Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 5/15 pp. 6-8
  • Ina Ya Kamata Ka Kasance Sa’ad da Ƙarshe Ya Zo?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ina Ya Kamata Ka Kasance Sa’ad da Ƙarshe Ya Zo?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Wuri Yake da Muhimmanci
  • A Koyaushe ne Wuri Yake da Muhimmanci?
  • Menene Ya Fi Muhimmanci?
  • “Ku Shiga Cikin Ɗakunanku”
  • Rahab Ta Ba da Gaskiya ga Jehovah
    Ku Koyar da Yaranku
  • Rahab Ta Boye ʼYan Leken Asiri
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Rahab ta Saurari Labarin
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Rahab Ta Ɓoye ’Yan Leƙen Asiri
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 5/15 pp. 6-8

Ina Ya Kamata Ka Kasance Sa’ad da Ƙarshe Ya Zo?

SA’AD da Jehobah zai kawo ƙarshen wannan mugun zamani a Armageddon, menene zai sami mutane masu adalci? Misalai 2:21, 22 ta ba da amsar: “Masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”

Ta yaya kamilai za su wanzu cikin duniya? Za a samo musu mafaka ne? Ina ne ya kamata masu adalci su kasance sa’ad da ƙarshen zai zo? Labarai guda huɗu da ke cikin na waɗanda suka tsira sun ba da ƙarin haske a kan waɗannan batutuwa.

Sa’ad da Wuri Yake da Muhimmanci

Game da ceton Nuhu da Lutu a zamanin dā, 2 Bitrus 2:5-7 ta ce: “[Allah] ba ya kuwa keɓe duniya ta dā ba, amma ya ceci Nuhu mai-shelan adalci, tare da waɗansu bakwai, sa’anda ya kawo rigyawa bisa duniya ta masu-fajirci;ya maida biranen Saduma da Gamurata toka, yana yi musu hukunci da kaɓantuwa, hakanan yana maishe su abin nuni ga waɗanda za su yi zaman fajirci; ya kuma ceci Lutu adalin, sa’anda ransa ya ɓaci ƙwarai domin zaƙuwa ta masu-mugunta.”

Ta yaya Nuhu ya tsira daga Rigyawa? Allah ya gaya wa Nuhu: “Matuƙar dukan abu mai-rai a garemu ta yi; gama duniya cike ta ke da zalunci ta wurinsu; ga shi kuwa, zan hallaka su tare da duniya. Sai ka yi jirgi na itacen jufra.” (Far. 6:13, 14) Nuhu ya gina jirgin kamar yadda Jehobah ya umurce shi. Kwana bakwai kafin a soma ruwan rigyawar, Jehobah ya umurce Nuhu ya shigar da dukan dabbobi cikin jirgin kuma shi da iyalinsa duka su shiga. Aka rufe ƙofar a rana na bakwai, “ruwa kuma yana nan ana yi duniya yini arba’in da dare arba’in.” (Far. 7:1-4, 11, 12, 16) Nuhu da iyalinsa “suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bit. 3:20) Suna bukatar su kasance a cikin jirgin idan suna so su tsira. Babu wani wuri a duniya da za su iya samun mafaka.—Far. 7:19, 20.

A batun Lutu kuwa, umurnin ya ɗan bambanta. Mala’iku biyu sun gaya masa wurin da bai zai zauna ba. Mala’ikun biyu sun gaya wa Lutu: “Wanda ka ke da shi duka cikin birni [na Saduma] kuma; ka fitarda su daga wurin nan, gama hallaka wurin nan za mu yi.” Suna bukatar su “tsira zuwa dutse.”—Far. 19:12, 13, 17.

Abubuwa da suka faru da Nuhu da Lutu sun nuna cewa “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba, ya tsare marasa-adalci kuma ƙalƙashin hukunci har zuwa ranar shari’a.” (2 Bit. 2:9) Tsirarsu ta dangana ne a kan inda suke. Nuhu ya shiga cikin jirgi, Lutu kuma ya fita ya bar Saduma. Amma hakan ne abubuwa suke faruwa a koyaushe? Jehobah zai iya ceton masu adalci ne a duk inda suke, ba tare da sun bar wurin ba? Don a amsa wannan tambayar, yi la’akari wasu labarai guda biyu na tsira.

A Koyaushe ne Wuri Yake da Muhimmanci?

Kafin Jehobah ya halaka Masar ta wurin kawo annoba goma a zamanin Musa, Ya umurci Isra’ilawa su fantsama jinin dabbar Idin Ketarewa a doki da dogarar ƙofofin gidajensu. Me ya sa? Domin ‘sa’ad da Ubangiji za ya ratsa ta tsakiya domin ya buga Masarawa; amma ya ga jinin a bisa dokin ƙofa da bisa dogaran ƙofa biyu, za ya ƙetare wannan ƙofa, ba kuwa za ya bar mai halakarwa ya shiga cikin gidajensu garin ya buge su ba.’ A wannan daren, “Ubangiji ya bugi dukan ’ya’yan fāri cikin ƙasar Masar, daga ɗan fāri na Fir’auna da ke zaune bisa kursiyinsa, zuwa ɗan fāri na ɗamrarren da ke cikin kurkuku; da dukan ’ya’yan fāri na bisashe.” An ceci ’ya’yan fari na Isra’ilawa ba tare da sun ƙaura ba.—Fit. 12:22, 23, 29.

Ka yi la’akari kuma da batun Rahab, ƙaruwar da ke zaune a birnin Yariko. Isra’ilawa suna gab da soma cin nasararsu na Ƙasar Alkawari. Sa’ad da Rahab ta fahimci cewa za a halaka Yariko, ta gaya wa ’yan leƙen asiri na Isra’ila cewa mutanen birnin suna jin tsoron Isra’ilawa. Ta ɓoye ’yan leƙen asiri kuma ta gaya musu su rantse cewa za a ceci ta da dukan iyalinta sa’ad da suka kame Yariko. ’Yan leƙen asiri sun umurci Rahab ta tara iyalinta cikin gidanta da ke jikin garun birnin. Idan suka bar gidan za a halaka su da sauran mutanen birnin. (Josh. 2:8-13, 15, 18, 19) Amma, daga baya Jehobah ya gaya wa Joshua cewa “ganuwar birni kuma za ya abka.” (Josh. 6:5) Wurin da ’yan leƙen asiri suke gani kamar wurin mafaka ce yanzu kamar tana cikin haɗari. Ta yaya za a ceci Rahab da iyalinta?

Sa’ad da lokaci ya kai da za a ci Yariko, Isra’ilawa suka yi kururruwa kuma suka busa ƙahoni. Joshua 6:20 ta ce: “Ya zama kuwa, yayinda mutane [na Isra’ila] suka ji ƙarar ƙafo, suka yi ihu da babbar ƙara, ganuwa ta abka sarai a wurin, har mutane suka hau sosai cikin birni, kowane mutum sosai a gabansa, suka ci birnin.” Babu ɗan adam da zai iya hana ganuwar faɗuwa. Amma ta mu’ujiza, faɗuwar ganuwar birnin ta tsaya a gidan Rahab. Joshua ya umurci ’yan leƙen asirin guda biyu: “Ku shiga cikin gidan macen nan karuwa, daga ciki kuma a fito da ita macen, da abin da ke gareta duka, kamar yadda kuka rantse mata.” (Josh. 6:22) An ceci dukan waɗanda suke cikin gidan Rahab.

Menene Ya Fi Muhimmanci?

Menene za mu iya koya daga ceton Nuhu, Lutu, Isra’ilawan da ke zamanin Musa da kuma Rahab? Ta yaya ne waɗannan labaran za su taimake mu mu san inda ya kamata mu kasance sa’ad da ƙarshen wannan zamanin zai zo?

Hakika, Nuhu ya samu ceto a cikin jirgi. Amma, me ya sa yake wurin? Domin yana da bangaskiya ne kuma ya yi biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuwa Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.” (Far. 6:22; Ibran. 11:7) Mu kuma fa? Muna yin dukan abin da Allah ya ce mu yi? Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (2 Bit. 2:5) Muna da himma a aikin wa’azi kamar Nuhu, ko da mutane ba sa son su saurare mu?

Lutu, ya tsira daga halaka ta wajen guduwa daga Saduma. Ya tsira domin shi adali ne a gaban Allah kuma ya yi baƙin ciki ƙwarai don lalatar kangararrun mutanen Saduma da Gwamrata. Lalata da ke ko’ina a duniya a yau tana baƙanta ranka kuwa? Ko kuwa mun saba da ganinta da hakan ya sa ba ta damun mu kuma? Muna yin iya ƙoƙarinmu don mu kasance “cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi”?—2 Bit. 3:14.

Isra’ilawan da ke ƙasar Masar da kuma Rahab da ke birnin Yariko, suna bukatar su kasance a cikin gidansu idan suna son su sami ceto. Hakan na bukatar bangaskiya da kuma biyayya. (Ibran. 11:28, 30, 31) Ka yi tunanin yadda kowace iyalin Baisra’ila za ta riƙa kallon ɗansu na fari sa’ad da ake “kuka mai-zafi” a kowace iyalin Masarawa. (Fit. 12:30) Ka yi tunanin yadda Rahab ta riƙe iyalinta gam sa’ad da take jin faɗuwar ganuwar Yariko take daɗa kusato inda suke. Tana bukatar bangaskiya sosai don ta yi biyayya kuma ta zauna a cikin wannan gidan.

Ba da daɗewa ba, ƙarshen muguwar duniya ta Shaiɗan za ta zo. Ba mu san yadda Jehobah zai kāre mutanensa a ‘ranar fushinsa’ mai ban tsaro ba. (Zeph. 2:3) Amma, duk inda muke da kuma yanayinmu a lokacin, muna da tabbaci cewa za mu tsira idan mun kasance da bangaskiya ga Jehobah kuma muka yi masa biyayya. Kafin lokacin, ya kamata mu kasance da halin da ya dace game da abin da annabcin Ishaya ya kira ‘ɗakunanmu.’

“Ku Shiga Cikin Ɗakunanku”

Ishaya 26:20 ta ce: “Ku zo, mutanena, ku shiga cikin ɗakunanku, ku rufe ma kanku ƙofofi: ku ɓuya kaɗan, har fushin ya wuce.” Mai yiwuwa wannan annabcin ya samu cikarsa ta farko a shekara ta 539 K.Z., sa’ad da mutanen Midiya da Pasiyawa suka kame ƙasar Babila. Sa’ad da suka shiga Babila, Sairus ɗan Pasiya ya ba da umurni cewa kada kowa ya fita waje domin an ba sojojinsa umurni su kashe kowa da suka samu a waje.

A zamaninmu, za a iya haɗa ‘ɗakuna’ na wannan annabci da fiye da ikilisiyoyi 100,000 na Shaidun Jehobah a dukan duniya. Irin waɗannan ikilisiyoyi suna da matsayi mai muhimmanci a rayuwarmu. Za su ci gaba da yin hakan a dukan “babban tsananin.” (R. Yoh. 7:14) An umurci mutanen Allah su shiga cikin ‘ɗakunansu’ kuma su ɓoye kansu “har fushin ya wuce.” Yana da muhimmanci mu koya kuma kasance da hali mai kyau game da ikilisiya kuma mu tsai da shawarar yin tarayya na kud da kud da ita. Muna iya sa gargaɗin Bulus a zuciya: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.”—Ibran. 10:24, 25.

[Hotunan da ke shafi na 7]

Menene za mu iya koya daga ayyukan ceto na dā na Allah?

[Hotunan da ke shafi na 8]

Da me za a haɗa ‘ɗakuna’ a zamaninmu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba