Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 6/15 pp. 11-15
  • Ku Zama “Masu-himman Nagargarun Ayyuka”!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Zama “Masu-himman Nagargarun Ayyuka”!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Himma ga Wa’azi da Koyarwa
  • Matasa da Suke Hidima da Himma
  • Ka Yi Biyayya ga Gargaɗi da Himma
  • Amfanin Halin Kirki
  • Ka Kasance Da Himma Don Bautar Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kana Da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kana Amfani da Abubuwan da Aka Rubuta Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 6/15 pp. 11-15

Ku Zama “Masu-himman Nagargarun Ayyuka”!

“[Yesu] ya bada kansa dominmu, domin shi fanshe mu daga dukan zunubi, shi tsarkake wa kansa jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.”—TIT. 2:14.

1. Menene ya faru a haikali sa’ad da Yesu ya isa wajen a ranar 10 ga Nisan, a shekara ta 33 A.Z.?

ARANAR 10 ga Nisan a shekara ta 33 A.Z., kwanaki kaɗan ne kawai suka rage a yi Idin Ƙetarewa. Mutane da yawa da suka zo Urushalima don su yi bauta suna haikali cike da farin ciki. Menene zai faru sa’ad da Yesu ya isa wurin? Marubutan Linjila guda uku, Matta, Markus, da Luka, duka sun ba da shaida cewa lokaci na biyu ke nan da Yesu ya kori waɗanda suke saye da sayarwa a wajen. Ya birkitar da teburan ’yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai. (Mat. 21:12; Mar. 11:15; Luk 19:45) Himmar Yesu ba ta ragu ba tun lokacin da ya yi hakan shekaru uku da suka shige.—Yoh. 2:13-17.

2, 3. Ta yaya muka sani cewa himmar Yesu ba ta tsaya a tsabtace haikali kawai ba?

2 Labarin Matta ya nuna cewa a wannan lokacin Yesu bai nuna himmarsa kawai ta wajen tsabtace haikalin ba. Ya warkar da makafi da guragu da suka zo wajensa. (Mat. 21:14) Labarin Luka ya ambata wasu ayyuka da Yesu ya cim ma. “[Yesu] yana koyaswa kowace rana cikin haikali.” (Luk 19:47; 20:1) A bayyane yake cewa Yesu ya nuna himma a hidimarsa.

3 Daga baya, manzo Bulus ya rubuta wa Titus kuma ya ba da bayani cewa Yesu “ya bada kansa dominmu, domin shi fanshe mu daga dukan zunubi, shi tsarkake wa kansa jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.” (Tit. 2:14) A waɗanne hanyoyi ne a yau za mu zama “masu-himman nagargarun ayyuka”? Kuma yaya misalan nagargarun sarakunan Yahuda za su ƙarfafa mu?

Himma ga Wa’azi da Koyarwa

4, 5. A waɗanne hanyoyi ne sarakuna huɗu na Yahuda suka kasance da himma don nagargarun ayyuka?

4 Asa, Jehoshaphat, Hezekiah da Josiah duka sun cim ma burin kawar da bautar gumaka a Yahuda. Asa “ya kawas da baƙin bagadai, da masujadai, ya rurrushe umudai, ya sassara Asherim.” (2 Laba. 14:3) Domin himmarsa don bautar Jehobah, Jehoshaphat ya “kawasda masujadai da Asherim daga cikin Yahuda.”—2 Laba. 17:6; 19:3.a

5 Bayan biki mai tsarki na Idin Ƙetarewa da Hezekiah ya tsara a Urushalima, “dukan Isra’ila da ke nan suka fita zuwa biranen Yahuda, suka parpashe umudai, suka sassare Asherim suka rurrushe masujadai, da bagadai cikin dukan Yahuda da Banyamin, cikin Ifraimu da Manasseh kuma, har suka lalatadda su duka. Sa’annan dukan ’ya’yan Isra’ila suka koma cikin biranensu, kowa zuwa nasa wurin.” (2 Laba. 31:1) Josiah ya zama sarki sa’ad da yake ɗan shekara takwas. Nassosi ya ce: “A cikin shekara ta takwas ta mulkinsa, tun yana da sauran ƙuruciya, ya soma neman Allah na ubansa Dauda: a cikin shekara ta goma sha biyu kuma ya soma kawarda masujjadai, da Asherim, da sassaƙaƙun sifofi, da gumaka na zubi daga cikin Yahuda da Urushalima, ya tsabtata su hakanan.” (2 Laba. 34:3) Saboda haka, duka waɗannan sarakuna sun yi himma don nagargarun ayyuka.

6. Me ya sa za a gwada hidimarmu da aikin da sarakunan Yahudawa masu aminci suka yi?

6 A yau mu ma muna kamfen na taimaka wa mutane su samu ’yanci daga koyarwar addinin ƙarya, har da bauta wa gumaka. Hidimarmu ta gida-gida tana taimakonmu mu sadu da dukan ire-iren mutane. (1 Tim. 2:4) Wata yarinya ’yar Asiya ta tuna yadda mamarta take yin addu’o’i a gaban siffofi masu yawa a gidansu. Ta wajen yin tunani cewa ba siffofi ba ne suke wakiltar Allah na gaskiya ba, sau da yawa yarinyar ta yi addu’a don ta san Allah na gaskiya. Sa’ad da ta buɗe ƙofarta da aka ƙwanƙwasa, sai ta ga Shaidu biyu da suke a shirye su taimake ta ta san suna mai girma na Allah, Jehobah. Ta yi farin ciki da ta koyi gaskiya game da gumaka! Yanzu tana nuna himma sosai ta wajen fita hidimar fage, tana taimaka wa mutane su san Jehobah.—Zab. 83:18; 115:4-8; 1 Yoh. 5:21.

7. Menene za mu iya yi don mu yi koyi da malaman da suka zagaye dukan al’ummar a zamanin Jehoshaphat?

7 Sa’ad da muke hidima ta gida-gida, muna wa’azi sosai a dukan yankinmu kuwa? A shekara ta uku na sarautarsa, Jehoshaphat ya aika a kira masa hakimai biyar, Lawiyawa tara, da firistoci guda biyu. Ya sa su koya wa mutanen dokokin Jehobah a dukan biranen. Sun yi wannan aikin a dukan ƙasar da kyau har mutane da ke al’ummai na kusa da su suka soma jin tsoron Jehobah. (Karanta 2 Labarbaru 17:9, 10.) Ta wajen yin ziyara a gidaje a lokaci da kwanaki dabam-dabam, za mu iya yin magana da mutane da yawa da ke cikin gidan.

8. Yaya za mu iya faɗaɗa wa’azinmu?

8 Bayin Allah da yawa a zamani suna shirye su bar gidajensu kuma su ƙaura zuwa inda ake bukatar Shaidu masu himma sosai. Za ka iya yin hakan? Wasu cikinmu da ba za su iya ƙaura ba suna iya yin wa’azi ga mutanen da suke zama a yankinmu amma suna wani yare. Domin mutane daga ƙasashe dabam-dabam da yake saduwa da su a yankinsu, Ron ɗan shekara tamanin da ɗaya ya koyi gaisuwa a harsuna talatin da biyu. Ba da daɗewa ba ya sadu da ma’aurata daga Afirka a kan titi kuma ya gai da su da yarensu, Yarbanci. Suka tambayi Ron ko ya taɓa zama a Afirka. Sa’ad da ya ce a’a, suka tambaye shi yadda ya san yarensu. Saboda haka, ya samu daman yi musu wa’azi da kyau. Suka karɓi mujallu kuma suka ba shi adireshinsu, sai ya aika wa ikilisiyar da ke yankinsu don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ma’auratan.

9. Me ya sa karanta Littafi Mai Tsarki a hidimarmu yake da muhimmanci? Ka ba da misali.

9 Malaman da suka zagaye duka al’ummar bisa umurnin da Jehoshaphat ya ba su, suna da “litafin shari’ar Ubangiji” tare da su. A dukan duniya muna ƙoƙarin mu koya wa mutane daga Littafi Mai Tsarki, tun da yake Kalmar Allah ce. Muna ƙoƙari sosai mu nuna wa mutane ainihin kalmomin Littafi Mai Tsarki a hidimarmu. Wata ta bayyana wa Linda, Mashaidiya, cewa jikin mijinta ya shanye kuma yana bukatar ta kula da shi. Ta faɗa da baƙin ciki: “Ban san abin da na yi wa Allah ba da ya ƙyale wannan ya same ni.” Linda ta ce: “Bari na tabbatar miki da wani abu.” Sai ta karanta mata kalmomin da ke Yaƙub 1:13 kuma ta daɗa: “Dukan wahala da mu da waɗanda muke ƙauna suke sha ba horo ba ne daga wajen Allah.” Sai matar ta rungumi Linda don ta nuna godiya ga abin da ta faɗa mata. Linda ta ce: “Na ƙarfafa ta ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki. A wani lokaci wanda muke tattaunawa da shi bai taɓa jin ayoyin da muka karanta daga Littafi Mai Tsarki ba.” Wannan tattaunawar ta sa aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da wannan matar.

Matasa da Suke Hidima da Himma

10. Ta yaya Josiah ya zama misali mai kyau ga matasa Kirista a yau?

10 Idan muka sake duba misalin Josiah, mun lura cewa ya yi bauta ta gaskiya sa’ad da yake matashi kuma yana ɗan shekara ashirin sa’ad da ya soma aikin kawar da bautar gumaka. (Karanta 2 Labarbaru 34:1-3.) Matasa da yawa a yau suna nuna irin wannan himmar a hidimarsu ta Mulki.

11-13. Waɗanne darussa za mu iya koya daga matasa na zamani waɗanda suka bauta wa Jehobah da himma?

11 Hannah wadda take da zama a Ingila, tana ’yar shekara goma sha uku kuma tana karanta Faransanci a makaranta sa’ad da ta ji cewa an kafa rukuni da ake Faransanci a wani gari da ke kusa. Babanta ya yarda ya riƙa bin ta zuwa taron da ake yi a wajen. Yanzu, shekarun Hannah goma sha takwas kuma tana wa’azi da Faransanci a matsayin majagaba na kullum. Za ka iya koyon wani yare don ka taimaki mutane su koyi game da Jehobah?

12 Rachel ta ji daɗin kallon bidiyon nan Pursue Goals That Honor God. Da take magana game da yadda take tunani sa’ad da ta soma bauta wa Jehobah a shekara ta 1995, ta ce: “Na ɗauka ina bin gaskiya yadda ya dace.” Sai ta daɗa: “Bayan na kalli wannan wasan kwaikwayon, na fahimci cewa shekaru da yawa da suka wuce ina dai bin gaskiya ne kawai. Ya kamata na nuna himma don gaskiya kuma na yi tunani da kuma ƙoƙari sosai a hidimata da kuma nazari na kaina.” Yanzu Rachel ta ga cewa tana bauta wa Jehobah da ƙarin himma. Menene sakamakon hakan? “Dangantakata da Jehobah ta ƙaru sosai. Addu’ata ta fi ma’ana, ina nazari sosai kuma ya fi gamsarwa, kuma labaran Littafi Mai Tsarki sun zama da gaske a gare ni. Saboda haka, ina more hidimar sosai kuma ina samu gamsuwa ta gaske yayin da na ga kalmomin Jehobah suna ƙarfafa mutane.”

13 Luke wani matashi ne da wani bidiyo ya ƙarfafa, wato, bidiyon nan Young People Ask—What Will I Do With My Life? Bayan da ya kalli wannan bidiyon, Luke ya rubuta: “Na yi tunanin abin da nake yi da rayuwata.” Ya ce: “A dā an matsa mini na biɗi arziki ta wajen zuwa babban makaranta tukuna kafin na mai da hankali ga makasudai na ruhaniya. Irin wannan matsi ba ya taimaka wa a sami ci gaba na ruhaniya; maimakon haka, yana raunana mutum.” Matasa ’yan’uwa maza da mata, me ya sa ba za ku yi amfani da abin da kuka koya a makaranta wajen faɗaɗa hidimarku yadda Hannah ta yi ba? Kuma me ya sa ba za ku yi koyi da misalin Rachel ta wajen biɗan makasudai da ke ɗaukaka Allah da gaske ba? Ku bi misalin Luke don ku guji haɗarurrukan da suka zama tarko ga matasa da yawa.

Ka Yi Biyayya ga Gargaɗi da Himma

14. Yaya Jehobah yake son a bauta masa, kuma me ya sa hakan yake da wuya a yau?

14 Mutanen Jehobah suna bukatar su kasance da tsabta idan suna son ya amince da bautarsu. Ishaya ya yi gargaɗi: “Ku tashi, ku tashi, ku fita daga can, kada ku taɓa wani abu mai-ƙazamta; ku fita daga cikin tsakiyatta; ku tsarkaka, ku masu-ɗaukan kayan Ubangiji.” (Isha. 52:11) Shekaru da yawa kafin Ishaya ya rubuta waɗannan kalmomin, nagarin Sarki Asa ya tsara aikin kawar da lalata a cikin Yahuda. (Karanta 1 Sarakuna 15:11-13.) Kuma ƙarnuka daga baya, manzo Bulus ya gaya wa Titus cewa Yesu ya ba da kansa don ya tsarkake mabiyansa ya sa su “zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.” (Tit. 2:14) A al’umma yau da ke cike da lalata, ba shi da sauƙi musamman ga matasa su kasance da tsabtar ɗabi’a. Alal misali, dole ne dukan bayin Allah, matasa da tsofaffi su ƙoƙarta su guji gurɓata kansu da hotunan batsa da ke ta da sha’awar jima’i da ake nunawa a kan allon talla, a talabijin, a fim, kuma musamman a cikin Intane.

15. Menene zai iya taimaka mana mu ƙi abin da ba shi da kyau?

15 Kasancewa da himma wajen yin biyayya ga gargaɗin Allah zai iya taimaka mana mu koyi ƙin mugunta. (Zab. 97:10; Rom. 12:9) Muna bukatar mu ƙi kallon hotunan batsa idan muna son mu “guje wa mugun rinjayarsa mai kama da ƙarfin maganaɗisu,” in ji wani Kirista. Idan mutum yana son ya raba maganaɗisu, dole ne ya nemi abu mafi ƙarfi da zai iya raba maganaɗisun. Hakanan ma, muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu guji batsa. Amma fahimtar yadda batsa za ta yi mana lahani zai taimake mu mu ƙi ta. Wani ɗan’uwa ya yi ƙoƙari sosai don ya daina zuwa dandalin hotunan batsa a Intane. Ya kai kwamfutarsa zuwa inda iyalinsa za su riƙa gani. Ban da haka, ya ƙara ƙudurta cewa zai tsabtace kansa kuma ya kasance da himma don nagargarun ayyuka. Ya ɗauki wani mataki. Domin yana bukatan ya yi amfani da Intane don sana’arsa, ya tsai da shawara cewa zai yi amfani da ita ce kaɗai sa’ad da matarsa take tare da shi.

Amfanin Halin Kirki

16, 17. Yaya halinmu mai kyau zai iya shafan waɗanda suke kallonmu? Ka ba da misali.

16 Matasa maza da mata da suke bauta wa Jehobah suna nuna halin kirki, kuma hakan yana burge masu kallonsu! (Karanta 1 Bitrus 2:12.) Wani baƙo da ya ziyarci Bethel da ke Landan ya canja ra’ayinsa game da Shaidun Jehobah bayan ya yi yini guda yana gyara na’urar da ake buga littattafai da ita. Matarsa, da take nazarin Littafi Mai Tsarki da wata Mashaidiya, ta lura cewa mijinta ya canja halinsa. A dā ba ya son Shaidu su zo gidansa. Amma da ya dawo daga Bethel bayan yin wannan aikin, sai ya soma magana mai kyau game da yadda aka nuna masa halin kirki. Ya ce babu wanda ya yi amfani da baƙar magana. Kowa yana da haƙuri, kuma yanayin na salama ne. Abin da ya fi burge shi, shi ne cewa ba a biyan matasa da suke aiki tuƙuru, suna ba da lokacinsu da kuzari don a buga littattafan da za a yi amfani da su wajen yin wa’azin bishara.

17 Hakanan ma, ’yan’uwa maza da mata da suke aiki don su kula da iyalansu suna yin kasuwancinsu da zuciya ɗaya. (Kol. 3:23, 24) Hakan na sa su kyautata aikinsu, domin shugabannin aiki suna daraja halinsu na aiki tuƙuru kuma ba sa son su daina yi masu aiki.

18. Ta yaya za mu kasance “masu-himman nagargarun ayyuka”?

18 Dogara ga Jehobah, yin biyayya ga umurninsa, da kuma kula da wuraren taronmu suna cikin hanyoyin da muke nuna himma don gidan Jehobah. Ƙari ga haka, ya kamata mu sa hannu sosai a aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. Ko mu matasa ne ko tsofaffi, ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu kasance da mizanan tsabta game da bautarmu, za mu sami sakamako mai yawa. Kuma za a ci gaba da sanin cewa mu mutane ne “masu-himman nagargarun ayyuka.”—Tit. 2:14.

[Hasiya]

a Asa wataƙila ya kawar da masujadai da ke tattare da bauta wa allolin ƙarya amma ba waɗanda suke inda mutane suke bauta wa Jehobah ba. Ko kuwa wataƙila an sake gina masujadai a kusan ƙarshen sarautar Asa kuma ɗansa Jehoshaphat ya cire waɗannan masujadai.—1 Sar. 15:14; 2 Laba. 15:17.

Daga misalan da ke Littafi Mai Tsarki da na zamani, menene ka koya game dab

• yadda za ka nuna himma ta wajen wa’azi da koyarwa?

• yadda matasa Kiristoci za su iya zama “masu-himman nagargarun ayyuka”?

• yadda za ka guji munanan halaye?

[Hotunan da ke shafi na 13]

Kana amfani da Littafi Mai Tsarki a kai a kai a hidimarka?

[Hotunan da ke shafi na 15]

Koyon wani yare sa’ad da kake makaranta zai iya taimaka maka ka faɗaɗa hidimarka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba