma ɗansa tuwo a ƙwarya, wato, kaɗaici. Ƙari ga haka, dangantakarsu ta zama na kud da kud kuma hakan zai sa yaron ya yi sha’awar tattaunawa da shi a nan gaba.—Ka duba wannan akwatin “Ka Kasance Mai Haƙuri!”
Da shigewar lokaci, matasa da yawa suna shawo kan matsalolin da ke hana su ƙulla dangantaka da Allah. Wannan nasarar tana sa su farin ciki kuma bangaskiyarsu tana ƙara ƙarfi. Ka yi la’akari da Ramón, matashin da aka yi ƙaulinsa ɗazu, wanda yake tsoron bayyana kansa a matsayin Kirista a makaranta. Da sannu sannu, Ramón ya gane cewa bai kamata ya guji yin magana game da imaninsa ba, ko da yin hakan zai sa a yi masa ba’a. Ya ce:
“Akwai ranar da wani yaro a makarantarmu ya yi mini ba’a a kan addinina. Gabana ya faɗi sosai, kuma na lura cewa dukan ’yan ajinmu suna sauraro. Sai na gaya masa ya bayyana nasa imanin. Abin mamaki, sai ya rikice gaba ɗaya! A nan ne na san cewa matasa da yawa suna da addini amma ba su san kome game da addininsu ba. Gara ni, zan iya bayyana imanina. Ashe abokan ajina ne ya kamata su riƙa jin tsoron bayyana imaninsu, ba ni ba!”
KA GWADA WANNAN: Ka tambayi ɗanka matashi yadda yake ji game da zama Kirista don ka san abin da ke zuciyarsa. A nasa ra’ayin, mene ne fa’idar zama Kirista? Waɗanne ƙalubale ne ke tattare da zama Kirista? Shin, fa’idar zama Kirista ya zarce ƙalubalen da ke tattare da hakan ne? Idan haka ne, ta yaya? (Markus 10:29, 30) Ɗanka matashi zai iya rubuta ra’ayinsa a takarda, ya lissafa ƙalubalen a gefen hagu, sa’an nan ya lissafa amfanin a gefen dama na takardar. Wannan lissafin zai iya taimaka wa ɗanka matashi ya san ko mene ne matsalarsa kuma ya san yadda zai magance ta.
Yadda Ɗanka Matashi Yake Amfani da ‘Hankalinsa’
Iyaye da masana sun lura cewa akwai bambanci sosai tsakanin yadda yara ƙanana suke tunani da kuma yadda matasa suke tunani. (1 Korintiyawa 13:11) Yayin da yara suke saurin amincewa da abin da aka gaya musu, matasa kuma sukan bukaci a ba su hujja kafin su amince da wani abu. Alal misali, za ka iya koya wa yaro ƙarami cewa Allah ne ya halicci dukan abubuwa. (Farawa 1:1) Amma matashi zai so ya san amsoshin tambayoyi kamar su: ‘Ta yaya zan san cewa akwai Allah? Me ya sa Allah mai ƙauna ya ƙyale mugunta? Da gaske ne cewa Allah ba ya da mafari?’—Zabura 90:2.
Wataƙila, za ka ga kamar ɗanka matashi bai da bangaskiya domin ya yi waɗannan tambayoyin. Amma a gaskiya, hakan yana nuna ci gaba ne. Balle ma, yin tambayoyi yana da muhimmanci ga Kirista domin hakan zai ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah.—Ayyukan Manzanni 17:2, 3.
Bugu da ƙari, ɗanka matashi yana inganta yadda yake amfani ne da ‘hankalinsa.’ (Misalai 3:21, 22) A sakamakon hakan, zai fahimci ‘fāɗi da ratar da tsawo da zurfin’ imanin Kirista, abubuwan da bai sani ba sa’ad da yake yaro. (Afisawa 3:18) Yanzu ne lokacin da ya kamata ka taimaki ɗanka matashi ya zauna ya yi tunani sosai game da imaninsa domin ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi.—Misalai 14:15; Ayyukan Manzanni 17:11.
KA GWADA WANNAN: Ka sake tattauna muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki da ɗanka matashi, batutuwan da kuke ganin ya riga ya sani. Alal misali, ka sa ya yi tunani a kan tambayoyi kamar su: ‘Wane tabbaci ne nake da shi cewa akwai Allah? Waɗanne abubuwa ne na lura da su da suka tabbatar mini da cewa Allah yana kula da ni? Me ya sa nake ganin cewa zan amfana idan ina kiyaye dokokin Allah?’ Kada ka tilasta wa ɗanka matashi ya bi ra’ayinka. A maimakon haka, ka taimaka masa ya gina bangaskiyarsa. Ta hakan zai gane cewa abubuwan da aka koya masa tun yana yaro gaskiya ne.
An Koyar da Shi Kuma Ya ‘Hakikance’
Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wani matashi mai suna Timotawus wanda aka koya masa nassi mai tsarki tun yana “jariri.” Duk da haka, manzo Bulus ya umurce Timotawus ya ‘lizima kai a cikin al’amuran da ya koya, [“abubuwan da aka tabbatar masa kuma ya gaskata da su,” NW].’ (2 Timotawus 3:14, 15) Kamar yadda aka koyar da Timotawus, mai yiwuwa ka fara koya wa ɗanka matashi ɗabi’un Littafi Mai Tsarki tun yana jariri. Amma yanzu, kana bukatar ka shawo kansa don ya amince cewa abubuwan da yake koya gaskiya ne.
Littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1, ya bayyana cewa: “Muddin ɗanka matashi yana zama a cikin gidanka, kana da ikon gaya masa cewa wajibi ne ya yi bauta iri ɗaya da kai.” A ƙarshe abin da ya fi muhimmanci shi ne ka sa ɗanka matashi ya so Allah ƙwarai, ba wai ya riƙa nuna cewa yana yin hakan amma ƙaunar ba ta kai zuciyarsa ba. Idan ka bi wannan umurnin, za ka iya taimaka wa ɗanka matashi ya ‘dage kan bangaskiyarsa,’ kuma yin rayuwa a matsayin Kirista zai zama zaɓinsa ba naka ba.c—1 Bitrus 5:9.
[Hasiya]
a An canja sunaye a wannan talifin.
b Domin sauƙin karatu, mun yi amfani da ɗa namiji a wannan talifin. Amma ƙa’idodin da aka tattauna sun shafi matasa maza da mata.
c Don ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro na Yuli-Satumba 2009, shafuffuka na 12-14, da kuma Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1, shafuffuka na 315-318.
KA TAMBAYI KANKA . . .
▪ Sa’ad da ɗana ya nuna yana shakkar imanina, yaya nake bi da al’amarin?
▪ Ta yaya zan yi amfani da batun da aka tattauna a wannan talifin don in inganta yadda nake bi da wannan yanayin?
[Akwati da ke shafi na 19]
Yaudara ce?
Ƙage: Shaidun Jehobah suna tilasta wa yaransu su bi addininsu.
Gaskiya: Shaidun Jehobah suna ƙoƙarin su koya wa yaransu yadda za su so Allah ƙwarai, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya umurce su. (Afisawa 6:4) Duk da haka, sun san cewa sa’ad da yaro ya girma, zai yanke wa kansa shawarar ko zai bauta wa Allah ko a’a.—Romawa 14:12; Galatiyawa 6:5.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 20]
Ka Kasance Mai Haƙuri!
Kana bukatar ka kasance da haƙuri sosai sa’ad da kake tattaunawa da ɗanka matashi. Hakan yana da amfani sosai, domin ɗanka zai fara gaya maka abin da ke damunsa. Wata matashiya ta ce: “A wata hirar da na yi da mahaifina da dare, na gaya masa cewa na buɗe dandalin hira da mutane a intane kuma ina da saurayi a ɓoye, kuma ina shirin shiga dandi. Na gaya masa cewa na sumbace saurayin kuma ina tura masa saƙo ta waya a kai a kai. Amma maimakon ya hasala, ya tattauna batun da ni cikin natsuwa! Ina gani, zan iya gaya wa babana duk wani abin da ke damuna. Na san cewa yana so ya taimake ni ƙwarai.”
[Akwati da ke shafi na 21]
Amfanin Samun Mashawarci
A wani lokaci ɗanka matashi zai amfana sosai idan wani wanda ya san ciwon kansa yana ba shi shawara. Ka san wani wanda yake da dangantaka mai kyau da Jehobah da zai iya ba ɗanka matashi shawarwari masu kyau? Me zai hana ka gayyace shi domin ya tattauna da ɗanka? Manufarka ba ta nufin cewa kana ƙaurace wa matsayinka na mahaifi ba. Ka yi la’akari da yanayin Timotawus. Ya amfana sosai daga yin cuɗanya da Bulus, kuma Bulus ma ya amfana sosai daga yin abota da Timotawus.—Filibiyawa 2:20, 22.d
[Hasiya]
d Daga wannan littafin Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1, fitowar shekara ta 2011, shafi na 318, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.