Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/15 pp. 17-21
  • Iyaye, Ku Kula da Yaranku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyaye, Ku Kula da Yaranku
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU SAN YARANKU DA KYAU
  • KU KOYAR DA YARANKU
  • KU JA-GORANCI YARANKU
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/15 pp. 17-21

Iyaye Ku Kula da Yaranku

‘Ka yi anniya ka [san] da irin zaman garkenka.’—MIS. 27:23.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya iyaye za su zama kamar makiyaya?

  • Mene ne zai taimaka wa iyaye su koyar da yaransu game da Allah?

  • Ta yaya matasa da yawa suka amfana daga ibada ta iyali?

1, 2. (a) Waɗanne irin ayyuka ne makiyaya a Isra’ila ta dā suke yi? (b) Ta yaya iyaye suke kamar makiyaya?

AIKIN makiyaya a ƙasar Isra’ila ta dā yana da wuya sosai. Sukan jimre zafin rana da kuma sanyi. Ƙari ga haka, sukan kāre garken daga mugayen mutane da kuma wasu dabbobi. Makiyaya sukan bincika tumakinsu kullum kuma su yi jinyar marasa lafiya ko kuma raunannu da ke cikinsu. Sukan kula da ’ya’yan tumaki sosai don ba su da ƙarfi kamar tumakin da suka girma.—Far. 33:13.

2 Ya kamata iyaye Kiristoci su kasance da halaye irin na makiyaya. Su ne ke da hakkin rainon ’ya’yansu “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Shin wannan aikin yana da sauƙi ne? Ko kaɗan! Yara suna kokawa da miyagun ra’ayoyi da duniyar nan take yaɗawa. Ƙari ga haka, suna fama da ajizancinsu. (2 Tim. 2:22; 1 Yoh. 2:16) Idan kuna da yara, ta yaya za ku taimake su? Bari mu tattauna abubuwa uku da za ku iya yi don ku kula da yaranku: Ku san su da kyau, ku koyar da su, kuma ku ja-gorance su.

KU SAN YARANKU DA KYAU

3. Mene ne ma’anar furucin nan iyaye su san da ‘irin zaman’ yaransu?

3 Makiyayi mai kyau yana binciken kowace tunkiya don ya tabbata cewa tana da cikakken lafiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ka yi anniya ka [san] da irin zaman garkenka.’ (Mis. 27:23) A matsayin iyaye, ya kamata ku san ‘garkenku,’ wato yaranku da kyau. Hakan yana nufin cewa wajibi ne ku mai da hankali ga abin da yaranku suke aikatawa da tunaninsu da kuma ra’ayinsu. Ta yaya za ku cim ma hakan? Tattaunawa da yaranku a kowane lokaci zai taimaka sosai.

4, 5. (a) Waɗanne shawarwari ne za su iya sa yara su bayyana ra’ayinsu ga iyayensu? (Ka duba hoton da ke shafi na 17.) (b) Waɗanne matakai kuka ɗauka don yaranku su bayyana maku ra’ayinsu hankali kwance?

4 Wasu iyaye sun lura cewa tattaunawa da yaransu yana ƙara kasancewa da wuya sa’ad da yaran suka zama matasa. A lokacin, yaran ba za su so su bayyana ra’ayinsu ko yadda suke ji ba. Idan haka ne yaranku suke, shin mene ne za ku iya yi? Ku yi ƙoƙarin tattaunawa da su sa’ad da hankalinsu ke kwance maimakon ku nace kuna doguwar tattaunawa da su. (K. Sha 6:6, 7) Ku shirya don ku yi wasu hidimomi tare. Za ku iya fita yawo da kafa ko kuma da mota, ko ku yi wasa ko kuma wani aiki a gida. Irin waɗannan yanayin zai iya sa su saki jiki kuma za su so su bayyana ra’ayinsu.

5 Idan har ila ɗanku ko ’yarku ba ta son bayyana ra’ayinta fa? Ku yi amfani da wata dabara dabam. Alal misali, maimakon ku tambaye ta abin da ta yi a ranar, za ku iya gaya mata hidimomin da kuka yi. Hakan zai iya sa ta faɗi abubuwan da ta yi a ranar. Idan kuma kuna so ku san ko mene ne ra’ayin ’yarku game da wani batu, ku yi tambaya game da batun, ba game da ita ba. Za ku iya tambayar ta ko mene ne ra’ayin abokanta game da wani batu. Bayan haka, sai ku tambaye ta irin shawarar da za ta so ta ba su.

6. Ta yaya yaranku za su san cewa kuna marmarin jin ra’ayinsu kuma ba ku saurin fushi?

6 Wajibi ne yaranku su san cewa kuna da lokacinsu kuma za ku saurare su ba tare da kun tsauta musu ba. Idan yara suna gani cewa ba ku da lokacin sauraronsu, matasa ba za su so su faɗi abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya ba. Mene ne za ku yi don yaran su yi marmarin bayyana ra’ayinsu? Maimakon ku riƙa cewa: “Za ka iya tuntuɓa na a duk lokacin da kake da damuwa.” Ya kamata yaranku su san cewa kun ɗauki matsalolinsu da muhimmanci kuma ba za ku yi saurin fushi sa’ad da suka faɗa maku ba. Iyaye da dama sun kafa misali mai kyau a wannan fannin. Kayla, mai shekara sha tara ta ce: “Zan iya tattaunawa da mahaifina game da kome. Shi ba mai katse mini magana ko kuma mai yin mugun zato ba, zai saurara kawai. Yana kuma ba ni shawara mai kyau a kowane lokaci.”

7. (a) Wane ra’ayin da ya dace ne zai taimaka wa iyaye su tattauna batu kamar fita zance da yaransu? (b) Ta yaya iyaye za su iya ɓata ran yaransu cikin rashin sani?

7 Sa’ad da kuke magana game da batutuwa masu wuyan bayyanawa da yaranku kamar fita zance, kada ku riƙa yawan yi musu gargaɗi don hakan zai hana su koyan yadda ya kamata su bi da batun. Alal misali: A ce kun je gidan abinci kuma kun karanta cewa abincin zai iya sa ku ciwon ciki. Wataƙila za ku bar wajen kuma ku nemi wani gidan abinci. Hakazalika, yaranku za su guje ku idan kuna yawan tsauta musu a duk lokacin da suka zo wurinku. (Karanta Kolosiyawa 3:21.) A maimakon haka, ku kasance da daidaitaccen ra’ayi. Wata matashiya mai suna Emily ta ce: “Sa’ad da iyayena suke tattauna batun fita zance da ni, ba sa sa in ji kamar yin hakan laifi ne. Suna mai da hankali ga farin cikin da ke tattare fita zance da kuma samun abokin aure. Hakan ya sa ina sake jiki sa’ad da nake magana da su game da batun. Saboda haka, ina gaya musu game da saurayin da nake da shi.”

8, 9. (a) Mene ne amfanin sauraron yaranku ba tare da kun katse musu magana ba? (b) Wane albarka kun taɓa samu sa’ad da kuka saurari yaranku da kyau?

8 Kamar yadda Kayla ta ce, za ku iya nuna cewa kuna da sauƙin kai ta wajen sauraron yaranku da haƙuri. (Karanta Yaƙub 1:19.) Wata mahaifiya da take rainon ’yarta ita kaɗai ta ce: “A dā, ba na haƙuri da ’yata. Nakan katse mata magana don gajiya ko don ba na son a dame ni. Yanzu da na canja halina, ’yata ma ta canja nata. Tana ba ni haɗin kai.”

9 Hakan ya taɓa faruwa tsakanin wani mahaifi mai suna Ronald da ’yarsa matashiya. Ya ce: “Sa’ad da ta gaya mini tana son wani yaro da ke makarantarsu, na yi fushi sosai. Amma da na tuna da yadda Jehobah yake haƙuri da bayinsa, sai na yi tunani cewa zai dace in bar ’yata ta bayyana ra’ayinta kafin in ba ta shawara. Abin da na yi ke nan kuma a lokacin ne na fahimci ainihi abin da ke zuciyarta. Sa’ad da ta gama bayani, sai na ba ta shawara cikin ƙauna. Abin mamaki, ta bi shawarar da na ba ta kuma ta ce za ta canja halinta.” Tattaunawa da yaranku a kowane lokaci zai sa ku fahimci tunaninsu da kuma yadda suke ji. A sakamakon haka, shawarwarin da kuke ba su za su yi tasiri a rayuwarsu.a

KU KOYAR DA YARANKU

10, 11. Me za ku iya yi don kada yaranku su bauɗe daga gaskiya?

10 Makiyayi mai kyau ya san cewa tunkiya za ta iya bauɗewa daga garken. Hakan zai iya faruwa idan ta soma cin ciyawa da ke ɗan nesa kuma da sannu-sannu ta ware kanta. Hakazalika, yaro zai iya bauɗewa kuma ya bi tafarkin da zai ɓata dangantakarsa da Jehobah saboda abokan banza ko kuma mugun nishaɗi. (Mis. 13:20) Ta yaya za ku taimaka don kada irin wannan abin ya faru?

11 Sa’ad da kuke koyar da yaranku kuma kuka gano cewa suna bukatar taimako a wasu fannonin rayuwa, ku yi aiki tuƙuru don ku inganta halayensu masu kyau. (2 Bit. 1:5-8) Ibada ta iyali da ake yi a kai a kai za ta taimaka musu sosai su yi hakan. An bayyana a cikin Hidimarmu ta Mulki ta Janairu 2011 cewa dalili ɗaya da ya sa aka tsara shirin ibada ta iyali shi ne a “ba iyalai zarafin ƙarfafa [dangantakarsu da Allah] ta wajen keɓe wani yamma a kowane mako don bauta ta iyali.” Shin kuna amfani da wannan zarafin don ku koyar da yaranku? Ku tabbata cewa yaranku suna godiya sosai domin kuna taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah.—Mat. 5:3; Filib. 1:10.

12. (a) Ta yaya matasa suka amfana daga ibada ta iyali da ake gudanarwa a kai a kai? (Ka kuma duba akwatin nan “Suna Godiya.”) (b) Ta yaya ka amfana daga ibada ta iyali?

12 Ku yi la’akari da abin da wata matashiya mai suna Carissa ta ce game da yadda Ibada ta Iyali ta amfane su. Ta ce: “Ina sha’awar yadda muke zama tare don mu tattauna batutuwa dabam-dabam. Hakan yana sa mu farin ciki kuma muna ƙarfafa dangantakarmu da juna. Mahaifinmu ba ya fasa gudanar da Ibada ta Iyali. Yana ɗaukan ta da muhimmanci kuma hakan yana da kyau don ya sa mu ma muna ɗaukan ta da muhimmanci. Ƙari ga haka, yana sa in girmama shi a matsayin mahaifina da kuma mai ƙarfafa dangantakata da Allah.” Wata ’yar’uwa mai suna Brittney ta ce: “Ibada ta iyali ta sa na kusaci iyayena. Ta sa na san cewa suna ƙaunata kuma suna so su san matsalolin da nake fuskanta. Tana taimaka ma iyalinmu ta kasance da ƙauna da kuma haɗin kai.” Babu shakka, koyar da iyalinku game da Allah, musamman ma ta ibada ta iyali, hanya ce mai kyau na kasancewa makiyayi mai kyau.b

KU JA-GORANCI YARANKU

13. Ta yaya za a iya taimaka wa yaro ya bauta wa Jehobah?

13 Makiyayi mai kyau yakan yi amfani da sandarsa don ya ja-goranci da kuma kāre garkensa. Dalili na musamman da ya sa yake yin haka shi ne don ya kai garken “wuri mai-albarka.” (Ezek. 34:13, 14) Shin wannan shi ne maƙasudinku a matsayin iyaye? Aniyarku ita ce ku ja-goranci yaranku don su bauta wa Jehobah. Kuna son yaranku su kasance da irin ra’ayin wani marubucin zabura da ya ce: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” (Zab. 40:8) Idan yaranku sun kasance da irin wannan ra’ayin, hakan zai motsa su su tsai da shawarar bauta wa Jehobah kuma su yi baftisma. Ya kamata su ɗauki wannan matakin sa’ad da suka isa su tsai da wannan shawarar kuma suna son su bauta wa Jehobah daga zuciyarsu.

14, 15. (a) Mene ne ya kamata ya zama muradin iyaye Kirista? (b) Me zai iya sa matashi ya yi shakkar bin gaskiya?

14 Idan yaranku ba sa son kyautata dangantakarsu da Jehobah ko kuma ba su amince cewa bautar Jehobah ita ce gaskiya ba fa? Ku yi ƙoƙari ku sa su ƙaunaci Jehobah Allah kuma su nuna godiya ga dukan abubuwan da ya yi. (R. Yoh. 4:11) Hakan zai sa su tsai da shawarar bauta wa Jehobah idan sun shirya.

15 Amma a yanzu, idan yaranku suna shakka fa? Ta yaya za ku iya ja-gorarsu kuma ku taimaka musu su tabbata cewa bauta wa Jehobah ita ce mataki mafi kyau da zai sa su yi farin ciki har abada? Ku yi ƙoƙarin sanin abin da ya sa suke shakka. Alal misali, shin ɗanku ko ’yarku ba ta amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne ko kuma tana tsoron bayyana imaninta a gaban tsararta ne? Shin ’yarku ba ta tabbata cewa bin ƙa’idodin Allah yana da amfani ba ne, ko kuma tana fama da kaɗaici da kuma rashin amincewar wasu ne?

16, 17. A waɗanne hanyoyi ne iyaye za su iya taimaka wa yaransu su yanke shawarar bauta wa Jehobah?

16 Ko da mene ne ya sa suke shakkar gaskiya, za ku iya taimaka wa ɗanku ya shawo kan hakan. Ta yaya? Wata shawara da ta taimaka wa iyaye da yawa ita ce yin ƙoƙarin sanin abin da ke zuciyarsu ta wajen yi musu tambayoyi kamar su: “Mene ne ra’ayinka game da matsayinka na Kirista? A ganinka, mene ne amfanin zama Kirista? Waɗanne hakkoki ke tattare da zama Kirista? Shin kana ganin amfanin da muke mora yanzu da waɗanda za mu mora a nan gaba sun fi hakkokin yawa ne? Ka bayyana.” Zai dace ku yi waɗannan tambayoyin a hankali kuma a hanya mai ban sha’awa, ba kamar kuna yi masa tuhuma ba. Sa’ad da kuke tattaunawar, za ku iya yin magana a kan Markus 10:29, 30. Wasu matasa za su so su rubuta ra’ayinsu a cikin sashe biyu, na farkon game da amfanin zama Kirista, na biyun kuma game da hakkokin da ke tattare da hakan. Rubuta jerin a kan takarda zai taimaka musu su san matsalolinsu da kuma yadda za su magance su. Idan har muna bukatar yin amfani da littattafan nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” wajen yin nazari da mutane a waje, yana da muhimmanci sosai mu yi hakan da yaranmu! Shin kuna yin hakan kuwa?

17 Yayin da yaranku suka girma, su ne da kansu za su yanke shawara game da ko za su bauta wa Jehobah. Kada ku ɗauka cewa don kun zaɓi ku bauta wa Jehobah, su ma za su yi hakan. Wajibi ne yaranku su yanke wannan shawarar da kansu. (Mis. 3:1, 2) Idan ƙulla dangantaka da Jehobah yana wa ɗanku ko ’yarku wuya, ku ƙarfafa ta ta yi wa kanta waɗannan tambayoyin: “Ta yaya na san cewa akwai Allah? Me ya tabbatar mini cewa Jehobah yana gani na da mutunci? Me ya sa na gaskata cewa ƙa’idodin Jehobah za su amfane ni?” Ku nuna cewa ku makiyayi mai kyau ne ta wajen ja-gorar ɗanku ko yaranku a hankali don su tabbata cewa bauta wa Jehobah ce abu mafi kyau.c—Rom. 12:2.

18. Ta yaya iyaye za su yi koyi da Babban Makiyayinmu Jehobah?

18 Burin dukan Kiristoci ne su yi koyi da Jehobah, Babban Makiyayi. (Afis. 5:1; 1 Bit. 2:25) Ya kamata iyaye musamman su san garkensu, wato yaransu da kyau kuma su yi iya ƙoƙarinsu wajen yi musu ja-gora don su mori abubuwan da Jehobah ya shirya musu. Saboda haka, ku kula da yaranku ta wajen ci gaba da rainon su a hanyar gaskiya!

a Za ka sami ƙarin shawarwari a Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba 2008, shafuffuka na 14-16.

b Don ƙarin bayani, ka duba wannan talifi mai jigo: “Bauta ta Iyali Tana da Muhimmanci don Tsira!” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2009, shafuffuka na 29-31.

c An ƙara tattauna wannan sashen a Hasumiyar Tsaro ta Afrilu-Yuni 2012, shafuffuka na 18-21.

SUNA GODIYA

Ka yi la’akari da kalaman matasa biyu da suka amfana daga ibada ta iyali.

“Ibada ta Iyali da ake yi da yamma yana sa ka kusaci waɗanda ke cikin iyali da kuma Jehobah. Za ka koyi abubuwa da yawa game da kanka da kuma dangantakarka da Jehobah. Tana sa ka san wuraren da kake bukata ka yi gyara.”

“Ibada ta iyali tana ba mu zarafin bayyana ra’ayinmu hankali kwance. Lokaci ne da muke mantawa da matsalolin yau da kullum kuma mu mai da hankali ga dangantakarmu da Jehobah. A dā ba ma yin wannan ibadar, amma yanzu muna yin ta. Hakan ba ƙaramar albarka ba ce!”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba