Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/15 pp. 8-12
  • Kana Da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI KOYI DA HIMMAR JEHOBAH DA YESU
  • HALIN SADAUKARWA YANA ƊAUKAKA JEHOBAH
  • HALIN KIRKI YANA SA MUTANE SU BAUTA WA ALLAH
  • KA RIƘA GIRMAMA ALLAH DA HALAYENKA
  • Ku Zama “Masu-himman Nagargarun Ayyuka”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Kasance Da Himma Don Bauta Ta Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo Kamar Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Kana Bin Kristi Sosai Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/15 pp. 8-12

Kana Da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?

“Yesu Kristi . . . ya bada kansa dominmu, domin . . . shi tsarkake wa kansa jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.”—TIT. 2:13, 14.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa kake ganin daraja ce ka kasance da himmar yin nagargarun ayyuka?

  • Ta yaya littafin Daniyel 2:41-45 ya nuna muhimmancin kasancewa da himma a hidima?

  • Ka bayyana yadda halin kirki yake sa mutane su soma bauta wa Jehobah Allah.

1, 2. Wace ɗaukaka ce Shaidun Jehobah kaɗai suke da shi, kuma yaya kake ji game da hakan?

MUTANE da yawa suna ganin ɗaukaka ce sa’ad da aka ba su lada don sun cim ma wani abu na musamman. Alal misali, wasu sun samu Kyautar Nobel don sun yi ƙwazo wajen sulhunta ƙasashe biyu masu gāba da juna. Mutum zai fi samun ɗaukaka idan Allah ne ya aike shi a matsayin jakada ko kuma wakili don ya taimaka wa mutane su ƙulla dangantaka da Mahaliccinsu!

2 A matsayin Shaidun Jehobah, mu kaɗai ne muke da wannan gatan. Allah da kuma Kristi sun umurce mu mu roƙi mutane su “sulhuntu ga Allah.” (2 Kor. 5:20) Jehobah yana amfani da mu don ya sa mutane su soma bauta masa. Ta hakan ne aka taimaka wa mutane miliyoyi da ke cikin ƙasashe sama da 235 su ƙulla dangantaka da Allah, kuma su kasance da begen yin rayuwa har abada. (Tit. 2:11) Muna nuna ƙwazo sosai sa’ad da muke gayyatar duk “wanda yake so, . . . ya ɗiba ruwa na rai kyauta.” (R. Yoh. 22:17) Domin muna ɗaukan wannan aiki da tamani kuma muna yin sa da ƙwazo, ya dace a kira mu mutane “masu-himman nagargarun ayyuka.” (Tit. 2:14) Yanzu, bari mu yi la’akari da yadda himmarmu don nagargarun ayyuka za ta taimaka mana mu sa mutane su soma bauta wa Jehobah. Hanya ɗaya da muke yin hakan, ita ce ta aikinmu na wa’azi.

KA YI KOYI DA HIMMAR JEHOBAH DA YESU

3. Mece ce “himmar Ubangiji” ta tabbatar mana?

3 Game da abin da sarautar Ɗan Allah za ta cim ma, littafin Ishaya 9:7 ya ce: “Himmar Ubangiji mai-runduna za ya aikata wannan.” Waɗannan kalmomin sun nanata cewa Ubanmu na sama yana son ’yan Adam su samu ceto. Misalin kasancewa da himma da Jehobah ya kafa mana, ya nuna sarai cewa ya kamata mu tallafa wa aikin da Allah ya ba mu a matsayin masu shelar Mulki da dukan zuciyarmu da kuma ƙwazo. Kasancewa da himma wajen taimaka wa mutane su san Allah ya nuna cewa muna yin koyi da Jehobah. Da yake mu abokan aiki na Allah ne, shin mun ƙudura niyyar mu saka hannu sosai wajen yaɗa bishara iyakar yadda yanayinmu ya ƙyale mu mu yi?—1 Kor. 3:9.

4. Ta yaya Yesu ya kafa misalin kasancewa da himma a hidima?

4 Ka yi la’akari kuma da himmar Yesu. Ya kafa mana misali na nacewa a hidima. Duk da cewa ya fuskanci hamayya mai tsanani, ya yi wa’azi da himma har ƙarshen rayuwarsa a duniya. (Yoh. 18:36, 37) Sa’ad da Yesu ya kusan mutuwa, ya daɗa ƙwazo wajen taimaka wa mutane su san Jehobah.

5. Ta yaya Yesu ya aikata daidai da kwatancinsa na itacen ɓaure?

5 Alal misali, a shekara ta 32 a zamaninmu, Yesu ya ba da kwatancin mutum wanda yake da itacen ɓaure a garkarsa da bai yi ’ya’ya ba har shekara uku. Sa’ad da aka gaya wa mai kula da garkar ya yanke itacen, sai ya ce a ɗan ba shi lokaci ya zuba wa itacen taki. (Karanta Luka 13:6-9.) Mutane kaɗan ne suka zama almajiran Yesu a sakamakon wa’azin da ya yi. Amma, kamar yadda aka nuna a wannan kwatanci na mai kula da garka, Yesu ya yi amfani da wata shida da ya rage don ya daɗa ƙwazo a aikinsa na wa’azi a ƙasashen Yahudiya da Feriya. ’Yan kwanaki kafin mutuwarsa, Yesu ya yi kuka don al’ummarsa waɗanda suke da “nauyin ji.”—Mat. 13:15; Luk 19:41.

6. Me ya sa za mu daɗa ƙwazo a hidimarmu?

6 Yana da muhimmanci sosai mu daɗa ƙwazo a yin wa’azi, tun da yake muna cikin kwanaki na ƙarshe. (Karanta Daniyel 2:41-45.) Babu shakka, zama Shaidun Jehobah babban gata ne! Mu kaɗai ne muke gaya wa mutane ainihin wanda zai magance matsalolin ’yan Adam. A kwanan nan, wata marubuciyar jarida ta ce ba za a iya sanin amsar wannan tambayar da ke gaba, “Me ya sa mutanen kirki suke fuskantar matsaloli?” Hakki ne da kuma gata a gare mu mu gaya wa mutane da suke son su saurara amsoshi da Littafi Mai Tsarki ya ba da a kan irin waɗannan tambayoyin. Muna da dalilin “huruwa a cikin ruhu” sa’ad da muke yin aikin da Allah ya ba mu. (Rom. 12:11) Da taimakon Allah, yin wa’azi da himma zai sa mutane su san Jehobah kuma su ƙaunace shi.

HALIN SADAUKARWA YANA ƊAUKAKA JEHOBAH

7, 8. Ta yaya halin sadaukarwa yake ɗaukaka Jehobah?

7 Kamar manzo Bulus, mu ma muna iya yin ‘rashin barci’ da kuma ‘rashin abinci’ don hidimarmu. (2 Kor. 6:5, Littafi Mai Tsarki) Wannan kalami ya kwatanta halin sadaukarwa kuma ya tuna mana da majagaba da suke saka hidimarsu a kan gaba yayin da suke biyan bukatun kansu. Ka yi la’akari kuma da masu wa’azi a ƙasashen waje da ƙwazo da suka ‘tsiyaye kansu’ kamar hadaya don su yi hidima a wasu ƙasashe. (Filib. 2:17) Dattawa masu aiki tuƙuru da ba sa cin abinci kuma ba sa barci a wasu lokatai don su kula da tumakin Jehobah kuma fa? Da akwai tsofaffi da marasa lafiya da suke iya ƙoƙarinsu don su halarci taro kuma su fita yin wa’azi. Muna farin ciki sosai sa’ad da muka tuna da waɗannan bayin Allah masu sadaukarwa. Irin wannan ƙoƙarin yana shafan yadda mutane suke ɗaukan hidimarmu.

8 A cikin wata wasiƙa da aka rubuta zuwa ga kamfanin jaridar Boston Target da ake wallafawa a ƙasar Ingila, wani da ba Mashaidi ba ya ce: “Mutane ba sa amincewa da addini kuma . . . Mene ne aikin waɗannan limaman coci tun da ba sa fita yi wa mutane wa’azi kamar yadda Kristi ya yi? Shaidun Jehobah ne kaɗai suke kula da mutane, da yake su ne suke zuwa wurin mutane kuma suke wa’azi da gaske.” A cikin wannan duniya da ke cike da son kai, halinmu na sadaukarwa yana ɗaukaka Jehobah Allah sosai.—Rom. 12:1.

9. Mene ne zai motsa mu mu kasance da himmar yin nagargarun ayyuka a hidimarmu?

9 Amma, mene ne za mu iya yi idan kamar muna rashin himma a hidima? Yin tunani a kan abin da Jehobah yake cim ma ta hanyar aikin wa’azi zai taimaka mana. (Karanta Romawa 10:13-15.) Mutane za su samu ceto ta wajen bauta wa Jehobah cikin bangaskiya, amma ba za su yi hakan ba idan ba mu yi musu wa’azi ba. Ya kamata hakan ya motsa mu mu kasance da himma don nagargarun ayyuka, kuma mu yi shelar bisharar Mulki da ƙwazo.

HALIN KIRKI YANA SA MUTANE SU BAUTA WA ALLAH

10. Me ya sa za a ce halinmu na kirki yana sa mutane su soma bauta wa Jehobah?

10 Ko da yake kasancewa da himma yana da muhimmanci a hidima, yin hakan kaɗai ba zai sa mutane su soma bauta wa Allah ba. Yana da muhimmanci kuma mu kasance da halin kirki, da yake sashe ne na biyu na nagargarun ayyuka da za su sa mutane su soma bauta wa Allah. Bulus ya nuna cewa halinmu yana da muhimmanci sa’ad da ya ce: “Kada mu bada dalilin tuntuɓe cikin komi, domin kada a yi zargin hidimarmu.” (2 Kor. 6:3) Sahihiyar magana da halinmu na kirki suna ɗaukaka koyarwar Allah, kuma su sa mutane su soma bauta wa Jehobah. (Tit. 2:10) Muna yawan jin labarin mai kyau daga bakin mutanen kirki da suka lura da halinmu na Kirista.

11. Me ya sa ya kamata mu yi tunani game da sakamakon halinmu?

11 Kamar yadda mutane suke lura da halinmu na kirki, suna kuma lura idan halayenmu ba su da kyau. Saboda haka, ko idan muna wajen aiki, ko a gida ko kuma a makaranta, ya kamata mu guji ba mutane dalilin kushe wa hidimarmu da kuma halinmu. Idan muka yi zunubi da gangan, sakamakonsa zai yi muni sosai. (Ibran. 10:26, 27) Ya kamata hakan ya motsa mu mu yi tunani a kan ayyukanmu da kuma salon rayuwarmu. Yayin da ɗabi’a na wannan duniya take taɓarɓarewa, mutanen kirki za su daɗa ganin bambanci “tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Mal. 3:18) Hakika, halinmu na kirki yana da muhimmanci wajen sa mutane su sulhunta da Allah.

12-14. Ta yaya jimre wa gwaji da muke yi yake shafan yadda wasu suke ɗaukan hidimarmu? Ka ba da misali.

12 Sa’ad da Bulus ya rubuta wa Korintiyawa wasiƙa, ya ambata cewa an tsananta masa, ya sha wahala, an yi masa dūka kuma an saka shi a fursuna. (Karanta 2 Korintiyawa 6:4, 5.) Sa’ad da muka fuskanci gwaji ga bangaskiyarmu, mutane da suka lura da yadda muka jimre suna iya soma bauta wa Jehobah. Alal misali, a shekarun da suka shige, an yi ƙoƙari a kawar da Shaidun Jehobah a wani yanki a ƙasar Angola. A wannan yankin, an kewaye wani ɗan’uwa da matarsa da mutane 30 masu son saƙonmu sa’ad da suke taro. Sai mutanen yankin suka taru suna kallon yadda ’yan adawa suke wa waɗannan ’yan’uwa bulala har jikinsu yana jini. Har mata da yara ma sun sha wannan zaluncin. Sun yi hakan don su sa mutane su ji tsoron kuma su daina sauraron Shaidun Jehobah. Amma, bayan wannan wulakancin, mutane da yawa daga yankin sun je wajen Shaidu don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su! Sai aka ci gaba da wa’azin Mulki, kuma hakan ya sa sun samu ƙaruwa da kuma albarka.

13 Wannan misalin ya nuna cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana kawo sakamako mai kyau. Mutane da yawa sun sulhunta da Allah don gaba gaɗin da Bitrus da wasu manzanni suka nuna. (A. M. 5:17-29) Hakan ya nuna cewa abokan makarantarmu da abokan aiki ko kuma danginmu suna iya soma son saƙonmu sa’ad da suka ga cewa mun dage ga yin abu mai kyau.

14 A kowane lokaci, ana tsananta wa wasu cikin ’yan’uwanmu. Alal misali, a ƙasar Armenia, ’yan’uwa kusan 40 ne suke cikin fursuna don sun yi ba-ruwanmu da yaƙi da kuma siyasa, kuma a watanni nan gaba za a saka da yawa a cikin fursuna. An saka bayin Jehobah guda 55 a cikin fursuna a ƙasar Eritrea, wasu cikinsu ’yan sama da shekara 60 ne. An saka Shaidu 700 a fursuna a ƙasar Koriya ta Kudu don imaninsu. Wannan tsananin ya ci gaba a ƙasar na shekara 60 yanzu. Addu’armu ita ce, amincin ’yan’uwanmu da ake tsananta musu a ƙasashe dabam-dabam ya sa a ɗaukaka Allah, kuma masu son adalci su soma bauta wa Jehobah.—Zab. 76:8-10.

15. Ka ba da misalin da ya nuna cewa yin gaskiya zai sa mutane su soma bauta wa Allah.

15 Yin gaskiya yana iya sa mutane su soma bauta wa Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 6:4, 7.) Alal misali, ka yi la’akari da wannan labarin: “Wata ’yar’uwa tana biyan kuɗin mota ta na’ura a cikin bas, sai wata ta gaya mata cewa ba ta bukatar biyan kuɗi tun da yake wurin da za su ba shi da nisa. ’Yar’uwar ta bayyana mata cewa ya dace ta biya kuɗi ko da ma ba nisa. Bayan da matar ta sauka, sai direban ya juya ya tambayi ’yar’uwar, “Ke Mashaidiya ce?” ’Yar’uwar ta amsa, E. “Me ya sa ka tambaya?” Sai direban ya ce, “Na ji kuna tattaunawa a kan biyan kuɗin mota, kuma na san cewa Shaidun Jehobah ne kawai suke yin hakan kuma suna yin gaskiya.” Bayan ’yan watanni, wani mutum ya je ya sami ’yar’uwar a taro kuma ya ce, “Kin waye ni? Ni ne direban bas da ya yi miki magana game da biyan kuɗin mota. Halinki ne ya sa na tsai da shawarar soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah.” Halinmu na yin gaskiya yana sa mu zama masu hidima da aka amince da su.

KA RIƘA GIRMAMA ALLAH DA HALAYENKA

16. Me ya sa halaye kamar su tsawon jimrewa da ƙauna da alheri ke sa mutane su soma bauta wa Allah? Ka ba da misali.

16 Muna sa mutane su soma bauta wa Jehobah sa’ad da muka nuna halaye masu kyau kamar su tsawon jimrewa da ƙauna da kuma alheri. Wasu da suka lura da mu, suna iya so su koya game da Jehobah da nufe-nufensa da kuma mutanensa. Halin Kiristoci na gaskiya ya yi dabam da ibada na munafunci da mutane suke yi. Wasu shugabannin addinai sun yi arziki ta yi wa mabiyansu zamba, kuma sun gina manyan gidaje sun sayi motoci masu tsada da kuɗin, har ma wani yana da gidan kare mai iyakwandishan. Hakika, mutane da yawa da suke da’awa su mabiyan Kristi ne ba su da niyyar ‘bayarwa kyauta.’ (Mat. 10:8) Maimakon haka, kamar firistoci na Isra’ila ta dā masu taurin kai, “suna koyarwa don neman riba,” kuma yawancin abubuwa da suke koyarwa ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. (Mi. 3:11, LMT) Irin wannan hali na munafunci ba ya sulhunta kowa da Allah.

17, 18. (a) Ta yaya muke ɗaukaka Jehobah sa’ad da muka nuna halayensa a rayuwarmu? (b) Mene ne yake motsa ka ka nace a yin nagargarun ayyuka?

17 A wani ɓangare kuma, mutane sun soma bauta wa Allah don koyarwar gaskiya da kuma alheri da aka nuna wa maƙwabta. Alal misali, sa’ad da wani majagaba yake wa’azi gida gida, wata tsohuwa gwauruwa ta sallame shi nan da nan. Ta ce sa’ad da ya ƙwanƙwasa kofa, tana kan tsani a cikin kicin tana canja ƙwan lantarki. Sai ya ce, “Yin hakan ke kaɗai haɗari ne.” Ɗan’uwan ya canja mata ƙwan kuma ya yi tafiyarsa. Abin da ɗan’uwan ya yi ya burge ɗanta sosai sa’ad da ya samu labarin, sai ya yi ƙoƙari ya nemi ɗan’uwan don ya yi masa godiya. Bayan haka, ɗanta ya yarda a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

18 Me ya sa ka ƙudura niyyar ka ci gaba da yin nagargarun ayyuka? Wataƙila domin ka san cewa sa’ad da muka kasance da himma a hidimarmu kuma muka yi abubuwa da suka jitu da nufin Allah, muna ɗaukaka Jehobah kuma muna iya taimaka wa mutane su samu ceto. (Karanta 1 Korintiyawa 10:31-33.) Muna kasancewa da himmar yin nagargarun ayyuka sa’ad da muke wa’azin bishara da kuma aikata yadda Allah yake so domin muna ƙaunarsa da kuma mutane. (Mat. 22:37-39) Idan muna da himma don yin nagargarun ayyuka, za mu yi farin ciki sosai kuma mu samu gamsuwa yanzu. Bugu da ƙari, muna jiran ranar da dukan ’yan Adam za su nuna himma don bauta ta gaskiya, kuma hakan zai ɗaukaka Mahaliccinmu Jehobah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba